Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
bata lokaci Mansoor, a lokacin za ka yi kokarin kaga ka nemi gafaranta yanzu adadin kwanakin da ka ƙara adadin ɓacin ranta a kanka, Maza mu je cikin gida ka duka ka nemi gafaranta."
Kafa da kafa Baba Ɗanjuma ya tasa shi har falon Inna Meri ta na zaune tana kallon Tibi tunda akwai wutar nepa. Walida na kwance kan kujera tana game da wayar Inna.
Sautin waƙa kuma na tashi daga ɗakin Matar Saddiqu haka take duk dare ta hana mutane sukuni.
Bayan sun shigo Walida ta mike tana gaishe su Baba kaɗai ya amsa ban da uban gayyar, Inna Meri ko mijinta kaɗai ta yi ma sannu da zuwa Mansoor ko kallo bai isheta ba.
Sun zauna kenan Shi Baba a saman kujera shi kuma Aji a ƙassn cafet.
"Daga ina wannan sautin ke fitowa?
Baba ya faɗa lokaci ɗaya yana kallon Inna Meri wacce ta yi kamar ba ta ji ba,Junoir ne kan jikinta ya yi barci shi kawai ta gyara masa kwanciya ta cigaba da kallon shirin gata nan gatan nan ku da ake haskawa a Karamchi tibi. Walida ce da ta kawo musu ruwa ta ce"Baba ɗakin Matar Yaya Saddiqu ce wlh tunda ta dawo wannan bangaren ba ta barin mu yi barci da saka kide kiɗe. Da Inna ta yi mgana sai cewa ta yi nan gidan Mijinta ne ba wanda ya isa ya takura mata."
Mansoor ya ji ransa ya baçi sai dai bai yi mgana ba ganin Baba ya yi shuru kawai bai ce komai ba Domin magajiya ta fi karfinsa har barazana ya yi mata na saki amman ta nuna bata damu ba sannan Inna Meri ta ce kada ya hana natar Saddiqu tarewa domin Allah kar ya sake mgana shi kuma yana ganin darajan Inna shi ya sa ya yi shuru.
"Je ki faɗa mata ta in ji ni na ce ta kashe sautin nan, ko ba ta san dare ya yi ba ne?
Baba ya faɗa cikin nuna ɓacin ransa, sai Walida ta amsa da toh, har za ta fita Inna Meri ta dago tana faɗin" Walida dawo abun ki, kyaleta Mallam ai gaskiya ta faɗa nan din gidan mijinta ne, ni ban isa na takura mata ba."
"To Inna ke sa'arta ne da za ta gaya miki haka? Ko ba ki isa ki ce ta daina abin da take yi ba ne?
Mansoor ya faɗa ransa bace, Inna Meri ta yi mirmishin takaici kafin ta ce" ta isa ne shi ya sa ta faɗi haka, me ya sa zan damu? duk wa ya ja min? Ɗan da na haifa ne da cikina ya sa na koma abun cin mutumcin acikin gidan nan tunda ko shima bai ɗauke ni wata aba mai daraja ba, to tunda ɗan da na haifa bai ganni da daraja ba wa zai kake tunanin zai kalleni da daraja?
Ta faɗa cikin jin ƙuna a cikin ranta.
"Ki yi haƙuri Inna.."
Ta yi masa shuru kamar ba ta jisa ba. Sai da ya ƙara faɗin" Ki yi haƙuri inna don Allah ki yafe min."
Sai a lokacin ta juyo tana kallon shi kafin ta ce" Haƙurin me kake ba ni? Ka min wani laifi ne? Ba ka min komai ba ta shi ka yi tafiyarka sabogiginka Allah ya yi albarka."
