Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
suka ɗaga masa hannu ya shiga motarsa ya bar wajen su kuma suna wajen ginin suna ganin yanayin aikin har kusan mangariba sannan suka bar wajen.
Aji kuma su ne har bayan mangariba a kasuwa suka sha ruwa, Mimi tare da Rukky shagon Atamfofi da lesuka suka fara zuwa Komai sai Mimi ta ce sai Aji ya zaɓar mata shi kuma ya gaji da azumi ga ciwon kai saboda hayaniyar kasuwa ya saka P.Cap ya rufe rabin fuskarsa saboda baya so mutane su gane shi, shi dai gaji ya yi komai sai Mimi ta ɗauka ta kara a jikinta tana ce masa ya yi mata kyau? Cikin kosawa ya ce"Ki ɗauki duk abin da ya yi miki saboda komai kiia saka yana miki kyau saboda ba kayan ba ne ma su kyau, ke ce mai kyan saboda haka ki ɗauki abin da kike so Aji ya na so shima"
Sai Mimi ta fara mirmishin jin daɗi Rukky na gefe ta zama yar kallo ana musayan kallon Masoya. Kayan ma anan suka bar su, Sai gobe za su dawo su gama dubawa akwatina daman a online Mimi ta gani ta siya masu kyau guda huɗu huɗu takws kenan, da ta ce sha biyu amman Aji ya ce" Takwas ɗin dai Hajiya ta, ni fa talaka ne kada ki karar min da arzikina da zai kai ni shekaru uku nan gaba."
Tana dariya ta ce"ba ka ce kai mai kuɗi ba ne?
Kai tsaye ya ce" Duk da haka ban kai ki kuɗi ba, Malama ki yi abun hankali."
Bayan shi ya ce ta siya duk abin da take so da ta ce shi ya ce haka sai ya sha mur ya na faɗin"Ni? To kila ba na cikin hayyacina ne, kin yi min farin yaudara, ko kuma dai ƙila gatse na yi miki, ke kuma kamar ƴar fari bakya gane baƙar mgana da gatse."
Tana masa dariya ta ce"Ka manta ni Auta ce? Sorry sai na yi ma Atm ɗin kalmar nan ta ƙare dangi."
Kai tsaye ya ce" Kya ci da kanki kuwa nan gaba."
Haka dai suka yi rahan su, a hanyar dawowa daga gidansu Rukky tunda har gida suka maida ta, Rukky ta ce"Yallaɓai muna godiya sai Allah ya kaimu."
Karon farko da ya yi mata mirmishi ya ce"To ƙawarmu asha ruwa lafiya, muma mun gode."
Da ya kai Mimi gida sai ta hana shi tafiya dole ya tsaya anan ya yi sallah ya ci abinci, Kunin gyaɗa ne mai zafi ya sha da kosai, Abincin kuma ya ce ta ba shi kawai ya tafi da shi daman wasu kololinta suna can Camp bai dawo mata da shi ba. Haka nan ta kara zuba masa ya tafi da shi bayan ya ce ya na binta ba shi abincin shan ruwa da kanta yake so ta yi masa girki ta ce in sha Allahu, har mota ta rako shi ta na shafa kansa ta ce Ka yi tuki a sannu ka ji ko Mijin Mimi?
Sai shima ya shafa hannunta kafin ya ce"In sha Allahu Matar Aji, ki kular min da kanki."
Kawai sai ta duka ta sumbaci kuncinsa.
"I miss u."
"I love u."
Shi kuma ya maida mata da martanin suka raka juna da mirmishi tana ɗaga masa hannu har ya fice daga gidan, bai wuce camp ba saboda a gidan Inna zai kwana saboda ya fi satin rabon shi da gidan. Sai dai ya yi musu sakon kayan azumi ta hannun Yaya Amina, ita ta ya ma kuɗin ta siya musu su dankali da kwai kayan abinci kuma Auwalu ne kamar yadda suka saba Kuma gabaɗaya ne har da can gidan har da su Baba Sani kamar yadda suka saba. Sannan sun siya gero da siga shi da Mu'azzam Inna ta ba ma gaje kwangilan ana kokon sadaka da kosai, sai kuma can gidan kakkanin Mu'azzam shima ya aika musu da sakon azumi kamar yadda ya saba. Matan kuma Aji ne yaa raba ma Yaya Amina da Yaya Halima dubu hamsin, Bintu kuma dubu goma ya ba ta, ta ce za ta kara jarin zoɓo ne.
Ko da ya isa giden ya na yin hon Walida ta zo da gudu za ta buɗe masa get ya ce ta koma shi ya fito ya buɗe ma kansa bayan ya shiga da motar ciki ya koma ya ja get ɗin ya rufe. Sai dai suka gansa da kwandon abinci Kafin ma Inna ta yi mgana ya ce daga gidansu Mimi yake.
