Idan An Ciza Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   6 / 49

15K to 18K   out of 146.6K words

da sura mai jan hankali maza. Wata zuciyar ta ce" Ba yana kishin ki ba? Sai kuma a zuciyarta  ta ce kishin banza da wofi ba shi da amfani a wajenta yanzu.

  Jin daɗin ma tana Annual Leave ne, shi ya sa ba ta aikin komai a gida sai kwanciya da tunanin. Tuni ta daɗe da blooking ɗin duka lambobin yan gidansu Mansoor domin ba ta so ma ta ɗauka a roketa abin da ba za ta iya ba, Ko Rukky ba su yi waya ba ballantana tasan abinda ke faruwa ra bon ta da mgana da ita tun ta na Abuja, kila za ta yi tunanin ba ta dawo ba ne. ita kuma ba ta so ma  ta sani saboda surutun Rukky ne ba ta so, daman itama tana daga cikin ƴan adawa da auran.

******

Bangaren Mu'azzam kuma tun da ya sauka garin yake lallashin Inna da ban baki da roƙon ta domin Allah ta shirya ta je gidan Hajiya ta ba ma Mimi hakuri ta dawo, haka duka yaran suka haɗe mata kai, ita kuma ta yi rantsuwan cewa ba in da za ta je suma kuma duk wanda ya je ba ta aike shi ba.
Abin a ya fi bata musu rai ma shi ne a ranar asabar da safe aka fara kwaso kayan Maeesha zuwa ɗakin Mimi ba sanarwa ba komai maza na giftawa, bayan Inna Meri da kanta ta zo ta share ɗakin ta goge.
Sannan ta fito da kayan abincin da aka bari a ɗakin ta watsar nan kofar ɗakin Inna Meri sai da Hibba da Walida suka kwashe suka shigo da su ɗakin Innar.

  Ganin Inna ta cije, domin ita ɓacin ranta ɗaya, yadda shi uban gayyar bai ma san ana yi ba tunda washegarin ranar da ya yi tsiyar bai ƙara dawowa ba to sai ta ga ko an shiga mganar ba amfani zai iya maimaita abin da ya aikata tunda bai san darajan matar ba, Sannan ita da kanta ta kira Alhaji Kabiru babansa na  Bauchi tana gayamasa abin da ke faruwa a tunaninta zai zo garin ya same shi ya yi mishi faɗa tunda ita dai daman ya renata ba ya jin mganarta.
Amman kawai sai ta ji ya ce"Haka aka yi kenan? Daman ai Gwaggon sa Yalwa ta faɗamin baya son yarinyar, kawai ya saketa sai ya zo gidana ya duba mata na aura masa ."
Haushi ya kama Inna to ko ɗiyar Babansa ya aura zai iya yi mata abin da ya fika haka in dai wanna mai bakar zuciyar ne.
Daga nan ba ta kara neman su ba, Domin ta na da tabbacin suma ya fi ƙarfin su.

  Mu'azzam tare da su Yaya Amina suka yi shawara, shi yanzu su Nasir yake jira Ahmad ne yace a jira shi zai shigo garin tunda dukkansu sun ji labari, kuma cikinsu duk wamda ya kira Aji baya ɗaukan wayansa su sun ce za su yi masa ne bisa zaman tare da abokantaka bisa Amana, za su je su yi gamgami su samu Mimi su ba ta hakuri, Sai Mu'azzam yace kafin su je, su matan su shirya su je su gani.
Ba tare da Inna ta sani ba suka haɗu a gidan Bintu domin Hibba cewa ta yi Walida za ta rakata gida ta ɗauko wasu kayan.
Inna bqta sani ba suka haɗu gabaɗayansu Har da Yaya Halima sai gidan Hajiya amman abin da ya ƙara ba su tsoro Hajiya da kanta ta ce musu Mimi ta kwanta kanta na ciwo kuma ba zai yuyu a tashe ta ba.
Zaman kusan awa huɗu suka yi tun la'asar anan ma suka yi sallar mangariba amman Mimi ba ta bari sun ganta ba. daga baya dai suka fahimci cewa Ita ce ba ta son su haɗu.