Ta faɗa lokaci ɗaya tana kokarin ɗaukan Junoir da ke kwance saman jikinta,
Da sauri Baba Danjuma ya ce"Ki yi haƙuri Meri ki tsaya ki saurare shi, tunda har ya gane kuskuren shi ya baki haƙuri domin Allah ki daina fushi da shi"
Inna Meri ta yi shuru ba ta yi mgana ba, Baban Inna na ta ban hakuri Baba Ɗanjuma na tayasa sai kawai ta ce"Ni fa ban riƙe shi ba. Har ga Allah na yafe masa Saboda ɓacin raina zai iya jefasa cikin bala'i, hannuna ne na ce na cire a kan rayuwarsa ya je ya yi duk rayuwar da ta yi masa dai dai."
Baba Ɗanjuma ya ce"To baki hakuran ba kenan?
" Wlh na yafe masa tuntuni a cikin raina."
"To in har kin yafe masa ina nema masa alfarman ki shirya ki je gidan Hajiya ki yi masa bikon matarsa."
Dariyar nishaɗi inna ta saka kafin ta ce"Au an zo wajen kenan? Tana gama faɗin haka ta mike ta sunkunci Junior lokaci ɗaya tana faɗin" Ai ya ce ba ya sonta shi ya sa ya ce ta tafi gidansu, in ya ga dama ya sake ta duk ban damu ba ni abu ɗaya ya dame ni yadda ya ɓatamin suna ya sakani jin Kunyar yarinyar nan da Iyayenta, Amman ni ban damu da duk abin da ya aikata ba wannan rayuwarsa ce abin da ya fi masa daidai shi zai yi."
"Ki yi hakuri Inna."
Abunda Kawai Mansoor ya ce kenan, Baba Danjuma a ka bar shi da cewa" ba ki dai yafen ba kenan?
Inna Meri ta ce"Na yafe masa, amman wallahi tallahi kafata ba za ta taka gidan su Binta da sunan yi masa biko ba. Shi ne ke auran nan in har ya na son natarsa yana da Kafa kuma ya san in da zai sameta amman in ni yake Jira to ya daina jirana na yi rantsuwa ba zan yi kaffara ba, ba in da zan je"
Tana gama faɗin haka ta shige cikin uwar ɗaka in da Walida ke kwance ta kasa kunne tana ganin Inna ta shigo sai ta yi barcin karya.
A ranta ko daɗi ta ji wlh kada Inna ta je, shi da ya aikata barnansa ya je ya gyara da kansa.
Ganin Inna ta shige ya sa Baba ɗanjuma ya kallesa kafin ya ce"Tunda ta na ce to ba za ta je ba, ka shirya ka je ka yi bikon matarka ka ji ko?
Cikin jinjina kai ya ce"In sha Allahu Baba., daman ai tsakanina da Mimi ba saki, amman za ta iya yin yaji wani lokacin in bukatar hakan ya ta so."
Kai tsayen shi ya faɗi haka, kuma har acikin zuciyansa haka yake nufi.
Sai Baba Danjuma ya ƙara faɗin" Ko kuma in za ka je ka min mgana sai mu tafi tare"
Da sauri yac e"A'a Baba kada ka damu ba sai ka je ba."
"Ka tabbata?
Sai ya gyaɗa masa kai, shi kuma sai ya dafa kaffaɗansa kafin ya ce"Sannan ka yi hakuri akan abubuwan da suka faru, kasan halin magajiya ita ta saka rigimar dawowar Matar Saddiqu ɗakin Fatima, yanzu in za ta dawo a ina za ka ijiye ta?
Mirmishi ya yi kafin ya ce"Wajen zaman ta ba matsala ba ne Baba, bakomai na gode ƙwarai Allah ya ƙara girma."
Baba Danjuma ya amsa da Amin bai daɗe ba ya ce zai tafi 30k ya ba ma Baba ya ce Auwalu zai kawo kayan abinci na wannan Watan Baba Danjuma nata godiya har ya tafi Inna Meri ba ta fito ba, ga shi ya na jin yunwa amman kuma yasan yau Inna ba za ta basa abincin ta ba.
