Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
ya ga dama zai ce ta je in ta tashi aiki, ko gidan Inna ne in bai yi ra'ayi ba sai ya ce daga wajen aiki ta koma gida, cikin lokaci Mimi ta sauya ta fara Kiba da Kumatu ta nacin mai kyau ta sha mai kyau ta kuma kwanta a waje mai kyau sannan hankalinta ya na kwance, duk wanda ya ganta ko ya yi waya da ita zai san ba ta da wata matsala.
Sau ɗaya ta taɓa shiga kasuwa ta yi cefane da kuɗin ta da ta dawo Aji ya yi mata faɗa kai tsaye yac e"Ni ban kasa a gidana ba Fatima, me ya sa za ki nemi ki kashemin Kokarina a kan ki? Ki bari duk ranar da na ce ba ni da shi ina bukatar taimakon ki sai ki taimakamin amman by now hqkkin ki na kaina naira biyar ban yarda ki kara kashe ma kanki da gidana a cikin kudin ki batare da kin gaya min ba."
Da sauri ta ce masa ya yi hakuri ba za ta ƙara ba tun daga ranar ba ta ƙara ba in abu ne ya kare shi za ta gayamawa ya je ya siyo.
Kitso ko da kunshi duk bayan sati uku wata makociyar Bintu ke zuwa tana yi mata ya biya ta. Maganar ma siya ma walida waya da ta zo wajenta ta ce ta ƙara tuna masa da ta yi masa mgana bai ce komai ba sai ta yi tunanin bari ta siya ma Walidan wayan amman da ta nemi izininsa sai ya ce a'a, sai dai ta masa kuka da cewa tunda haka ya ɗauka shike nan amman ita walida ƙanwarta ce ganin haka ne ya sa ya ce ba haka ba ne waya shi ya yi alƙwari amman ba zai hana ta ta siya mata wani abun ba.
Ai ko dai Walida ta sha gwangwanja a lokaci ɗaya sai ga waya da sabuwar laptop, Shi ya siya waya Mimi ta siya mata laptop tunda ta kusa gama ma koyon computer, an kusa yaye su daman wattani shida ne Walida kamar ta suma saboda daɗi Inna na yi mata dariya. Haka ta riƙa kiran yan'uwanta ta na gaya musu abun arzikin da ya sa me ta, Hajiya kuma har gida ta zo ta ga gida ta yi ma Inna Meri murna sannan itama Innan ta na zuwa duba Hajiyan lokaci bayan lokaci.
Gidajen yan'uwansa ko Mimi ta leka sau daya, gwara ma gidan Bintu da mijinta ya siya mota sun je Allah ya sanya alheri ta bi Walida sun tafi tare, gidan Yaya Amina sau ɗaya taje haka ma gidan Yaya Halim gwara ma can gidansu Hibba in aka yi wani abu Inna ta gaya masa sai ya ce ta shirya ta bi su, ita dai daga gidan Hajiya sai gidan Daddy shima tare su kan je sai gidan Rukky da yanzu ya ke barinta zuwa amman Rukkyn ma ta fita zuwa wajenta lokaci bayan lokaci.
Sannan Meesaha ma ta zo wajenta ya fi sau biyar, ita dai ba ta sakar mata ta yi ta kawo mata mganganu Saddiqu yanzu babu komai ya daina zuwa Lagos ɗin sai zaman banza a gari, ita kuma Mimi sai ta ba ta shawaran tunda ta yi karatu ta nemi aiki domin ta taimaki mijinta. Mansoor bai hanata mu'amala da kowa ba domin ya ce ita ba yarinya bace ta san yadda za ta tafiyar da komai, ba ruwan shi da yana da matsala da wani shi dai matarsa kawai ya sani ita yafi kiyyewa fiye da kowa, in ta zo in ta na da abu za ta ɗauka cikin mallakinta ta yi mata taimako ba ta tasallake iyakarta, Tasan wanda take aure shi ya sa ba ta karambanin taɓa abin da yake na shi ne sai da izinin shi.
