Idan An Ciza Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   27 / 49

78K to 81K   out of 146.6K words

to sai ya nuna kamar ya hakura sai kuma ya nuna kamar bai haƙura ba.
Ko da ya kai ta gida ma bai shiga ba ya yi tafiyarsa. Wajem sati fa ya na mata wannan halin sai ta yi masa mai gabaɗaya ranar da aka kai azumi goma ta shirya masa abun shan ruwa ta kira shi ta ce ya zo ya ce ba zai zo ya ga abin haushi ba ,sai kawai ta ce zan zo to na kawo maka"
Da sauri ya ce"Ba ki da hankali ne? Ki tsaya gani nan zuwa wlh kada ki ce za ki taho."

Daman ta shirya masa ne, ta san in ya ji ta ce za ta so sai ta shi hankalisa tunda daman ko ranar sai da ya ƙara mata fadan zuwan da ta yi, ko Minti talatin ba'a yi ba sai ga shi ya zo amman ya ce ba zai shiga ciki ba sai dai ta kawo masa ya tafii da shi, ita kuma sai ta shagwaɓe masa tana faɗin" Mu shiga ciki mana, ba sai ka ga abin da ka ce ina maka rowa ba?
Ya kasa mata musu saboda ta rike hannunsa sannan ta ma masa fari dole ya bita cikin falon ya zauna ta haɗo masa kayan shan ruwa tun yana basarwa har ya saki jiki, Ita kuma tana cire mayafi ya ganta cikin wata riga mai roba ta kama ta. Kirjinta rabi duk a waje ssannan ba ta saka ɗankwali ba ta ɗaure gashinta kawai, Aji na cin abinci ya na kallonta ƙasa ƙasa, Sai bayan sun gama ta kwashe abin da suka yi amfani da shi sannan ta dawo gabansa ta juya masa dakyau sannan ta kashe masa ido ɗaya tana faɗin" Ga gama kallon ne?
Haka ta faɗa tana masa dariya sai kawai ya kalleta cikin wani yanayi kafin ya ce"Kaɗan na kalla."
Baki ta rufe tana dariya, ba ta san lokacin da ya ta so ba jinta kawai ta yi a jikinsa ya rumgumeta kamkam, itama sai ta lafe a kirjinsa tana shaƙan kamshin turarensa mai saka ta natsuwa. Rungumeta kawai ya yi sai ita ce ma da ya ɗago ta sumbaci bakinsa sai ya kalleta sai ta ji kunya ta juya baya sai kawai ya yi mirmishi kafin ya ce"Daran ranar ba ɗaga kafa wallahi."
Haka ya faɗa sannan ya koma ya sha mur kamar ba shi ya faɗa ba da zai tafi ya ba ma Hajiya 5k, baba Uwani 3k, ita dai ya ce ko sisi ba zai ba ta ba, da ta ce tukwaicin girki fa? Sai ya ce to ai ladanta na wajen Allah Tun da ta ciyar da mijinta sannan shi ba shi da kuɗi ta gama talauta shi ma gaɓadaya shi ya yi mganar sai ya bar ta da dariya.

Tun daga ranar ta samu ya huce, yabq zuwa a sati sau biyu su yi Buɗe baki, gefe daya tana ta shiryen shiryen tarewa gini kuma yana ta nisa sun yi mgana da Mommy dole kayan gida komai sabo za'a siya ita Mommy ta yi mgana da Daddy ya ce ba laifi in an gama gidan sai aje aka ga abib da ya kamata a siya, ita dai bangaren Mimi kayan ɗakinta da a ka kwaso daga gidan Wanzamai ta ce a bar mata sai ta saka shi a wani falo tun da ya ce falo biyu ne nata sai bedroom uku sai shi falo ɗaya Bedroom guda biyu, ga sallah na matsowa kuɗin da ya tara Mimi duk ta yi kasa da su, Hibba ya ba ma kwangilan kayan sallah na Inna da Walida Junoir, sai Mariya da Baba da magajiya, Bintu ma ya yi mata kala ɗaya.
Inna kala uku, Magajiya biyu, Baba ma shadda da yadi guda biyu su Baba Sani Kuma Mu'azzam ya yi musu har da su mariya suma ya kara musu da kala ɗaya ɗaya. Magajiya sai dai ta ga Baba ya shigo da kaya Hatta Mariya kala uku ne Mu'azzam kuma ya haɗo musu da kuɗin dinki.
Gaje da Harira ma ya yi musu Atamfofi kala daya daya, suna ta godiya Magajiya ta kasa mgana domin kaf a cikin ƴayanta ba wanda ya ke mata kayan sallah sai Mu'azzam da Mansoor, Auwalu na fama da kanshi Saddiqu kuma bai garin ina ya ga ta zama bashi kaɗai ya ishe shi, Dole kanwar ñaki zuru'an Innan dai sume suke taimakon su tunda ga sutura har bangaran abinci tunda in sun ci su ne, in kuma sun sha suma sune.
Mariya sai murna take yi tana da kala huɗu, tunda saurayinta ya yi mata ɗaya sannan su ka haɗa kudi su biyar za su yanka sa Nasir Makama, Ahmad Mu'azzam da Aji domin su raba a tsakaninsu, Aji kuma ya ce zai ƙara da shiga tantan saboda Can gidan da su Baba Sani.

