Idan An Ciza Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   22 / 49

63K to 66K   out of 146.6K words

amman yana ganinta sai ya ganeta ita ce wannan kawar ta Mimi wacce ba ta masa ba munafuka ce, illau ga shi yau ya ga shaida sai wani kyfta ido ta ke yi alamun ba ta da gaskiya.
Shi kuma cikin yanayin takunsa na masu karfi da Kuzari ya ƙarisa gabansu duka hannayensa zube a cikin aljihun wandonsa.

  Sai da ya zo gaban Mimi Sannan ya tsaya ya kuma saka hannu ya ɗan daga gularsa sama yana ƙare mata kallo daga sama har ƙasa ya juya yana kallon megadi na zaune a mazauninsa da radion sa ya na ji. Sannan ya juya ya na kallon Mimi Sai dai ba fara'a ko kaɗan a fuskarsa sannan Rukky dake wajen ko kallonta ma bai yi ba, sai ma ya yi kamar bai san da wanzuwar a wajen ba.

"Haka kike fitowa waje ba hijabi ba mayafi Mimi.?

  Haka ya fara faɗa lokaci ɗaya yana ƙara daƙune fuskarsa kamar wanda aka faɗa masa wani mummunan saƙo, Mimi ta kalli Rukky itama ta kalleta a ranta dai sai da ta ce mai hali baya fasa halinsa amman a fili sai ta haɗe rai itama ta juyar da fuska tana faɗin" Wa ya gaya maka na dawo? sannan me yasa ka zo ba Sanarwa?
Ta faɗa tana wani masa jijjigan jiki lokaci ɗaya tana taɓo hannayen Rukky wacce ta dukar da kanta ta ƙasa ta kasa  ɗagowa saboda Aji ya yi mata ƙwarjini ba ta ɗauka za ta kasa haɗa ido da Ajin in suka haɗu gaba da gaba ba.

"Alhaji ne ya gaya min kin dawo. Sannan domin zan zo wajen matata ai ba na bukatar ɗan saƙo."

  Haka ya ce mata yana kallonta cikin ƙara nazarinta da sauri ta kallesa kafin ta ce" Wani Alhajin? Kafin ya samu damar magana ta zaro ido tana faɗin" Wai Daddy ne Alhaji? Ba za ka iya kiransa da sunan Daddy ba kenan?
Ta faɗa cikin masa wani kallon kasa ƙasa, cikin mamakinta ya ce"Daddy kuma? To ai kinsan ni a gidan da aka haifeni da in da na taso, Inna da Baba muke cewa, in kin ji mun ce Alhaji alamamun girmamawa ne."
Ita kanta ba ta san ta masa wannan kallon ba sai da ta ga ya yi mirmishi wanda tun zuwansa wajen bai yi ba sannan ya ce"To na bari, Daddy ba shike ban ba?
Sai ta gyaɗa masa kai, kawai sai ya gyara tsayuwa a ransa ya na faɗin"Rigimammiya kawai."
Rukky ce ta ga kamar Har Mimin ta manta da ita. Sai ta matsa gefe tana faɗin" Mimi zan tafi, yamma ta yi"
Ta gama faɗa lokaci ɗaya tana duba agogon fatan dake tsitsiyan hannunta na hagu sai a lokacin Mimi ta tuna da ita domin har ga Allah in tana gaban Aji mantawa take yi da kowa da komai ciki har da ita kanta ma.

"Aji ga ƙawata Rukkaya, Rukky ga Aji ku gaisa."

  Mimi ta faɗa cikin Mirmishi tana kallon su duka, Aji ya yi shuru yi ya yi ma kamar bai ji ba sai can ya ce"OH na ganta."
Daga haka ya juyar da kansa yana kallon wani ɓarayin Rukky ta watsa ma Mimi wani kallo ita kuma tana faman roƙonta da hannu a kan ta gaishe shi abin da ba su sani ba duk yana kallonsu ta gefen Ido, abin da ya bashi mamaki ita yanzu ƙawar Fatima Jira take yi ya gaisheta? Amman yarinyar ba ta da hankali ya fara tunanin haka.

