Idan An Ciza Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   7 / 49

18K to 21K   out of 146.6K words

zai yi mgana sai kawai kuma ya fasa, ya ta shi ya shige ciki jikinsa a sanyaye Hibba ta bi shi da kallo gaskiya magana ce fa sai an faɗa Yaya Mansoor ɗin nan ya cika jinkai da Isa, shi wai ya na takama da cewa Mimi na son shi wato ba za ta iya rabuwa da shi ba. Daman illah ne babba mace ta nuna ma Namiji soyayya mai tsananin da za ta ya iya yin komai saboda shi kuskure ne babba ga Maza ma irin su Mansoor da ba su san darajan da ƙimar da Ubangiji ya ba ma mace ba. Tana tattara kwanukan da suka ɓata ne take wannan tunanin, haba ka yi laifi amman taurin kai da jinkai su saka mutum tunanin kai ne ma za'a ba ma hakuri haka ake yi tsakani ga Allah, gwara Mimin ta sha zamanta sai ta ga karyan tsiya ita dai tasan wlh shima yana sonta in ya ga zai iya rasa ta dole dai ƙanwar na ƙi.

********

*Bayan kwana uku.*

Kimanin Mimi na da kwanaki takwas kenan a gidan Hajiya, Rukky ba ta sani ba saboda Bibi ba ta sani ba domin haushi ya sa Makama bai gaya mata ba, Sannan Mimi na cikin hutun ta ne, ba ta zuwa wajen aiki kuma ita ba ta dame ta a waya ba tunaninta yanzu ba da ba ne, Mimi na da aure ita ba ta san ta na yawan kiranta saboda wannan mara mutumcin mijin nata.

  Ranar tana wajen aiki Na Misau na zencen Mimin sai ta ɗaga waya ta kirata amman Sai ba ta same ta a waya ba sai ta yi tunanin in ta tashi daga wajen aiki za ta biya ta dubata, la'asar ta baro ma'aikantarsu ta hau adaidaita zuwa Gidan Wanzamai a kofar gida ta haɗu da Baba Danjuma a lokacin su ka gaisa, shi kuma bai yi mata wani bayani ba sai da ta shiga gidan, abin da ya bata tsoro shi ne ganin wata a ɗakin Mimi, Saboda lokacin da ta shigo Inna na ɗakinta, Walida kuma ta tafi makarantar Islamiya.
Shi ya sa ta shiga ɗakin Mimin kai tsaye sai kawai ta ga komai ya sauya har da mai ɗakin ma gabaɗaya.

  Cikin mamaki ta ke kallon Maaesha kafin ta kara komawa baya a tunaninta ko ta yi makuwan shashen ne. Sai dai ta ƙara ganin tabbas nan ne.
Cikin mamaki ta ce"Ko na yi makuwa ne? Ba nan ne ɗakin Mimi matar Mansoor ba?
Maeesha na zaune ta na cin Aya ta yi waata yar dariya kafin ta ce" A da ba, amman yanzu ya zama ɗakin Maeesha matar Saddiqu."
Rukky ta yi shuru tana kallon Maeesha cikin tarin mamaki, amman ba ta sake mgana ba gabanta na faɗuwa ta fita daga ɗakin rike da wayarta tana ƙara kiran layin Mimi sai kuma ta shiga dalilin da ya sa ko ɓarayin dakin Inna Meri bata kallah ba.
Allah ya taimake tana fita sai ta ga mai adaidaitan da ya kawo ta bai tafi ba ya tsaya mgana ta waya sai kawai ta faɗa ciki dai dai lokacin da Mimi ta ɗaga kiran Rukky.

"Baby Ruƙayya.."

  Mimi ta faɗa cikin sanyin murya, Ita kuma Rukky Kamar zuciyar ta za ta fito waje ta ce"Fatima kina ina ne? Na zo gidan mijin ki a ɗakin ki na ga wata, ko kin ta shi ne ban sani ba?
Mimi ta yi dariya daga bangarenta kafin ta ce"Eh! Ina gidan Hajiya ki zo ki same ni."
Cikin faɗuwan Gaba Rukky ta ce"Mimi me ya faru ne? gaba na faɗuwa."
"ke dai ki zo, ba komai sai alheri."
Daga haka ta katse wayar,  Rukky gabaɗaya sai da jikinta ya yi sanyi, mai adaidatan na mganar Hajiya komawa za mu yi? Tace Eh amman yanzu anguwan Hashidu Estate za su je, nan da nan ya juya kan adaidata suka nufi gidan su Hajiya.