Da ya fito ya tsaya jim ya na kallon ƙofar ɗakin Mimi, na wani lokaci sannan ya kaɗa kai ya fice, dole zai ɗauko mataki daga Saddiqun har matarsa ba su isa su raina masa uwa ba.
Bayan fitan sa ma Baba Ɗanjuma da kansa ya tsaya kofar ɗakin ya yi ma Maaeesha mganar ta kashe wannan Sautin ba ta da yadda za ta yi dole ta kashe, Saddiqun baya nan ya koma Lagos daga nan ya shiga ɗakin Magajiya ya ja mata kunne ya ce ta yi mata Surukarsa mgana wlh baya son diɓan albarka ta daina takura ma Meri da daddare da sautin banza in ba haka ba wlh za ta bar masa gida.
Magajiya ta buga shewa ta ce saboda Meri zai kori matar ɗansa? To lalle kuwa sai dai itama Merin ta bar gidan. Shi dai bai biye mata ba ya fice zuwa ɗakin sa ya barta tana Kumfar baki ko kunyar Mariya dake ɗakin ba ta ji.
Mansoor Aji kuwa yunwa ta saka sai da ya biya ya siya nama da lemu sannan ya koma gidansa, rabonsa da abinci tun eea ɗin da ya sha da safe. Sai da ya yi wanka sannan ya zauna ya ci ya ɗora da lemu.
Tunaninsa yadda zai tunkari Mimi ne, Dama tuni ya ke so kiran ta amman ba shi da dalili amma tunda yanzu Baba ya yi mgana ya samu abun fakewa.
Yana kwance daga shi sai hajeren wando ba riga ya ɗauki wayarsa ya laluɓo Lambar Mimi da ya yi mata saving da LIFE PARTNER , Sunan ba iya rubuce ba ne har a gaske ma itace cikon rayuwarsa, ba wanda yasan ma sunan da ya saka mata wayarsa kenan hatta ko da ita kanta.
Yana kiranta sau ɗaya ya dauka da rawan jiki za ta ɗauka sai ga shi sai da ya yi mata Missed call biyar ba ta ɗauka ba, kuma shi ya san ba ta da ɗabi'an barcin wuri yana da tabbacin Idanuwanta biyu.
Nan da nan wata zuciyar ta harzuƙa shi, kamar shi Mimi za ta yi ma wannan wulaƙancin?
Sai kawai ya shareta bai ƙara kira ba amman kuma ya kasa sukuni har ya kwanta amman ya kasa barci yana ta juye Juye.
Sai kawai ya sake ɗaukan wayan ya ƙara kiranta har sau uku ba ta ɗauka ba.
Saboda ɓacin rai har wani duhu duhu ya fara gani kawai sai ya shiga wajen saƙo ya rubuta mata haka.
"Ni ne za ki wulaƙanta Mimi? ni ko? To ya yi miki kyau."
Ya gwada ne domin ya samu tabbacin tana ganin nashi ko ba ta gani ba?
Hasaahen shi ya zama gaskiya domin ba daɗewa, sai ga martanin saƙon ta.
"Maganar saki ne? Kada ka damu za ka iya turomin ta text nassages, ko kuma ka aiko min da takardata gidan Hajiya ko wajen Daddy."
Idanuwansa har rawa suke yi da ya karanta ßakon Mimi, bai san lokacin da ya yi mirmishin takaici ba, lalle ma wannan yarinyar da shi za ta yi wasaa ko?
"Ina jiran sammaci ne."
Abin da ya aika mata da shi kenan, amman ha wajen bayan awa ɗaya waya na hannunsa ya na gadi amman ba ta dawo masa da amsa ba.
"Kin yi shuru? Ko kin fara karaya ne?
Haka ya sake turamata nan ma shuru. Sai ya koma ya sake kiranta kawai sai ya ji ta danna masa lamba busy.
Wayar ya bi da kallo a fili ya furta" Kan uba can!"