Inna na mirmishi ta ce"Suna lafiya ko?
Ya ce lafiya lau sannan ya yi ma Inna barka da shan ruwa Walida ma ta gaishe shi Junior kuma an samu carrton bai ma san ya shigo ba sai da ya ji an ɗaga sama sannan ya washe baki yana fadin"Daddy"
Abinci ya ce Walida ta kai kitchen cikinsa ya cika sannan kafin ya shiga ciki Sai da ya ba ma Walida hakuri kan mganar wayar da ya ce zai siya mata zuwa bayan sallah ta ce bakomai. Sai ya ce ma Inna bari ya shiga ya yi wanka, Da Junior ya shiga ɗakin amman ya na shiga wanka ya fito ya dawo falon wajen kallon cartton ɗinsa.
Aji so yake yi in an gama gidan can gabaɗaya sai ya kwashe kayan shi ya koma can gabadaya. Bayan ya yi wanka ya sauya kaya an kira sallar isha'i sai ya fita sallah da zai dawo ya biya ya siya ma su Inna tsire tana ta saka albarka, gabaɗaya ya gaji shi ya sa ya ce bari ya shiga ya kwanta.
Ya na kuma kwanciyar sai barci sai cikin dare ya farka ya ga Mimi ta kira shi ma, bai samu kiranta ba sai da asuba. Ranar lahadi me yana gida ko da ma ba lahadi ba ne an ba da hutu matasan yan Gombe United ɗin duk sun tafi gida hutu sai yan nesa ne da kuma waɗanda ba sa son tafiya su suka rage kawai a camp ɗin suna sake bitan traning ɗin su.
Da wuri ya je ya ɗauki Mimi suka biya ma'aikatarsu suka ɗauki Rukky tunda ita ta shiga duba wani abu, suna kasuwan nan har bayan la'asar bayan sun gama da bangaren Atamfa, leshi, abayoyo, material sai bangaren jakunkuna da takalma sai bangarem kayan kwalliya da bangaren Undies, su dai kam bai bi su ba ya ce su shiga su kaɗai, sai da aka je shagon mayafai y aga Mimi ta na jidan mayafi kala kala sai da ta gama zaɓa sannan ya kalleta yana daga gefe ya harɗe hannuwansa a saman ƙirjinsa sannan ya ce" Duk waɗanan mayafan na waye?
Ta kannne ido ɗaya kafin ta ce" Ana mana."
Sai kawai ya karkace kai kafin ya ce"Amman kinsan ba na son wannan abun ko?
Kai tsaye ta marairace kafin ta ce"Naka ne fa, in za mu fita tare zan riƙa yi maka kwalliya." Ya kasa mgana yana ta kallonta kawai Rukky ma ta saka baki tana faɗin"Yallabai a yi hakuri duk saboda a yi maka kwalliya ne."
Mai shago ma dake son ciniki sai da ya tanka kafin ya ce"Ango a yi hakuri, ka ji dai ta ce wannan na fita auting ɗin Amarya da ango ne."
Kai tsaye Aji ya ce"Wani Ango? Ba fa Amarya ba ce, Yaji ta yi duk wannan abin daka gani domin za ta yi kome ne."
Mimi ta ji kunya ba ta san lokacin ta ɗauki mayafi ɗaya ta sarke wuyan Aji da shi ba, shi kuma sai ya rike mata gefen hijabi yana faɗin" Yi hakuri na manta to kin daka barkonu a ke cewa ba Yaji ba ko?.
Ya faɗa yana kallon Rukky da mai shago da suke ta musu dariya.
Saboda haushi ledan mayafan gabaɗaya ta hana yaran shago ɗauka tac e shi zai ɗauka zuwa mota hakan ban ya rumguma yana faɗin" Allah dai na gani."
Mimi ta taso masa da faɗin" Yana ganin mene?
Da sauri ya ce"Irin son da nake yi miki mana."
Sai aka bar Mimi da mirmishin jin daɗi, Mai shago da suka gama burgeshi ya ce"Allah ya sa ke da ƙara yin wani yajin har abada Hajiya."
Sai aka bar Mimi da jin kunya Rukky na dariya ta amsa da Amin Aji ya amsa da cewa"Ai ba za ta ƙara ba saboda tana tsananin sona, na bayaa da ta yi duk burga ce na sani."
Mimi ta ɗauki Jakarta ta maka masa a baya yana dariya ya ce", Shi fa illah ka yi yaji kenan har ƴaƴa da jikoki sai ya bika"
Mai shagom mayafai ya sha nishaɗi, Rukky kuma haka take ta dariya tana ma Mimi raɗan daman haka Aji yake? Mimi na dariya ta ce Ya fi haka ma in ya yi niyar yin raha.
