Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
soyayyen Naman kaza pepe sai kayan Snaak ɗin da Mimi ta ba da a ka yi gabaɗaya bayan an kawo ta diɓar masa tsire kuma daman na Aji ne sai aka raba uku ɗaya Mimi da danginta ɗaya kuma na su Inna da yan'uwansa ɗayan kuma nashi.
Matan su Nasir duk suna gidan Mimi har da matar Ahmad.Tun da ya ce shi zai koma amman ita sai bayan salla anan za ta yi azumi sannan cikinsu ba wacce ta zo hannu rabbana. Daddy kuma turmi biyar ya yi mata da kudi 100k Ƴaƴan yaddiko ma haka kowace da zaninta har Rukky da Jaheed sun tura mata kuɗi sannan ƴan ma'aiikatansu suma ba su zo hannun rabbana ba. sun haɗa mata kudi sun siya mata zannuwa da kayan jarirai tunda lokacin bikinta ya zo a kurewar lokaci ba su samu sun yi mata ba.
A ji dai suna gidan Makama gabaɗayansu ya sha farar shadda tana kyalli.Nasir ya so har wasa a buga Aji ya ce a'a Walima dai ya shirya domin a taya shi murnan samun ƙaruwa.
Bayan an sha ruwa Walida da Mariya suka kawo musu abun buɗe baki anan gidan Makama suka ci suka sha.Sallar mangriba ma sai Ahmad ne ya yi musu limanci, suma ɗin duk sun haɗa masa kudi ya ce ba zai amsa ba su kace ya raina ne sai ya karɓa ya saka albarka dagan gida ya koma saboda ya yi wanka walimar karfe takwas na dare abunci kuma da ababen shan su Mu'azzam za su ɗauka zuwa can Camp ɗin su.Gayyar da ya yi kaɗan ne daga yan Tream ɗin su sai abokan shi sai kuma yan nasaran Team Tudun Wada team da sauran Clubs ɗin ƙwallon kafa na Gombe manyan ciki. Sai Coach din su na gombe United da sauran shugabbanin ƙananun kungiyoyinsu.
Ko da ya koma gida, ba'a wani ragu ba yawanci duk nan za su kwana sai illa yan Kano ne suka koma gidan Hajiya. Yana shigowa falon su khadi ne da su Bibi sai su Yayan Yaddiko. Khadi tana ganinshi ta fara sakin guɗa tana masa kirarin Angon karni baban Maryama mjin Fatima. Karon farko da ta ga dariyansa hayaniyarsa ya fito da sauran da ke ciki, ana cikin haka sai ga su Yaya Amina da kaya niki niki na suna shi yas a ya sulala zuwa ɗakinsa ya ɗaga waya ya kira Mimi sai gata, ta zo ita da Ummi sun sha kwalliya ya kama su ya rumgume sannan ya sake ta ya ce zai shiga wanka ta zaɓa masa kayan da zai saka kafin ya fito ta fito masa har da takalmi shadda mai ruwan sararin samaniya har da babban riga ya fara korafin babban rigan tana damin shi ta shagwaɓe mass lokaci ɗaya tana faɗin" Don Allah ka saka, kai fa yanzu ka girma sunan ka Baban Maryam."
Da kalaman ta samu ya saka ta saka masa hula da agogo baƙaƙe ta fesa masa turare, Ya yi kyau har sai da ta ɗauki wayarsa ta yi musu hoto.Nasir sai faman kiran shi yake yi ya ce su na can ga su ma za su yi sallar sai yace shi zai tsaya a hanya ya yi sallah sannan ya ƙariso.
Zuwan su Yaya Amina ya sa har ya fice ba ba a lura ba ana kallon kaya ana saka albarka, yana hanya Daddy ya kirashi ya na masa tsiyan haka ake yi shike nan tunda yana uba baza'a gayyace shi waliman ba ne? Sai Aji ya ji kunya kwarai ya ba shi hakuri da cewa bai san ya na son zuwa ba. Nan Daddy ya ce ya bashi address in ya tashi daga in da ya je zai biyo ko da bai daɗe ba nan da nan ya tura masa adireshin Camp ɗin su dake cikin gari.
