Chapter 26 Reading JIDDA by Maman Maama HN Novels

JIDDA by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   26 / 101

75K to 78K   out of 300.2K words

abinda zai faru tsakani na da kai kenan da ranar nan ban fito daga hostel na gaishe da
yan gidan su Mufida ba"
"Da nasan sakayyar da zaka yi min kenan da ban amshi fake soyayyar ka ba"



"Da ana chanja kaddara Umar da banyi kawance da kanwarka ba ballantana har in hadu da kai"



Ya sake kokarin magana. "Allahumma ajirni fi musibati. Jidda me nayi miki mai zafi haka? Wacce Zuwaira
kike magana akai ne? Bayan ni na gaya miki bansan wata Zuwaira ba ballantana har tace miki wai daga
gidanta nake yanzu nayi bacci a.... common Jidda......I thought you trusted me. Dan me zaki dauki words
of a stranger akan na mijin ki?"



Nace "trust? Of course I trusted you tun daga ranar dana ganka har zuwa ranar da ka tarwatsa trust dina
da bango, ranar da ka yi min karya kace baka san ta ba bayan kuma ka santa. Har ka rants min kace kai
wallahi baka santa ba"



Yace "to waye yace miki na santa? Bayan nima har yanzu neman ta nake in hada ta da police....."



Na daga masa hannu cikin tsawa nace "stop lying damn it. Just stop lying. I saw the paper okay. Paper
din da kace min ka bawa police I saw it a aljihun ka bayan ka gaya min ka bawa police, sai daga baya ka
dauke ta ka fita da ita daga gidan nan"



"And I saw you on Facebook as her friend. And then she told me everything da yake tsakanin ku da kuma
everything daka gaya mata akaina"



Naga ya motsa bakinsa amma sai ya kasa cewa komai.



Na koma na tsaya a gabansa nace "daga gidan ta kake, yes or no?"



Yayi saurin girgiza kai "wallahi Jidda ba daga gidan ta nake ba. Yes I know her and I lied to you about that
amma wallahi abinda ta gaya miki na cewa daga gidan ta nake kuma wai..... Jidda wallahi karya take yi"
na sake taku bawa ina girgiza kaina "you just won't stop lying will you?" Sai na juya na tafi hanyar
corridor ina cewa



"Tunda ba zaka fada min gaskiya ba sai kaje ka fada wa Abba, dan gidan mu zan tafi kuma sai na gaya
masa kaf abinda ya faru da dukkan abinda tace min"



Taku biyu yayi ya kamo ni tun kafin in shiga corridor din "innalillahi Jidda me kike cewa? Ki tsaya muyi
magana ni da ke ki yardada abinda nake gaya miki. Karya take yi min, sharri take yi min, so take ta haɗa
ni da ke?"



Na juyo ina kallon sa, in akwai abinda yafi karshen tashin hankali to anan gurin yake. Nace "it seems like
kowa yanzu a duniya sharri yake yi maka. Kowa yanzu kokari yake yi ya hada ka dani. While kai kuma
cigaba kake yi da yi min karya. Just admit cewa daga gidan ta kake"



Ya daga kafada "ta yaya zanyi admitting laifin da nasan ban aikata ba? Ni ba daga gidanta nake ba, ni ban
ma san a inda gidan ta yake ba" naji raina yana cigaba da baci, zuciya ta ta a kara kuna nace "sanda na
kira ka dazu kana ina? And don't tell me kana surgery"



I saw him struggling with his inner self, "ina tare da Mahmud abokina" na dafe kaina da naji yana neman
sara wa tare da rintse ido na dana fara ganin duhu da su, ya samu damar rike ni. "Wallahi Jidda da gaske
nake. In baki yarda ba ga wayata ki kira shi da kanki ki tambayeshi zai fada miki haka. Na taso daga aiki
na gaji sosai ina jin bacci ba zan iya driving ba shine na tsaya a gurinsa nayi bacci, ina farkawa na taho
nan, sai da na shigo gidan nan ma sannan naga missed calls din ki"



Na saki goshin da na rike ina kallon sa nace "shi Mahmud din shine ya dauki wayarka kenan yaga sanda
na kira ka kuma ya kira ta ya gaya mata cewa na kira ka at that exact time, sannan kuma ya gaya mata
sunan da kayi saving number ta dashi? Kuma ya tura mata number dina cikin wayarta?"



