Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
ladan Kabarin Abi, bayan ta shirya ta ɗauki kanta hoto ta tura ma Aji sannan ta fita zuwa ɗakin Hajiya su ka gaisa Hajiya ta ga sai faman nishaɗi take yi cikin zolaya ta ce"Binta dai za'ayi kome ko? Daman ance kome ai ya fi sabon aure daɗi ko?
Mimi ta rufe fuska tana dariya kafin ta ce"Kai Hajiya ta"
Hajiya na ƴar dariya ta ce"Ai na gano ki, tunda Mansoor ya zo ranar nan kike cikin nishaɗi, to gaya min yaushe ne komen na mu.?
Mimi ta zauna kusa da ita lokaci ɗaya tana sagala hannunta saman Kafaɗan Hajiya tana faɗin" Saboda ginin da za'ayi ya ce sai bayan sallah lokacin duk na gama sauran shirye shiryena."
Hajiya na Mirmishi ta ce"Ya yi kyau, To gidan shi da aka ce ya gina fa?
Mimi ta ce"Ban gaya miki ba? Ai Inna Meri ta koma gidan da zama"
Nan Mimi ta ba ta labarin da Hibba ta gaya mata ta ƙara da cewa" To shi ne ya ce yana da fili gwara a gina kawai."
Hajiya ta jinjina kai kafin ta ce"Ma sha Allah, na ji daɗin haka Allah ya sa albarka, ke kuma da ku ke mganar tsayawa wasu shirye shiryr? Me za ki shirya? Na ga dai komai kina da shi?
Mimi ta mike tana dariya kafin ta ce"Ke fa kika ce kome ya fi sabon aure daɗi ko?
To ai sabon biki zan yi da zai tabbatar da Komen da zan yi ya fi sabon aurana na farko."
Kafin Hajiya ta samu bakin mgana Mimi ta fice da sauri tana faɗin" Sai na dawo Hajiya za mu yi mgana."
Hajiya ta bi ta da Allah ya tsare tana Cigaba da jan casbahanta lokaci ɗaya tana wani mirmishin jin daɗi. Farincikinta ta ga Binta ta koma ɗakinta ta yi zamanta cikin Salama.
****
KARAMCHI TV
Ma'aikatan Karamchi kowa ya yi murna da dawowar Mimi, bakinta ita kuma ya ƙi rufuwa sai gaisawa take yi da mutanen arziƙi, wani farinciki na ratsata sun gaisa da Salim Bunza ya na zolayanta da cewa"Tunda kin dawo nima ya kamata na ɗauki hutuna nima."
Cikin Magiya ta ce"Ka rufamin asiri mana Bunza, in ka tafi yanzu ai sai aiki ya nemi kashe ma mijina mata."
Sai kawai ya yi mata dariya Na Misau na gefe ya ce" ƙila ma sai ya haɗa mana da zanga zanga."
Suna ta raha da nishaɗi. Ta je Office ɗin Manaja suka gaisa shima sai da ya yi mata tsiya" Na ɗauka wannan rigimammen mijin naki ya hana ki dawowa aiki damu ne gabaɗaya.?
Mimi na dariya ta ce"Ko ɗaya yallaɓai kawai dai ba na gari ne har Umra na je na dawo kuma matar Yayana ta haihu na tsaya sai da aka yi suna na dawo, nan ɗin sai da na zauna na huta tukunna."
Ya na jinjina kai ya ce"To ai shinke nan muna yi miki barka da dawowa."
Daga nan suka tattauna abin da ya shafi aiki kafin ta haɗu da editor ita ta karanta labaran safe na ranar oaraba. Jama'ar gari na ta nurnan ganinta domin wasu har sun gaji da tambayan Ina Mimi take a tunaninsu ta daina aiki da gidan talabijin na karamci ne ne sai kuma kwatsan a ka ganta ta yi kiba ta yi bul ɓul, kamar ba ita ba har wasu ma su kallon tashar suka ce kamar tana da shigar ƴaron ciki.