Ko da ya isa hall ɗin cikin Camp ɗin su da suka yin meeting ko wani taro ya cika da jama'a. Yana zuwa a ka fara gaisawa da shi ana masa fatan alheri ji kawai kake yi ana faɗin" Congratulation Captain Allah ya raya mana mai sunan mama Maryama."
Walima ce daman an ci an sha an yi badali da nama da Kaji, an ci tsire an sha lemuka an sha zoɓo da kunin Aya har da masu guzuru su Musa Zinder sun fi kowa murna da wannan walima domin sun ci sun sha sai hqmdala, ana gabda tashi sai ga Daddy ya zo ya dai gaggaisa da mutane bai tsaya ba sai a mota aka saka masa tsiren da Sank ɗin sa zuwa goma na dare kowa ya watse bayan an gama yi ma Maryama(Ummi) addu'an rayuwa cikin aminci, bayan an gama taron yana wajen tawagan ƴan Team ɗin shi suka same shi da roƙonsu suna son zuwa gidanshi su ga Maryama(ummi) sai ya ce su bari zuwa jibi sai mota ta kwashe ta kaisu su ganta Coach ma har gida ya je ya yi barka ya ba ma Mimi wani abu ya ce ta siya ma Ummi abun wasa.
Ranar ba'a gida ya kwana ba shi da Mu'azzam suka kama hotel, a daran ne Aji ya ce dole suna bukatar wani gida in dan irin haka ya faru su samu wajen sauka. Zuwa washegari taron suna ya tashi saboda azumi daga Khadi har Madiha a ranar suka koma Jawahir daman tun 12 yan kano suka mika hanya. Gida daga Mimi sai Inna Zainaba, naman suna kuma daman yan kano kawai a ka dibarmawa da yaji sai gidan Daddy sai Hajiya su khadi duk ba su tafi da shi ba gwarama Jawahir an ce ta kai ma Dr, Hibba da Mu'azzam kuma ba su koma ba sai washegari duka duka kwanan su huɗu ne saboda azumi a ranar kuma doguwar motar Team Gombe United ta kwaso su Zinder gabaɗaya dai yan Team din zuwa gidan Aji karo na farko suka yi ma Mimi barka. Kowanne sanye da kayan suna Bluee ɗin riga da wando, daga ma morning Training suke Aji ya ce a kawo su.
Ummi ta sha ɗauka Kb har kallon Aji ya yi yana faɗin"Captain ina kamu in ta girma."
Suka fashe masa da dariya Aji ya yi mirmishi bai yi mgana ba ,Inna zainaba da suka ba ta sha'awa ta ce" Haba ina za ka jira ta? Kai da ko yanzu ka isa aure."
Da sauri Kb ya ce"Ko ta uku ko ta huɗu don Allah Captain."
Ya fada har yana magiya harara Aji ya sakar masa kafin ya ce"Kun ganta ko? Maza back to camp now."
A tare suka amsa da" Yes Captain."
Ba Inna Zainaba ba har Mimi sun matukar burgeta, ta ji da a ce namiji ta haifa ba abin da zai hana bai gaje ubansa ba.
