Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
su har da guziri.
Inna ta tafi da kwana ɗaya Aji da Mimi da Bintu da yaya Halima suka sauka a garin kwami Walida na gida wajen Magajiya domin da taji Inna na mganar ta koma wajen Amina sai ta ce me zai hana tazo ta zauna tunda ga Mariya? To daman ai magajiyan ke nuna wani abu Inna na jin haka ta ce walida ta koma can sai ta dawo gidan kuma a ka rufe, Walida ba ta so amman ba ta da yarda za ta yi.
Sun je sun iske Baba Karimu har an ɗaura sa, Mimi ta ga gidan da aka haifi mijinta Mansoor nan ya bar su za su kwana da safe tare da sauran mutanen da za su je biki za su karisa Bauchi, ya ba da kuɗi a hannun Sadi babban yaron Baba karimu kuma ya ce in akwai wani abu a kira shi.
Inna ta isa Tureta tun a daran da suka tafi, Kuma tun bayan da suka yi waya ba su ƙara ba sai da ya dawo daga Kwami suka yi mgana ta ce jikin Tanimu ya yi tsanani gobe za su kaisa asibitin sakkoto.
A ɗakin Matar Sadi Mimi da Bintu suka kwana sun ga karamci, Mimi garin ya gama burgeta da safe suka ɗauki hanyar Bauchi har da matar Sadi, kowa ya ga matar Mansoor sai ya ce yar gayu mai kyau da ita, sun isa Bauchi da wuri tunda sun samu mota mai kyau.
Can ma ana ta maraba maraba da baki daman an san da zuwan su. Gwaggo Yalwa jiki ya yi kyau kamar ba ita ba, nan fa aka shiga ina aka saka da iyalan Inna Meri.
*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3015*
*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*
_Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_nfection_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_
_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*08089965176*
*07084653262*
Ranar Jumma'a suka sauka a garin Bauchi, suka kwana asabar kuma a ka tashi da hidimar biki. Mimi sun yi waya da Aji amman bai gaya mata zai zo ɗaurin aure ba, Shi kan shi ba zuwa a cikin tsarinsa amman a safiyar ranar sun yi waya da Inna ta ce maza ya shirya ya je ɗaurin aure.
Sai ya yi tunanin bari ya yi ma Nasir mgana sai ya raka shi su tafi tare.
Haka ko a ka yi daya ke ɗaurin auran na Rana ne ɗaya da rabi ne. Shi ya sa suka samu ishashen lokaci. A can Bauchi kuwa Mimi ta ga karramawa sosai wajen Maman Bauchi tare da sauran yaran gidan, ta yi mamakin yawan iyalan gidan daman Aji ya gaya mata duka ƴaƴa mata gare shi Allah bai taɓa ba shi haihuwan wani ɗa Namiji ba Sai mata amman kuma Allah na son shi da Rahama tunda da sun taso sai kuma Allah ya kawo musu mazajen da ya ke aurar da su zuwa gare su. Da safiyar ranar bikib an raka Mimi ta je ta gaishe da Baba Yakubu da yake shi mutun ne mai faɗin mgana kai tsaye, Kai tsaye yace ma Mimi" Ke ce matar Mansoor ɗin?
Ta ɗaga kanta sai ya yi mirmishi kafin ya ce"Ba shakka shi ya sa a baya ya yi ta cewa baya so da na ce ya zo gidana na bashi mata sai ya ce min shi bai ce baya son ki ba."
Kan Mimi na ƙasa ba ta yi mgana ba shi kuma bai damu ba sai ya cigaba da faɗin" Duk da fa yaƙi amman ban janye maganata ba, har yanzu ina da sauran yara in ya na so bazan hana shi ba."
Ya karishe faɗa da sigar zolaya Maman Bauchi na wajen Sai ta yi saurin cewa" Alhaji mganar nan ai ta wuce ko? Kai dai a matsayinka na uba ka saka ma auran su albarka." Sai ya kaɗa kai kafin ya ce" Haka ne to Allah ya yi ma auran ku albarka"
Mimi ta amsa da Amin acikin ranta maman Bauchi ne ta amsa a Fili.
Sai ya gyara zama lokaci ɗaya ya na faɗin" Meri ashe ta na can garin su ko? Jiya ta kirani mun gaisa ta ce min ɗan'uwanta ne ba shi da lafiya."