"ina yini"

  Haka Rukky ta faɗa Kamar ba ta so. To daman dole Mimi ta saka ta, sai da ya nishaɗu sannan ya juya yana kallonta lokaci ɗaya yana faɗin" Barka da ƴamma"
Sannan sai ya juya yana kallon Mimi kafin ya ce"Na ɗauka tana jiran na gaisheta ne."
Sai Rukky ta ji kunya ya kamata da sauri ta ce"A'a na bari ku gama gaisawa ne."
"Gaisawa? da wa? Ba gaisuwa muke yi ba ko kin ji sanda ta gaishe ni?
Sai Rukky ta kasa mgana shi kuma sai ya cigaba da faɗin" Ko ita ƙawar taki ba ta isa ta zauna in gaisheta ba, koda nake auranta ba ta isa ba."

  Daga Rukky har Mimi kai suka jinjina, kafin Rukky ta ce"Ta cancanci ka gaisheta mana, ka fa ba ma ƙawata wahala."
Ta faɗa tana yar dariya mirmishin gefen baki ya yi kafin ya ce" Ita kaɗai?  ba ta gaya miki nima ta ba ni wahala ba? Mun ba ma juna wahala shi ne gaskiyan magana."
Ya faɗa yana kallon Mimi ita kuma sai ta harareshi ta na tura masa baki har sai da ya yi yar dariya Rukky na tsaye tana kallon Ikon Allah a tunaninta Mimi ba za ta sakar masa fuska a zuwan farko amman kalli abin da take yi. Shi kuma agogon hannunsa ya duba kafin ya kalli Mimi ya na faɗin" Kina  da mintina goma,ki sallami baƙuwar ki, ina son mgana dake."
Yadda ya yi maganar cikin ba da umarni ya sa Mimi ba ta ga damar masa musu ba sai ta ce ya shiga falo ya jira ta bari ta taka ma Rukky kamar zai ce rakiyar ba ta isa haka nan ba sai ya fasa bai shiga cikin gidan ba ya tsaya nan yana jiranta daga in da yake suka matsa gaba kaɗan yana gani Rukky na ta magana Mimi na marairaicewa kamar hakuri take ba ta shi fa baya raba ɗayan biyu duk abin da Mimi ta aikata ba tunaninta ba ne tunanin wannan ƙawar ta ta ce, kuma daman tana da fuska da yanayi na munafukai.

  Dole Mimi ta sallami Rukky ganin uban gayyar ya kasa ya tsare ta na fita daga get ɗin Mimi ta dawo wajensa tana faɗin" Ba ka ciki ba ?
Kai tsaye ya ce"Ke nake jira, sannan kada ki ƙara fitowa a haka ba ki saka babban mayafi ko hijabi ba."
Baki buɗe ta ce" A cikin gidan?
Kansa ya ɗauke kafin ya ce"E na dai gaya miki."
Yanayin yadda ya haɗe rai ne ya sa dole ta yi shuru tana gaba yana Binta a baya har zuwa falon gidan Hajiya ta ce ya zauna sai ya samu kujera mai zaman mutum biyu ya zauna ita kuma ta ce tana zuwa.
Sai ta juya tana tafiya ya bi ta da kallo yana haɗiyan miyau har ta ɗauke ma ganinsa Ajiyar zuciya ya sauke dole ma ya ijiye duk makaman yaƙin sa matarsa yake bukata cikin lokaci.

  Ɗakin Hajiya ta fara shiga ta isketa tare da Baaba Uwani suna mgana ta gaya mata zuwan Aji sai ta koma ɗakinta domin ta gyara fuskarta, ita kuma Hajiya ta fito tare da Baaba Uwani ta gaishe shi ya amsa cikin yanayinsa sannan ta shiga kitchen ta kawo masa ruwa da lemu, Hajiya kuma har kasa ya sauka ya gaisheta ta na masa tsiyan ba ta ce in Binta ba ta son auran ita a zo a yi da ita ba kansa na ƙasa ya ce shikeman in ta ƙi komawa sai ya zo kawai su daidaita Hajiya na ta dariya bayan tambayan su Meri ya ce tana gaisheta kai tsaye Hajiya ta ce"Ai ka gaya mata na ce na yi fushi, tunda abun nan ya faru ban ganta ba sannan ba ta kirani ba." Mirmishi kawai ya yi ba tare da yayi wata magana ba, nan Hajiya ta bar shi ta shige ciki ta je ta na yi ma Binta tsiyar ta shanya shi, ita kuma har kaya ta sauya daga baya sai ta fasa domin zai ɗauka ta hakura ne tunda har da kwalliya sai ta maida wanda ta cire har da saka uban hijabi sanda ta dawo falon yana zaune ya gama shan ruwa kenan kujeran dake kallonsa ta zauna shi kuma ya na kallonta daman tun shigowarta. Cikin mamaki ya ce"Wannan hijabin fa?  fita za ki yi ne?.
Kai tsaye ta ce"A'a ba kai ka ce na riƙa saka hijabi ko a cikin gida ba ne?

