Idan An Ciza Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   18 / 49

51K to 54K   out of 146.6K words

ya tafi sai bayan la'asar ya dawo ya je ya yi wanka ne ya sauya kaya ko da ya dawo ma sun yi dubaran yin girki Tunda Bintu ta taho da kayan abinci da gas tunda daman Inna na da shi ita ce ba ta cika amfani da shi ba. Sai ya ji daɗi daman yana can ya na tunaninsu sun yi waya da Mu'azzam ne wanda ya ce Auwalu ya kira shi ya faɗa masa ga abib da ke faruwa sun yi mgana sabbin kayan gidan da za'a saka ma Inna suna gama waya Mu'azzam ya tura ma masa 100k yace a kara da shi ai ko ya sha faɗaa domin Mansoor ya ce shi bai ce ya kawo wani abu ba, shi kuma ya ce ai Inna mamansu ce gaɓadaya shima ya na neman albarka sai bakin Mansoor ɗin ya mutu.

  Nan ya ce su Yaya Halima su zauna su rubuta duk abib da za su bukata na kayan amfani gida oabulai kayan gadaje da Kujeru kuma ya ce har da su duk su je su zaɓo Atm dinsa na babban bankin sa First  Bank ya damka musu su kuma su ka ce tunda yamma ta yi sai da safe za su yi sammakon fita  Gabda mangariba ya bar gidan shi kanshi ya samu natsuwa tunda nan yaci abincin rana Jallop ɗin shinkafar da suka dafa da daddare ma Bintu na dafa shinkafa da miya ya ce su ijiye masa zai dawo tuni sun gyara gidan gabaɗaya sun tsabtace komai kayan Inna sun samu matsugunni cikin wardrope Walida kuma tuni ta manta da duka ta ware tana murna ita abin daɗinta wannan kayattacen tiolet na cikin ɗakin da aka ce nan za ta zauna ga Wardrpoe ɗin bango daman tun lokacin ginin aka gina da shi sai dai aka saka masa Kofifi kawai.

  Bintu a nan ta kwana tunda ta kira Bashher ta gaya masa Inna ta sauya gida za ta tsaya ta taya su gyare gyare. Da kan shi ma ta yi masa kwatance ya zo ya kawo ma ta su Hussaini tunda abokiyar zamanta ba ta nan ta na gidansu ana suna, ya zo ya ga gida shima ya yi mamaki, amman jin gidan Babban Yaya ne sai bai yi mamaki ba.
Yaya Halima da Yaya Amima gidajen su suka koma su ka kwana sai washegari suka dawo da sassafe suka tafi kasuwa su uku tare da Bintu tun safe sai yamma a kamfanin da suka siya kayan su suka basu motar da ta ɗauko musu kayan da kuma ma'aikatan su Kafin dare duka an haɗa gadajen, falom ma tuni an zagaye shi da sabbin kujeru masu kyau da yarari, har da labulayan suka siya da karafan su ma'aikatan suka haɗa musu komai tunda an riga daman an ɗinka su a kirchen ma sun yi ma Inna ɗaki domin har kololi sabbi suka siya mata da sauran kayan amfani kitchen da na tiolet gida dai ya fito kamar gidan wata amarya yana kuma tashn shin kamshi tun da daman sun siyo turarukan tsinke da na rushi.

  Gadon Inna shine 6by7,Na Walida kuma karami ne 6,by 6 ne. Gida ya fito ras da shi sai son barka, Inna Meri duk ta damu wai shi Baban Inna ina zai riƙa kwana? Ya
na dariya ya ce"Inna ina da wajen kwana ga Camp ɗin mu, sannan ga ɗaki na nan in ina son kwana tare daku zan zo na yi kwanciyata sannan daga yau mun zama family daya ko da Mu'azzam ya zo da iyalansa waje ɗaya za mu rika kwana a matsayin Ahali ɗaya in sha Allahu."
Sai Inna ta jinjina kai domin itama ta ji matukar ɗadi ganin iyalanta a waje ɗaya.

  Maƙota na ta zuwa ganin gida suna murna Mariya kwananta biyu sannan ta koma gida ta labartama Magajiya gidan Inna da yadda aka saka komai sabo, Bintu ce da gayya ta ke yi ma jama'a kwatance ana zuwa ana ta yabo da cewa Inna Meri ta samu muhalli mai kyau in aka ce waya siya mata gidan? sai ace babban ɗanta mana sai dai ki ji ana tambayan shi ko aikin me ya ke yi haka? sai ace  ai Babba ne a ƙwallon kafa, Jummai ta zo itama ta ga waje ita da su Gaje Magajiya dai da zuwaira bakin ciki bai bar su ba hatta su Baba Sani sun zo gidan nan da Auwalu sai ga su zaune a falon Inna suna hira sun ci sun sha wai yau sune ke yi ma Inna hira suna dariya, hasken wuta ko'ina da yake ana barin wuta sannan kuma Mansoor ya kira an duba za'a saka ma Inna Sola a gidan, Baba Ɗanjuma kuma ya zo ya yi kwanaki biyun sa kamar kada ya koma gidan wajen Magajiya da aka barta daga ita sai halinta ba mai lekowa gidan daga nan ta gane duk jama'ar na Meri ne ita kuma Maeesha gida iyayenta suka ce a maidata ta haihu acan gida daga magajiya sai halinta Mariya ma guduwa take yi gidan Yaya Zuwaira ko gidan su Walida.