  A Gaggauce Rukky ta shigo, gidan Hajiya na falo Baaba Uwani na kitse mata kanta da ya cika da farin ga shi. Tsabar ma ruɗewa da gaisuwan da tambayan Mimi duk a lokaci ɗaya ta yi su, Hajiya ta ce tana ciki ta shiga ta same ta ai ko har da gudunta ta wuce Hajiya da Baaba Uwani suka bi ta da Kallo Hajiya ta girgiza kanta kafin ta ce"Ina ga ta ji labarin Binta na gida"
Baaba Uwani ta ce"Hajiya yanzu ba za'a gyara lamarin nan ba?
Hajiya ta ce" To Hamza ne kan batun ya ce na cire bakina, sai in har Mijin Binta ya tako da kansa sannan za'a yi maganar gyara."
Baaba Uwani ta yi shuru kafin ta ce" kuma bai zo ba ko? Ni fa kamar sau ɗaya ma na taɓa ganinsa tun bayan auran nan."
Hajiya ta jinjina kai kafin ta ce"Zuwan na shi bai wuce ɗayan ai zuwa biyun."
Baaba Uwani na son cigaba da Magana amman Hajiya ta kauda mganar ta fara mata zencen mutanen can garin su na Akko sai su saki hiran Binta suka kama ta mutanen gida.

  Mimi na kwance ta na latsa wayarta Rukky ta faɗo ɗakin cikin damuwa. Kamar ta faɗa kanta haka ta faɗa saman gado tana faɗin" Kar dai ki faɗa min kun rabu ne?
Mimi ta miƙe da sauri ta na faɗin" Rukky me ye haka? Kin bani tsoro wlh."
Ba ta damu ba sai ma gyara zama da ta yi ta na faɗin" Don Allah ki gayamin abin da ke faruwa ko zan samu natsuwa."
Mimi ta yi shuru kafin ta ce" Eh mun rabu amman ba mu rabu ba."
"Ban gane ba?
Rukky ta tambaya cikin zullumi.
Sai Mimi ta gyara zama tana faɗin"Rukky labarin na da tsawo amman takaice shi ne na dawo gida ne.

"Saboda mene?

  Ta tambaya tana mai tsare Mimi da ido, ita kuma ta kauda kanta saboda Idanuwanta sun fara tallah kwalla, babban baƙin cikinta yadda ta fahimci ba ta da wata faraja a wajen Aji kwananta takwas da dawowa Gida amman ko kiran ta bai yi ba, ba Saƙo ba zuwa kenan ya nuna ma kowa cewa bai Damu ba da zamanta da tafiyarta duk ɗaya ne a wajensa.
Kawai sai ta saka ma Rukky kuka, ita kuma baki buɗe take kallonta kafin ta ce"Mimi me ya faru ne? Ki bar kukan nan ki yi min bayani domin Allah."
Miƙewa Mimi ta yi zuwa gaban window ɗin da ke ɗakin lokaci ɗaya tana faɗin" Ruƙayya ban taɓa tunanin hukuncin da na yanke ma rayuwata na auran Aji kuskure ba ne sai yanzu, na yi gaggawa me ya sa bayan na ciza ban tsaya na hura ba? Rukky Aji ba ya sona iya wancan Soyayya na yarinta ta gushe a zuciyarsa ya aure ne kamar zai rama abin da Abi ya yi masa a shekarun baya, Rukky Aji baya sona tunda na aure shi bai taɓa kama hannuna da gangan ba sai dai bisa Kuskure."
Ta yi shuru ta na sauke numfashi Saboda kuka ne ke cin zuciyarta.