Haka ya faɗa, har ya na wani hararan wayarsa, wai shi ne Mimi ta kashe ma waya? Wasa wasa kasa sukuni ya yi yana kwance yana ta juye Juye ya kasa barci har cikin dare sai da ya tashi ya kara kiram Mimi ba ta ɗauka ba har asuba ma sai da ya kara kiranta ta kuma ƙara danna masa busy
Ransa ya kai kololuwar ɓaci.
Yana kiranta yana Hargagi shi kaɗai.
"Mimi ki ɗaga kiran kafin ranki ya ɓaci."
Amman ba ta ɗaga ba Daga karshe ma wayarta a kashe ya ji. Haka nan ya shirya ya tafi camp suna da morning traning, amman kowa ya gansa yasan ran maza a ɓace ne daga can gida ya wuce ya gaida Inna Meri amman tunda ta ce lafiya lau ba ta ƙara masa mgana ba haka ya gama zamansa Shuru kuma ga shi ya na jin yunwa amman Inna Meri ba ta bashi Koko da Kosan da ta yi ba, har ya gaji ya yi mgana kaii tsaye Inna Meri ta ce ya kare kuma yana ganin shi ga shi a fulas tunda a gabansa ta juye.
Daga nan yasan saamun Kwanciyar hankalinsa da kuma ganin farin cikin Inna shi ne ya je ya samu Mimi su yi mgana.
Yana durkushe a gaban ta ya ce"Inna yau zan je na samu Mimi mu yi mgana za ta dawo in sha Allahu."
In dutse na mgana to Inna Meri ta yi mgana haka ya kwashi sanyin jikinsa ya fice. A tsakar gida ya ga Maeesha kazama ce ta fito daga ɗaki ta na tsintar da yawu nan kofar ɗaki, kusan amai ya tashi yi kallo ɗaya ya yi mata ya fice ganinta ma ya sa ya tuna da Maganar da ya ce zai yi ma Auwalu.
Yana hanyar komawa gida ya kira shi ya gayamsa cewa ya ja ma ƙaninsa kunni ya tsawatar ma matarsa domin Inna Meri ba sa'arta ba ne, in kuma bai iya ja mata ba to shi zai yi abin da rayuwaka za su ɓaci, Auwalu ya ba shi hakuri ya ce zai yi mgana da Saddiqun.
Shi daman yasan wannan zaman ai ba za'a wanye lafiya ba.
A daran ya so zuwa gidan Hajiya da fakewar ba zuwan kanshi ba ne saboda Inna ne da Baba Ahalin zuwan kanshi ne, domin har a daran ya kirata a kashe, Bai samu zuwa ba saboda ya samu wayar Coach Team ɗin kwallon kafa na Anguwan Jeka da Fari suna bukatar a shirya musu wasan sada zumunci da Team ɗin Tudun wada, kuma a matsayin sa na Captain na Gombe united gabaɗaya yana kula da sauran kananun Team din dake Jiharsa, abin da ya ɗauke masa hankali kenan da zuwa Gidan Hajiya in ya fita tun safe sao dare ba ya samun zama.
Sai da aka shirya wasan da za a buga a Stadium ɗin su na cikin gari, sannnan ya samu kansa, kwana huɗu tsakanina ya shirya da Daddare saboda har a lokacin Inna ba ta masa magana daga gaisuwa shike nan ko a waya ya kira suna gaisawa ta ke ce masa sai an juma, Mu'azzam ma yanzu ya fahimci ya daina goyon bayansa su Nasir daman an yi rabuwan ba daɗi shi zai neme su kuma bai neme su suma suka ce sai dai a dauwama a haka har gwarama Ahmad sun yi mgana sau biyu.
Shigar farar shidda ya yi har da hula, wani farinciki ya ke ji zai je ya ga Mimi amman sai ta raina kanta shi za ta yi ma wulakanci Saboda ta ga yana nin ta ko? To zai gaya mata ba saboda ta isa ba ne, Saboda Inna ne da Baba, Ya tuna har Babansa Kabiru na Bauchi ya kira shi kan maganar abin da ya ba shi mamaki ce masa ya yi ya zo gidansa ya zaɓi mata. Sai ya ce masa ai bai saki matar ta shi ba sai kawai ya ce"To ka sake ta mana, ba an ce ba ka son ta ba?