A cikin waɗanda suka kalli labaranta na safiyar ranar har da Inna Meri da Walida da kuma Maeesha dake can gidansu tana jego, Tuni ta ji kishi ya kama tana ganin Mimi, ta tabbatar da kome za ta yi ba za ta kama kafar ta ba. Sannan ta ji a bakin matar Auwalu cewa ba sakinta ya yi ba, kenan auran su na nan za ta iya dawowa a kowani lokaci kila ma a katon gida na alfarma kamar yadda Inna ta koma katon gida na alfarma duk da ba ta je gidan ba amman ta ji labarin tsaruwan gidan a bakin Mariya ta kuma ji labarim komai sabo ne, ita a ganinta ita ya dace ta riƙa samun wannan abubuwan ba wasu ba. Sannan ita ya kamata ta zama a bar kwaten ce ba wata can ba.
Bayan komawrarta gida ba daɗewa ta haihu samu mace kuma Saddiqu ya ce sunan Magajiya zai saka ma ƴarsa, asalin sunan Magajiya Mardiya ne da farko ita Maeeshan ta ɗauka Magajiyan ne sunan har ta fara bala'in ba mai sakan ma ƴarta suna Magajiya sai daga baya ta ji sunan ashe Mardiya ne sai ta koma ta yi laushi, An yi suna na karya da garari duk abin d Saddiqu ya ce ba shi da shi sai Maeesha ta ce bashi ne aka ci zai biya daga baya, Ita kanta Magajiya sai da ta raina kanta ta kuma gane amfanin Meri da uaƴanta a tare da su da ace suna gidan komai na sha'in taron suna da kuɗi ba zai yi mata wahala ba, itama ta yi taron suna a nan gidan amman dakyar aka samu a ka yi fate, Auwalu ne ma ta samu dubu goma a wajensa zuwaira biyar amman Jummai tana nema itama. Kuɗin da za ta haɗa ma a siya zannuwan suna ba ta da shi sai da ta ci bashin Atamfa da rigar yarinyar sai Inna Meri itama ta yo turmi, sai da Bintu ta hana ta amman ta ce ba ruwansu ta kuma matsa musu suma sai da suka leka sunan nan gidan Wanzamai daga nan suja wuce gidan su Maeshan.
Har Gaje na yi musu tsiyan tunda Inna ta bar gidan suka daina ganinsu, Yaya Amina ce ma ke ba da hakuri amman Bintu cewa ta yi" To me za mu zo mu yi muku? Tunda daman wacce muke zayan domin ta kun kore ta daga gidan? Ai ita ce mu , mune ita dole ko ku daina ganin mu ai ga gidan nan mun bar ma masu gidan sai su haɗa duka su yi ta zama har ranar busa ƙaho."
Saboda su Zuwaira ta yi mganar su ma dai ba su tanka ba. Sai ga shi ko Kunya Zuwaira ta ja Yaya Amina gefe ta na mata mganar, In sun zo da abun suna don Allah su kawo a haɗa anan ana haɗa na dangin uba ne daga bangaren su, sai Yaya Amina ta ce bari ta yi ma su Halima magana.
Aiko dai Halima ce kaɗai ta ba da 5k, Daman ita Yaya Amina rigar ƴarinya ne da kuma pampers, Bintu kuma da Yaya Amina ta yi mgana sai ta ce ita kam ba ta da shi kuma ba za ta matsa ma kanta ba ashe sai yanzu aka san su ma ƴanuwan Saddiqun ne ƙiri ƙiri kuma su san tana da shi amman ta ce ba ta da shi dole suka ƙyaketa sana'ar saida ruwa take yi da zoɓo amman Bintu kafiya gare ta abin da ba ta yi nyya ba, ba mai sakata dole.