  Rukky ta yi kasaƙe tana sauraran Mimi cikin mamaki ta ce" What? Hoto kike a wajen sa?
Mimi ta Juyo tana fuskantar Rukky kafin ta koma ta zauma kusa da ita, ita kaɗai ce aminiyarta sai ta ji tana son gayamata abin da ya faru tun farko har zuwa karshe..
Sai ta samu kanta da fara ba ma Rukky labarin auran da Aji har zuwa abin da ya Faru ta dawo gida amman ta sakaya yadda ya ke cin zarafin iyayenta ta dai nuna mata ba shi da zuciya mai kyau tunda bai san afuwa da yafiya ba sannan ya na amfani da abin da ya faru yana mu'amalanta da shi.
Cikin Kuka Mimi ta ce"Rukky da kansa ya ce na tafi din ya nuna bai damu ba, yau kwana na takwas a gidan nan bai kirani ba sannan bai zo ba,  ƙannensa ma da suke zuwa da abokansa wah sun yi ne domin suna son aure da shi ba saboda shi ba. Na rasa wani irin miji nake aure? Wlh Ajj ya sauya a baya ba haka yake ba Rukky, ina son mijina amman ya zama dole na yi nesa da shi ko zai fahimci Muhimmancina a rayuwarsa."

  Ta ƙarishe faɗa tana gunjin kuka, Tausayinta ya kama Rukky sai ta kama ta Rumgume tana bubbuga bayanta alamun lallashi, har sai da ta yi shuru sannan ta dago kanta suna fuskantar Juna Rukky ta fara faɗin" Na ji daɗin yadda kika nuna masa ke ma macece, sannan na ji daɗi da Daddy ya goya miki baya sannan na ji daɗin yadda baki saurari ƙannensa da abokansa ba, Ire iren mijin ki Fatima yan burauba ne hanyar Sauƙi ba ta bille musu sai an biyo musu ta bayan gida, Na fahinci wlh ƙarya yake yi yana sonki in baya sonki ba wata Hajiya ko Mommy da yake gani da mitumcin da saboda su zai aure ki. Sai dai tsabar bakar zuciya da Tunanin banza ya sa yake ta gasa miki aya a hannu kuma ya yi anfanin da cewa kina son shi duk kashin da zai yaɓa miki ba za ki iya ɗaga kai ba, To Wlh ya yi karya har shi ya isa? Mimin ce zai yi ma wannan cin zarafin? Kinga share hawayen ki na rantse da wanda raina ke hannunsa sai Aji ya zama a tafin hannun ki, sai Aji ya nuna ma duniya kece mace mafi daraja a wajensa, Wlh tallahi sai kin rama kwatakwacin abin da ya yi miki kila ma fiye da wanda ya yi miki. Sai ya wahala sai ya raina kansa sai ya yi laushi sai ya yi la'asar ba tun farko ya ki sharen masallaci ba, to ai yanzu ina baki tabbacin zai yi na kasuwa sai mun saka shi ya ƙasƙaatan da kanshi in da yake tunanin ya fi karfi sai Aji ya zo ya duka yana miki magiyan da roƙon ki dawo cikin rayuwarsa ke kuma a lokacin kike da damar rama duk abin da ya yi miki har ma fiye da hakan."

  Har Rukky ta gama maganarta kallon ba ki da hankali Mimi take yi mata.
Kafin ta girgiza kanta lokaci ɗaya tana faɗin" Ba ki da hankali Rukky Ajin ne duk zai zauna na yi masa haka? Ke wai duk ba ki saurari labarin da na ba ki ba ne?  Nan matar ƙaninsa Hibba ba abin da ba ta ce na yi ba amman daga karshe me na samu? Bayan cin mutumci da wulaƙanci.?
Rukky ta bigi Kafaɗan Mimi  lokaci ɗaya tana na faɗin" ke dilla gafara can, kina wani abu kamar  ba mace ba, wa ya gaya miki ba abin da kika samu? Kin samu mana ke ce ba ki fahinta ba amman tabbas Aji na sonki so kuma mai tsananin da shima ba zai iya rayuwa ba sai dake. To tunda ya yi kuskuran bari mu ka sani ya shiga uku, Ajin banza ajin wofi, ai sai dai ya cigaba da amsa wannan sunan a waje amman a gabanki sai dai shi ya zama Ajin waje ke ki zama ajin cikin gida, na yi rantsuwa ko Kaffara ba zan yi ba yana can cikin tunaninki ya tsaya ne yana tunanin za ki neme sa ku daidaita, yana tunanin kina son shi saboda haka ba za ki iya dogon fushi da shi ba to ya yi kuskure, tabbas sai kin rama tabbas sai ya gwammaci YA CIZA ya hura kafin ya ƙara aikata laifi mai kama da wanda ya aika miki a baya tabbas zai gane kuren shi duk wannan jin kan da bakar zuciyar da wani jin haushi sai ya sauke shi, shi ɗin banza da Wofi tunda dai yana son mu ai kuma ya tashi  aiki."