  Dariya ta ba shi har sai da ya dara sannan ya kaɗa kai kafin ya ce"Kin yi nesa da ni, ta ya ya za ki iya jin abin da zan faɗa? Ki matso nan domin ba zan ɗaga murya ba."
Ya faɗa yana nuna mata kujeren dake gefensa mai zaman mutmn uku ba musu ta miƙe ta koma nan ta zauna sai da suka ɗauki wani lokaci kowa na sake saƙe sannan Aji ya yunƙura kaɗan yana faɗin"Ina fatan hutun da kika yi ya ishe ki?.
Kallon bangane ba ta yi masa sai ya cigaba da faɗin" Na san ban kyauta ba. Mu manta abin da ya faru a baya Mimi ki dawo gare ni domin na nuna miki komai ya wuce."
Kai tsaye ta kalle shi domin ta ga da gaske yake yi sai kawai ta kauda kai kafin ta ce"Ni fa na ɗauka takardan saki na ka kawo min."
"Subhanallah, ki daina wannan zencen ni ban aureki domin na sake ki ba"
"To ana dole ne? tun da  ka ce ba ka sona? Sannan ba za ka iya daraja iyayena ka manta abin da ya faru saboda ni ba, ni ma kuma ban ga laifina domin na ce ba zan cigaba da zama da kai ba."

  Yadda take mganar da alamun abin na taso mata ne domin kamar za ta yi kuka,  huci ya fitar daga bakinsa kafin ya ce" ɓacin rai ne ya sa duk na faɗi wasu mganganun, ki yi hakuri."
Mamakin yadda ya yi saurin laushi ta yi sai ta kalle shi shima ita yake kallon cikin irin kallon nan mai kassara oafiyan jikin ƴa mace, ita ta yi saurin kauda kanta kafin ta ce" Wasu mganganun?  kamar su wanne kenan?
Bakinsa ya ciza leɓen kasa kafin ya ce"Na ƙaryata kaina Mimi, ke sai ki yarda cewa ba na son ki?
Ya faɗa cikin wani sauti ba ta son kallonsa Saboda kada ya ga rauninta kanta na gefe ta ce" Na yarda tunda da bakin ka ka faɗamin alfarman Hajiya da Mommy nake ci."

  Bai san ya aka yi ba shi dai kawai ya gansa zaune kusa da Mimi kafaɗanta na dukan Kafadansa haka itama taji mutum zaune gefenta kafin ta samu zarafin mgana ta ji kawai ya yi mata wani irin riƙo mai karfi lokaci ɗaya yana faɗin" Shike nan kuma sai ki yarda da duk abin da na ce? Ke ba ki san bacin rai ba? Raina ne ya ɓaci shi ya sa na faɗi haka."
Ya faɗa cikin sanyin murya ta ɗago tana kallonsa shima ita ya ke kallo,ta buɗe baki za ta yi mgana kawai ya saka hannunsa samman bakin yana faɗin" Shiii."
Sannan ya hura mata iskar hucin zafin ɓakinsa kusan suman zaune ta yi kafin ta dawo hayyacinta ya yi mata magana cikin raɗa raɗa kamar wanda ba ya so a ji.

"Ke ce ta farko, ke ce ta biyu ke ce har ta uku da ta huɗu. Sannan ke ce a baya da shekaranjiya  yau da gobe  har da jibi da gata, ke na zaɓa ke ma kinsan ba zan iya daina son ki ba Fatima."

Ya faɗa ya na kureta da kallonsa, kasa jurewa ta yi sai ta kwace kafaɗanta ta matsa baya tana sauke numfashi.