Mimi ƙiri ƙiri ta ce ba zai kai mayafan nan Mlmota ba sai sun je shagon hijabai sannan haka nan da ledoji niƙi niƙi a hannu suka je shagon hijabi ta zaɓa amman anan suka bar masa sai an ɗinka yau ɗin ma sai mangariba suka fito daga kasuwa booth da bayan mota ciki da kaya Dakyar Rukky ta samu wajen zama.
Suna hanyar maida Rukky gida, Mimi take gaya masa abin da Rukky ta ce sai ya yi mirmishi kafin ya ce" Ba haka nake ba fa, duk ita ta maida ni haka." Mimi ta daki kafaɗansa tana faɗin" Wallahi ka daina gaya ma nutane na yi yaji ba na so"
Ta faɗa ta na shan mur.
Kai ya jinjina kafin ya ce"To ai shike nan na yi shuru da bakina."
Rukky dai ta na shan kallo suka sauketa gida suna ta mata godiya yau bai tsaya shan ruwa ba. Sun rabu dai akan gobe ba zai zo ba sai jibi ta yi masa abin shan ruwa kuma ta ci kwalliya saboda zai mori kallon matarsa sa son ran shi.
A gidan Inna Meri ya sha ruwa ranar. Washegari kuma gidan Nasir ne tunda shi ya gayyacesa tare da Makama, kamar ba zai je ba ba sai kuma ya tuna yanzu fa ya ce ya gyara sai ya shirya ya je,.Sai a ranar ma ya iya ganin Nafisa da ƴaƴan Nasir, Nasir na ta yi masa tsiyan ya ji kunya bai san ƴaƴan sa ba, shi kuma ya ce kada ya damu tunda dai shi ubansu ne ko da sun girma ne za su iya gane shi. Nafisa kuma sai da ta tambayi Mimi kai tsaye Aji ya ce" Nasir bai gaya miki ba? Ai ta yi yaji ne amman za ta dawo bayan sallah.'
Me su Nasir za su yi in ba dariya ba, ita kanta Nafisan sai da ta yi dariya, da zai tafi 10k ya ba ma Nafisa da yaran da ya koma gida ya kira Mimi sai ya gaya mata Nafisa ta tambayesa shi kuma ya gaya mata ta yi yaji, Mimi ta riƙa dariya tana fadin ita kam ta shiga uku da wannan yajin.
Shi kuma ya ce wlh kada ta ƙara. Domin yaji a aure yana da tambari, kawai miji bai sake ka ba sai ka dawo gida ka ce ka gaji da auran saboda samun waje, ta ce eh ta ji ai ta tauna tsakuwa aya kuma taji tsoro, ya ce kuma da wannan don wannan.
Ranar labara tunda sun yi anan zai sha ruwa a masallacin kusa da gidan Hajiya ya yi sallar mangariba dabino kawai ya ci ya karisa gidan. Da yake ya zama ɗan gida yanzu ya na zuwa kai tsaye falon yake shiga, Tabbas ya ga baƙuwar mota a haraban gidan amman tunaninsa bai kawo masa wani abu ba. Ƙananun kaya ne a jikinsa rigar mai ruwan kasa ce wandon kuma baki ne kafarsa takalmi ne mai buɗewa. Sai Kuma yau bai saka hula ba sumar kansa ta sha gyara tana ƙyalli, sallamar da ya yi ƙokarin yi ta makale ne a fatar bakinsa lokacin da ya yi mugun gani, to mugun gani mana, Mimi ce cikin kayatticiyar kwalliya na wani leshi fiteed gown, ta yi ɗaurin gashinta a waje daga baya, kuma ba mayafi ga kayan sun kamata tsam tana tsaye gaban wani namiji tana yi masa dariya.
Wani irin Kolulin abu ne ya ji ya taso masa ya tokare masa kirji saboda Kishi har duhu duhu ya koma gani. Daga anan sai ya ga kamar Mimi rumgume da wannan mutumin tuni idanuwansa suka kaɗa suka yi jajir, jijiyon kansa suka ɗaga. Ya ma kasa yin wani motsi, Mimi ce ke facing kofar ita ta fara ganin shi daman roƙon Jaheed take yi ya tafi kafin Aji ya zo ya gan shi ya ja za mata wani bala'in ashe aikin gama ya riga ya gama. Ba ta san Jaheed ya zo garin ba sai kwatsam tana wanka ya zo gidan bayan ta gama yi ma Aji abincin shan ruwa ita ba ta ma san ya zo ba ta shirya ta fito ne Hajiya ke gaya maya Jaheed na falo yana jiranta.