  Irin yadda Rukky ke mgana cikin ƙwarin gwiwa ya sa Mimi sai da ta yi dariya kafin ta jinjina kai tana faɗin" Ruƙayya ba irin su Aji ake yi ma haka ba, Da bakin shi fa ya ce ba ya sona alfarman rokon su Hajiya ya sa ya aureni, to a haka ne kike tunanin wai zo ya na roƙo na? Rukky ba ki san Aji ba ne shi ya sa."

  Rukky  ta kalli Miki cikin tausayawa kafin ta murmusa lokaci ɗaya tana cewa"Ƙarya fa yake yi, duk kalaman da ya faɗa miki karya ne, kuma zai ƙaryata kansa da kansa a gabanki nan ba da jimawa ba."
Mimi ta karkace kai kafin ta ce"Rukky ba na tunanin haka, ni nasan wanda nake aure Rukky"
Rukky ta ce" Ki yarda da ni, ni kuma na yarda da kaina, amman kafin nan ya kamata ke ma kinsan kuskuren ki a kan wannan lamarin gabaɗaya."
Mimi ta kalli Rukky amman ba ta yi mgana ba sai Rukky ta kama hannuwanta ta rike lokaci ɗaya tana faɗin"In har kin yarda dani to ina ba ki tabbacin Aji zai zo da kafarsa, sannan zai ta bulayin neman ki, zai iya yin komai saboda ke Mimi."
Mimi ta yi shuru ta na kallon Rukky itama ta na kallonta na wani lokaci kafin Mimi ta Sauke ajiyar zuciya tana faɗin" Shike nan na aminta dake, amman sai na k..

  "Shii..., Ki yi shuru kawai, kawo kunnen ki ji."

  Rukky ta faɗa dai dai tana jawo kunnen Mimi ta yi mata mgana na tsawon mintina goma sannan ta sake ta. Sannan lokaci ɗaya suka koma suna kallon juna, Mimi ta ɗage giranta sama kafin ta ce" Are u sure Ruƙayya? Rukky ta amsa mata da ceewa"very very sure.."
Hannu Mimi ta ba ta suka tafa lokaci ɗaya tana  faɗin" Yoh have my word, zan yi gwargwadon abin da kika ce."
Ita kuma Rukky sai ta aika mata da Jinjina tana dariya.
Mimi ta sauke numfashi, kafin ta ce"Sai yanzu na ji na samu yar natsuwa, ina jin ki faɗamin kuskurena, ni kaina nasan ai na yi gaggawa." Rukky ta gyara zama L
lokaci ɗaya tana faɗin" kuskuren ki guda ɗaya ne, na yadda ki ka nuna masa kina tsananin son shi, za ki iya komai saboda shi, kin nuna masa sai da shi za ki iya farinciki, r da wannan damar ya samu yana miki yadda ya ga dama, da wannan damar ya ke tunanin zai iya yi miki komai ki shanye, a tunaninsa saboda kina son shi zaki iya jure duk mganganun da zai ga ya miki, yana tunanin ko dukan ki yake yi  ba za ki iya ɗaga kai ba. Shi Namiji ba ka nuna masa ka mutu saboda Son shi, ko kana son shi sai ka koyi iya Sarrafa soyayyar ta yarda ba zai zama makamin da zai samu galaba a kan ki ba, amman ko a yanzu lokaci bai kure miki ba za ki iya gyara abin da ki ka ɓata tun farko." Mimi ta sauke numfashi kafin ta ce" Tabbas kin yi gaskiya,  da wannan damar ya samu galaba a kaina ya ke tunanin ko ni ce ya yi ma ba dai dai ba sai dai na yi hakuri na bi shi tunda Ina son shi, to ya yi kuskure daga yanzu zai fahimci hasashensa ba gaskiya ba ne."
Rukky ta ba ta hannu suka tafa lokaci ɗaya tana faɗin" Thats my Girl."

