Author : MAMAN MAAMA Category : KDP NOVELS
na bashi, briefly ya duba sannan ya
shiga mota ya koma.
Washegari Musa ya dawo, ya tarar da yaya Muslim a sitting room dan haka ya shiga suka gaisa sannan ya
nemi ya kira masa ni, ina jin cewa shine na tashi na fita a raina ina son in gaya masa gaskiya dan ya daina
wahalar zirga zirga mu daina bata wa juna lokaci, gaskiyar ita ce baiyi min ba a matsayin miji amma bashi
da wata makusa kuma na tabbatar mata da yawa zasu karbe shi hannu bibbiyu.
Na shiga na gaishe shi ya amsa da fara'ar sa yana jin dadin na gaishe shi, sai naji na sake jin rashin dadin
abinda zan gaya masa. Nace "yaya Musa, kai mutumin kirki ne sosai, Abba da Umma ma duk sun yaba da
kai, amma ba Abba da Umma ne zasu zauna da kai in ka aure ni ba" ya mike tsaye "ke zaki zauna dani
kuma ke baki yaba dani ba ko?" Na mike nima nace "ba haka bane ba. Bana jin shi so yana tafiya ne a
haka. Bamu da zabi akan wanda zuciyar mu zata so ko kuma take so....."
" Ke taki zuciyar bata so na" ya karasa min, "kin nuna min haka, but you don't have to say it please" na
sunkuyar da kaina nace "kayi hakuri, na dauka hakan shine dai dai" sosai nake jin babu dadi a raina.
Amma sai naji yace "ba kya sona saboda shi ko? Saboda shi yana da mota ni bani da ita? saboda yafi ni
abin duniya?" Na dago kai da mamaki ina kallon sa, ya gyada kai "yes, na san wanda yake zuwa gurinki
da farar Benz, na dauka cewa akwai sauran true love a duniya, na dauka akwai sauran yammatan da zasu
zabi talaka akan mai kudi, na dauka zanyi amfani da soyayyar da nake yi miki in ribato taki soyayyar, na
dauka....."
Na daga masa hannu "ko kadan ba ina son Umar bane ba dan wani abun da yake dashi, ban taba karbar
ko kwandala daga hannun sa ba, na dauk in nayi maka bayani zaka fahimta sannan kayi min uzuri" ya
danyi murmushin takaici yace "na fahimta kuma nayi miki uzuri....."
Kamar daga sama aka daga labulen dakin Umar ya shigo, daga dukkan alamu yazo ne ya rasa dan aike
kuma yaga kofar gurin a bude sai kawai ya shigo, hannun sa daya rike da key din motarsa dayan kuma
rike da manyan ledoji biyu masu dauke da tambarin sahad stores. Ya tsaya yana raba ido a tsakani na da
Musa, sai kuma ya ajiye ledar hannunsa akan kujerar kusada shi yace "ohh sorry guys, na dauka Tahir ne
a ciki ko wani" ya kalle ni "I will wait outside" nayi saurin gyada masa kai duk da kururuwar da zuciyata
take yi min a cikin kunnuwa na.
Yana fita Musa ya kalli ledojin daya ajiye sannan ya kalle ni yana karyayyen murmushi yace "kuma kika
ce baki taba cin ko kwandalar sa ba, am sure aljanu yayi wa siyayya bake ba" na fara kokarin kare kaina
"wallahi....." Sai kuma naga kamar rantsuwar bata da amfani sai nayi shiru, ya girgiza kai "save it" yace
tare da kama hanyar fita, har sai daya kai bakin kofa sannan ya juyo yace "in kin chanja ra'ayin ki, gidan
mu yana nan a bakin layin nan" sannan ya karasa fita.
A daidai lokacin ne kuma naji tashin motar Umar, da sauri na wuce Musa na fito a dai dai lokacin da
Umar yaci tayar mota ya bar layin a guje, na tsaya ina bin motar da kallo, Musa ya karaso ya tsaya a kusa
dani shima yana kallon motar sannan ya juyo ya kalle ni yace "yayi fushi, daga dukkan alama yana da
kishi, amma kar ki damu in dai yana son ki da gaske zai dawo".
Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din
08067081020
Please banda kira, WhatsApp only
*π Jidda π*
*By*
*Maman Maama*
*Episode eight : Bashir*
Bai dawo ba har bayan sati daya, shima kuma Musa bai dawo ba. A cikin satin nan gabakidaya hankali na
a tashe yake kusan kullum sai nayi wa Farhan mita a daki "yayi fushi dani Farhan. Watakila ma ya dauka
yaudarar sa nake yi Musa nake so, bai san a lokacin da ya gan mu da musan ma ina gaya masa bana son
shi ba ne ba"
Ita kuma sai tayi dariya, ita abin wai dariya yake bata "lallai Jidda kinyi zurfi da yawa, wai ke din ce kike
tada hankali akan namiji? Jiddan dana sani ce kuwa? Ni ina ganin wannan dama ce a gare mu da zamu
gane in da da gaske yake son ki, dan ni a ganina dan wannan abin bai isa ace ya barki ba, sai dai in dama
ba da gaske yake ba" tabbas gaskiya ta fada, sai dai in dama ba da gaske yake ba, amma anya kuwa?
Rashin sa yana nufin rashin chance dina na karatu.
Kusan kullum sai na kira Mufida munyi ta hira duk da nasan basa tare amma na fahimci hakan yana
kwantar min da hankali dan nasan lafiyar sa kalau, ko dai ya fasa ne ko kuma yayi fushi sosai.
Kullum kuma ina saka ran inji ko Mufida zata yi min maganar sa amma shiru. Ina ta tunanin ko ni inyi
mata in gaya mata yazo kuma ga yadda muka yi dashi ko da kuwa ban nemi shi ta bangaren ta ba at least
ban rufe ta da komai ba, kar daga baya taga kamar na munafunceta. Amma still na kasa yi mata
maganar. Ranar nan kuma sai gata tayi min da kanta "yanzu mutumin ki ya kira ni wai dan Allah in tura
masa hoton ki, nace nima bani da shi" ta karasa maganar tana dariya. Naji wani sanyin dadi a raina
amma sai nace "wanne mutumin nawa kenan?"
Tace "kya ji da shi ma can, na sani ai kuna tare da yaya Doctor amma kina ta wanibasarwa ko?" Na dan yi
murmushi "to kinga laifi nadan na basar da shi? Ji nake kanwarsace ta bani shawarar in rabu da shi" sai
ta danyi shiru, na dauka zata chanja topic amma sai naji tace "Yaya Doctor ne yana da wuyar sha'ani
Jidda, ke kuma ba experience kuke da shi akan samari ba shi yasa na baki shawarar rabuwa da shi dan
banyi tunanin da gaske yake ba" nace "amma me yasa kika yi wancan tunanin? Mai yasa kike tunanin
yaudara ta zaiyi?" Tace "shi yana daukan irin wannan relationships na yammata da samari ne kamar
wasa, in yayi budurwa sai kun gama sakin jikin ku da ita sai ya tubure yace shi fa ba da gaske yake ba
kawai friendship ne. Ni wannan abin na gudar miki."
"A yanzu haka Mama babu abinda take so irin taga yayi aure, ita da kanta take samo masa yammatan da
take ganin maybe zai so amma sai yace shi basu yi masa ba. Kinga kafin ya tafi India akwai wata second
cousin din mu da Mama ta hada su sukayi dating sosai har mun fitar da anko fa, kawai bawan Allahn nan
sai yaje ya samu Baba wai Mama zata yi masa auren dole"
Ta karasa maganar tana dariya nima sai naji maganar ta bani dariya "wallahi yarinyar baki ga yadda kowa
ya ringa tausaya mata ba yadda kika san zata mutu akan sa amma yace shi wallahi baya son ta, haka ya
hada kayansa yayi tafiyar sa India, haka Mama tayi ta bawa iyayen yarinyar hakuri. To irin haka nayi
gudun kar ya faru dake shi yasa nayi warning din ki a kansa, saboda yana da saurin shiga rai musamman
ke da babu kowa a zuciyarki, bana so kiyi ending up like cousin din can ta mu" na gyada kaina ina
fahimtar ta kuma ina jin dadin abinda tayi min sannan na bata labarin so far abinda ya gudana tsakani na
dashi, har form din da ya kawo min da zuwan da yayi gurin Abba na.