Ana sallah saura kwana huɗu Hibba da Mu'azzam suka sauka a garin, da kaya niki niki na kayan fulawa duk ta siyo komai anan za su yi cincin da sauran cimar fulawa, Matan su Yaya Amina kuɗi yan'uwa suka ba su, Bintu dai an mata kaya ita da yayanta, Ana jibi sallah suka yanka san su, naman duka gidan Inna aka kawo sannan ga kaji Mu'azzam ya siya guda goma. Biyar nan gidan Inna uku Magajiya biyu Baba Sani da Baba Danjuma. Shi kuma Aji naman tantan na 50k ya shiga aka raba na Magajiya kashi Biyu su Baba Sani kashi ɗaya, sai ga shi karon darko Magajiya da aka kawo mata nama da kaji ta buɗe baki ta ce Allah ya yi albarka sannan Auwalu ma ya kawo musu Nama tunda a kwangilan aikin gidan Aji Alhamdulillah, ya na samu kuma haka ya gaya ma Magajiyar. Shuru kawai ta yi ta kasa magana ko Jummai ma da ta kira Mu'azzam dubu goma ya tura mata, Saddiqu kuma sai kiran babu, domin ya ce Maeesha ta matsa masa sai da ya tura mata wasu kudaɗe biyar ba'a samu ta hannunsa ba, in da ace ma dasu aka dogara da an mutu ba'a ci ba.

Ana gobe sallah gabaɗayansu sun haɗu a gidan Aji da ake gini har an saka get da Kofifin cikin gida yanzu POP suke yi da plasta sannan masu saka tayil da Interlock na cikin gida na aikinsu Ahmad ya ce"Lalle Aji ka tara kuɗi."
Aji ya ce"Duk sun ƙare, Mimi kaɗan ya rage ba ta maidani talaka ba."
Nasir ya ce"Ta cancanta ne."
Suna gidan har aka sha ruwa lokacin da Ma'aikatan su ka ta shi akwai wanda ke kwana a gidan saboda barayi. Dag nnan gidan Makama suka wuce nan suka shirya shan ruwa suna gidan Rukky ta zo kawo mata ɗinkunanta kawai sai ta gan su cikin mamaki ta kama baki tana faɗin" Yallaɓai na Mimi ashe kana nan?
Aji na Mirmishi ya ce"Nan fa gidan abokina ne, za ki iya ganina ko wani lokaci."
Nan fa aka gaggaisa, ta shiga ciki Nasir ya ce"Yayar matar ta ka akwai girman kai."
Makama ya ce" Da alamu dai kana ciki da ita domin ina ganin ka, kana satan kallon ta.".

Nasir ya fara rantsuwan ba haka ba ne, Makama na rantsuwan ya gano shi, Aji na gefe ya ce"To miye! In kana sonta ka shiga cikin Manema kawai kai namiji ne mijin mace huɗu"
Me za su yi in ba dariya ba domin Nasir ne ya ce"Kwarai mutumina." Da alamu ya na so yana kaiwa kasuwa, da Rukky ta fito za ta tafi kawai sai Makama ya ce ga Nasir zai kaita gida, Aji ya dafa kafaɗansa yana faɗin" Sa'a dai Nasiruddeen Angon Nafisa da Rukayya."
Dariya har su Mu'azzam na dafe ciki ganin Nasir ya miƙe ya jinjina ma Aji hannu lokaci daya yana faɗin"Na gode namijin duniya, Angon Mimi."
Suna ta masa shakiyanci har ya fice. Shi kuma ya kaita gida amman hiran na su sama same ne ya dai karɓi lambar wayarta sai da ya dawo sannan suka watse Nasir da Ahmad tafiyar su ɗaya Mu'azzam da Aji ma haka.