  Yaya Amina ce ta yi ma Hajiya mganar a yi hakuri abun bai kai haka ba don Allah Mimi ta dawo ɗakinta su suna sonta, Inna ma kunya ce da nauyi suka hana ta zuwa.
Amman sai Hajiya ta yi dariya kafin ta ce" Ayya ni kaina zan so hakan, amman kuma mganar ba ta hannuna tana wajen Binta da Babanta ne, abin da duk suka yanke shike nan."
Fahimtar da suka yi lamarin ya wuce tunaninsu haka suka dawo gidan Inna jiki ba daɗi suka iske wani ƙarin abun haushi ƴan'uwan Maeesha sun dawo da ita sun yi kaca kaca da shashen suna ta shewar su, Inna dai ba ta gaya musu ba ne amman Ko darajan gaisuwa ba ta samu ba.
Sai da suka dawo ne suka faɗa mata abin da ya faru da in da su ka je, Inna Meri ta yi mirmishi kafin ta ce"Sun yi min dai dai, ku kuma Allah ya ƙara sai da na ce kar ku je, wanda ya ɓata bai san hanyar gyara ba sai ku?

  Mu'azzam da ya zo ya ji labarin abin da ya faru sai jikinsa ya yi sanyi, yanzu haka Aji ya bar masa gida shi a Camp yake kwana in kuma ya je da niyyar su yi mgana sai ya ce suna da traning haka dai duk ya shanshantar da maganar Mimi, shi kuma Mansoor tunaninsa ya bi Mimi gidansu ya ba ta hakuri kamar ya sauko ne ya yi Arha, a tunaninsa auranta na hannunsa to zai tsaya ya ga iya gudun ruwanta shi bai ce ta tafi ba, ita ce ta zaɓi tafiya shi kuma ya goya ma zaɓinta baya, kuma ba ya son kowa ya shiga maganar kotun da ta ce za ta kaisa ya ke jira, ɗayan tunaninsa nasa kuma na gayamasa Mimi na son shi ba za ta iya rayuwa ba shi ba, tabbas duk in da ta je ma za ta dawo ko labarin an kwashe kaya bai samu ba balle ya dawo cikin hayyacinsa ya fahimci shirmen da ya tafka yana nan yana shirme da tunanin banza..

  Ahamad ya shigo garin. A kuma daran suka ka haɗu su huɗu zuwa gidan su Mimi, suma ɗin dai Hajiyar kawai suka samu gani, a cewarta Mimi ba ta jin daɗi ta kwanta alhalin tana nan tunda Hajiya ta ce  mata abokan Mansoor ne da ƙaninsa ta roƙi Hajiya da ta ce ba ta garin ta tafi Abuja ita kuma Hajiyan ta ce ba za ta yi ƙarya ba. Sai da Mimin ta marairace tana faɗin" Don Allah Hajiya ki taimaka min, ko na je mun ga juna ba zan yi musu abin da suke so ba."
Dole Hajiya ta fito ta sake ƙaryan Mimi ba ta jin daɗi ta kwanta, Suma sun ta rokon Hajiya suma kuma ta ce magana na hannun Mimi da babanta.
Jin haka ya sa suka ce bari su karisa gidan tsohon Sanatan su gan shi, daga gidan Hajiya can suka nufa sun kuma ci sa'an yana na gidan nan da nan aka yi musu iso zuwa falon da yake ganawa da baƙin sa.