"Yanzu still kina tunanin ba da gaske yake ba?" Tace "I can't say gaskiya. Ina tsoron in bada shaida a
kansa kuma yazo ya bani kunya" ta karasa tana dariya, sai kuma tace "amma dai abinda zan iya cewa
shine ban taba ganin yayi going this far ba, ban taba ganin yayi getting involved with iyayen yarinya ba. I
think ya kamata in bawa Mama wannan labarin...." Nayi saurin katse ta "na shiga uku rufa min asiri. Ki
bar maganar a tsakanin mu please, in yana so Mama ta sani da kansa zai gaya mata" a haka muka kare
maganar. Sai dai ni bata kare a zuciyata ba haka nayi ta bitar maganganun Mufida a raina. A karshe sai
na yanke shawarar in Umar ya gama fushinsa ya dawo to zansan yadda nayi na tambayeshi game da
relationships din da yayi a baya dan inji nasa side of the story din.
Ranar nan muna cikin waya da Mufida Farhan ta shigo, sai take min sign da in karbi number din Umar a
gurin Mufida ni kuma sai na harare ta kawai, da ta sake yi min magana sai na murguda mata baki na
cigaba da waya ta, there is no way da zan ce Mufida ta bani number din yayanta duk kuwa da
kasancewar Mufida kawata ce.
Bayan mun gama wayar sai Farhan ta karbe wayar ta sake kiran Mufida "Mufida ga fa kawarki nan taki ci
taki sha saboda sunyi fada da yayanki. Allah kuwa. Ki kira shi kice ko dai yazo ko kuma zuciyarta tayi
bindiga" na mike tsaye da sauri na bita ita kuma ta fita a guje da wayar a hannun ta, a tsakar gida suka
hadu da Umma tayi sauri ta mika mata wayar ta sannan ta shige dakin Hajiya dan tasan ba zan bita can
ba.
Nayi sauri na karbi wayar a hannun Umma na saka a kunne na ina cewa "karya take yi Mufida, sharri
take yi min" naji Mufida tana dariya "kwaji dashi ma daga ke har shi, dazu ma sai da ya kira ni yana
tambayata wai munyi waya da ke? Ni bani na hada ku ba kuma bana son in kasance a tsakiya in kunyi
fada ma sai dai ku shirya kanku ni dai ba zan shirya ku ba" nace bafa fada muka yi ba, sharrin Farhan ne"
sai kuma na bata labarin abinda ya faru, tace "lah! Babbar magana, yaya Doctor ne da kishi haka? Ban
taba gani ba. Zan kira shi in gaya masa kin kira kina tambayarsa" nace "ki rufa min asiri kar kiyi mini
sharri ke ma" ta sake dariya, "tsokanar ki nake yi. Ki share shi zai dawo ne da kansa"
Naji dadin yadda Mufida tayi reacting, kuma na bi shawarar ta na share shi nima har sai da yayi kwana
goma rabonsa da gidan mu.
Ranar nan Sulaiman ya zo gurin Farhan sai muka fita tare, muna zaune muna hira wanda mostly su biyu
suke kayarsu sai dai in sun ambaci sunana sannan sai in basu amsa.