Ya sanar da ita ya na so ya samu lokaci su je can kwami ta ga tushensa da ganan su shiga Bauchi in sun dawo kuma ya ba ta izinin za ta je Abuja ta ga Mommy ko na kwana biyu ne Mimi na ta murna, shi kuma ya yi mata kara ne ganin ba ta taɓa nuna masa ƙosawar ta ba, shi kuma farincikinta yake so, adalci ya ke son yi mata kamar yadda ta yi masa, kuma ba ya son yau ace Mimi ta ji ta na son wani a bu ya kasa yi mata shiyasa kafim ma ta tambaya yake kokarin yi mata shi, Har cewa ta yi ya kamata su je kano ya ce ita da kano sai Hibba ta haihu, ai ta je kafin tareewarsu ba ta gaji da zuwa ba. Dole ta kama bakinta, iya ma Abujan ta gode ma Allah da ya barta shima baya nan lokacin za su je kaduna.
In ya na gida tana girki ya kan taya ta da niko wannan ɗauke wannan, baya takura kansa abin da zai iya shi yake yi, ya ce girki na mata ne amman ba shi zai hana ya ɗan taimake ta da abin da ba'a rasa ba. Rayuwa dai suke yi dai dai rayuwar mallam bahaushe.
*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3014*
*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*
https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC
No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.
_28TH. MAY 2023_
*SUNDAY, 12:00PM*
Tunda yau lahadi ana cikin hutun ƙarshen mako, da ga shi har ita suna gida ba su fita ba gwara shi caach ya kira shi da safe ya fita zuwa camp sun yi mgana a kan wani gagarumin taron da babban kungiyar ƙwallon Kafa ta ƙasa baki ɗaya za ta shirya a garin Abuja wato Super Eagles shi Aji baya son zuwa taron Caach ɗin su kuma ya matsa masa ya na so ya wakilci jaharsu tunda shi ne Captain tunda abin kamar dukk an gayyaci manya manya kungiyoyon ƙwallon kafa na Nageria ne gabaɗaya.
Shi kuma Aji ya ce Coach ya fi shi matsayi shi ya kamata yaje, shi kuma ya na nuna masa shi dai ɗin ya kamata ya je haka suka rabu ba su samu matsaya ba. Tunda Aji ya kafe har da cewa tafiya za su yi zuwa garin su shida Mimi amman Coach ya ce ya ma fara shirin tafiya Abuja ba fashi, da wannan haushin ya dawo gida Mimi na barci ba ta tashi ba daman sanda ma ya fitan ba ta sani suna kwance ne suna barci ya zare jikinsa ya fita, sanda kuma ya dawo sai ya yi zamansa a falo kawai yana wani lissafin.
Shi fa ko da yake sanannen ɗan ƙwallo a jiharsa shi mutum ne mara son shigewa mutane kada ma ace yana neman wani abu ko kuma neman fada da wajen zama. Shi ya sa rayuwarsa yake yi kai tsaye baya neman kowa sai wanda ya neme shi Coach ɗin su ma ya yi ta son haɗa shi da sanannu manya a ƙwallon kafa na ƙasa gabaɗaya amman Aji sai ya riƙa noƙewa.
Gajiya ya yi da zama a falo yana ta saƙe sake bai isa ya gujema wannan tafiyar ba Coach kamar uba yake gare sa. Da dai ace sanda ya yi turjiyan ne ya amince shikenan amma yanzu tsarinsa ya rushe, zuwan shi kwami da Bauchi ba zai samu ba sannan Mimi ma ba zai hana ta tafiya Abuja tunda ya riga ya yi mata alƙwari kuma ya san ta sanar da Mommy, sai dai yanzu su tafi tare shi ya je ya yi abin da ya kaisa ita kuma ta je gidansu ta zauna in ya gama abib da ya kai sa sai su dawo tare, ga kuma babbar salla ta ƙarato sai dai su ɗaga tafiyarsu Kwami zuwa bayan sallah. Gajiya ya yi da zama ya tashi ya kunna talabijin a tashar kwallon ƙafa daman su yake kallo ko tasoshin wa'azi Mimi kuma daman kallo bai dame ta ba barta da barci sai kuma waya,wayar ma ba sosai ta dame ta ba.