  Shima dai bayan sun gama gaisawa, Nasir ne ke rattaba hawabin ban hakuri Alhaji Hamza ya gama karantarsu duka da jinsu sannan ya gyara zama yana faɗin" To duk na ji bayanan ku, abin da nake son sani shi Mansoor ɗin ne ya aiko ku, ko kuma kune ku ka aiko kan ku?
Daga yanayin yadda suke magana ya sa ya fahimci ba shi ya turo su ba. Sai kawai ya yi wata yar dariya kafin ya ce"Me ya hana shi zuwa da kansa ya yi bikon matarsa?
mu'azzam ke faɗin saboda baya gari sun tafi buga wasa.
Sai kawai Daddy ya ce"Shike nan kun gama naku bangaren a matsayin ku na abokan sa na amana kuma an gode muku, abin da nake  so daku shi ne ku cire bakin ku a wannan maganar shi dai shi ne mijin Mimi in har kuma yana sonta zai zo ya zauna a gabana kamar yadda kuma kuka zo kuka zauna a gaba na.".
Sun san gaskiya Daddy ya faɗa shi ya sa su ka kasa masa musu hakanan jiki ba ƙwari su lka yi masa sallama su ka fito daga gidan a hanya Nasir nata faɗa yana faɗin" Wallahi ni na cire hannuna kuma abin da Baban Mimi ya faɗa mana gaskiya ne, akwai bangaren da mu ba mu isa mu gyara masa ba sai in har ya gyara da kansa."
Ahmad ya ce" Wannan gaskiya ne, shima zuwa yanzu yakamata Aji ya san ya girma ya daina wannan taurin kai."
Makama kuma ya karɓe da faɗin" To wai ba ya son ta ne? In bai son ta ya sake ta kawai kowa ya huta tun da shi girman kansa da jin kansa ya sa har yau bai gane annabi ya faƙu ba."

  Suna tafe ne a motar Mu'azzam, suna wannan mganar shi dai Mu'azzam ya ma kasa mgana Ahmad ya ba da shawaran duk in da Aji ya k a neme shi cikin dare su gayamasa halin da ake ciki.
Mu'azzam ya ce yana Camp ɗin su nan da nan suka juya mota zuwa cikin gari.
Aji na cikin ɗakinsa aka sanar da shi yana da baƙi ya ɗauka Mu'azzam ne sai da ya fito kawai ya ga su Nasir bai yi mamakin ganinsu ba, Sanin halin da ake ciki.
Waje ya samar musu suka zauna saman wasu fararen kujeru Da Ahmad kaɗai suka gaisa Nasir ya fara masa masifan ashe bai ji shawarwarin da ya basa ba.
Kai tsaye Aji ya ce"Naji mana, amman sai zuwa gaba zan yi amfani da su"
Cikin mamaki ya ce"Saboda mene ba yanzu ba?
Aji kuma ba tare da tunanin komai ba ya ce"  To ba ka ga Mimin ba ta nan ba ne? Ka bari sai ta gaji da yajin da ta yi ta dawo tukunna."
Gabaɗayansu baki suka saki suna kallonsa
Makama ne ya daki kafarsa lokaci ɗaya yana faɗin" Kana tunanin za ta dawo ne ba tare da ka je ka ba ta hakuri ba?
Cikin kwarin gwiwa Aji ya ce"Of course.".
Sai kawai Makama ya yi wata dariya kafin ya ce" To in ma kana wannan tunanin tuntuni ya kamata ka daina, yanzu haka daga ganmu nan daga gidan su muke, mun je gidan hajiya Mimi ba ta bari mun ganta ba Hajiya ta turamu wajen Babanta tsohon Sanata, yanzu haka daga gidansa muke muka yo nan wajen ka."