Sai ga shi tafiya ma can gidan mai jegon Jummai ta ce su jira zuwa la'asar su tafi gabaɗayansu sai a tafi da kayan gabaɗaya shi ya sa suka jira, Inna Meri daman ba ta zo ba tana gida tare da yara. Su ne sai wajen biyar da wani abu suka isa gidan su Maeesha suka iske a na ta shan DJ.
Mai jego ta ci gayu har da mai kwalliya ta ɗauko da mai hoto sannan sun yi abinci mai rai da lafiya har da Alala da zoɓo an tarbesu dai sama sama sai da ma suka buɗe kayan da suka kawo ne sannan suka ga ana ta duban juna ana taɓe baki, Atamfa biyu ce cotoon ɗaya ɗayar roba ce sai rigar ƴarinyar guda uku da sabulan wanka da Pampers ɗin Yaya Amina, kuɗin kuma ba su san ina a ka siya fallayan zannuwan guda biyu wai Mejego sai ta yi goyo da shi, Gaje ce ke kora wannan bayanin Amman ko alama ba su ji daɗin wannan kayan ba ko godiya nan in da suka sauke kayan nan aka bar su kamar sun kawo kashi Binta na ta dariya ƙasa ƙasa ga shi kuma Walida abokiyar gulmarta tana wajen koyon Computer, Mariya dai daman a gidan ta kwana tun jiya ta na can waje cikin ƴan rawa anman ta zo ta gaishe da su Yaya Amina har ta na zolayanta da Amarya tunda an saka ranar auranta Shekara.
Ko Jaririyar ba'a ba su sun ɗauka ba sai da Yaya Halima ta yi mgana sannan Maeeshan ta kawo musu. Su kuma aka fi ma sakar ma fuska tunda an gan su sharr ba wahala a jikinsu barin ma Bintu da take ta wani shan ƙamshi ko gaishe da mejegon ma ba ta yi ba, ana ta gulma dai a gidan ana raɗan su waye su Bintu? Maeesha ta ce ƴayan Inna Meri ce ta bangare da ta koma matar da ta zo ta yi ma Jinjira wanka ta mata gashi, Domin Inna Meri ranar da ta zo barka har Maeesha sai da ta ji kunyar abin da ta aika mata nuna komai ba komai ta yi ba ta zage ana ta hidima da ita a lokacin yarinyar tana kuka ashe xibiya ce ba a yi gashi ta kume nan fa ta ce a saka ruwan zafi ta zauna tana ta ga shin cibiya sai ga Yarinyar ta yi shuru tana raba ido washegari kuma ta dawo ta kara yi mata ta shafa mata wani mgani a daran cibiyan ta faɗi. Sannan tunda aiki a ka yi ma Maeesha sai ta ba su shawaran kada ta yi wanka ganyen yanzu sai zuwa gaba amman a riƙa yi mata da towel kada jikinta ya ɗanyan ce amman ta ce a riƙa ba ta abinci sosai kuni da ruwan shayi tana sha saboda shi zai taimake ta. Uwar Aishan ta ji daɗi domin ita ce yar fari ba sanin haka ta yi ba.
Kafin su bar gidan nan sun ga abu har hoto ma suna gani ana yin hotuna ba wanda ya gayyace su, Bintu ce ma da shegen neman mgana ta shiga hotunan bayan ta ɗauki Jaririyar ta rike su Zuwaira dai sai rakuɓewa a gefe kamar wasu almajira shi ya sa ana kiran sallar mangariba suka yi musu sallama daga gidan suka rabu, Yayan Inna Meri can suka koma gidan ta saboda ɗauko yaran su Zuwaira kuma suka yi gidan Wanzamai suna ta ƙananun mganganun wulakancin da aka yi musu suka koma ma da Magajiya abin da ya faru, To me za ta ce? Baba Danjuma ma ko sisi bai ba da ba ya ce ba shi da shi yanzu ta fahimci in ta cika ma matsa masa sai ya hau masifa yana maganganu, Kamar kada Inna Meri ta bar gidan shik enan ta koma ta yi sanyi kamar ba ita ba.