Bai san fitowarta ba sai ji kawai ya yi ta saƙalo hannayenta daga bayansa zuwa wuyansa lokaci ɗaya tana ɗora kanta a saman kansa cikin yar shagwaɓa ta ce"Shi ne ka tashi ni ba ka tashe ni ba ko?
Ta faɗa ta na sosa kirjinsa da ɗayan hannunta ɗayan hannun nata kuma ta fara sosa masa kunninsa guda ɗaya, juyowa ya yi bayan ya riƙe mata duka hannayenta sannan ya zagayo da ita har gabansa ya zaunar da ita kan cinyarsa suna masu kallon juna ya ce"Kina ta sharan barci duk kin bugemin jiki, kina ta munshari, ga shi kin saki baki galala da miyan barci."
Ya faɗa lokaci ɗaya har ya na kauda kansa yana ƴar dariya. Rufe baki ta yi tana kallonshi cikin mamaki kafin ta ce"Ni ne ke minshari da miyan barci?
Ta faɗa har ta na zaro ido cikin tsoro domin har ga Allah ta ɗauka da gaske ne.
Rumgumeta ya yi yana faɗin" E, mana, ban taɓa faɗa miki ba ne, amman kada ki damu ke na ke so ba zan damu da minsharinki da miyan barcin ki ba" Yadda ya ƙarishe maganar da dariya ne ya sa ta gane abin da ya ke nufi, da sauri ta saka hannu ta mintsine shi a cikinsa har sau biyu kuma mintsinin da zafi da ya sa dole ya saketa ya yi gefe yana raɗin"Mimi ba na son mugunta fa daga faɗin gaskiya?
Mikewa ta yi daga kan cinyarsa ta riƙe kugu daga ita sai rgar barci fara mai shara shara iyakarta gwiwamta sannan surar jikinta duka yana buɗe ne gashin kanta ma yana ɗaure ne kanta ba hula ba ɗankwali.
"Waye mai miyan barci da minshari?
Haka ta faɗa ta na zare masa ido har da ɗaga hannu kamar za ta kai masa duka ya saka hqnnuwansa ya kare kansa yana faɗin" Allah ya baki hakuri Inna Fatima."
Ya faɗa yana yar dariya sai kawai ta ja cution ɗin kujera ta mara dukanshi da shi ya na karewa da hannunshi yana dariya bai hana ta ba sai da ta gaji ta bari shi kuma daga kwancen ya saka hqnnu ya jawo ta ta faɗo jikinsa ya rumgumeta ita kuma tana neman ƙwace kanta lokaci ɗaya tana faɗin" Ina miyan barci ko?
Ya na yar dariya ya ce"Na tuba na janye mganata ina ga ni ne me miyan barcin da minshari ban sani ba"
Hararansa ta yi kafin ta ce"Za ka ma sani ne." Ta faɗa ta na kokarin tashi ya sake riƙeta ya nannaɗeta a cikin jikimsa yana mata raɗa a kunne ba ta san lokacin da ta yi dariya ba. Bai bari ba sai ya fara yi mata cakulkuli ta fara dariya kamar za ta shiɗe tana faɗin" Cikina na ciwo don Allah ka bari."
Sai da ya ga tana hawaye sannan ya kyaleta ya koma ya na sumbatan bakinta.
Daga nan suka rike kan juna suna sumbatar bakin juna cikin shauƙi da soyayya.