Cikin mamaki ya ce"In ji waye ya ce ba na son matata?. Kai tsaye ya ce" In ji Gwaggon ka Yalwa ta ce ka ce ba ka son ta ko ƙarya ta yi maka?
Baki ya riƙe ya na mamaki, kafin ya ce"A'a ba ta yi ƙarya ba. Sai dai in ba ta ji da kyau ba, Baba Na gode da yayin ka amman ba na jin bayan Mimi zan iya auran wata macen, matata na sona nina kuma ina sonta, kawai dai akwai dalilin da ya sa abubuwa suka yi faruwa ne, kuma ba laifi ba ne in ka ɓata ma mace rai ta yi yaji, in ta je gida ta huta nima na huta zamu daidaita daga baya.".
Da haka ya samu ya kashe bakin Baban na shi, wai ya ba shi mata? Bai jin ma in ya yi wani auran zai iya yin adalci. Mace ɗaya ce a cikin zuciyarsa tun farko ita ya zaɓa a yanzu ma ita ya kara zaɓa.
Yana tafe ne a mota yana wannan tunanin, Sai ga shi a kofar gidan Hajiya ya yi jon megadi ya leko da ya ga shi ne suka gaisa ya buɗe masa get ya shiga da motarsa ciki,bai yi niyar shiga can ciki ba ba sai ya ɗauki waya ya Kira Mimi amman ba ta ɗauka ba sai ya cije baki ya tura mata saƙo.
"Ina haraban gidan Hajiya ki fito da kayan ki ina jiran ki.".
Shuru shuru sama da mintina ashirin ba Mimi, tun yana mota sai ga shi ya fito, ya jingina da motar ta shi.
Haushin kanshi ya fara ji yadda ya tsaya Mimi na yi masa wulakanci ta manta hala har yanzu shi mijinta ne? Ya kamata ya nuna mata har yanzu tana ƙarkashinsa ne.
Yana wannan tunanin sai ga sakonta ya shigo jiki na rawa ya buɗe.
"Ka shigi cikin gida. Domin ba zan iya fitowa ba."
Ya yi jim yana tunanin wai ita a dole za ta rama ne? Sai kawai ya yi yar dariya ya kulle motar ya nufi hanyar falon Hajiya kofar na kulle sai da ya kwankwasa Baba Uwani ta zo ta buɗe masa tana ganin shi ne ta gaishe shi cikin girmamawa a bakin kofar ya tsaya yana faɗin" Mimi, ki yi mata mgana ki sanar mata ina jiranta."
Ya faɗa yana duba agogon fatan dake tsitsiyan hannunsa na hagu.
Baaba uwani ta yi shuru kafin ta ce"Binta ba ta nan ta yi tafiya. Sai dai Hajiya shigo ciki ka zauna bari na gaya mata zuwan ka."
"Ba ta nan? Ta yi tafiya?
Haka ya riƙa nanatawa a cikin tansa Bai san ma Baba Uwani ta koma ciki ba yana tsaye ne yama jin zufa na keto masa Mimi ta maida shi wani cartoon ne ko kuwa wani sakarai ko sauna? Ba ta nan? To gidan iban wa ta je da auran sa a kanta?
Yana wannan tunanin yaji muryan Hajiya na faɗin" Na yi fushi tunda sai yau nake ganin Megidan nawa."
Dalilin da ya sa ya ɗan saki fuska kenan ya tako kafarsa zuwa cikin falon ya ysaya ya cire takalminsa sannan ya karisa kusa da Hajiya ya zauna a kasan cafet.
Dai dai lokacin da Baaba Uwani ta kawo masa ruwa da lemu da ƙaramin kofi.
*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3005*
*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*
https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC
No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.
Cikin girmamawa suka gaisa da Hajiya,