Saddiqu daman ya gaya mata duk kuɗinsa sun kare wajen aikin nan da aka yi ma Aisha, Duk abin da ma za ta yi na suna ya ce ta ci ba shi abinci ma da sauran su duk iyayenta ne za su yi da kuɗin su. kudin aikin ma sai da ya Kira Mu'azzam ya taimaka masa da 100k tunda an ce za'a yi aikin amman ba shi da ko dubu 20 dole dai ƙanwar naki ƴaƴan Inna Merin da suka ci ma mutumci sune su ke tallafe da su, Shi kuma Baba Danjuma ya koma gefe kawai ya saka ma Magajiya ido daga ita har ƴayanta ya ga in da hassada za ta kai su.
Shi har Allah Allah yake yi kwanakin girkin Inna su shiga in ya tafi can ya fi samun kwanciyar hankali da natsuwa, in ko yana wajen magajiya ko fara'a ba ya y. Saboda Magajiya tun da ya aureta bai taɓa samun kwanciyar hankali da ita ba ko da yaushe masifa da bala'i.
****
Ana azumi saura kwana huɗu Mansoor ya koma gidan Hajiya Wajen Mimi, ya iske Yaddiko ta zo duba Hajiya da ta ganshi sai da ta ce ma Hajiya" Sun daidai ta kenan?
Hajiya ta ce"Eh, tace bayan sallah za ta koma in sha Allahu." Yaddiko ta ce ya fi mata tunanin kashe auran da take yi,Hajiya tace daman ba da gaske ba ne duk shegentaka ne.
Yau bai wani jima sosai ba. Ya dai kawo mata zanen da mai zane ya yi na tsarin gidan ta ce komai ya yi yana faɗa mata har an fara saka doundiom in sha Allahu za'a gama cikin wata ɗaya da wani abu tunda akwai kayan aiki, abincin ma da ta yi masa sai dai ta kwashe masa ya tafi da shi saboda ana jiransa ne za su yi meeting a Camp, Ita daman Mimi da Rukky kaɗai take shawara kuma itama ta ce duka tsarin Mimi ya yi dai gwwra dai yasan yanzu mai daraja zai ɗauka, bayan Rukkyan kuma ba ta gaya ma kowa ga abib da ke faruwa ba Hajiya dai ta yi mgana da Mommy ta kira ta itama ta gaya mata sai bayan Sallah Saboda ginin gida haka ma ta gaya ma Daddy da ya zo gidan sai ya ce ai Mansoor ɗin ya kira shi sun yi magana, sannan ya ƙara da cewa"Ki yi hakuri Mimi kin ji ko? Kin ga ribar hakuri ga shi yanzu gidanki ke kaɗai yake ƙokarin samar miki, shi ya sa akace komai mai wucewa ne"
Hajiya ta amsa masa da wannan gaskiya ne sun rabu da cewa duk abin da take so, ta kirasa kawai shi uba yake gare su in sha Allahu komai zai yi musu in dai yana da shi, Har khadi ta kirata sun yi mgana shi ne Khadi ta ce"Ai sai ki zage da gyaran Headquater saboda ya san da, da kuma yanzu akwai bambamci."
Dariya kawai ta yi, amman ta ce za ta yi har gyaran jiki tunda wancan lokaci duk a firgice take ba ta yi komai ba. Har Dr da Jawahir sun kirata amman ban da Madiha itama ko ba ta ko nemeta ba, saboda haka ta dai fahimci har abada suna da bambamcin rayuwa da ra'ayoyi ita da Madiha kuma dukkansu ba za su samu daidaito ba, kowa kawai ya tsaya kan ra'ayin sa.
