Idan An Ciza Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   4 / 49

9K to 12K   out of 146.6K words

saki baki ya kasa mgana.
"Ka da ka ce za ka bar aikinka ka taho, na gaya maka ka yi zaman ka, matar ka kuma za'a turo maka ita gobe, Inna na cikin damuwa ku yi min alfarman barin mata Junoir awajenta tunda an yaye shi."
Mu'azzam kasa mgana ya yi sai da ya ji ya ƙara faɗin" Is an oder Mu'azzam."
Shike nan kawai ya ce ya kashe wayarsa.

Baba da ya kira shi daga baya abin da ya faɗamai kenan kar  ma wanda ya yi yunanin zuwa wajen Mimi su bar shi da ita, shi a tunanin shi Mimi ba za ta iya dogon Fushi da shi ba za ta dawo Saboda tana son shi sannan yana tunanin in aka bita kanta zai yi girman da za ta fahimci Aji na dai dai da ita zai tsaya ya ga iya gudun ruwan ta amman da gaske ne ya yi nadama sannan yana ta tunanin shawarwarin Nasir a gare shi yana kuma tunanin gaskya ya faɗa masa Kamar lokaci ya yi da zai daina ganin laifi wani a kan wasu. Saboda yadda ma bai saurari Mu'azzam ba, bai samu sanar dashi rigiman ɗaki ba.

********

*MIMI*

Mimi yadda ta kwanta da Kuka haka ta tashi  da wannan kukan, Hajiya ce ke ta faman lallashinta dakyar ta yi shuru har ta samu ta yi wanka amman ta saka wani abu a cikin ta ta kasa, ji ta ke yi kamar ba ta da ɗandano a harshenta sai da Hajiya ta nuna ɓacin ranta sannan ta iya shan Tea shima kaɗan, ba ta da aiki sai kwanciya tana hawaye domin in ta tuna irin cin zarafin da Aji ya yi mata sai ta kasa tsaida kukanta.
Hajiya duk ta damu ita da Baaba Uwani, ta kasa kiran kowa sai daga baya ta bi shawaran zuciyarta ta kira Alhaji Hamza ta ce ya zo gida in ya samu sarari yau tana neman shi ya ce sai zuwa dare domin baya gari ya shiga Bauchi.

  Mimi ta riga ta fitar da auran Aji acikin ranta a yadda ta ke jin kanta ba ta tunanin za ta iya kara zaman aure da shi, Shi ya sa ta na gani su Bintu da Hibba na kira ba ta ɗauka ba ta ga har kiran Mu'azzam ba adadi ba ma su kaɗai bakwata kwata ba ta ɗauki wayar kowa ba. Daga karshe ma sai ta kashe wayar gabaɗaya tunda tana da tabbacin Shi uban gayyar ba zai kira ba, to wanda ya ce in ta tafin ma zai fi, kuma a mganganunsa babu so ko tausayi da gaske yake baya sonta kenan tuni ya daina sonta a tunanita yana sonta har yanzu ashe ashe bata sani ba shi baya wannan tunanin kanta ya aureta ne domin ya ɗauki fansa abin da ya faru a baya shi ya sa ya riƙa kuntata mata amman duk dai ta daure, Shi ya sa jauswaa suka ce IDAN AN CIZA a hura saboda kar a gaba a yi nadama ita dai ga ta cikin nadaman saurin amincewa da auran Aji da ta yi cikin gaggawa.

  Yini ta yi kwance a ɗaki sallah kawai ke ta da ita. Bayan Tea ɗin da ta sha da safe ba abin da ya ƙara shiga cikin ta. Baba Uwani Saboda ita ta yi alalan manja da rana amman Mimi ba ta iya ci ba, Hajiya ta ce a dama mata kunin gyaɗa shi ne ma ta samu ya shiga cikinta a cikin kwana ɗaya ta rame Idanuwa sun Kumbura kamar ba Mimi yar gayu ba, Hajiya kuma har waya sun yi da Mommy amman ba ta iya gaya mata wani abu ba. Sannan da yamma Yaddiko ta zo duba ta amman har ta tafi ba ta gaya mata Mimi na gidan ba, ta bari dai Alhaji Hamza ya zo shine matsayin uba a wajenta in ya Kirata suka yi mgana ƙila ta iya gaya masa abin da ya faru.
Ta yi niyar kiran Meri amman sai ta fasa,a tunanin ita kanta Merin ya kamata ta nemeta amman shuru, ita kuma Inna Meri kunya da nauyi suka saka ba ta yi tunanin kira ba har tunanin zuwa gidan ta yi amman Kunya take ji ya sa ta rasa mafita a lokacin.