Mimi ta cigaba da jegonta cikin gata ko sati uku ba ta yi ba ɗinkinta ya warke tunda ta na samun kulawa ta koma asibiti an ce komai lafiya, Inna Zainaba ne ke kula da ita sai Hajiya da kan leko itama hakama Inna, an yi salla karama duk tana cikin Jego amman fa gaskyan Aji ne jegon nan ya yi mata matukar kyau kamar ba ita ba, Sannan Ummi ta yi wani irin kiba. Daman Aji bai yarda an yi wannan exculation ɗin nan ba ruwnta a ke ba ta ya ce ba zai iya daukan hakki ba, bayan sallah da wasu kwanaki Mimi ta yi arba'in sai kuma ta fara gyara kanta daman kuma Inna Zainaba ta ma ta kokarin shiga cikin ruwan bagaruwa sannan Yadikko ta aiko mata da Gumba ta na sha da Madara ita kuma sai ta siya haɗin kazan Uwargida na Surayya Dee, Bojuwa saboda ita dai Mimi ta amince da kuma yarda da haɗin kazan Surayya Dee saboda ta na daɗewa a jikin ta kafin ta gama aiki sannan uban gayyar yana ruɗewa in ta samu gyara daga surayya dee bojuwa mai kayan gyara.+234 803 277 3332 kuma har
ta aiko mata da shi har ta fara amfani da shi.
Inna Zainaba kuma ta fara shirin komawa Kano, ta sha tara arziki kuɗi kawai 30k Aji ya ba ta bayan zannuwan da Mimi ta haɗa mata Inna ma da omonta da sabulanta da yaji da ta saka a ka daka mata.Kwanansu Hamsn Inna Zainaba ta koma kano da sha tara na arziƙi.
Mimi ba ta je ko'ina ba bayan ta gama jego, Sai da Aji ya gama famshe kwanakin da ya yi kewarta ta ma kusa arba'in biyu sannan ya bar ta taje gidan Hajiya ta yini sai dare yaje ya dawo da ita gida.bWashegari gidan Daddy ta yini, ba ta kara fita ba sai bayan kwana biyu ta je gidan Yaddiko daga nan ta lelleka gidan yayanta dake kusa. Washegari kuma gidan Inna ta yi yinin ta, Inna ko Ummi na bayanta tun da suka zo, sai dare ya zo su ka koma gida daga nan jefi jefi tanq fita ta je can gidan wajen Magajiya daga can ta leƙa su Gaje Yaya Jummai da Yaya Zuwaira sai gidan natar Auwalu da gidan bintu tun da Aji ya ce ta yi su a rana ɗaya ba zai iya da yau a fita gobe ma a fita da sunan yawon arba'in ba har gidan Mallam Hashimu inna ta saka sun shiga. Gidajen su Yaya Amina ba sai daga baya ya kaita ta gaishe su.
Ta rasa wannan kulle na Aji sai ya ce shi dai ba ya so ta fita daga gidan, abunda ya sa ba ta damu ba, ba iya danginta ba ne har da na shi Abuja kaɗai yace za su je tare su kai ma Mommy Ummi ta ganta, amman sai Inna sun ɗaga saudiya tunda an biya mata da wuri jirginsu zai ɗaga a farko farko.
Amman sai kafin nan shirye shiryen tafiyar walida makaranta a ke yi. Ta je ma kanon ta dawo ta yi Rigistration ta dawo ta haɗa kayanta, Aji ya yi mata provition da sauran bukatu ya kara mata hijabai da takalma Mimi kuna ta siya mata dogayen riguna da mayafi kowa dai ya kawo wani abu ya bata daɗin abun ma a gida za ta zauna
Ta sha dai faɗa da nasihan ta kula da kanta Allah ya masa ga Mu'azzam ga Hibba, Ita da dawowa sai bikin mariya
Tafiyar Inna ma saudiya tana kano ba za ta ga tafiyar ta ba.
Inna an daga kasa mai tsarki. Har Mu'azzam sai da ya zo suka yi sallama gabaɗaya ya'yanta suka rakata sansanin Alhazai na gombe har da su Magajiya da Gaje su Baba Ɗanjuma ana gaba gaba, gida kuma Saffiya ta zo daga Tureta za ta zauna har sai Inna ta dawo kada gidan ya zauna ba kowa. Aji ya sauya ma Inna waya da za ta tafi saboda a rika jinta an yi waya da ita bayan tafiyarta da kwana hudu suna madina ana can ana ta ibada kuma Inna duk ta haɗu da mutanen kwarai ƴan Jihar gombe da suke tare a can Madina sai abun ya zo da sauƙi, salla babba ke kan gaba sannan ga bikin Mariya. Shi ya sa tafiyarta Abuja ya kasance ita kaɗai ta samu tafiya ta je ta kai ma Mommy Ummi ta ganta can a ka yi ta koke koken tunawa da Abi kwananta huɗu Aji ya kirata ya ce shima ga shi zai zo Abuja ya samu waya daga shugaban kungiyar kwallon kafa na kasa gabaɗaya wato Super Eaglees Yusuf Tijjani yana nemansa da gaggawa.