Sai Mimi ta ɗaga kanta gefe ɗaya kuma Maman Bauchi sai ta kwace hian suna cikin mganar sai ga Bintu da Anty Halima sun shigo sai a ka haɗu ana ta tattauna mganar kan Baba karimu da ya samu hatsari Mimi na gefe ba Kasafai ta kan saka musu baki ba.
Bayan sun baro falon megidan suna komawa ɗakin maman Bauchi da suka sauka suka ƙarya. Sannan suka leka ɗakin da Yalwa ke ciki itama jiki ya yi saukí Sai hamdala. Daga nan sai suka yi wanka suka shirya tunda babu wani aiki duk aikatau su ka kai, ko wanke wanke da shara akwai masu aiki balle su baki da sun ce za su yi wani abu sai Mama ta hana ta ce ga masu aiki sannan ga ƴan'uwanta nan sun zo z su yi komai. Amaren kuma suna gidan da ke kallon na Baba Kabiru can su ka kwana Bayan sun yi wanka sun shirya Bintu ta ja ta suka koma can gida suna ganin shiryawan Amarya da ƙawayenta.
Mimi ta yi shigar wani leshi ne jikinsa baki aamman kwalliyarsa ja ne sai ta yi amfani da jan mayafi da takalmi da jaka ja, ba wani kwalliya ta yi ba amman kayan sun karɓeta ta yi wani irin fresh fatar ta na wani irin santsi kamar wata baturiya sannan ɗinkinta mai flenting ne ta baya ya yi mata wani irin cif a jikinta.
A wajen sai ta zama abun kallo, ga ta yar gayu ga kyau ga kwarjini sannan ga Ilimi da kamala ga turanci domin tana gidan ta samu wayar wani ma'aikacin gidan radion Jamus ba ta yi mamakin in da ya samu labarta ba sun yi mgana da harshen turanci a kan suna son su yi aiki da ita, ba wannan ne na farko ba. Har NTA na ƙasa ma sun kirata D.W ma haka har da BBC, Sai dai ba ta da ra'ayi zuwa ko'ina ta fi kaunar zama a jiharta tun a baya ma balle yanzu da ta yi aure ta auri miji irin Aji ba zai taba barinta ta je wani gari ko ƙasa da sunan aiki ba. To ta sha turanci fa sai ta zama kawai abun kallo in an tambayi Amare wace ce Mimi? Sai su ce matar yayansu ne yaron yayan Abbansu da ya rasu ɗan ƙwallon nan da suke ba su labari saboda suma suna yawan faɗa mana ƙawayen na su suna da wani yaya a Gombe ɗan kwallon kafa ne, to daman mai mata irin Mimi me kuma zai ƙara neman wajen wasu matan? Ai ya gama samun dukkan jin daɗin nan duniya.
Suna tare da Amaren har a ka ɗaura aure, Tana ma cin alalan da a ka yi ne ta gama cin waina kena ta samu kiran Aji, yana tambayan ta tana ina? Sai ta ce suna makota tare da Amare sai ya ce ta fito ga su a waje abun sai ya ba ta mamaki ta tsame hannunta kan abin da take ci ta fita ta wanke hannu ta lulluɓa mayafinta a saman kanta ta fita, ba sa waje ashe suna cikin gida suna gaisawa da mutane ciki ta shiga sai gamu da Yaya Halima sai ta nuna mata ɗakin da Gwaggonsa Yalwa ke ciki tace suna ciki, ta yi mamakin ganin shi tare da Nasir ko alama bai sanar da ita zuwan shi ba, har da Mommy da Hajiya sun yi waya da safe su ka ce ko mijin nata zai zo ɗaurin aure ne? Sai ta ce musu a'a saboda ba su yi mganar zuwan na shi ba.
Ta ji daɗin ganinsa kwana biyu kawai sai da ta yi wani irin kewarsa ta na masa mirmishi ya na yi mata, ya sha shadda fara dinkin zamani tqzarce har da hula sai ya yi wani irin kyau kamar ba shi ba.
sun gaisa da Nasir da tambayan yara, Sai kawai ta ce"Da na san za ka zo, da na ce ka zo min da ƙawata."