  Cikin mamaki Aji ya ce"Me ya sa kuka je? Na ce ku fita daga wannan mganar."
Mu'azzam ya ce"Yaya me ya sa za ka ce mu fita daga mganar nan? Ko kasan har an kwashe kayan Anty Mami har matar Saddiqu ta tare a ɗakin ta tun jiya."
Aji ya ƙurama Mu'azzam ido gabansa ya faɗi amman bai nuna ya razana ba sai ma kai da ya kauda kafin ya ce" Wannan duk ba matsala ba ne, in ta dawo ba za ta rasa wajen zama ba"
Nasir baƙin ciki ya kusa kashe shi. Da ya sa kawai ya miƙe ya na faɗin"Ku kyale shi ku zo mu tafi, abin da muka yi maka ba saboda kai muka yi ba. Saboda hallacin zaman tare da kuma ƙaninka Mu'azzam, mun je babanta ya ce mun gama namu, in har kana son matarka sai ka shirya ka je da kanka ka ramkwafa ka roke shi, itama Mimin wlh ba za ka same ta sauki ba, in kana tunanin za ta dawo saboda tana sonka ne to ka yi ma kanka ƙarya. Gwara ma ka farka daga wannan mafarkin naka da ba ka da ranar farkawa, in ka tsaya wannan jinƙan kan naka na rantse da wanda raina ke hannunsa  za ka iya rasa ta rasawa na har Abada."

"Nasir..!

  Aji ya miƙe ya faɗa a fusace yana nuna Nasir  shi kuma ko a jikinsa sai ma juyawar da ya yi ya yi tafiyarsa, Makama ma ranshi ya ɓaci shima bayan Nasir ya bi sai Mu'azzam aka bari da Ahmad suna tausan Aji, wanda ransa ya ɓaci wai Nasir na gaya masa zai iya rasa Mimi na har abada.
Cikin haushi ya ce"To sai me in ba ta dawo ba? Ai igiyar auran na hannuna ba sai na ga ta tsiya ba, Au  so suke sai na je na duka Ina veeging ɗin su sannan matata za ta dawo? Lalle ko sai dai ta cigaba da zama a gidansu da aurena a kanta ba in da zan je."
Ya ƙarishe faɗa cikin tsawa sannan kamar Kabubuwa haka ya shige cikin Camp ɗin ɗakunansu ya bar su nan.
Jikinsu suma a sanyaye suka fito, ba su ga su  Nasir ba sun yi gaba sun fara takawa da kafafasun kafin ma Mu'azzam da Ahmad su shiga mota su cin musu sun tare mashina sun hau kowa ya yi hanyar anguwar shi rai ɓace, Mu'azzam ya rasa yadda zai yi bai ji daɗin abin da ya faru kwata kwata ba. Daga abun alheri sai kuma ya koma haka.
Yaya Mamsoor wani lokacin bai san abun arziƙi ba.

  Sai da ya maida Ahmad gida, Sannan ya dawo nan gidan Mansoor ya kwana, amman sai da ya kira Hibba ya ce ta shirya da Asuba za su wuce.
Haka ko aka yi ana Idar da sallah suka ɗauki hanya sai dai su bar ma Inna Juinor, saƙon test nassges ya turama Aji na cewa ya wuce tare da Ahmad suka tafi  ya sauke shi a kano daga nan ya hau motar Kaduna.




*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3004*

*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*

https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC

No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.

Tun da safen Aji ya ga saƙon ƙaninsa Mu'azzam amman bai kira shi ba sai can dare lokacin sun sauka gida suna Hlhuce Gajiya.  Bayan sun gaisa da tambayar hanya ba jiran komai kawai Aji ya kashe wayarsa, Daman lokacin suna zaune ne a falo suna cin abinci lokaci ɗaya suna kuma tattauna maganar shi da Hibba.

  Da ya ga bai masa mganar ba ne ya sa sai shi ya ƙara kiran shi, kamar ba zai ɗauka ba sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗaga lokaci ɗaya yana faɗin" Ka yi mantuwan kuɗi ne a gidana?
Sai da Mu'azzam ya yi yar dariya kafin yace"A'a daman zan gaya maka Junoir na wajen Inna muka bar shi."
"Good.."
Aji ya furta lokaci ɗaya kafin ya gyara kwanciyarsa yana gidansa ne a kwance amman kwanciyar ma ba ta yi masa daɗi a kwanaki nan baya samun ishashen barci sai dai ya kwanta ya yi ta Juye juye yana faman tunane tunane.