Da a ranar za ta dawo sai ya ce ta jira shi ya zo garin amman sai yamma ya ƙariso gidan suka gaisa da Mommy nan ya sauka tunda akwai bangare bangare ya yi wanka ya ci abinci har washegari suka hau jirgi suka koma gida Aji bai gayamata dalilin shi na zuwa Abuja kuma ita ba ta tambaya ba sanin halinshi amman koma menene ya damu kwarai ta na ganinshi yana ta shiga tunani. Sai a ranta ta yi masa fatan koma Menene Allah yasa ya zo masa da sauƙi.
Bsai ana babbar sallah saura kwana biyar da ya sake komawa Abuja ne ya dawo mata da takardan ya zama cikakken ɗan kungiyar kwallon kafa ta kasa gabaɗaya. Ba kuma kokarin kowa ba ne sai na Coach ɗin su, Wanda har gida shi da Mimi suka je masa Godiya yace ba komai shi Mansor kamar ɗa ya daukesa zai yi komai domin cigabansa, Ya je har gida ya sanar ma da Baba Ɗanjuma shina tare da su Baba Ɗanlami sun je yi ma Coach godiya duk da Aji ya iya buga wasa amman lamarin sai da hanya, Sai Agent ya cinna kai kuma ba kyauta sai ka biya shi, ya gaya Mu'azzam shi kuma ya gaya ma su Nasir sai kiran shi a ke yi ana mishi murna duk da ya san ya samu cigaba amman har ga Allah ya na kewar Team dinsa na Gombe suma da suka ji labari har da masu kuka karahenta dai Pele ne zai samu horo zai maye kujeran Captain ɗin wanda Bayan sallah zai koma Abuja tunda can Camp ɗin su na kasa gabaɗaya yake.
Inna na Saudiya ya kirata ya faɗa mata ta yi addu'a ta ce tunda ta sauka garin ma'aiki take ma ƴa'yanta da zuru'anta addu'an samun albarka, da kuma yi ma kasarta da waɗanda suka rasu addu'a.
An fara shirin bikin Mariya tunda bayan sallah ne da wata ɗaya sun raba abun, Mu'azzam zai ji da kayan wuta, tibi da Fridge gas, da su cafet shi kuma Aji zai yi abunda uba ke yi gado da kujeru Matan kuma sun haɗa kansu za su yi kitchen, Mimi kuma tace za ta yi labulayan da zannuwan gado, tunda ga ta ga FHB CLOTHING Phone no 08034109622
Wtsapp no.08080266674, domin zannuwan gadon su masu kyau ne da inganci.
Auwalu kuma ya ce zai ji da kayan gara da abunda za'a ci da biki. Saddiqu kuma da ke da ƙaramin karfi ya ce zai taimaka da abin da ya samu, Magajiya sai kuka ganin Yayan dai Inna su ne za su rufa mata asiri a bikin yarta, kuma kowa ya fara ba da kuɗi domin bangaren da ya ɗauka bayan an sallaci babbar salla a ka fara shirin biki tuni Aji ya ba da rabin kuɗin aikin gado da kujeru bayan an gama zai cika kuɗi sannan shi zai yi har kafita kowa dai ya na ta kokari kan bangaren shi.