Nasir na dariya ya ce" Tafiyar ba tawa ba ce, ni kaina sai da safen nan na sani, kin san halin mijin nan naki akwai yi ma mutane karfa karfa."
Wani kallo Aji ya yi ma Nasir shi kuma sai ya na dariya, Yalwa na gefe itama tana mirmishi, nan ɗakin a ka kawo musu abinci suka ci, suna gama ci wajen uku da rabi su ka ce za su tafi lokacin Baba Kabirun ma bai dawo ba ya na can yana sallaman bakin da suka zo daga nesa.
Kawai sai Aji ya kira wayar Mimi kai tsaye yacl ce ta shirya ta fito suna jiran ta, Sai mamaki ya kamata saboda ita dai sun yi da shi sai gobe za su koma gida.
Cikin mamaki ta fito ta same su nan ƙofar gida baki a buɗe ta ce" Na ji kace na zo mu tafi ka manta sai gobe za mu koma tare da su Bintu?
Kai tsaye ya ce"Su dai za su dawo gobe amman ke yau za ki koma gida."
Mimi ta ɓata rai kafin ma ta yi mgana ya ce"Gobe kaɗai gareni jibi za mu tafi katsina wasa sai mun yi sati, kinga ni ba zan je na zauna a gida ni kaɗai ba."
Mimi ta yi kamar za ta yi kuka har ga Allah ita ba ta saka ran komawa a ranar ba,
Kawai sai ta ji ya na rage murya har ya na faɗin" kin manta ma jibi za ki koma wajen aiki? Gwara ki zo mu tafi kin ji ko?
Cikin shagwaba ta ce"Su Bintu fa da Anty Halima?
Kai tsaye ya ce" Ina ruwan ki da su? Sun fi ki sanin hanya in sun gama bikinsu za su dawo ke dai ki je ki ɗauko jakarki mu ta fi kada mu yi dare a hanya."
Mimi ba ta da wata mafita dole, ta juya za ta koma cikin gida amman kuma sai ta rasa abin da za ta ce musu kawai sai ta ce za ta bi miji su koma gida? Sai ta dawo ta na ce masa" To ni me zan ce musu? kawai sai nace musu zan bika?
Kallon sama da ƙasa ya yi mata kafin ya buɗe mota ya shiga lokaci ɗaya yana faɗin" To shike nan sai ki zauna."
Ya faɗa a fusace dole ya sa ta koma cikin gida ta samu Yaya Halima ta gaya mata ita kuma sai ta yi dariya kafin ta ce"Ki bi mijin ki Mimi ai an gama biki, mu za mu zauna har zuwa jibi kada ki damu."
Yaya Haliman ce ta sanar ma mutane tafiyar Mimi ba wanda ya damu da tafiyarta Maman Bauchi har waje ta raka Mimi da abun arziƙi na jaka da kofunan biki da za su raba, ko Bintu ba ta samu komawa ta yi ma sallama ba suka ɗauki hanya.
Aji ke tuki Nasir na gefen bangaren mai zaman banza, ita kuma Mimi tana baya ta na ɓata rai. Shi ko Aji sai ya basar da ita ya koma suna ta hiran su shi da Nasir.
Suna hanyar Rukky ta kirata cikin damuwa tana tambayanta ina ta je ta zo gidan ta bata nan? Mimi tace ba ta nan ta je Bauchi amman yanzu tana kan hanyar dawowa.
Yadda ta ji muryan Rukky a sanyaye ne ya sa ta ji jikinta itama ya yi sanyi har sai da ta ce" Me ya faru Rukky? Daga can bangaren Rukky ta ce"Bakomai sai dai kin dawo ɗin."
Daga haka sai ta katse wayar sai abun ya ba ma Mimi mamaki kamar ta yi ma Nasir mgana sai kuma ta fasa ta bari gwara sai ta koma sai ta kira Rukkyn su yi mgana.
Wajen mangariba suka isa Gombe sun biya gida sun sauke Nasir, wani abun mamaki ita dai Mimi ba ta ga ko sau ɗaya sun yi waya da Rukky ba ahalin kuma ta san a baya ba haka suke ba dole ta fara zargin akwai wani abu a ƙasa.