  Da daddaren bayan Mangariba Hajiya ta shiga ɗakin ta iske Mimi kan sallaya da hijabi fuskar nan ba fara'a amman tana shekin damuwa.
Hajiya ta tsaya a kanta ta yi shuru ta kasa mgana sai da Mimi ta gama laziminta ta mike ta naɗe darduman ta maida shi ma'ajiyarsa sannan ta koma gefen gado ta zauna.
Hajiya tasamu gefenta ta zauna lokaci ɗaya tana faɗin" Binta ba na son ganin ki cikin wannan damuwar, kuma ni tun jiya kin kasa yi min bayanin abin da ke faruwa."
Ta gama faɗa cikin yar damuwa. Sai kawai Mimi ta murmusa kamar za ta yi kuka cikin sarƙewar murya ta ce", Hajiya ina bukatar kaya na, ki faɗa ma Mommy a kwasomin kayana daga gidan su Mansoor."
Hajiya ta zaro ido kafin ta ce"Kaya fa kika ce Mimi? daman da gaske kike yi ba za ki koma ba?.
  Ba ta ce koma ba sai kawai ta juya ta kwanta tana faɗin" Na faɗa miki tun jiya Hajiya, aure tsakanina da Aji ya ƙare."
"Saboda mene?  Ba ki faɗa min dalili ba, kin kuma ce bai sake ki ba."

  "Eh bai sake ni ba! Amman zai sake ni dolen shi ballantana ma shima yana ra'ayin haka." Hajiya ta yi zuru domin Mimi rufe Idanuwanta ta yi kamar mai barci duk sai ta kasa gane kanamari haka ta mike ta fita Jiki a sanyaye bayan fitan ta Mimi ta mike zaune ta na bin bayan Hajiya da kallo.
Ba za ta iya faɗa musu abin da ya faru ba domin tama da tabbacin sai sun tsane shi ita kuma ba niyarta ta ɓata masa suna ba, su yi rabuwan Lafiya tun da baya sonta ba amfanin zaman aure domin alfarma.
Ba ta san cewa Hajiya ta kira Daddy ba sai can wajajen tara na Dare har ta yi sallar Isha'i na tana kwance tana tunani Baaba Uwani ta zo ta kira ta ta ce Hajiya da Daddy suna jiran ta a falo.
Sai  da gabanta ya faɗi, kenan ya zama dole ta faɗa ma Daddy dalilinta domin ta san shi da tsarin sanin abin da ya faru kafin ɗaukan mataki.

  Jiki a sanyaye ta saka hijabin da ta yi sallah na Hajiya ne ma tunda kusan rabin da kwatan kayanta suna can gidan, jiki ba kwari ta ƙarisa falon shi kan shi Daddy ya ga yanayinta sai bai ji daɗi ba domin Hajiya ta gama yi masa bayanin abin da ya faru cikin wani yanayi ya ce"Haba Hajiya me ya sa tun a daran baki kirani kin faɗa min ba?
Hajiya ta ce"Na ga dare ya yi, na ɗauka kuma za ta gaya min abin da ke faruwa amman taƙi ce min komai faɗi kawai take yi ita ta ce ta na so da farko yanzu kuma ta ce ba ta so a kyaleta ɗazu da mangariba tana min maganar a kwaso mata kayanta ne."

  Daddy ya jinjina kai yana kallon Mimi da ta zauna a kasa saman cafet kanta yana ɗan nazarinta duk yadda aka yi ruwa ai baya tsami banza, duk inda ka ji mace ta ce ta gaji da auran da ta zaɓe shi da kanta to ba daɗi cikin yanayin mganarsa ya kira sunanta ta amsa sai ya umarceta da ta taso ta zo ta zauna a kusa da shi a saman Kujera, da ta taso sai ba ta zauna a sama ba sai ta zauna a kasa a kusa da kafafunsa lokaci ɗaya tana gaishe shi ya amsa cikin sakewa kafin ya ce" Me ya faru ne Mimi? Hajiya ta ce kina ta Kuka kuma kin ƙi yi mata bayani ina fatan za ki yi ma Daddyn ki bayanin abin da ke faruwa." Sai ya ga ta yi shuru kanta na ƙasa, da sauri ya ce" Kar  ki damu, matukar ke kike da gaskiya ba zan taɓa goyon bayan ki koma ba."