Sanda suka koma gida su Hibba na ta fama da suyan nama ga Walida da Mariya na ta fama da suyan dumblan ba su ci abinci ba domin cikinsu ya cika sai suka zauna a falo suna ta hira da Inna Meri, Inna na faɗin Yalwa ta kira ta tana godiya ta ce Mansoor ya tura mata 50k Aji ya ce ba shi da kuɗi ne ya so ya fi haka shina Mu'azzam Inna na ta saka albarka, sannan ta ɗauko musu wata farar keda da kaya ciki Mimi ta aiko da shi ta yi ma Inna Atamfa da hijabi da takalmi, sai kuma Walida Abaya da mayafi, Aji bai ma san da saƙon ba kwata kwata nan ma Inna ta yi ta saka albarka sai da suka koma ɗaki shi da Mu'azzam ya kira Mimi, yana ce mata ta ga kuɗi a hannunta baja baja tana ta hidima da shi a ciki ta yi ma su Inna kaya
Ita kuma ta ce"Eh da yake kai kaɗai ke da Kuɗi ka manta nima aiki nake yi"
Ya ce"To ma su aiki, ni ai kin san zaman banza nake yi."
Dariya ta yi masa kafin ta ce"Kayan sallah ta fa? Ba ka aiko min da shi ba?
Kai tsaye ya ce"Amman ba ki da tausayi, duk kuɗina ya kare ki ɗauka cikin na lefe ki ɗinka mana."
Mimi ta shagwabe tana faɗin"Haƙƙin ka ne fa ka min sutura, da ci da ciyarwa."
Aji ya yi shuru kafin ya ce"Ai zan ci kuma zan yi ciyarwan in sha Allahu.
Sai daga baya ta gane maganarsa ai sai ta saka Ihu ta kashe wayarta ta bar shi ya na Mirmishi, Mu'azzam ya fito daga wanka ya tsaya kawai yana kallon Yayan na shi sai daga baya ya ganshi, ya ga yana kallonsa sai ya basarwa ya miƙe yana faɗin" Ka fito? Mu'azzam na yar dariya ya ɗaga masa kai har ya shiga tiolet ɗin yana bin sa da kallo ya na yar dariya.

A daran aka faɗi an ga watan salla washegari a ka ta shi da shirin zuwa sallar Idi. gaɓadaya gidan har da su Inna, Mu'azzam zai je ya ɗauko su Baba Danjuma su uku tunda matan su ba sa zuwa. Hatta Magajiya kuwa Amman Inna sallar Idi ba ta taɓa wuce ta ba, Aji kuma zai ɗauki Inna da su Hibba. Masallacin takwas da rabi suke tada salla nan cikin gari ne Aji da Mu'azzam shigar fararen shadda suka yi harda babban riga da baƙaƙen takalma da huluna da agogo baƙaƙe, Ahmad ya ɗinka musu daga kaduna zuwa da shi kawai ya yi Mu'azzam ya biya komai da komai, in ka gansu kamar yan biyu, Inna na kallonsu tana mirmishi sai kwalla addu'a take yi a cikin ranta Allah ya kara haɗa kawunan su Hadda Junoir shima an ɗinkka masa shaddan matan kuma kowacce ta ci gayunta lalle ne kaɗai ba su yi ba sai sun dawo daga idi tun da ba lokaci.

Rufe gidan a ka yi gabaɗaya, a masallacin Idi su ka haɗu da su Mu'azzam da kuma su Nasir tunda duk can suke zuwa. Bayan an idar da sallar idi kenan zaratan abokan suna ta hotuna daman Nasir da matarsa ya zo haka Ahmad da Makama, kawai sai kuma su ka haɗe da Mimi, ita ta kawo su sallar idi ita da Hajiya da Baaba Uwani. Kamar haɗin baki matan abokan suka haɗe gabaɗaya Mimi ta ji kunyar Inna ta duka ta na gaisheta Inna ta ta da ita tsaye ta na saka mata albarka, Hajiya kuma na ta yi ma Inna tsiyar Idonta kenan shike nan sai yara su raba zumunci inna na dariya ta ce tana nan zuwa.

Mimi ta sha kyau cikin abaya mai ruwan kasa, ta naɗa mayafinta a kanta.
Saboda su Inna da su baba ba su daɗe ba, Hibba da Mimi sun yi mganar sai sun yi waya sannan suka rabu kowa ya shiga motar da ya zo, Aji dai sai da ya jira Mimi saboda go slow, sai da ya samu suka fita sarari tare sannan suka tafi tare zuwa juction ɗin da suka rabu.
Bayan duk an koma gida aka fara ciye ciye da cin nama, ranar Idi ce ranar zama cikin Iyaye da ƴan'uwa Aji da Mu'azzam a gida suka yini cikin yan'uwansu amman sun kira ƴan'uwansu sun yi musu barka da salla har Baba Yakubu ya kira bayan ya kira can Kwami ya yi musu barka da sallah Sannan sai ga shi ya kira Dr. sulaiman, ya yi masa barka da Sallah sannan ya kira Mommy itama ya yi mata barka da sallah har da Daddy kuma sun ji daɗi, Ita Mimi ma mommy ke gaya mata da farko sannan Dr ma ya faɗa mata Daddy sai da ya zo gidan ne ya ke ce mata mijinta ya kira shi sai ta ji daɗi kenan dai da gasken Ajinta ya sauya.