Sun ɗauki lokaci suna farantama juna rai sannan suka saki juna suka koma su ka sake rumgume juna suna maida numfashi, kan Mimi na saman kirjin Aji shi kuma ya saka hannunahi ya na shafa gashin kanta, Idanuwanta a lumshe tana jin wani irin farinciki na ratsa ta a nan duniya gani take yi kamar tafi kowa dacen samun abokin rayuwa nagari, shi ma a bangarensa addu'a yake yi Allah kada ya bashi ikon kuntata ma Mimi, Allah ya zaunar da su lafiya ya kaɗe fitina.
"Me za mu yi breakfast da shi yau Aji?
Haka Mimi ta faɗa, tana ƙamƙame dashi, kai tsaye ya ce" Duk abin da Mimi ta shiryama Aji kinsan bai taɓa juya mata baya ba."
Buɗe idanuwanta ta yi kafin ta ce" Ko mu soya kwai ne mu gasa buredi, mu sha Tea ko?
Sai ya gyaɗa mata kai kafin ya ce" Ni fa ba ruwana da wannan bangaren, ke dai kawai ki ciyar da ni, ni kuma ina yin aikina na ci da ciyarwa." Ya faɗa lokaci ɗaya yana kashe mata ido ɗaya, Sai kawai Mimi ta daki kirjinsa cikin sigar wasa tana masa mirmishi, sannan ta miƙe lokaci ɗaya tana faɗin" Rana ta yi, bari mu karya karfina ya dawo jikina tukunna."
Da kallo ya bita za ta shiga kitchen sai ya kwala mata kira ta juyo kai tsaye ya ce"Ba na hana ki shiga kitchen ba takalmi ba dankwali ba?
Sai Mimi ta dafe kanta kafin ta shagwaɓe tana faɗin"Na manta ne Aji."
Miƙewa ya yi bayan yac e mata bari ya zo cikin bedroom ɗin su ya shiga ya ɗauko mata hula da silafas ɗinta na cikin hida ya zo har gabanta ya duka ta saka takalmin sannan ya kama kanta ya saka mata hular sannan ya kalleta kafin ya ɗan rankwasheta yana faɗin"Ba ki san saka Dankwali ko?
Sai na yi miki aski"
Baki ta tura kafin ta ce"Aski? To sai ka kalli gashin wa?
Ya na juyawa zuwa kan kujeran da ya tashi ya ce" Aure zan ƙara, ba zan zauna da mai kai kamar na maza ba."
Tsaye ta yi ta na buga kafa za ta fara masa kukan shagwaɓa, ya na jinta sai ma ya ɗauki romot ya ƙara ƙaran talabijin ɗin lokaci ɗaya ya na faɗin" Fatima ina jin yunwa fa. Ɗaya saura na rana ban karya ba fisabilillahi fa"
Haka ya faɗa ya sa ta faɗa kitchen ɗin lokaci ɗaya tana faɗin"Da laifin ka me ya sa baka tashe ni ba?
Bai san ko ta ji ba ya ce"Mace tagari ba ta jira miji ya tada ta sai dai ta tada shi, amman ke sai barci kamar kasa, zan ga ranar da za ki haihu Fatima."
Ita ba ta ji sa ba. Ta kunna gas ta fara ɗora ruwan tea ɗin bayan ta saka kayan ƙamshi da ganyen shayi, sannan ta fara koƙarin Kwaso ƙwan da za ta soya buredi ya na can saman dinning wanda za ta gasa ga shi kuma sai da ta fara fasa kwan ta tuna sai kawai ta fito bakin kitchen ɗin tana kiran sunan Aji bai jita ba sai da ta ƙwalaa masa kira da Karfi sannan ya juyo lokaci ɗaya yana na rage ƙaran talabijin ɗin.
"Miye ne?
Haka ya ce mata yana haɗe rai, shi fa baya son mace ta riƙa saka shi aiki kuma ya lura halin Mimi ne ta riƙa saka shi aiki kamar wani ɗanta.