  Kan Mimi na ƙasa ta ce"Daddy na haƙura da auren ne kawai."
"Saboda  me ya sa  kika ce haka? An taɓa hakura da aure ne Mimi in dai ba wanda kike ke zaman shi ba ne ya ce ki je ya gaji da ke ba."
A ranta ta ce kusan hakane amman gili sai ta ce" Saboda akwai tazara mai yawa tsakanina da shi Daddy, abaya na yi tunanin in na aure shi zan iya haɗe wannn  tazaran dake tsakanin mu. Amman daga baya sai na fahimci ba zan iya gyara abin da Allah bai so ya gyara ba. Don Allah kar ku matsamanin akan sai na koma na gaya masa ya aikomin da takardan sakina."
Hajiya ta saka salati, Daddy kuma sai ya yi shuru ganin Mimi na matsan kwallah.
Amman sai bai nuna wani abu tunda har Yanzu ba'a zo in da yake so ba.
Cikin sigan lallashi ya ce"Duk naji, amman ba haka nale son ji ba, Kin dai  san ni a matsayin Major nake a wajen ka sai in da karfina ya kare wajen kwatar miki yanci in dai na tabbatar dake aka zalunta. Saboda haka ki natsu ki gayamin abin da ya faru."
A cikin Lallashi ya gama maganar yana dafa mai kanta, Mimi kuma sai kuka kawai take yi ba ta yi mgana ba, shi kuma bai takura mata ba ya ce ta natsu ta yi masa bayani.
Ganin ta yi shuru ya sa ya gyara zama yana faɗin" Mimi ba zan iya gane komai ba inkina wannan kukan shi aure ai ya na da dokokinsa da tsarin sa, ba zai yuyu ba wani ƙwaƙwaran dalili ba kawai na ce ki zauna a gida ki kashe auran ki ba. A'a dole sai mun san abinda ke faruwa, tunda kin ki mgana bari na kira shi Mijin naki sai ya zo mu tattauna kila shi ya yi mana bayanin abin da ke faru."

  Ya faɗa kamar gaske har ya na ciro wayarsa kamar ya na da lambar Mansoor Ahalin ba shi da ita, Mimi na ganin haka ta ɗauka da gasken kira zai yi da sauri ta ce"Kar  ka kira shi Daddy, zan gaya maka abin da ya Faru."
Sai ya yi mirmishi ya ijiye wayarsa a gefe yana faɗin'" Yauwa ina jin ki uwata."
Kan Mimi na ƙasa ta ce" Daddy cewa ya yi baya so na, ba ya sona.."
Ta karishe faɗa Cikin kuka, cikin mamaki Daddy ya ce"Baya son ki? To me ya sa ya aure ki?
"Yace Saboda Hajiya da Mommy sun je sun roƙe shi. Sannan kuma Daddy kamar auran ɗaukan fansa ya yi dani tunda sai ya riƙa tafiyar da ni akan abin da ya faru ysakaninsa da Abi a shekarun baya."

"Ka ji wani sakarci kuma?

  Daddy ya faɗa ransa ba ce yana kallon Hajiya da ta kasa mgana, Mimi na kuka ta gyaɗa kanta tana faɗin" Shi ne na taho kawai daddy tunda babu amfanin zama da wanda baya somka sannan yake kokarin yin ramakon wani abin da ya faru a baya a kanka."
"Yes! Kin yi dai dai abin da kika yi, wannan ai shirme ne, kuma ba ma bautar ubangiji ya maida auran ba sai wasan yara.vGaskiya ya bani kunya ina ganinsa kamar he is matual ashe sakarai ne mara wayau? Kuma yasan kin taho amman bai dakatar dake ba?
Mimi ma sharan ƙwallah ta ce"Ya sani har cewa ma ya yi zai fi in da har na tafin."
Daddy ya jinjina kai kafin ya yi wata yar dariyansu ta manya yana kallon Hajiya lokaci ɗaya ya na faɗin"U see ko Hajiya? A baya an ga laifin Major ne amman ta wani bangaren yana da ƴar gaskiyarsa. Sai da na so na hana Hajiya tado da wannan maganar ki duba duk alfarman da a ka yi masa muka aura masa ƴar mu kamar sadaka  amman ki ji fa irin wulakancin da ya biyo baya har yana fadin in ta tafin zai fim So is ok gwara da kika taho domin ki nuna masa kinsan me kike yi, Is Good,.."

  Sai ya dakata yana dai dai ta kansa Hajiya kuma sai ta ce"Hamza a bi komai a sannu, Ina ta Merin duk tana nanabubuwan nan suka faru?
Da sauri Mimi ta ce"Ba ta sani ba Hajiya, itama ba jin mganarta yake yi ba, ko ta hana shi ba ya hanuwa wani lokacin ma bata san ya aikata wani abun."

  "Ashe yaron ba shi da tarbiya ban sani ba? Komai aka haɗa da jaki sai ya ci ƙara, Kuma daga jiya zuwa yau bai kira ki ba kuma bai bai turo kowaba?
Mimi ta gyada kanta kafin ta ce"Eh! sai dai ƙannensa sunta kirana a waya ban ɗauka ba."
Daddy ya ce"That Good! gwara da ba ki ɗauka ba, shi ba shi da baki ne sai kannensa ne za su ci masa albasa? Na fahimci ya na da jinkansa. To shike nan ki kwantar da hankali ba za ki koma ba sai in har ya yi nadaman abin da ya aikata ya kawo kansa in har ya na son ki kuma kina da daraja zai sauke kansa ya kawo kansa, ni kuma zan nuna masa cewa ba Isar sa ba ce ya sa na bashi auran ki,  ba  kuma chanchanta ba ne shima alfarman Hajiya da Murja ya ci, in kuma aka yi wata huɗu bai zo ba kuma bai yi wani abu da zai nuna kina da daraja a wajensa ba zan nema miki Saki,in ya nuna taurin kai sai alƙali ya karɓa miki takardan ki."