  Shurun da ya ji Mu'azzam ya yi ne,  ya sa yasan cewa akwai mgana a bakinsa, to daman ai yasan akwai mgana a bakin Mu'azzam, shi ya sa ya ƙara gyara kwanciya yana faɗin" Me kake son faɗa ne Mu'azzam?
Mu'azzam ya yi shuru yana tauna mganar, Hibba na gefensa tana masa inkinya da hannu akan ya yi masa mgana domin ta gaya masa shi kaɗai ne zai iya gaya ma Yayan na shi gaskiya ya ji, ya sanar da shi Inna tana fushi da shi, kuma fushin uwa bala'i ne gare shi gwara tun farko ya je ya neme ta gafara in yana so ya ga da kyau.

  "Uhm! Ina sauraran ka, ko kunya ta kake ji ne?

Aji ya faɗa cikin zolaya saboda Mu'azzam ya saki jikinsa, shi kansa ya san yana bukatar a yi masa faɗa. Saboda yana aikata wasu abubuwan da ya san mutane da dama ba sa jin daɗin sa, sannan Mu'azzam ƙaninsa ne duk duniya ba shi da wanda ya fisa kusa da shi irin shi.

"Yaya Mansoor, kan maganar abin da ya faru ne, kasan dai ba ka kyauta ba ko? Inna na fushi da kai, sannan ka ɓata ma su Nasir rai ya kamata ka kira su ka ba su hakuri."

  Aji ya yi shuru kafin ya ce"Zan dai iya zuwa na duƙa na ba ma Inna haƙuri tunda Ita ta haifeni, amman naganar na ba su Nasir haƙuri bai ta so ba, domin ba ni na aike su ba."

  Mu'azzam bai yi mamaki ba sanin halin yayan na shi sai kawai ya ce"Ni na ba su  hakuri tunda ni na gayyace su a lokacin.'
Aji ya yamutsa fuska kafin ya ce"Allah ya ƙara, kai ma rashin jin mgana ta ne, me na gaya maka?
Sai kawai Mu'azzam ya ce" Maganar ita Anty Mami fa? Ya kamata ka je Yaya bai kamata wannan abin da da kake yi ba."
Aji ya yi jim kafin ya ce" Itama za ta dawo in sha Allahu."
"Yaushe? Ba fa za ta dawo ba sai ka je ya kamata ka darajata, sannan iyayenta su gane ka daraja ƴar su"
Aji ya yi gajeren mirmishi kafin ya ce" Daman ai ta tafin ne saboda na je gidansu ina roƙo? To ku kyaleta ta yi ta zama mana waya damu?
Mu'azzam na shirin ƙara mgana. Kawai ya ji Yayan na shi ya ce"Kai ni fa barci nake ji, Kai ba ka gaji ba ne? Maza ka je wajen matarka sai da safe."
Bai ba shi zarafin mgana ba kawai ya katse  wayarsa ya bar shi nan sake da baki, Daman Hibba ta shiga ciki ne ta ba shi waje su yi mgana sai ga shi ta dawo yanayin da ta ganshi yasan ta san abin da ya faru.

"Ba'a dace ba ko?

  Mu'azzam ya yi shuru kafin ya ja numfashi ya ce" Ya ce zai je ya ba ma Inna hakuri, amman ba zai ba ma su Nasir ba. Maganar Anty Mami kuma ya ce za ta dawo da kanta amman shi ba zai je gidansu yana roƙo ba."
Hibba ta kaɗa kai kafin ta ce" Ina mamakin yadda yake da ƙwarin gwiwan a kan wai Mimi za ta dawo da kanta? Ina tsoron wannan jin kan na yayanka ya tashi a banza Mimi ta ja shi kasa warwas. Sannan in da ta na ɗaukan wayana sai na gayamata kada ta sake ta koma sai ya raina kansa."
Wani kallo ya yi mata, kamar

6 / 49