  Zuwan Rukky ba ƙaramin garinciki ya kawo ma Mimi ba har su Hajiya na Jiyo hiransu da shewan su. Sai bayan isha'i Rukky ta tafi bayan ta ci abinci ta yi sallah Sannan su ka yi sallama da Mimi akan sai sun yi mgana ta waya su kaɗai suka san irin muguntar da suka shiryama Bawan Allah Baban Inna.
A baya ba ta cika barin wayarta na awa huɗu a kunne ba amman yanzu da shawaran Rukky da ta ce ta daina kashe wayarta tun ba karya ta yi ba. Ta riƙa barin wayarta a kunne amman kada ta amsa kiran yan koran Aji ta bari shi Ajin da kansa ya kawo kansa sannan.
Shi ya sa har Mu'azzam da su Nasir ta rufe su ko sun kirata ba za su sameta ba a daran ma sai da su ka yi waya da Mommy itama abun ya ba ta haushi da Mimi ta ba ta tabbacin Mansoor bai kira ba kuma bai zo ba. Cikin ɓacin rai ta ce"Na fara yarda da Maganar Alhaji Hamza, in bai kira ba kada ki kira shi in bai zo ba, ba za mu bi shi ba sannan ba za ki koma ba in watanni uku suka cika kotu zan kaisa ya sauwaƙe miki tunda bai san hallaci da mutumci ba."
Kenan itama Mommy ta fara Dawowa daga rakiyarsa Hajiya dai yar cewa a bi komai a sannu.

*******

Har aka shafe wajen sati biyu da komawar Mimi gidan Hajiya, Ba Mansoor ba ƙeyarsa bai ƙara tako kafarsa gidan Inna Meri ba, ita kuma daman ta ce ta cire hannunta a kansa.
Baba Ɗanjuma ne yaga rashin jankalin Mansoor ya yi yawa sai ya kira shi a waya yace duk abunda ya ke yi yau da daddare ya zo gida ya same shi.
Sai ya amsa masa da toh, shi kuma daman Kunyar Inna meri yake ji, yana so sai ta fara hucewa sannan yana fargaba ya shigo gidan ba Mimi a cikin shi. Har gabansa faduwa yake yi in ya tuna bata nan bayan ganinta a cikin gidan ƙarƙashin Inuwarsa Kuzarinsa har karuwa yake yi in ya shigo gidan ya ganta, yana so ya kirata amnan kuma yana tunanin in ya kirata kenan ta yi nasara shi ya sa yake iya sarrafa damuwarsa amman shi duk a tunaninsa Mimi za ta dawo domin kanta bai taɓa tunanin za ta iya ba shi Wahala ba.

  Wajajen karfe tara ya zo anguwan a mashin ɗin haya saboda motarsa sai an mata juye, mashin kuma duk ya yi kura tunda ya daɗe bai yi amfani da shi ba, Sai kawai ya hayo na haya ya zo a kofar gida ya iske Baban Danjuman na jiran shi, ya san akwai mgana aiko ya sha faɗa kamar zai dake shi yana kuma nuna masa illar abin da ya aikata Mahaifiyarsa na fushi da shi amman ya nuna bai damu ba.
Kansa na ƙasa ya ce"Na damu mana Baba, kawai dai na ga ranta Inna  ya ɓaci sai na bari a ɗan kwana biyu in ta ƙara hucewa sai na zo na bata hakuri."
Baba kamar ya kai masa duka cikin takaicinsa ya ce" Haba Baban inna ina tunaninka yake ne? Ita uwa in ta yi fushi ba ta bukatar a

7 / 49