Haka suka isa gidansu Mimi na shan kamshi, Aji kuma sai ya nuna kamar bai gane ba ya na ta ɗiban ta da mgana ita kuma ta na basar da shi, kuma duk gajiyan nan haka ya saka ta sai da ta yi musu girkin dare ya je ya siyo amman ya ce shi wlh ya daina siyan abinci yana magidanci har da cewa zai taya ta amman kuma ban da ɗauko miko ba abin da ya yi mata. Sai juya kayan miya kawai ko greeting cewa ya yi baya son hannunsa ya taɓa ya ji, ganin da ta yi duk fushin da ta ke yi bai gane ba dole ta saki fuska kamar komai bai faru ba. Daman ya gaya mata ranar litini zai yi tafiya shi ya sa a daran dai kamar in ya tafi ba zai dawo ba. Da kuma safiyar ranar suka tashi da wayar Inna da labarin rasuwar ƙaninta Tanimu, saboda haka za ta jima tunda yanzu sai bayan an yi bakawai, duka dai yaran sun kirata sun yi mata gaisuwa ya yi nisa ba lalle ace sun tashi daganan zuwa can shiyar sakoto ba.
Ranar lahadin a gida suka yini washegari litini kuma tun safe su Aji suka kama hanyar katsina tare da sauran team ɗin su, Mimi dai ta sha dokoki kada ki yi kaza kada ki yi kaza, har sai da ta gaji da amsawa da To, shi dai ta kular masa da kanta da gidansa, itama ranar a wajen aiki ta yini ba kuma su haɗu da Rukky ba an ce ta zo ta fi daga baya ta kuma kira wayarta ba ta same ta ba, Bintu ta kirata ta na masa tsiyan shike nan sai ta gudu ta bi mji tana ta dariya nan take gaya mata suma ba su daɗe da shigowa garin ba, an ba su kayan fulawanta gobe Bintun ta ce za ta zo ta kawo mata.
Suna cikin wayar ne ra ga madiha na ta kiranta bayan sun gama sai ta kira ta wanda tun bayan tarewanta sau ɗaya suka yi mgana nan ta ke gaya mata ta shigo garin tana gidan Hajiya ta na so ta zo ta ga gidanta amman Hajiya tace ta yi tafiya sai ta ce mata ta dawo tun shekaranjiya tana wajen aiki amman in ta ta shi za ta biyo ta gidan Hajiya.
Haka ko a ka yi da gidan su Rukky ta so ta wuce amman zuwan Madiha ya sa ta fasa, saƙo ta turama Aji kan cewa Anty Madiha ta zo za ta biya ta gidan Hajiya, da yamma ta je ta iske ta ko a gidan hajiya kamar ita kaɗai ta zo ba yara ba mijin ta ce wasu kaya ne suka kawota za ta ƙarisa Abuja ta ga kayan da ganan ta ga Mommy, sun gaisa sama sama kamar yadda suka saba Madiha sai wani ƙare mata kallo ta ke yi ƙasa ƙasa ita dai a dole sai ta samun abun kushewa sai kuma ga shi ta kasa samu. Duk Mimi na kallonta a ranta tace mai hali dai baya fasa halinsa, amman saboda ta kure Madihan ya sa ta ce mata ta zo su je gidanta ta kwana.
Cikin mamaki ta ce"Gidan ki kuma? Shi mijin na ki fa?
Mimi ta ce"Ko ya na nan akwai ɗakuna, balle ma baya nan sun tafi katsina buga wasa."
Hajiya na gefe ta ce" Ai ko dai ki je ki kwana gidan ƴar'uwan ki Madiha."
Sai ba ta yi gaddama ba. Bayan sallar Isha'i Mimi ta ɗauke ta a motar ta zuwa gidanta Madiha ta sha mamaki domin duk kyan gidan a hoto a fili ya zarce tunaninta.
Acikin bedroom ɗinta ta sauke Madiha ta kuma tuɓe tana ta hidima da ita abincin ta yi musu mai rai da lafiya suka ci suka sha ruwa.
Vduk kushe irin na Madiha ta rasa abun kushewa sai bin ko'ina ta ke yi da kallo, ta na gani Mimi na waya da Aji bayan ya sanar da ita sun sauka lafiya, ita kuma sai take gaya masa ga Yayarta ta zo.
Kai tsaye ya ce"Wacce daga ciki? Ta kaduna ko ta Lagos?
Sai tace masa da ta Lagos abin mamaki sai ya ce ta bata wayar