"Allah da gaske nake yi, ba ki yarda ba ne?

  Numfashi ta ja ta sauke kafin ta ce" In hakane kana sona? Me ya sa da na ce zan tafi ba ka hana ni ba? Cewa fa ka yi wai is better na tafin"
Cikin dafe kansa ya ce"Mimi. Ke wai ba ki san gatse ba ne? Ni fa gatse na yi miki ban taɓa tunani  za ki yi fushi ki taho gida ba wallahi"
Wata harara ta yi masa kafin ta ce"Ai dole na zauna tunda ni ba ni da zuciya sannan ban san ciwon kaina ba."
Da sauri ya ɗaga hannayensa sama lokaci ɗaya yana faɗin"ba haka na ke nufi ba, ni dai ki yi hakuri ki saka ranar da za ki koma don Allah."
Shuru ta yi masa ganin haka ya sa ya matso kusa da ita, ba ta sani ba sai jin maganarsa kawai ta yi a kusa da ita.

"Kin ji My Mimi? Komai ya wuce ko?

  Da Sauri ta matsa can karshen kujera kafin ta ce"A a.
Cikin mamaki ya ce"To me ya rage? Na amsa duka laifukana na kuma ba da haƙuri."
"Akwai saura?
Haka ta faɗa ta na kallonsa shima kai Tsayen ya ce"Me ya yi saura kuma?
Kai tsaye ta gyara zama tana faɗin" Matsayin Mahaifina a wajen ka nake son sani yanzu, domin ba zan cigaba da zama da kai kana kiransa da azz.."

"Ya isa. Haba Mimi na ce fa na yi nadama ki yi hakuri mana."

  Ya katseta da sauri domin yana jin kunyar sunan da ya kira mahaifinta da shi , ita kuma sai kuka cikin yar shagwaɓa ta ce" Kai fa ka kira shi da hakan"
Da sauri ya ce"Ai ban yi gaddama ba, na tuba bazan kara ba kin ji ko?
Sai ta ɗago tana kallonshi Idanuwanta duk hawaye kafin ta ce"Ka na nufin ka yafe duk abin da ya faru.?
Shuru ya yi na wani lokaci kafin ya ce"Eh na yafe masa, na gane riƙo ba shi da amfani, na yi miki alkwarin ba zan ƙara duban ki da wannan abun ba. Sannan zan ɗauke shi a matsayin kaddara in sha Allahu."
Cikin jin daɗi ta ce"Da gaske kake yi?
Sai ya jinjina mata kai kafin ya ce" In sha Allahu, Allah ya jiƙan Abi ya sa ya huta."
Mamaki ya kama Mimi ba ta san lokacin da ta fara dariya ba ga hawaye lokaci ɗaya cikin girgiza kai ya ce"Kin ji daɗi? Ina fatan komai ya wuce?
Ta na goge hawayenta ta ce" Eh, tunda ka yarda ka yi kuskuren  kuma ka amsa za ka gyara, shike nan nima na haƙura."
Cikin jin daɗi ya ce"Nago de, to goge hawayen shagwaɓɓiya mai kuka da dariya kawai."
Hararansa ta yi ba ta yi mgana dukkansu zukatansu ya cika da farinciki.

"Yaushe za ki koma? Yau ko gobe?

   Kallonsa ta yi a karkace kafin ta ce"Ko zan koma sai ka amince da wasu sharuɗɗai na nima, a baya kai ka saka naka nima a yanzu lokacina ne ma gindaya maka naka."

  Baki sake ya ce"Topha, ka ji wata sabuwa."
Tana murgaɗa masa baki ta ce"Ba dole, in ba ka amince ba sai n ace na fasa komawa."
Da sauri ya ce" WANE AJI? shi ɗin banza zayyano su ki kaddara ma duka sun tabbata."
Tana dariya ta miƙe lokaci ɗaya tana faɗin" Komawa na tare da wannan sharuɗɗan guda ɗaya in ka tsallake ba zan koma ba."
Tagumi ya yi kafin ya ce"Ya na iya? Tun da ɓarawo ya shiga hannun mata ai ya shiga uku."
Yadda ya yi mganar ne ya sa ta ƙyalkyalce da dariya  Shi kuma ya na kallonta da Mirmishi ta juya kenan sai ya kira sunanta.

