Author : MAMAN MAAMA Category : KDP NOVELS
nostril suna budewa suna rufewa da sauri, abinda yake yi in ransa ya baci, sai nayi dropping
bomb din. "Kafin ta fita, sanda tana wanka, ina neman kudi a jakarta, I saw a condom"
Ya mike da sauri har sai da kujerar da yake kai ta fadi, ya nuna ni "you saw something that looks like a
condom, amma baki tabbatar ba, right?" Na mike tsaye nima sannan nace a nutse "I know what a
condom looks like, condom na gani ba abinda yake kama da condom ba" ya dafe kansa "maybe tsinta
tayi, maybe bata san ma menene ba ta dauka ta saka a jakar ta, maybe ma ba jakar ta bace ta wata ce ta
ara, maybe kuma wani abin ne na makaranta ya kawo sai sunyi binciken da suke buƙatar condom. It can
be anything"
Nace "maybe. Maybe not. Allah kadai ne ya sani sai kuma in anyi bincike sannan za'a tabbatar. Mama ya
kamata ka nuna wa ta saka ido a kanta, kai ma kuma ka saka ido a kanta, in kun ga wani abu sai a
gaggauta yi mata aure, shine dalilin da yasa na gaya maka dan ayi wa tufkar hanci tun yanzu".
Ban san ya suka yi da Mama ba but Mufida told me a waya cewa Mama ta takura mata, yanzu ta hana ta
zuwa ko'ina sai ranar da take da lecture din nan guda daya da ake binta ita ma kuma tare da driver zasu
je ya jira ta ta gama su dawo gida tare, har timetable din su Mama ta aika aka kawo mata dan haka tasan
ranar da take da lecture da ranar da bata da ita.
Naji dadin hakan, at least za'a dakile ko ma menene yake faruwa da ita.
Bayan wannan ya wuce, lokacin tafiya aikin hajji yayi sai ga Surayya ta kira ni tana ta murna tagaya min
zasu je hajji ita da Bashir "wallahi Jidda abin mamaki, kawai yazo yace ya biya min zamu tafi tare. I am
sooo happy" na taya ta murna "Masha Allah. Allah ya kaiku lfy ya dawo da ku lafiya yasa karbabbiya za'a
yi"
Sai kuma ta nuna min target dinta na yi wa mijinta addu'a a gaban ka'aba, tare kuma da shawartar sa da
shima yayi wa kansa addu'a, na nuna mata cewa hakan dai dai ne. Fews days bayan nan suka tafi.
Sai dai.......
Bayan sun dawo banji labarin sun dawo ba, ina ta lissafi amma shiru, har satittika suka wuce, ina son
tambayar Umar amma bana son yi masa maganar duk data shafi Bashir. Sai na gwada number dinta, sai
kawai naji ta shiga, a raina nace sun dawo kenan.
Muka gaisa da ita sosai sai nayi mata mitar yadda bata gaya min sun dawo ba. Sai tace
"Hummm. Jidda kenan. Zan baki labarin abinda ya faru tunda already kin riga kinsan halin da nake ciki.
Kin san Bashir a Saudiyya na kama shi da mace turmi da tabarya?"
(Wannan abin ya faru da daya daga cikin readers din Jidda, she told me the story, ni kuma nayi deciding
saka shi a cikin labarin dan in nuna wa masu karatu how deep zina can cut into a person's Iman, yadda
har mutum zai iya tafiya macca da niyar sauke farali sai kuma ya buge da aikata zina a cikin gari mafi
tsarki a cikin ranaku masu alfarma)
Naji kamar zan yar da wayar hannu saboda yadda maganar ta razana ni. Nace "innalillahi wa inna ilaihir
rajiun" tace "Wallahi. Kin san dai nasan yana yi amma ban taba kamashi in the act ba sai a can, na dawo
daga masallaci inda na dauki tsahon lokaci ina nema masa shiriya sai na zo masaukin sa na tarar da shi
turmi da tabarya da wata matar da ban sani ba. Bayan sun ganni sun kuma san na gansu sai na juya na
koma masallaci, banyi masa addu'ar shiriya ba sai nayi wa kaina addu'ar Allah ya bani iko da nasarar
rabuwa da aurensa. Sai a lokacin na gode wa Allah da ya karbi dan dana haifa bai raya shi ba, sai a
lokacin na fahimci abinda ake cewa akan duk sanda mutum yayi addu'a da iklasi ana karba sai dai in ba
alkhairi bace sai a chanja masa da mafi alkhairin ta, sai lokacin da na fahimci jimawar da nayi ina yiwa
Bashir addu'a ita ce Allah yayi amfani da ita ya nuna min kiri kiri cewa shi ba mai shiryuwa bane ba,
sauran kuma hukunci ya rage nawa?"