"Buredi za ka ɗauko a saman dinning.."
Ta faɗa cikin yar shagwaɓa, hararanta ya yi kafin ya ce"Ke fa? Kafar ki na ciwo ne?
Wani kallon ƙasa ƙasa ta yi masa kafin ta ɗaga masa hannuwanta lokaci ɗaya tana faɗin" Na saka hannuna a kwai ne, don Allah ka kawo min."
Kamar ba zai ta shi ba haka ya tashi yana tura baki kamar mace ita kuma tana danne dariya yana ganinta sai ya dakata yana faɗin" Dariya ma kike yi ko ? To Allah ba zan ɗauko ba."
"Afuwan haba Nawan, Aji na ajin zuciyata."
Haka ta faɗa har ta na masa fari Mirmishi ya yi kafin ya ce"Eh mana tunda kin sakani aiki ba, dole ki yaudare da kalamai mana."
Haka ya je ya ɗauko mata shima ba ta karɓa ba, ta ce hannunta ba kyau ya kai mata kirchen, da sauri ya shiga ya sauke mata samman wani faranti har yana sauri ya fita ta bi shi tana Faɗin" Ka tayani mana,ko gasa buredin Aji"
Ko juyowa bai yi ba ya fice yana faɗin"Yunwa nake ji, don Allah ki yi sauri."
Daman ta san ba zai tsaya ba ba ta san me ya sa ba baya son ta yata aiki ba, aiki in dai ba shi ya yi niyya ba ita kuma tana so ta ga suna aiki tare cikin soyayya da ƙauna.
Bayan ta gama fasa kwan sai ta tuna bata yanka albasa da kayan miya ba, wanke hannayenta ta yi ta yanka buredin ta saka masa butter ta saka shi cikin oven yunda Aji ba ya son gasaahen buredi da ƙwai ya fi son shi da Butter ya yi taushi.
Gani ta yi aikin baya mata sauri tana yanka su tattasai, ta ƙwalama gogan kira ya ƙi amsa mata sai ta da ƙara ɗaga murya sai ga shi a bakin kitchen ɗin lokaci ɗaya yana faɗin"Wai na ci miki bashi ne Mimi? Kada ki ce za ma ki ƙara aike na domin nima yunwa ta saka ba ni ma da kuzari."
Ya faɗa yana harɗe hannayensa a saman ƙirjinsa, har ya na wani kauda kai ganin haka ya sa da sauri ta marairaice tana faɗin" Aji to ka kama min na gama da wuri mana."
Hararanta ya yi kafin ya yi mgana da tare shi da shagwaɓa tana faɗin" Don Allah haba mana."
Ɗaure fuska ya yi kafin ya ce"Me kuma zan yi yanzu?
"Albasa za ka yanka min don Allah."
Ido ya zaro kafin ya ce"Albasa? Mugunta ko? Kin san fa ranar haka ki ka sakani ina ta kukan dole."
Dariya takke so ta yi amman sai ta kanne ta lamgwabar da kai kamar za ta yi kuka kafin ta ce"Shike nan bar shi ma,"
Yadda ta yi mganar ne ya sa dole ya shiga Kitchen ɗin ya na faɗin" Ina albasan?
Tana mirmishi ta nuna masa ya ɗauka sannan ya dauki wuƙa, ta nuna masa wani ƙaramin vol ya ɗauka ya fara yankawa a ciki yana ƙunƙuni ta na jin sa sai ta kanne ba ta yi magana ba sai da ta ga ya na ta yankawa manya manya sai ta kalle sa kafin Ta ce.
"Haba Aji, sun yi girma yankan"
Hararanta ya yi har ya fara ƙanƙance ido kamar yajin ya fara tasowa.
Haka nan ya gama yanka mata sannan ya tace ruwan tea ɗin ya juye cikin flaks ɗin ruwan zafi, ita kuma ta fara soya kwan shi kuma ta ce ya duba buredin a oven, ya cire