Ya tsaya shiru yana kallona, and i guessed he was trying to understand magana ta, sai na saukaka masa
na bashi amsa "she sent me a text message and called me Baby Dove. Now, explain to me ta yaya ta
samu number ta kuma ta san cewa na kira ka sannan kuma ta yaya ta san wannan sunan idan har ba kwa
tare?"
Ya tsaya shiru kamar mutum mutumi ba tareda ya iya furta koda kalma daya ba. Na sake shi nace "now
finally mun fahimci juna cewa daga gurinta kake, abinda ya rage shine kayi admitting dukkan abubuwan
da ta fada min. Daga karshe ni kuma sai in dauki shawarar data bani in san inda dare yayi min tun kafin
ka karasa tsofar dani"



Na juya na shige ciki, ina jinsa ya biyo bayana a corridor "Jidda. At least ki bani damar yi miki bayani. Ban
san me tace miki ba, ammana tabbatar miki da cewa karya take yi kamar yadda take yin karya cewa daga
gidan ta nake, in na miki bayani zaki fahimta. In kin bani dama zan yi miki bayani"



Na rike hannun kofar dakinana juyo "ba sai ka bata lokacin ka ba gurin yi min bayani ba na riga na
fahimci komai" na nuna shi da danyatsa na "you never loved me, ka aure ni ne dan biyan buƙatar gangar
jikinka, kuma I guess ka gama biya tunda har ka koma gurin karuwan ka"



Ya bude ido da baki duka "that's rediculous! Yanzu har akwai wanda zai gaya miki yace miki bana son ki
kuma ki yarda?" Na juya na shige daki ina cigaba dayi masa bitar abubuwan da ta fada da karfi yadda zai
shiga cikin kansa sosai kamar yadda ya shiga nawa kan



"Ba sona kake yi ba sha'awa ta kayi a wancan lokacin, Ka saka ni a makaranta saboda ka samu time din
biyan mummunar buƙatar ka sai kuma Abba yayi maka cikas yace aurar dani zaiyi dan ya karbi kudin
fansho baya son su kare bai yi min kayan daki ba"



Naji dukkan rage din dana ke ta kokarin rikewa ya kwace a lokaci daya, na fara diban kayan da suke kan
dressing mirror dina ina jifan sa dasu ina kara "I hate you. I hate you"



"Zaka dauki magana ta kaje ka gaya wa ƙaruwar ka saboda kana son shiga tsakanin cinyoyin ta? Ka wuce
kaina ma har ka tafi kan iyaye na? Me nayi maka? Me iyayena suka yi maka?"



Shock din magana ta yasa ya daskare a guri daya, wanny ya bawa wadansu daga cikin kayan da naje
jifansa dasu damar samunsa, wata kwalbar turare ta daki bango ta fashe a tsakanin mu, sai a lokacin ne
ya motsa ya tsallake ta da sauri ya janye ni da kar in taka. Ya fara kokarin rike ni ina tureshi.
"Menene laifin da Abba yayi maka da har zaka yi zancen sa da ƙaruwar ka? Menene laifinsa dan ya dauki
kudin da yayi shekara da shekaru yana tarawa ya kuma yi wa yarsa aure da su? Halaliyar sa, gumin sa,
menene laifin sa da har za'a aibanta shi har haka?"