"Ko maganar banyi masa ba na rabu dashi, amma muna saika a airport sai nayi hanyar gidan ubana kuma
ina zuwa na gaya masa cewa na gama auren Bashir, suka dage lallai sai na koma ni kuma nayi musu
hauka, na zauna na ringa rusa ihu ina cewa wallahi ba zan koma ba, babanmu har da dauko bulala zai
dake ni ni kuma nace sai dai ya kashe ni amma ba zan koma ba, a ka shiga tsakani dai aka hana shi
dukana"
"Amma can you believe har yau Bashir bai biyo ni ba kuma iyayensa ma basu zo ba? Na ji baban mu ya
fara mita kasa kasa, na san shima ransa ya baci da abinda suka yi. Insha Allah Jidda wannan shine
karshen wahala ta"
"Ni kam na kai limit dina na hakuri, nayi iyakacin iyawa ta ubangiji ma ya sani. Ba zan koma gidan Bashir
ba, Allah ya sani. Ina kuma kyautata zato na a gare shi ina saka ran zaiyi min chanji na alkhairi"
Na jima ina lissafin maganar Surayya, zancen limit din da ta fada got me thinking about komai yana da
limit, rayuwa, lokaci, haihuwa, komai yana da farko kuma yana da karshe, ma'ana hakuri ma yana da
limit, akwai lokacin da mutum zai kai limit din sa na hakuri in yace zai yi crossing kuwa to tabbas zai
tarwatse ko kuma ya tarwatsa wadanda yake tare da su.
A year pass by, tun da muka yi case din Mammy. And then one day ranar friday na dawo daga aiki da
magrib, lokacin ana ta sallah a masallatai sai na tarar maigadin mu baya nan ya tafi masallaci, ya saya
bakin gate din bai rufe shi sosai ba, na tsaya kenan da niyar yin horn ko Asabe tana kusa sai ta zo ta bude
min sai na hangi wani abu daga crack din da bai rufu ba a gate din. Asabe ce a tsaye Umar yana tsaye a
bayanta, too close, tayi wata magana sai yayi murmushi sai kuma ta juya ta bashi wani abu da yake
hannunta, and I noticed wayarsa ce, ya karba ya saka a aljihunsa sannan yasake yi mata wata magana
suka yi dariya.
My heart was boiling a lokacin, Umar din da ko guri daya baya zama da Asabe amma ya akayi suka yi irin
wannan tsayuwar kuma me ya kai wayarsa hannunta? Me suke cewa?
Nayi horn, sai naga sun kalli gate a tare sai yayi mata magana ita kuma ta shiga cikin gida da gudu, shi
kuma sai ya taho zuwa gate din ya bude karamar kofa ya fito yana murmushi, ya zo window na,
"welcome back Madam, nawa zaki biya in bude miki gate?" Naji haushin yadda yake kokarin yi min wasa,
Umar ba karamin pretender bane ba nace "no barshi kawai Baba Adamu ya idar da sallah sai ya bude
min, kasan shi namiji ne ya tafi masallaci" sai ya saka hannu ya ja hancina "kin ci sa'a sunan ki Hauwa'u,
sunan matata ne, da ace Jidda sunan ki da ba zan bude miki ba" ya bude gate din na shiga da motar sai
yace min zai je masjid, ya fita.