  Kayan ɗakin Inna na da kuwa su Bintu suka raba a tsakaninau Kujerun da gadon Yaya Amina ta ɗauka tunda jinyar mijinta a lokacin ya sa duk ta saida kayan ɗakin ta Cafet kuma da sauran kayan amfani Yaya Halima ta ɗauka ta kuma ɗauki kula da sauran filet filet da yake komai na Inna sabbi ne Mansoor ya sauya mata sannan Mu'azzam haka, kamar kayan ɗakin wata Amarya sakin wawa Fridge ne kaɗai suka kaima Inna can gidan tunda daman ba su siya ba suka ce nata bai yi komai ba. Kaf suka kwashe koma ko roba ba su bari ba Sai ma datti da suka bari Bintu ce daman ta je ta rufe ɗakin ta leka ɗakin Magajiya ta ba ta key ɗin ta ce ta ba ma Baba in ya dawo ga shashen nan gabaɗaya Inna ta bar musu in ta ga dama ta koma ɗakin Innar gabaɗaya wannan dai ya rage nata. Sai ga Magajiya shuru ta kasa maida mgana da Baba Ɗanjuma ya dawo ya ba shi makullin shima cewa ya yi ta riƙe ta ba ma Saddiqu ya haɗa ma Matarsa duka ta zauna a ciki Meri ce kuma ta samu wani sauyim alheri, Ita dai ba ta je ba amman har Vadeo gidan Mariya ta ɗauko a waya ta numa mata tabbas Meri ta samu kyakyawan sauyi.

  Duk saboda abib da ya faru ya sa maganar Mimi ta ɗan sarara a ran Aji, amman kuma bai manta da mganar Mariya da ya ce za su yi da Auwalu ba ya same shi sun yi mgana ya ce ya san yaron zai bincika ita kuma Walida aka sama mata wani shagon koyon Computer za ta yi na wata shidda 30k Mu'azzam ya biya kuɗin ya ce tunda yayan na shi ya yi hidima, kuma da yake an san mai shagon ba matsala a  anguwan su Yaya Amina ne, za ta rika ziwa monday to friday daga karfe goma zuwa huɗun yamma.
Sai da ya ga ta fara zuwa sannan ya fara Samun natsuwa su Nasir har gidan sun zo gaida Inna shi tare da matarsa Nafisa ya zo Mu'azzam  ne ma yake gayamusu Makama ma yazo amman duk ba su samu Ajin ba sai daga baya Inna ke gaya masa zuwan su.

  Sai da kimanin sati biyu ya shuɗe da zuwansa kano  sabgogi sun saka bai kara neman wayar Mimi ba itama ba ta neme shi ba, amman dai ya na akan bakan shi na zuwa gidan da aka ba shi auranta.
Sai ya bari ranar lahadi da daddare saboda yadda zai same shi baban nata a gida. Shigar manyan kaya ya yi a ranar kuma ya je aka rage masa gashin kansa sai ya saka hula yana kamshin turare, bai je da mota ba sai mashin yana zuwa megadi ya gane shi, Shi kuma ya tambaye shi Alhaji na nan? Megadi yace ma sa Eh bai daɗe da dawowa ba sai ya ce ya shiga ya gaya masa Mansoor ne mijin Mimi.

  Megadi ya tafi da sauri ya isar da saƙo Daddy na tare da matansa a lokacin sai kawai ya yi yar dariya kafin ya ce" Ɗan tselan uwa ashe dai ya san in da zai zo ya samu masalaha,"
Kai tsaye ya ce a shiga ada shi falon baƙi, Mama na zaune ta ga ya tashi ya na saka hula kai tsaye ta ce"Sai ka saurare shi?  watan Mimin nawa a gida bai nemeta ba sai yanzu?
Ya na fita daga falon ya ce"In ji wa ya ce bai neme ta ba? Ke dai ba ki san komai ba, bari na je dai."
Anty ce kaɗai ta bi shi da adawo lafiya, Mama kuma haushi ta ji tana ta ya ɗan ta kishi yana ta murna kuma murna za ta koma ciki.