Da sauri ta bar gaban Jaheed ta fara takawa zuwa wajen Aji amman wani kallo da ya yi mata ya sa ta tsaya cak. Da ya sa Jaheed ya juya shima sai ya ga abin da ya sa Mimi rawan jiki ya gane shi saboda yadda Mimi ta so shi ya sa har hotonsa yana da shi a wayarsa sannan yana da duk wani labarinsa
Ya yunkura domin ya bi bayan Mimi sai kawai Aji ya juya da sauri ya bar falon, Mimi ta mara mishi baya da sauri tana kiran sunan shi.
"Aji.."
"Mansoor"
Amman ina ko juyowa bai yi ba, yana zuwa da sauri ya shiga motarsa ya kunna ta zo tana ƙwankwansa masa gillas ya yi banza da ita. Ribas zai taka yana ƙokarin taka ta sai ta yi tsalle ta koma gefe dai dai lokacin Jaheed ya kariso sai ya riƙe mata kugu yana tambayanta ko Lafiya take, wannan rikon a Idon Aji da sai da ya ji kamar ya mutu hon ɗin ma da karfi yake saki Megadi ya buɗe masa get ya fice da gudu kamar zai tashi sama.
*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB30011*
*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*
https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC
No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.
Hankalin Mimi ya yi bala'in ta shi. Jikinta sai rawa yake yi, ba ta ma san Jaheed ya riƙe ta ba sai bayan da Aji ya bar gidan sannan ta juya da sauri ta koma cikin falon tana rawan jiki da na zuciya saboda tsabar firgita da Irin kallon da ta ga Aji na yi mata
Kamar za ta faɗi har da gudu take haɗawa Jaheed ya bi bayanta yana kiran sunanta amman ina ko jin sa ma ba ta yi, wayar ta na cikin ɗakinta a gaggauce ta shiga ta ɗauko wayar ta fara laluɓan lambar wayarsa ta fara kira amman tana ta ringing amman bai ɗauka ba, da wayar ta tsinke sai ta ƙara kira wajen kira a jere ya fi sau goma amman bai ɗaga ba.
Haka ta fito falo a firgice sai suka ci karo da Hajiya da ta fito daga ɗakinta amman yanayin da ta ga Mimi ne ya sa ta san ba lafiya saboda ba ta ma tsaya ba sauri sauri ta wuce ta, Sai Hajiya ta bi bayanta tana kiran sunanta. A falo Jaheed na zaune Baaba Uwani na zaune a kasa a gefensa ta na ta yi masa surutu amman da alamu baya sauraranta mamakin irin tashin hankalin da ya gani a tare da Mimi ne kan wannan Mijin nata da ta ce ba ta son auran yanzu.
Kawai yana zaune sai gani ya yi ta dawo falon kamar za ta fita saboda tsabar ruɗewa. Sai ya miƙe da sauri yana kiran sunanta daidai hajiya ta kawo cikin falon, ta tsaya kawai tana bin su da kallo cikin mamaki, Mimi ta rasa ina za ta je ta ji daɗi, ha waya a hannunta tana sake kiran Aji amman tana ta ringing amman ba ya ɗauka, Jaheed kuma ya ƙariso kusa da ita lokaci ɗaya yana faɗin" Mimi wai saboda ya ganmu ne kika ruɗe haka? To ba kin ce sakin ki zai yi ba?
Tana jin shi sai ta yi kamar ba ta ji ba, Ta cigaba da kiran wayarsa tana matsawa daga gaba zuwa baya. Ganin ba ta tanka sa ba sai ya saka jannu ya riƙo hannunta lokaci ɗaya yana faɗin" Zo ki zauna..'
"Kar ka ƙara taɓani.."
Haka Mimi ta faɗa a fusace kamar za ta yi kuka tana yi ma Jaheed wani irin kallo, Hajiya ta karisowa tsakiyar falon lokaci ɗaya tana faɗin" Me ke faruwa ne?
Ita kuma Baaba Uwani faɗi take yi. "Subhanallah Binta me ya faru"
Jaheed kuma sai ya tsaya sororo yana kallon Mimi wacce ta cigaba da danna wayar ta. Sai Hajiya ta juya tana kallon Jaheed lokaci ɗaya tana faɗin" Jaheedu me ke faruwa ne?
Shi ne ya ɗan yi bayanin ain da ke faruwa ya ƙarishe da faɗin" Ni ban san me ya faru ba kawai na ga duk ta ruɗe saboda ya zo ya ganmu tare ya fita a fusace ta bi shi tana masa magana ya yi banza da ita. Saura Kaɗan fa ya ture ta da mota Hajiya."
Hajiya ta yi shuru ta na kallon Jaheed kafin ta ce"Dole za ta damu mana, mijinta ne fa kuma ba daɗi ya zo ya ganku tare."
Cikin mamaki ya ce" Mijinta kuma? Ba ta ce ba ta son auran ba yanzu?
Sai Hajiya ta kasa mgana Mimi kuma tana cikin tashin hankali amman sai da ta watsa ma Jaheed wani banzan kallo kafin ta ce"Da na ce