Na jima a motar ina zaune na jingina kaina da jikin stirring ido na a rufe ido na, a hankali na furta "ya
Allah" sai kuma na bude motar na fita da sauri na shiga cikin gidan. Yasmin tana kallo, Asad kuma yana
game. Suka mike da sauri suka tarye ni nayi kissing din su daya bayan daya sannan nace "ana sallah kuna
zaune ko? Maza aje ayi alwala. Kar a jika jiki amma" suka wuce sai kuma nace "ina Asabe?" Yasmin tace
"ta shiga dakin ta yanzu da gudu" na gyada kai kawai sai na bita dakin, ina shiga naji dakin yana warin ta.
Tana kwance ta lulluba, na tsaya a kanta sannan na sa kafa na dake ta "ke Asabe!" Tayi shiru kamar ba
da ita nake ba sai na daka mata duka "ke! Kar ki raina min hankali mana" ta tashi zaune tana mitsitstsika
ido kamar wadda ta tashi daga bacci "mommy kin dawo?" Naji kamar in sharara mata mari "kar ki raina
min hankali wallahi zan ci ubanki, uban me kike yi a waje" tace "waje kuma mommy? Ni ina nan ina bacci
fa, ni banje waje ba" na damki rigarta na daga ta sama "uwarki kenan na gani tare da Umar a waje ko?"
Ta fara karkarwa "mommy dan Allah kiyi hakuri, wallahi ba wani abin muke yi ba" nace "me yake ce
miki?" Tace "hoto ya nuna min a wayarsa" nace "hoton me?" Tace "hoton sa ne, kawai nuna min yayi
yace yayi kyau shine nace yayi kyau" na saki rigarta na fita daga dakin hannu na guda daya a dafe da
kirjina ina jin zuciyata kamar zata fito na shiga dakina na rufe kofa sannan na jingina da jikin kofar.
"innalillahi wa inna ilaihir rajiun".
Ba wai maganar da sukayi ce ta taba ni ba, ba kuma yadda naga sun tsaya din ba, a'a yadda yake
munafurta ta tare da nuna kamar basa ma yi wa juna magana amma kuma a bayan ido na har sunyi
sabawar da zai dauki hoto ya nuna mata ya tambayi opinion din ta, sannan kuma da yaji na dawo yace ta
tafi daki tayi pretending kamar bacci take yi shi kuma yaje ya tsayar dani da surutu har ya bata damar
kwanciyar.
Tabbas Umar bai daina halinsa ba. A cikin gidan mu kenan a gaban ƴaƴan mu, Allah kadai yadan abinda
yake yi a waje. Wata zuciyar ta gaya min cewa in tattara Asabe in auna ta kauyen su, sai kuma nayi
tunanin idan na dauke Asabe daga gida na hana shi kula ta a gida zan hana shi kula wadansu a waje ne?
Sai na yanke shawarar zan barta, sai dai zan saka ido a kansu sosai maybe ta nan zan kama shi. But
amma kuma anya? Umar? Umarul Faruq? Asabe fa? Yarinyar da har yanzu daga ni har shi bama iya cin
abin da ya shiga hannun ta, bama iya amfani da cup ko spoon din da tayi using. Anya ban zurfafa zargi na
ba akan Umar?
Amma kuma duk da haka zan saka ido a kan su sosai, kuma ba zan nuna wa Umar ina zargin wani abu ba,
dan da zarar ya fahimci wani abu zai rufe duk wata kofa da zata sada ni da gaskiyar magana.
Da ya dawo daga masallaci yayi ta kame kamen tsokana ta da yara, ni kuma nayi iyakacin kokari na na
ganin na boye damuwa ta amma na kasa, har muka je daki muka kwanta sai cewa yayi. "Dazu da na
dawo daga office na tarar yaran nan basu dawo daga islamiyya ba, hankali na ya tashi nayi ta tunanin
inda suka tsaya, kin san yanzu yanayin da ake ciki na rashin tsaro, nayi ta tunanin da ina da number din
yarinyar nan da sai in kira su inji me ya tsayar da su. Shine bayan sun dawo na karbi number dinta,
saboda gaba" nayi shiru kawai ina kallon sa, rashin gaskiya a rubuce a fuskarsa, jin ban ce komai ba sai ya
cigaba "ina cikin karba ne ma kika dawo".