Da yake kofar waje a bude take kuma ni ce nake zaune a kujerar da take facing kofar, ina hango
wulkawar mutane duk da cewa su ba zasu hango ni ba, a haka naga tsayuwar motar sa wadda ko cikin
mafarki zan gane ta, tun daga nan na daina jin hirar su Farhan na koma kallonsa, komai nashi yayi min
komai nashi yana burge ni, ina kallon sa ya fito daga motar ya rufe sannan ya tsaya a gaban motar yana
kallon gidan mu, yana kallon kofar sitting room din da take a bude, sai kuma naga ya tako ya shigo cikin
railer din still yana kallon budaddiyar kofar sannan kuma naga ya kalli takalmin Sulaiman da yake ajiye a
bakin kofa.
Sai kuma naga ya daga labulen dakin da sauri yana rarraba ido a cikin dakin. Na mike tsaye da sauri ina
kallon sa kamar yadda shima ya tsayar da idonsa a kaina. Cikin saurin magana nace "Yaya Doctor wannan
saurayin Farhan ne, sunan sa Sulaiman".
Sai da naji Farhan tayi dariya sannan na fahimci abinda nayi, sai kuma naji kunya, ina kallon sa yayi
murmushi sannan yace "hey Baby" Farhan tace "baby ce kam, dan yadda tayi ta kuka wai saboda kayi
fushi da ita idan ba baby ba babu mai yin haka" na juya na harare ta, ido na yana kawo kwallar haushin
tonon sililin da tayi min, yace "Allah da gaske Farhan? Da gaske tayi kuka?"
Sulaiman da yake kallon mu yace "ga wani kukan nan zata sake yi ai" nan take sai hawayen ya karasa
zubowa. Na zauna ina gogewa da hijab dina, Umar ya zauna a kasa a gaba na yace "innalillahi. Kukan ne
kuma? Ashe ina da aiki babba a gaba na" Sulaiman yace "ba kadan ba, sai ka shirya aikin rarrashi" na
harare shi, Umar yayi sauri ya tare bangaren Sulaiman "noooo wannan hararar ni kadai za'a yi wa ita,
tawa ce ni kadai" na dawo da ido na kansa sai ya koma ya zauna a gabana "na gaya miki ai, ina da
tsananin kishi" na murguda masa baki sai ya lunshe idonsa yace "kara wani"
Duk suka yi dariya Sulaiman ya mika masa hannu yace "salamu alaikum, gwara mu gaisa kafin ayi maka
hararar da zaka narke ban samu ladan musabaha ba" suka gaisa sai kuma muka fara hira gaba-daya mu
hudun, mostly akan soyayya tsakanin yammata da samari. Ana cikin hirar ne Umar yace min "before I
forget irin ta ranar nan, ina son ki bani exam number da center number din ki na waec, result din ku ya
fito, gashi har na siyo scratch card zan dubo miki. Dama ina ta addu'a Allah yasa ta fito kafin a kira ku
pretest, dan I was suppose to go with credentials dinki sanda zan karbi form, dan dai an daga min kafa
ne"
Naji hankali na ya tashi "yaya Doctor in na fadi kuma fa? In ban samu abinda suke bukata ba fa?" Yace
"sai mu jira neco ta fito, in baki ci a waec ba zaki ci a neco" nace "in ita ma banci ba fa?" Yace "common
Baby, zaki ci fa, kuma in ma baki ci din ba akwai private neco da ake yi around december, sai in nemi
wani in biya shi ya rubuta miki ki sami 9 distinctions, babu wani problem fa, tunda kina da ni baki da
sauran matsala".
Sulaiman yace "wai maganar me kuke yi ne? Kamar makaranta kuke magana akai ko? I thought Abba
baya bari ayi karatu sai bayan aure" Umar yayi saurin kallo na sai na sunkuyar da kaina kasa, Farhan tace
"ya sauko ai Abban, ya bar Jidda tayi as long as Umar ne zai aure ta, tunda shine yake nema mata
makarantar"
Yace "ohh okay, good" sai tace "nima zai iya barina in fara idan kai ka samo min" ya girgiza kai "a'a don't
start there, mun riga mun gama magana da ke cewa sai munyi aure first year din mu zaki tafi school,
wannan shine tsarin mu ni da ke bana so kuma dan kinga wasu sunyi nasu tsarin ki ce ke ma irinsa kike
so. Kinji?" Ta gyada kai a hankali, amma daga gani ba haka ranta yaso ba, sai ya mike yayi mana sallama
ita kuma ta bishi zata raka shi waje.