Bayan sallah da kwana goma ya je Abuja, Kuma daman ya yi bankwana da Gombe United komai na shi ya kwaso zuwa gida, Sai da ya yi kwallah domin an ce sabo shi a ke yi ma kuka ya shaku da yaran nan sosai amman duk da haka ba'a rabu ba.
A can Abuja Camp ɗin su na Super Eagless ya samu wajen zama tunda nan Horo ne zai samu na tsawon wattani uku, ya kuma ga bambamci domin akwai ƙwararru sosai a buga wasa duk da shima ya yarda da ƙwarewansa.Sai dai su yi waya da Mimi duk son shi da kada ya yi nesa da gida Allah bai so ba ya na ji ya na gani ya koma Abuja da zama.
Ba ya fita ko'ina ko da yaushe yana cikin Camp, sai dai ya yi waya da ƴan'uwa. Mimi ko ta haddace da lukatan da ya ke free suna makale da waya da Ummi ta ƙara wayau, ta kuma zama burtuka. Sannan ta koma aiki tunda itama zaman shurun ya yi mata yawa. Su Inna ne wajen jirgi na biyu a dawowa tunda daman suna cikin yan farko farko a masu tarbanta babu Baban Inna ba Mu'azzam kowanne aiki ya yi masa yawa sai dai sauran yayan nata gida ya cika da masu sannu da zuwa Inna ta sauya kamar ba ita ba kai Allah mu ma ya kai mu Saudiya domin Alfarman ma'aiki (SAW) Amin.
Sai da suka kira wayarta suka mata barka da dawowa, Inna Meri ta yi mamakin grman Ummi saboda ta zama kamar yar turawa. Safiya na nan ba ta koma ba sai bayan bikin Mariya, a satin bikin kayan Inna suka iso na Tsaraba ba kuma wanda ba ta ma tsaraba ba, makota kuma sun sha tsaraban dabino da ruwan zamzam karshe ita ta kare ba ta samu komai ba.
Baba Danjuma jallabiya da sallaya hakama su Baba Danlami sallaya matan su kuma ɗankwali, Magajiya ta samu doguwar riga Mariya ma haka, Walida dai ta sha tsarabarsa su Bintu ma haka Mimi kuma an siya mata sarka da kuma kayan wasa na Ummi sannan ta siya zannuwan gado ta ce na Mariya ne.
Bintu dai har da kukan ta Inna ba ta siyo mata hakurin makka ta saka ba,Inna ta ce a raba ta da shegenka ita baitar ubangiji ta je, da tsufanta ina ruwanta da wani haƙorin makka. ƴaayansu dai ai sun sha taraba suma sai son barka.
Ta ijiyeme Baban Inna da Mu'azzam Jallabiya da darduna sai ruwan zamzam da dabino.Sannan ta ji daɗin yadda suka haɗa kai aka rufa asiri tunda Magajiya da bakinta take faɗa mata an gama gadaje da kujeru. Har katifa Aji ya turo kuɗi an siya Mu'azzam ya siya kayan wuta daga can za su zo da shi su matan kuma sun ta siya kayan kitchen. Kafin dai zuwa ranar jere komai ya kamallah har gara Baba Ɗanjuma ya rika saka mausu albarka gabaɗaya.
Biki saura kwana huɗu Mu'azzam da Hibba da Walida suka iso, daman tuni dangin Magajiya sun fara cika gida Mariya kuma ta na gidan Bintu ana ta mata dilka da gyaran jiki Yaya Amina ba ta yi mata wasa da kayan gyara ba, Mimi ma ta siya mata kayan gyara wajen Surayya Dee ta siya mata kazar haɗin Amarya da mganin sanyin sadidan na Bojuwa. Ita fa Mimi saboda aminta da kayan Surayya dee, duk in da ta ga ana neman kayan gyara sai ta yi ma mutane maganar kayanta, domin suna da inganci ƙwarai ta gwada kuma ta na ganin nasibin kayan gyara daga surayya dee bojuwa.+234 803 277 3332, ke ma ki gwada domin dacewa da ingamcin