Yace "Jidda kema kanki kinsan wannan maganar banza ce, ni kaina kin taba gaya min da wanne kudi
Abban mu yayi mana kayan daki?" Na ture shi ina nuna shi da dan yatsa, "kar ka kara. Kar ka sake kiran
Abba da sunan Abban ka dan bai haife ka ba, bai haifi da irin ka ba. Shi Abba talaka ne daya shafe
shekaru yana koyarwa a matsayin malamin makaranta yake kuma cin gumin sa yana kula da iyalansa. Kai
kuwa babanka mai kudi ne, mai kudin da har ya iya siya maka gida ya baka kai kuma ka saka karuwa a
ciki ta zauna har na tsahon shekara guda ba tare da ya sani ba. To albishirinka, yanzu zai sani. Yanzu
kowa zai san wanene Umar"



Sai naga ya ja da baya sannan kuma da sauri ya fita daga dakin, nayi tunanin guduwa yayi ko kuma
magana tace tayi masa zafi sai na bishi da sauri dan ban gama da shi ba tukunna.



Kofar dakinsa na gani a bude dan haka nan na shiga. Yana tsaye a gaban locker din da yake ajiye mana
First aid drugs, ban lura da abinda yake yi ba dan bashi bane a gaba na ba, na tsaya a bayansa na cigaba



"Gwara ma ka nemo takarda da biro, in baka dasu ni zan ara maka dan a yau dinnan ba gobe ba zan bar
gidan ka" ya juyo sai kawai naga ya rungume ni, na fara kokarin kwacewa amma sai ya matse ni sosai da
dukkan karfin sa, ya saka fuskar sa a dai dai tawa, ina jin yadda fatarsa ta dauki zafi numfashin sa yana
fita kamar na mai zazzabi a hankali yace



"Ba zan rabu da ke ba Jidda. Not now, not ever. Saboda ina sonki fiye da yadda nake son kaina. In kinga
na rabu dake to ki tabbatar kabari aka kai ki ko kuma ni aka kaini. Am sorry for this and for everything"



Sai naji shigar allura a cinya ta, nayi kokarin yin motsi da fatan allurar zata same ni a inda ba zan tashi ba
amma ya rike ni gam gam har sai daya zare syring din ya jefar dashi.



A hankali naji jikina ya fara saki, sannan kaina ya fara juyawa ina ganin abubuwa suna rabuwa bibbiyu.
Sai naji ya sake ni sannan kumaya dauke ni chak ya dora akan gadonsa, na bishi da kallo ina ganin
yaddaykae gyara min kwanciya har da saka min pillow a baya na da kuma kasan marata yadda zanji dadi,
sai kuma ya gyara min hannu na daya lankwashe sannan ya durkusa a gaban gadon yana shafa fuska ta.



"Am very sorry Baby, nayi miki allurar bacci saboda ina tsoron kai kiyi hurting kanki ko babyn mu" ni sai a
lokacin ma na tuna akwai cikin sa a jikina. Ya cigaba "ina kuma fatan zuciyarki zata huce kafin ki farka
dan in samu ki bani dama inyi miki bayanin da na tabbatar zamu fahimci juna. Amma tun kafin nan ina
tabbatar miki da cewa kaso tamanin cikin dari na abinda matar can ta gaya miki karya ne. Babbar karyar
kuma ita ce zancen Abba, wallahi ban gaya mata ba"



Na bude bakina zanyi magana amma shima naji yayi min nauyi, kalma dy ce ta fito daga ciki "Umar". "I
am here with you. I am never going any where" ya fada yana zura yatsunsa cikin nawa, sannan ya
sunkuyo yayi kissing goshina. "Umar" na sake fada, sannan hawayen da nake ta fatan suzo tun dazu suka
ki zuwa sai yanzu suka zubo daga idona.



Na mayar da idon na rufe. And I slept..



Sanda na farka cikin dare ne, ba zan iya tuna karfe nawa ba ne ba amma nasan dare ya raba sosai.
Abinda na fara gani shine fuskar Umar. Yana zaune a gaban gadon da yawa ta a hannun sa, daga dukkan
alamu ya hado tane daga inda ta tarwatse. Tashin hankali rubuce baro baro akan fuskar sa.



Na dafe kaina da naji yana barazanar tarwatse wa, motsin da nayi ya jawo hankalin sa kaina, yayi sauri ya
ajiye wayar sannan ya karaso yana kokarin mayar da ni ya kwantar. Na daga masa hannu kuma naci saa
ya dakata bai karaso din ba.