Na danyi murmushi, wato ya lura na gansu tare, wannan kame kamen duk na rufe gaskiya ne, na girgiza
kaina nace "ka kyauta. Allah ya kare mana su" ya kwanta tare da lumshe idonsa, ina ganin yadda yayi
ajjiyar zuciya sannan yace "ameen" nima na kwanta a kusa da shi na rufe ido na, abinda ya manta shine
ranar Friday ne babu islamiyya.
Tun daga ranar na saka ido a kan Asabe sosai, ina lura da duk wani move din ta a gidan sai dai ko kadan
ban taba nuna musu ina lura da su ba. Amma kuma inda zan gane cewa Umar ya iya covering tracks
dinsa ko kallo ban taba ganin yayi mata na kirki a gaba na ba, hantarar nan dai ce da tsawa da kyara,
amma ban daina lura da su ba until one fateful day, da weekend, ranar ana muku mukun sanyi duk
muna gida har yara. Muna falo gabakidaya Umar yana ta wasa da yayansa yana yiwa Asad doki suna
zagaya falo ni kuma ina kwance da Yasmin a jikina ina karanta mata story book. Sai aka yi knocking, na je
na leka sai naga wata yarinya yar aikin makota na wadda suke islamiyya aji daya da Asabe. Ta gaishe ni
na amsa sannan tace tana neman Asabe, sai nace ta zagaya ta kofar kitchen ta baya ta shiga, Asabe tana
bayan ko kuma dakinta.
Na koma na cigaba da abinda nake yi sai Yasmin ta fara complain din sanyi yayi yawa, Umar yace rashin
motsa jiki ne yake saka mu jin sanyi ni da Yasmin amma shi da Asad ai basa jin sanyin, sai yace a fita waje
ayi skipping, a ga wanda baya exercise a cikin mu, a ga wanda jikin sa yayi nauyi. Muka fara musu nace
zan iya shi kuma yace ba zan iya ba. Yasmin ta tashi da gudu ta tafi dauko mana skipping rope a dakin su
ni kuma na dauki cups din da muka sha juice na tafi zan mayar kitchen.
Store (dakin Asabe) da kitchen kusan a tare suke amma kofar kowanne daban sai dai kofofin a jikin juna
suke. Ina shiga kitchen din naji an ambaci sunana sai naja na tsaya a bakin kofa, muryar Asabe naji
"ke tsoron mommy fa yake yi kamar mala'ikan da zata cire ransa haka yake tsoron ta"
"Ya ke tsoron ta ko ke kike tsoron ta? Ke fa sokuwa ce wallahi. Yanzu kayan da na baki fa ko sau daya
bana jin kin taba sakawa"
"Uhm uhm ba zan saka kayan nan ba, alkuran tagan su a jikina ubana zata ci, watakila ma ta kora ni
gidan mu kuma wallahi duk abinda ta fada ta zauna kenan ba zai musa mata ba"
"Eh bai iya musa mata ba amma ai ya iya ya lallabo ya danne ki in bata nan ko?"
Suka yi dariya....
"Ke ya daina zuwa fa, tun wata rana da ta gan mu muna magana a waje, bai kara kula ni ba, na gaya miki
tsoron ta yake ji kamar mala'ikan mutuwarsa alkuran. Ni tsoro nake ji ma kar alkawarin da yayi min ya bi
ruwa"
"Alkawarin da yayi miki ba zai bi ruwa ba in dai har kina yin abinda nace miki, yo sau nawa anayin haka?
Yar aikin gida ta auri mai gida kuma ta kori matar gida? Watarana sai dai in ce nazo gidan kawata"
Suka yi dariya.......