Maganar haɗa Lefe kuma Mimi ta dage ta ce tare za su riƙa shiga kasuwa da Aji. Ya yi kokarin zamewa amman ta ce in ba zai iya samaar mata lokaci ba sai a bar siyan kayan dole ya se su riƙa shiga da weekend tunda ba ya samun lokaci, ba ma haka ba shi kunya yake ji ba zai iya tuna ranar da ya shiga kasuwa da sunan siyayya ba, in kayansa ne Store yake zuwa yawanci kuma yaddika da Shaddodi Ahmad yake turama kuɗi ya siya ya ɗinka masa daga can Kaduna.
Shi daman ta bangarensa daga Mu'azzam sai Inna kawai ya yi mgana da su, ko Baba bai samu sun haɗ ba, ballantana su yi mganar sai Auwalu da kwangilar ginin ke hannun shi, Inna meri ta yi ta saka albarka filin ya na can wata anguwa mai suna Dubai quaters anguwan ta masu hannu da shuni ne gaskiya shi ya sa tun a lokacin da ya siya filin ya na da daraja, Inna Merin ce ta gaya ma su Amina halin da ake ciki sai Bintu ta ce kwanaki ta kira Mimn ta ce mata in sha Allahu bayan sallah za ta dawo suma suna ta murna kada Mu'azzam da Hibba su ji labari ita da yanzu ta ke fama da oaulayi domin ana shirin maida Junior sai ga ciki ya ɓulla dole a ka rabu da shi sai Bayan Sallah tun da Mu'azzan ya ce anan za su yi sallah in za su koma sai su tafi tare da shi.
Bangaren su Nasir kuwa ba kiran su ya yi ba, a group chart ɗin su ya shiga ya yi sallama sannan ya yi tagging ɗin Nasir da Makama sannan ya yi mgana." Ba dai kyau gaba a musulunci, ni na kwashe ladan Assalamu Alaikum"
Sai da suka yi mamaki domin tunda aka buɗw group ɗin a ka saka shi ko kala bai taɓa cewa ba sai ranar.
Makama dai ya tanka ya ce su ba gaba suke yi da shi ba, shi ne dai ya nuna ba su da wani matsayi a wajensa, shi kan Nasir ya gani sai ya yi kamar bai gani ba, Makama kuma sauka ya yi ya kira wayar Aji suka yi mgana Daman Sarkin zuciyan Aji ne da Nasir, Ya dai ba shi hakuri har kuma ya yi masa bayanin yadda a ke ciki, makama yace zai zo su haɗu domin ya je ya ga ginin.
Nasir kuma sai da Aji ya dauke girman kai ya kira shi sannan suka daidai to. Ranar asabar ranar da aka tashi da azumin farko suka haɗu da yamma a can filin in da a ka fara ginin har ya kusa kaiwa linter.
Nasir ya daki kafaɗan Aji lokaci ɗaya yana faɗin"Shege Ajin duniya wato shi kan shi Gidan Aji. ma na dabam ne."
Makama ya ce"Tsarin ginin na turawa ne zaman gidan mace ɗaya, in da rabo Mimi ba ta cikin masu zama da kishiya."
Aji ya ce"Wannan kuma na Allah ne, in yana cikin Kaddara na fa? Amman yanzu kam ita ce a baya ita ce kuma a gaba."
Dariya suka saka har suna tafawa, suna taren Mimi ke ta kiranshi wai shi suke jira sai a lokacin ya tuna yau za su fara shiga kasuwa kawai sai ya Kalli su Nasir kafin ya ce"Nan zan bar ku? Saboda zan je na ɗauki Mimi za mu shiga kasuwa."
Nasir ya buɗe baki Makama kuma na dariya tun kafin ma su yi mgana ya ce" Wlh ta matsa min wai tare za mu riƙa zuwa haɗa lefe, in na ce a a kusan ta tun a baya yar rigima ce"
Nasir na kaɗa kai ya ce"Ƙwarai hanzarta ɗankwali yaja hula, lalle Mimi ta ciru tuta yau Aji za'a je kasuwa zaɓan kayan mata."
Shi da Makama har suna tafawa dariya kawai ya yi musu