Na mike zaune na ziro kafafuwana kasa ina kokarin mikewa tsaye "dan Allah ki kwanta Jidda. Kar ki je ki
fadi fa ga shi ba ke kadai ba ce ba" na juya na zanga masa harara tare da dogon tsaki sannan na mike
"ina zaki je?" Ya sake tambaya ta na ce "sallah zanyi, sallar magrib da isha da ka yi min allura ka hana ni
yi akan lokaci, alhaki a kanka kuma ban yafe ba"



Bai ce komai ba na shiga toilet nayi alwala na fito na tayar da sallah a zaune dan yadda nake jin kaina
yana juyawa ba zan iya yi a tsaye ba. Nayi magrib nayi isha sai da na idar na fara addu'a nazodai dai
gabar da nake yi wa Umar addu'a kullum sai naji n kasa, naji bansan me zan roka a gameda shi ba, shin
Allah ya raba ni da shi zance ko kuma ya cire min sonsa? Ko kuma addu'ar zanyi Allah ya daidaita mu.
Naji messages din Zuwaira suna replaying a kaina kamar yanzu ne take aiko min dasu, sun saukar da
wani irin daci daci yaji yaji a cikin zuciyata wanda ya kawo hawaye cikin ido na, sai na rufe fuskata da
hijab dina nafara rusa kuka kamar Allah ne ya aiko ni inyi shi. Duk kukan da banyi ba jiya shi na hada
nake yi yanzu. Bai rarrashe ni ba har sai da nayi ya ishe ni sannan na goge ido na na dafa gado na mike
na tafi bakin kofa.



Ina murdawa naji ta a rufe, na juyo cikin dacin rai ina kallon sa "open this door" ya bini da kallo da
jajayen idanuwan sa da suka yi kamar shima kukan yayi, na sake maimaita wa "ka bude min kofa nace"
ya mike tsaye yana girgiza kansa. "Bazan iya barin ki ki fita ba Jidda har sai munyi magana mun fahimci
juna. Kiyi hakuri ki dawo ciki"



Na saki hannun kofar sannan na dawo na wuce shi na koma kan gado na kwantana ja bargo na rufe har
kaina sannan na cigaba da kuka na, sai dai ban dade ina yi ba bacci ya dauke ni tunda har lokacin akwai
sauran allurar da yayi min a tare dani.



Ban kuma farkawa ba sai bayan assuba, har gari ya fara haske. Na tashi ina jin kaina ya bude sosai, jikina
da zuciyata kuma sunyi nauyi. Yana zaune akan sallaya da Alqur'ani a gabansa yana karanta wa, da alama
anan ta kwana dan banga alamar an kwanta a kusa da ni ba, nayi shiru ina tunanin last time da naga yayi
karatun Alkur'ani.



Na sauko na shiga toilet nayi alwala na dawo na tayar da sallar asuba, ina idarwa na danyi adduoi na
sannan na fara azkar wadanda narike a kaina dan dama a wayata nake karantowa kullum wanda Aunty
Surayya take turo mana a group din Maman Maama novels, yanzu kuma wayar tana hannunsa kuma
bani da niyyar yi masa magana ballantana in tambaye shi inda take.



Ina cikin yi naji ya katse karatun ya tashi ya mayar da Alqur'anin inda yake sannan ya bude kofa ya fita
sannan naji ta rufe ta waje. Na ja tsaki na harari kofar a raina ina cewa dole dai zai bude ni kuma dole in
tafi gidan mu.