Cups din da suke hannuna ne suka zame suka fadi kasa suka tarwatse. Karar faduwar su ta saka suka fito
daga dakin a tare suna rarraba ido, kawar tata ce ta fara ganina sai tayi hanyar waje a guje, ita kuma
asaben tayi kokarin komawa ciki da gudu, na damko ta na dawo da ita baya sannan na jata zuwa cikin
kitchen din na buga ta da bango.
Ta dora hannu biyu a ka ido kamar zai fado kasa "mommy wallahi ba zancen ku muke yi ba, alkuran ba
maganar ku muke yi ba" na shake wuyanta nace "kashe ki zanyi dan ubanki, na haka rami na binne
gawarki nace kin bata dan uwarki" ta zaro ido "alkuran mommy ba ke mommyn muke nufi ba"
Na shake wuyanta da hannu daya sannan na fara laluben abinda zan dauko da daya hannun, abinda zaiyi
mata illa nake nema, hannu na ya sauka kan fork din da muka gama cin abinci dashi dazu, na dauko na
dora tsinin sa a wuyanta sannan nayi mata straight tambaya "menene tsakanin ki da mijina?".
Ta tsorata sosai, idonta ya ciko da hawaye "dan Allah kiyi hakuri kar ki kashe ni, wallahi ba laifi na bane
ba, yace kuma in na gaya miki sai ya kashe ni" nace "laifin uban waye to? Huh? In baki gaya min ba ni
kuma zan kashe ki din, ko ki mutu yanzu ko kuma ki mutu in ya kamaki sai ki zabi daya"
Cikin rawar murya tace "sau daya ne wallahi, kuma ba laifi na bane ba, shine yazo ranar nan ba kya nan,
yace in bashi kaina zai bani kudi, yace kuma in ban gaya miki ba zai aure ni, yace kuma in na gaya miki zai
kashe ni"
And that was my limit..........................
Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din
08067081020
Please banda kira, WhatsApp only
*From the readers*
Kamar yadda nace zan ke kawo labarai daga masu karatu, wadanda suka shiga exact or similar situation
as Jidda, tare da fatan sauran masu karatu zasu dauki one or two lessons from them. Please mutanen
nan suna cikin groups din mu, in kin san ba zaki fadi alkhairi ba dan Allah kiyi shiru.
*1*
Assalamu alaikum
sannu d kokari mm... jidda jarabawarta kennan Allah ya Bata ikon cin shi with Straight As amin..
Waenda ke magana ga jin Dadi ga daula Basu taba shiga irin abun bane so bazasu gane ba amma koni na
salamawa umar🤮💔💔 Don abun nashi God forbid it...
Na samu kaina a same situation, Nashi was drugs 💔💔💔sai already he was a womanizer dama, so abun yayi
Mana yawwa😰. babana kaman na jidda shima d munyi dare ya Fara sunturi kenan😃 Yana tsoron a koro
mashi 'ya gida. Nima na gwada gayawa mamansa case din drugs din tun sanda ya fara dan muyi tacling
matsalar da wuri, sai na dauki waya na kirata nace idan wane ya kwanta tun jiya sai ya wuni bai sallah,
abun babu dadin Fadi, d ta dauki waya tace Mai kazo Ina nemanka sai Yana ta gujewa d ta gaji d rashin
zuwanshi sai tace toh ai sai kazo Don matarkace ta kawo kararka, baya gida sai ya dawo wai me kikace
ma Haj nace me kuwa? Sai ya kirata sai ta Soma cewa ita me tace nace, kuma babbar mace ce sosai da
shine karamin danta, yaje ya gaya mata karya da gaskiya ni ban san me suka yi ba tunda bana gurin, a
rannan ta ce wai ai bana kiranta sai zan tayar nata d hankali🙄🤔🤔 nace ni kuwa yar mama d baba ban Kara
kiranta na daina...muka koma kaman jidda d mama🥴 daga nace ki Fadi ma danki gaskiya d tun a lokacin
anyi bincike d ba a kai nan b.... Kaman yanda mama