Bayan sun fita na mayar da hankali na kan Umar ina jiran ya fara jero min tambayoyi amma sai kawai naji
yace "ina fatan banyi laifi a gurin Abba ba?" Na girgiza kai na, yayi ajjiyar zuciya "har na tsorata, na dauka
nayi masa shishshigi" na danyi murmushi, sai yace "da na sani da na taho wa da Farhan form din ita ma
ta cike, naga kamar tana so" nace "Abba ba zai barta ba ai, cewa zaiyi ai ba kai ne zaka aure ta ba" ya
gyara zama "wato ya bar ki ne saboda ni zan aure ki?" Zuciyata daya ma gyada kai sai ya daga hannunsa
"yes!" Sai a lokacin na lura da abinda nace, na rufe fuska shi kuma yana dariya.
Daga nan sai ya zauna ya fara min bayanin yadda tsarin neman admission a school of nursing yake "zasu
kira ku kuyi pretest, daga nan wadanda suka ci zasu je ayi musu interview idan sunci sannan sai a basu
admission" nan take na rude, shi kuma yana ta yi min dariya tare da kara jaddada min cewa tunda ina da
shi bani da problem.
Da zai tafi yau ma har sai daya fita sannan ya tuna cewa bai karbi details din da yake nema ba, sai yace in
karbo na Farhan ita ma ya dubo mata. Na koma gida na binciko a cikin takarduna na makaranta sannan
naje na taya Farhan neman nata a dakin hajiya muka fita tare muka kai masa.
Washegari da rana sai ga Mufida ta kira ni tana min albishir cewa naci duk subjects Ιin da ake bukata,
nayi ta murna ina tsalle itama tana tayani, sai ta bani labarin cewa itama ta ci amma ta fadi English "sai
na sake resitting kafin in samu admission" sai naji babu dadi kuma na jajanta mata. Tace "mutumin ki
farko cewa yayi wai in bashi number din da muke waya da ita, sai da na bashi kuma nace ta Umma ce sai
gashi ya sake kira na wai ya kasa kiran ta, wai kunya yake ji, in ta dauka bai san me zai ce mata ba, gashi
bama tare bare ya bani mu fara magana" ta sake dariya. "Wai yaya Doctor ne yake jin kunya"
Nayi tsaki "ke bama son rashin kunya fa, ki kama kanki ko kuma jikin ki ya gaya miki" tace "ohh, wato
dan kin zama budurwar yayana shine har zaki fara dorawa kanki girma ko?" Nace "eh mana, da shekarun
sa nake amfani ai yanzu ba da nawa ba" tace "yayi kyau Aunty, daga yau Aunty zan ke kiranki da shi"
muka yi ta hirar mu sannan ta sake congratulating dina muka yi sallama.
Next zuwan da zaiyi ya taho min da printout na results din mu ni da Farhan kuma alhamdulillah duk
munyi abin kirki sosai. Kusan kowa na gidan sai da na nuna masa, Abba ma yana zuwa naje na nuna
masa kuma na gaya masa wanda ya dubo min, naga alamar yaji dadin hakan kuma yayi mana addu'ar
fatan alkhairi.
Da aka saka ranar da zamu yi pretest din shi da kansa yazo ya samu Abba ya sanar masa kuma ya roke
shi ya bar ni inje, Abba ya bari kuma yayi min fatan alkhairi. Da ranar tazo ma Umar din ne yazo dauka
na, na shirya cikin sabuwar abaya ta maroon da Aunty Afia ta siya min, light make up tunda exam zanje,
sannan nayi rolling mayafin abayar, amma dana kalli kaina a madubi sai naga nayi kyau sosai fiye ma da
yadda na saka ran zanyi, sai dai na lura cikar