Bai jima sosai ba ya kuma dawowa, ya sake rufe kofar ya saka key din a aljihun sa sannan yazo gabana ya
ajiye min tray din hannunsa wanda yake dauke da cup din tea da kuma plate din da naga soyayyen kwai
a ciki. Sai kuma ya zauna kusa dani, kafadar sa a jikin tawa mun jingina a jikin gado.
"Ki ci abinci dan Allah....." "ba zan ci ba" "kin san dai ba ke kadai bace ba ko? Little Jidda tana bukatar
abincin ita, Idan ke kina fushi da Umar little Jidda bata yi saboda ke zaki iya chanja Umar a duk lokacin da
kika so ita kuma ba zata iya ba"



"Ba zan ci ba" na sake maimaita wa. Yayi ajjiyar zuciya "okay amma zaki saurare ni ko?" Nace "kunne ne
yake ji ai, kayi ta magana zasu ji ka" yace "zanyi kokarin shigar da magana ta zuwa kunnen, sannan inyi
fatan zata wuce har cikin zuciyar Jidda kuma jiddan zata bawa kwakwalwar ta damar duba maganar da yi
mata kyakykyawar fahimta"



"Da farko dai zan baki hakuri akan laifin da nayi miki. Laifin da nayi miki kuwa shine nayi miki karya nace
ban san Zuzu ba alhalin na santa din. Sai dai ina so ki sani cewa nayi hakan ne dan gudun bacin ranki.
Dan nasan in dai nace na santa sai kinja maganar har ta kaiki ga sanin abinda zai bata miki rai. Na dauka
in nace ban santa ba shikenan zamu rufe babinta har abada"



Na juyo ina kallon sa, hawaye yana bin fuska ta "for how many years ka san ta?" Yace "getting to eight,
kamar yadda ta gaya miki" na gyada kai. Ya fara fadar gaskiya at last.



Sai ya cigaba



"But wannan shi kadai ne gaskiya a cikin dukkan maganganun data gaya miki" na dago kai da sauri, there
we go again, karyar ta dawo.



Ya gyada kai yana kokarin nuna min iyakacin gaskiyar sa kenan. Nace "kana nufin bata zauna a gidan nan
ba? Baka ajiye ta a gidan nan har na tsahon shekara guda da watanni ba?" Ya dafe kai "shine maganar da
nasan in nayi miki admitting na santa tun a wancan lokacin sai kin binciko kuma ba lallai bane ki fahimci
yadda maganar take ba. Jidda wallahi ba irin zaman da ta gaya miki munyi bane ba, ba irin zaman da kike
tunani bane ba"



Na fara girgiza kaina, "you are not ready to talk, tunda ba zaka gaya min gaskiya ba" ya kama fuskata ya
juyo da ita ina kallon sa. "Look at me Jidda, ta zauna a gidan nan amma wallahi ba irin zaman da kike
tunani bane ba. Budurwar Mahmud ce, suna tare tun muna buk sai ta samu matsala da iyayen ta akan
lalacewar tarbiyyar ta suka kore ta, ni kuma lokacin Baba ya siya min wannan gidan babu komai a cikinsa
sai ya roke ni in bata aro zata zauna ta karasa karatu anan tunda yana kusa da makaranta, shine na basu,
suka zauna ita da friends dinta suna zuwa school daga nan, har lokacin da zan tafi India nace lallai su
tashi dan zan bar key a gida kuma in Baba da Mama suka san da mata a gidan nan ba zasu fahimce ni ba,
zasu yi min irin fahimtar da kika yi min yanzu ne"



"A lokacin ne take gaya min wai ita dama tana so na ne, kuma zata iya rabuwa da Mahmud indai har zan
karbi soyayyar ta kuma zamuyi aure. Na nuna mata ni ba zan ci amanar friend dina ba, besides kuma ni
tarbiyyar ta bata yi min a matsayin matar da zan aura ba."



"She kept stalking me through social media, sun bar gidan nawa amma taki rabuwa dani kullum sakon
yau da ban na gobe daban ni kuma ban taba nuna mata na yarda ina son ta din ba amma ba wai ina
wulakanta ta bane ba, a gurina we are just friends."



"Ina dawowa sai ta cigaba da yi min zancen aure, wai ta gaji da zama babu aure and other stuffs, kuma
wai ita ni take so ta aura ba Mahmud ba, shi kuma dana gwada yi masa maganar aurenta sai ya nuna
min shi ba zai iya aurenta ba cos sun riga sun lalace a waje. Wannan yasa nima kuma na kara

26 / 101