"Mimi.."

  Sai ta juyo tana kallonsa sai kawai yace"Amman dai mganar kin samu ba da gaske ba ne ko?
Tana ɗage masa gira ta ce" Da gaske ne mana, in baka amince da sharuɗdana ba da shi za'a yi."
Nan da nan ya haɗe rai yana faɗin" Kin san dai kina da ma tarin laifi wajen Ubangiji, kin yi ta zuwa garuruwa ba tare da izinina ba, in kuma ban yafe ba Allah ba ki sha ba."
Kugu ta riƙe lokaci ɗaya da  bakin tana faɗin "Ba ka yafe ba ka ce! To ai da izinin ka na je ko'ina tun da kai ka ce na je duk in da nake so."
Zai yi mgana ta yi saurin cewa"Ka yafe ko ba ka yafe ba?
Yanayin yadda ta tsare shi da ido ya sa ya koma ya jingina da kujera kafin ya ce"Wannan shi ne a dake ka, sannan a hana ka kuka, ya na iya?  Na yafe."
Ya faɗa kamar ba ya so, Mimi ta saka masa dariya ta juya tana wani irin taku zuwa Koridin da zai sada ta da ɗakunan su.
Shi kuma ta barshi da bin ta da kallo kamar wani sauna kira mana shashaaha.

  Ta na shiga ɗakinta ta buɗe wata ƙaramar jakarta dake rataye ta ɗauko biro da takarda a cikin wani Memo ta yanka na bikin Biban su Dukky ne. Da farko ba wannan zencen sharuɗɗan amman yanzu ta ji ta na so shima ta jarabasa, kai tsaye ta fara rubutu bayan ta zauna a saman gado, wasa dai da ta kusa cika takardan nan da rubutu sannan ta ninke ta, ta koma falon ta miƙama Aji lokaçi ɗaya tana faɗin"Sai ka koma gida sannan ka buɗe ka karanta a tsanake, in ka amince sai ka yi ticking ɗin duka sannan ka saka hannu a ƙasa, nima sai ka dawo min da takardan na saka hannu, sannan saɓa alkwarin mu dai dai yake da sunan ba zan koma ba."
Karɓan tarkadan ya yi lokaci ɗaya yana faɗin" Kamar Interviuw ɗin ɗaukan aiki?
Hararansa ta yi da sauri ya ce"Sorry Matas"
Ita kuma sai ta koma tana wani hura hanci bai daɗe ba ya ce zai tafi saboda bayan mangariba zai gana da Coach ɗin su ya ce yana son ganin shi, ko Hajiya bai tsaya ma sallama ba ya ce Mimi ta gaya mata da zai tafi ko rakiya ba ta yi masa ba sai da ya ce"Matas ba rakiya?.
Kai tsaye ta ce"Sai ka cike sharudɗanmu tukkunna"
Sai ya jinjima kai kawai ba tare da ya yi magana ba.

  Shi dai yana mamakin me ta rubuta? Me kuma take so? Ya san dai ba za ta ce kuɗi ba, Saboda zaman da za su yi da Caach ya sa bai samu damar duba takardan lokacin da ya koma ba.Sai wajen ɗaya suka gama Meeting ɗin ga shi ya gaji ga shi ya na jin yunwa amman hakanan ya kwanta bai duba takardan ba, da Safe kuma yana cikin barci wayar Inna ya ta da shi ta ce ya fita bakin Camp ɗinsu Walida ma jiran shi.
Ya yi ta mamakin lafiya riga ya saka ya fita ko da ya je ma ba kowa ya na shirin kiran Inna sai ga Walida ta sauka daga mashin, Da kwandon abinci riƙe rike sai da ya yi hawaye Allah sarki uwa.
Cikin ɗan faɗa ya kalli Walida yana faɗin"Inna ta ba ki wahala?  ba shago za ki tafi ba? Sai ta gyaɗa masa kai kafin ta ce"Eh, ita ta ce na biya na kawo maka.".
Sai ya karɓa yana yi ma Inna fatan Aljjana acikin ransa mai mashin ɗin bai tafi ba shi ya

22 / 49