*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3008*

*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*

https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC

No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.


Mansor na tsaye a tsakiyar falon gidan tsohon Sanata Alhaji Hamza sulaiman Dabo. Hannayensa harɗe a kirjinsa, lokaci ɗaya yana nazarin falon, ya taɓa shigowa falon kusan sau biyu wani lokacin a can baya Mimi ta matsa masa ya shiga suka gaisa na farko rashin lafiyan Hajiya na biyu ya manta falilin.
A haka Daddy ya zo ya same shi yana tsaye bai zauna ba, yana ƙarisowa ya miƙa masa hannu suka yi masabaha.
Sannan Daddy ya nuna masa kujera ya ce ya zauna amman sai bai zauna ba sai ya zauna a saman tattausan cafet ɗin da ya malale fallon gabaɗaya saboda ya tuna wayar su da Mu'azzam yana hanyar tahowa nan ya yi ta hadadda masa ya je neman sulhu ne kuma surukinsa ne ya kamata ya nuna masa girma da daraja.

"Haba ka tashi ka zauna saman kujera mana."

Kan Mansoor na ƙasa ya ce"A aa nan ma ya isa Alhaji."

Sai Daddy bai ja ba kawai sai ya gyara zama suka gaisa yana tambayan shi wajen iyayanshi a sanyaye ya ce Alhamdulillah, shuru na wani lokaci ba daɗewa sai ga Anty ta shigo da farantin ruwa da lemu ta sauke nan saman center table ɗin dake falon, Itama Mansoor ya gaisheta ta amsa cikin sakewa kafin ta ce"Ah yallaɓai ya ka bar surukin namu ya zauna a ƙasa kuma?

Daddy ya yi mirmishi kafin ya ce" Biko ya zo shi ya sa ya ninka biyayyarsa." Tare suka yi dariya shi da Anty sannan ta fice shi ko Mansoor kansa na ƙasa domin sai ya ji Daddy ya yi masa kwarjini ya kuma rasa ta ina zai fara ma mganar, In hr Mimi ta faɗa musu dukkan abin da ya aikata mata ai da Kunya, Shi kuma Daddy nazarinsa yake yi ta gefen ido amman bai nuna ba, wata Jarida ma ya ja anan gefe yana karantawa kamar yadda Daddy ya yi masa kwarjini haka shima Daddy ya ga ƙwarjinin Mansoor ya cika falon gabaɗaya.

"Ka sha ruwan mana."

Daddy ya katse shi lokaci ɗaya yana kallon sa, sai Mansoor ya muskuta ya ɗan mike ya isa ga wajen ruwa ya saka kofi ya tsiyaya Kaɗan ya sha sannan ya ijiye kofin sannan ya koma in da ya tashi ya zauna. Shuru ya sake wanzuwa na wani lokaci kafin Daddy ya sake katse shurun da cewa" Ya wajen aikin na ku? Kwanaki abokanka da ƙaninka suka zo sun ce wasa gare ku masu yawa baka samun lokaci."

Sai ya samu kansa da amsawa da E, shi kuma Daddy sai ya jinjina kai kafin yac e"Good! Allah ya saka albarka," Aji ya amsa da Amin cikin yanayin maganarsa amman muryansa ta yi kasa sosai.
Gani ya yi Daddy ya yi kamar bai san dalilin zuwanshi ba, ya ma cigaba da karatun Jaridarsa lokaci ɗaya kuma ya na amsa waya in an kira shi.
Mansoor kuma na duke ya rasa ta in da zai fara dakyar ya iya kundunbalan ɗagowa ya na kallon Daddy kafin lokaci ɗaya ya fara da faɗin.

"Alhaji dama kan mganar Fatima ne.."

Sai ya dakata shi kuma Daddy sai ya kalle shi kafin ya ce"E, ina jin ka, Mimi ba ai ta dawo mana nan cikin kuka, ta ce ka ce ba ka sonta sannan ta ce za ta tafi ka ce is better da ta tafi ɗin, ni kuma da na ji haka sai na ce ai ba dole a cikin aure kuma in ka ga alaqa ta fara lalacewa gwara rabuwar shi ya fi alheri."

Mansoor ya yi shuru kafin yac e" Alhaji ni ban ce ta tafin da gaske ba"

"To me ya sa bayan ta taho a daran ko washegari ba ka biyo sahun ta ba, in ba ka nufin ta tafin ba?

Kai tsaye Mansoor ya gyara zama yana faɗin" Ina da dalilina Alhaji, saboda ka san su mata wani lokacin in ransu ya ɓaci gwara ka yi nesa da su su huce, na ga ranta ya ɓaci a lokaci to ba laifi ba ne domin ta dawo gida ta huta amman ba na nufin wai ta tafi saboda ba na sonta, in ba na sonta ai ba zan yarda na aureta ba. Kawai na bata lokaci ne ta huta sannan ta huce daga ɓacin ran da take ciki."