Ranar ba su yi waya sosai ba saboda kowa na can cikin ahalinsa. Ranar yawon sallah na farko ma duk suna gida ranar na uku ne gidan Inna ya cika da su yaya Amina da jikoki ranar kuma aka yi abincin sallah su kuma su Mu'azzam da su Nasir gari suka shiga suna ta ziyarce ziyarce sune har gidan surukan Nasir da Makama. Rukky na gida itama tunda Bibi itama gidan ta je Nasir dai bai furta yana son Rukkaya ba amman ta fahimci haka. Daga nan suka je gidan surukan Ahmad bayan nan suka zagaya duka gidan iyayensu har gidan Wanzamai da wajen inna suka mata barka da sallah gidan Hajiya ne ƙarshe Mimi ba ta san ma da zuwan su ba gidan Hajiya cike da yaddiko da ƴaƴanta da jikokinta ta ji kiranta yana faɗa mata ga su sun yi ma Hajiya barka da sallah.

Sai a ranar wasu cikin ƴaƴan Yadikko suka ga mijin Mimi lalle ya ci sunan shi Aji haka suke faɗa Hajiya ta ji dadi tana ta zolayansu Kowanne su sai dai ya bata goron sallah, Ba su wani tsaya ba suka ce za su karisa gidan Daddy naman da cake din sai package din shi Mimi ta yi musu, ta yi kyau cikin leshinta doguwar riga kamar ka sace ta ka gudu. Daga anan sai gidan Daddy shima ya na gida sun kuma samu harda Jaheed tunda shima yaran na shi duk sun zo gaisuwan sallah hakika ya ji daɗin wannan ziyaran duk da shima gidan cike da mutanensu yan Siyasa sai a ranar Aji suka taɓa musabaha da Jaheed kowa na kallon kowa. Sai bayan sun baro gidan ne Makama ya kalli Aji yana faɗin"Yau dai ka ga rival ɗin ka Aji."
Tun da shinl ne daman ya kawo ma Aji labarin Jaheed ɗin da ya ji a wajen Bibi.
A wajen ginin Aji suka yada zango aiki akwai ake yi ba dare ba rana domin nan da kwana goma Aji ke bukatwr matarsa daga can suka ka rabu kowa ya yi gidan shi.

Washegari kuma Hibba ta tafi gidansu itama ta yi gaisiuwan sallah. Mimi kuma a ranar suka yi mgana da Aji ya jadadda mata kada abin da za ta yi ya wuce nan da kwana goma. Dole ta kira Rukky domin su fara shiri mganar gida daman ya yi mata vedio ta gani ta tura ma Mommy ta ce ba matsala tuni ta ba da oder komai da komai, mganar gyaran jiki suka fara yi, kayan gyara kuma Khadi ta haɗa ta da wata Surayya Dee mai saida kayan mata da gazar sababi tana kano ne aiko mata da shi kawai za'a yi, kayan surayya dee mai suna Bojuwa kaya ne masu inganci da daɗewa a jikin mace kafin su sake, ku yi amfani dashi domin zamowa tauraruwa kamar Mimi a gidan Ajin ta.+234 803 277 3332

Sannan ma yaddiko ta aiko mata ds su gumba, Mommy kuma ta siya wasu kayan daga wajen Surayya mai kazar sababi na Amare da uwayen gida +234 803 277 3332 ta siya mata babban Package har da kaza da matsalan ta yanzu wajen aiiki ne amman sun yi shawara da Rukky za ta samu manaja ko hutun sati ɗaya ya taimaka ya ba ta, duk shirin nan da ake yi Madiha ba ta saka kanta a ciki ba Khadi ta kira ta ta faɗa mata za ta je Gombe Mimi za ta koma sabon gida sai ta ce ba za ta samu zuwa ba, ita dai ta ce za ta je Dr kuma ya ce Jawahir za ta zo daman kuma ta yi arba'in za'a kawo ma Daddy Baby shi da Hajiya.







*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3012*

*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*

*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura

27 / 49