  Hajiya ta ce"A'a Hamza abun bai dace ba ka yi hakuri a bi komai a sannu mana"
Daddy ya mike ya na gyara  babban rigansa lokaci ɗaya yana faɗin" Hajiya kar ki hanani shiga wannan mganar, ki duba mganar yarinyar nan gabaɗaya gani yake ba ta da wani daraja a wajenza tunda mun bi umarninsa mun aura masa ita ai bai eahala ba tunda har ya ke fama da jin kai yana cewa gwara ta tafi ɗin zai gane a baya alfarman ki yaci yanzu ne zai gane shayi ruwa ne, Mimi ki daina kuka sha kurimin ki kin ji?
Sai ta gyaɗa masa kai kafin ta ce" Daddy a kwaso min kayana."
Kai tsaye ya ce"Dole ai akwai sabon zama, in har ya na son auran ku muma sai mun zuba masa namu sharuɗdan ciki har da gama zaman ki a wannan gidan nasu zan yi magana da Maman yara duk yadda ake ciki za ta kira ki zuwa gobe za'a dawo miki da komai naki gida in sha Allahu."
Sai Mimi ta ji dadi acikin ranta domin gwara dai kowa yasan ita kan ta gama zaman aure da Aji.

  Hajiya kuma sai cewa take yi a bi a sannu amnan Daddy ya ce wannan karon Hajiya ta cire bakinta gani ya yi kamar sun ba shi auran bai wahala ba.
Mimi tana tunanin in da ta zauna ta faɗa nusu yadda ya tafiyar da ita tun farkon auran fa? Da mganganun da yake gayamata da zarafin iyayenta da yake ci? Ta tabbata sai sun ji sun tsane shi shi ya sa ta sakaya maganar.
Bayan tafiyar Daddy Hajiya ta dawo tana nuna ma Mimi illar abin da za ta aikata amman ta ce ita fa tana kan bakanta, abun haushima shi fa bai ma san ya aikata ba dai dai ba sannan ita ba za ta cigaba da zama da mara afuwa ba, sannan ba za ta iya zama da wanda bai iya sarrafa zuciyarsa ba Sannan da bakinsa ya ce baya sonta ba ta ga amfanin zamanta ta da shi ba.

  Zuwa da safe dai tuni mutanen dake kusa susan Mimi na gidan Hajiya, Mommy ma ta sani saboda Hajiya da kanta ta kirata ta sanar da ita abib da ke faruwa ta ce za ta shigo Gombe cikin satin, sannan bangaren Daddy kuma da ya koma ya tattauna da Mama itama ta ba da hoyan bayan haka, ta ce haba auren ai ya yi kaskanci ba Dole ya yi abin da yake so ba saboda an ba shi Mimi kamar sadaka.
Ita ta kira Jaheed taa gaya masa abin da ke faruwa ya yi mamaki kwarai.Har Maman na zolayanshi da cewa ƙila in da rabo Mimi rabon shi ce nan da nan farinciki ya cika zuciyarsa.

  Kuma Daddy ya ba da umarnin a nemo mota a je a kwaso duka kayan Mimi a kai mata gidan Hajiya, amman ko shi a cikin ranshi ba shi da niyar kashe ma Mimi aure ita kanta a mganganunta fushi ne kawai amman tana son mijinta kuma shima yana sonta amman girman kai ne ya hana shi zama ya fahimci yadda zai iya nuna ma mimin so. Shi ya sa ya zaɓi ya yi amfani da karatun siyasar sa ya gyara auran Mimi sannan ya cire wannan jin kan da fushi daga zuciyar Mansoor ba tare da ya bari ko Mimin ta san ga manufarsa ba.




*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3003*

*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*

https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC

No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.

Daddy na yi ma Mama maganan kwaso kaya ta kira ƙanwarta Hajiya Turai suka yi maganar ta nema musu mota, Har tana ƙyanƙyasa mata abin da ya faru Hajiya Turai ta ce"Haba ni fa daman na sani duk burgan banza ne, yarinyar nan ba za ta iya zama a wannan gidan ba."
Mama na ƴar dariya ta ce"Uhm to ai komai ya ƙare" ita kamar har wani jin daɗi take yi ita da suka yi mgana da Daddy sai ga shi har Antyn yara sai da ta sanar mata da ga abin da ke faruwa kowa ya ji

4 / 49