Magana ɗaya bayan Ɗlɗaya haka Manaoor ke fitar da ita, Daddy yana kallonsa amman yana mirmishi kafin ya gyaɗa kai ya ce"Na ji dalilin ka, ta wani fannin kana da ƴar gaskiyar ka ta wani fannin kuma ba ka da shi, amman duk ba wannan ba babban abin shi ne ga rashin ba ka sonta sannan ta ce ka kasa manta abin da ya faru a shekarun baya sai ka riƙa kallonta da abin, ka ga kuwa ai ba kyau irin haka riƙo ba shi da amfani sannan tunda har da bakin ka ka ce ba ka so ai ba wanda zai yi maka dole da sai ka zauna da ita ko ba haka ba?

Kan Mansoor Aji na ƙasa ya ce"E, ta nan kam ina da laifi, amman na gane kuskurena Alhaji a yi hakuri in sha Allahu hakan ba zai kara faruwa ba."

"Maganar rashin son fa? Ba zan ba ka bikon ƴata ba sai na ji gaskiyar mgana.*

Ya faɗa ya na ɗan haɗe rai. Sai Mansoor ya sadda kansa ƙasa cikin jin nauyi kafin ya ce"Ita ce ko a da, a yanzun ma ita ce har gobe da jibi ma ita ce, ɓacin rai ne ya sa na yi mata mganganu cikin fushi amman in sha Allahu hakan ba za ta ƙara faruwa ba."

Sai Daddy ya saki fuska yana faɗin" Alhamdulillah Allah ya sa na ji daɗin haka, ka burgeni yadda ka amshi laifukan ka sannan ka ce za ka gyara sannan na amince zan baka damar yin bikon matarka saboda dalilai guda biyu na farko ka yi laifi kuma ka amsa laifin ka, ka ba da hakuri sannan ka yi niyar gyara na biyu kuma na ji labarin ka je Abuja da kano ba ka samu ganinta ba hakam ma ya saka ni yarda da mganarka ta farko. Tabbas da farko da ta dawo gida da Koke koken cewa ita a raba auran ku in da ban yi zurfin tunani da duka rayuka sun ɓaci amman sai na bata lokaci kamar yadda ka ce itama ta sauka daga fushinta na tabbata a yanzu ba za ta so rabuwar auran ku ba sai dai daman an tauna aya ne domin tsakuwa ta ji tsoro. Sannan ina son na yi maka nasiha shi riƙo ba shi da amfani mu kasance ma su afuwa tunda Allah ma muma yi masa laifi, yana yafe mana kuma shi ya ce mu kasance masu afuwa, sannan shi kan shi Yaya Kabiru kafin rasuwarsa wallahi ya yi nadama kan abin da ya aikata maka kuma Hajiya da Brr. sun je sun yi mgana da kai sun kuma nema masa afuwarka sannan kafin rasuwarsa shi ya ce duk abin da Mimi take so a yi mata dalilin da ya saka aka yi auran ku bisa duk Sharaɗɗun da ka saka ka ga ba wanda ma ya maida kansa, To me ya sa kai ba za ka yi hakuri ka manta baya ba? Sai ka bar abu na shekaru ya hana ka sukuni da zaman lafiya? Shi kan shi Yayan ina yake yau ? Ai ba shi a duniya ya ma manta shi ya taɓa rayuwar duniya, ni ma ƙila ban sani ba nan kusa ne, wataƙila kaima nan kusa ne duk ba mu san gawan fari ba, sai fatan Allah yasa mu dace sannan ka sani Allah ya yi ma masu Afuwa wani babban tanadi, Ina ba ka shawaran ka manta baya don Allah domin samar ma kan ka da zuciyarka salama."

Gabaɗaya jikin Mansoor ya yi sanyi mganganun sun shiga zuciyarsa sosai daman kuma shi tuni ya saki wannan abun Sai ya ji kamar ana rage masa nauyin zuciya cikin jinjina kai ya ce"In sha Allahu komai ya wuce. na gode Alhaji Allah ya ƙara girma." Sai Daddy ya ji daɗi har ya nuna a saman fuskarsa ya kalli Aji Lokaci ɗaya yana faɗin" Na ji daɗin yadda ka saurare ni, da duka amincewata Mimi za ta koma ɗakinta, zan kirata da kaina na ce ta dawo amman sai ka same ta ku tattauna wannan kuma tsakanin ku ne ba zan shiga ba."
Aji ya rankwafar da kai yana godiya Daddy yace"Ba laifi. Na gode kwarai Allah ya yi ma rayuwa albarka

18 / 49