Idan An Ciza Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   31 / 49

90K to 93K   out of 146.6K words

suna shigowa ya fice ko kallo bai ishi Aji ba. Tun bayan abin da ya faru ko ƙara ganinsa bai yi ba sai yau.
Sai ga Zuwaira na godiya Magajiya ma na kwance tana faɗin" Na gode Allah ya jiƙan mahaifa." Mimi ta amsa da Amin Amin dama tun shigowarsu sun gaisa da su Zuwaira. Har Maeesha na ce mata hala aiki ne ya hana ta zuwa asibiti sai ta amsa mata da cewa wallahi, har yarinyar sai da ta ɗauka kafin su tafi, ta fahimci Maeeshan na so ta kara shige mata ne tunda har ƙofar gida suka rako su ita da zuwaira.

Suna shirin tafiya sai ga su Baba Ɗanjuma da ƴan'uwasa Baba Ɗanlami ya ce ya kamata Mimi ta shiga ta gaida su Gaje ai Baba Baba Ɗanjuma ne kaɗai uban mijinta ba. Shi ya sa Mimin ta shiga gidan ta gaida su Gaje sun kuma ji daɗi kwarai duk da ba ta wani daɗe ba,.Suna hanyar komawa gida yaron Gwaggo Yalwa ya kira wayar Aji ya na gaya masa jikin Gwaggon ya ta shi kwana biyu, a tunanin Mansoor Inna ma ba ta sani ba saboda bai ji ta yi masa mganar ba sai kawai suka biya daga nan wajen Inna ya gaya mata halin da ake ciki sai ta ce daman ta kwana biyu ba ta je ba ya kamata ta shirya ta je ta duba ta, Aji dai ya ce ba zai samu halin zuwa ba amman ya na tunanin in ya samu sarari sai su tafi tare da Mimi tun da ba ta taɓa zuwa ba.

Haka ko a ka yi, Inna ya yi ma shirin tafiya da kuɗin mota da abin da za ta je da shi, ita kaɗai ta tafi, Walida kaɗai aka bari a gida da farko har Mimi ta ce ta dawo gidansu ta zauna kafin Innar ta dawo. Gogan ya ce a'a bai gama cin amarcinsa ba. Ko ta koma gidan Bintu ko kuma a nemi wata mafitar to sai ga shi ma Mariya ta ce za ta zo ta ya ta zama har Inna ta dawo tunda jikin Magajiyar da sauki, shike nan sai a ka samu mafita Inna Meri kuma ta je ta iske jikin Yalwa sai a hankali daga kwana huɗu sai ga ta ta yi sati amman tana waya da ƴayanta suna jin halin da ake ciki.
Ta ce za ta ɗan kwana biyu saboda ta kula da Yalwan an kaita asibitin Bauchi, Baba Yakubu ma ya taimaka, a gidansa suka sauka ana ta faman hidiman asibiti. Ganin Inna Meri sama da sati biyu ba ta nan ya sa suka yi magana da Mu'azzam gwara ya je Bauchin ya duba su, sun shirya tafiya tare da Mimi amman kuma sai zuwan su Mommy ya sa tafiyar da ita bai yu yu ba, shima a ranar bai tafin ba sun yi Meeting sai a washegari amman a daran sun je gidan Hajiya sun gaida Mommy da Inna Zainaba kano ta fara sauka shi ne suka ƙariso gamobe tare.

Mimi ta yi mamakin ganin yadda Aji ya zauna suna ta hira da Mommy kamar ba shi ba daman Dr shima ya gaya mata suna waya sosai, balle Daddy da sai dai ta ji ya ce mun yi mgana da Daddy ya ce ya na gaishe ki. Washegari ya kama hanyar Bauchi tare da Yaya Halima da ta tambayi izini a ka barta sun je sun iske jikin yalwa da sauki amman duk ta rame Inna da matan Baba Yakubu ke kula da ita ciwon sugar ne bai kwana ba a ranar ya juyo amman nan ya bar Yaya Halima za su dawo da Inna nan da kwana uku, tun da nan gidan Baba yakubu za'a bar Yalwa saboda tana zuwa ganin likita sai zuwa gaba in ta ƙara murmurewa sai ta koma tunda can Karimu ma yana fama da kansa ne, ƴayan Gwaggo Yalwan ma kowa na ta kanshi da iyalansa ne.


*****


Bayan wata ɗaya.
02:20AM.



Suna ƙamkame da juna, ba su daɗe da samun natsuwa ba, sun yi wanka sun tsarkake jikinsu saboda babu kyau zama cikin najasa, sun lulluɓe jikinsu da bargo har zuwa cikin su, kansu na kan matashi guda ɗaya sun kuma juya suna fuskantar juna bayan sun kamkame juna kamar za'a raba su, Mimi nata wasa da suman kan Aji ba tare da ta yi mgana ba amman sun taru sun yi shuru suna jin bugun numfashin juna ɗakin ya yi duhu amman akwai iskar fanka kaɗan kaɗan yana hurasu lokaci ɗaya yana yawo da labulen window ɗin bedroom ɗin Aji.

Kitso Mimi take yi masa sai ta yi sai ya warware duk ta yamutsa masa gashin kai, da ya gaji ya riƙe mata hannuwa lokaci ɗaya yana faɗin" Yarinya ta ga gashi ba irin na ta ba." Dariya ta yi masa ta na shafa kitson dake kanta a wajen aiki Aisha Farida ta yi mata da kuma ta ce a wajen aiki aka yi mata sai ta tuna diraman da suka kwasa tsakanin da Aji faɗa ya fara yi mata me ya sa ta je ta buɗe gashinta gaban maza, an taɓa yin wani kitso ne a wajen aiki ban da wulakancin? Ta yi masa bayanin a wani keɓantattacen waje ne maza ma basa shigowa amman ya kasa ganewa amman ya gargaɗeta kada ta sake yin irin haka baya so, dole ta koma tana ban hakuri domin ta manta waye take aure shi ya sa ta ba shi wannan labarin.

Hannunsa ta kama ta ɗora bisa kanta tana faɗin" Ka ji bambamcin ko sai na yi maka bayani?
Shafa kanta ya yi kafin ya ce"Tsawon gashi kawai za ki fi ni, amman santsi wane mutum? Ni fa da ina da barin shi ya taru da tuni na fiki gashi."
"Me ya sa to ba ka bar shi ya tarun ba? Ai da yanzu sai ka fara kitso."
Ta faɗa tana ƴar dariya kara jawo ta jikinsa ya yi lokaci ɗaya yana faɗin" Inna ba ta so ta ga na tara gashi, ni kuma ina so amman saboda ita na ke ragewa shi ya sa in dai zan je gida sai na saka huka saboda ba na son ta yi min faɗan na tara suma ban yi aski ba."
Mimi ta kara tusa yatsunta a cikin sumar kansa da ya tara, sai kamshi take yi tunda ta na shan gyara kafin ta ce" Nima ina so zan dinga yi maka kitso ka ji."
Sai ya tura mata kan yana cewa"Ki yi mana, Za ki tsefe shi da kanki ne yarinya."
Ta fara curkuɗa masa kan amman kitson baya kamuwa da ta yi sai ya warware, gajiya ya yi ya janye kansa yana faɗin"Mu yi barci MIAJ." Galala ta yi ta na kallon shi a cikin duhun ɗakin saboda mamakin sunan da ya kirata, to a ina ya san tana amfani da wannan sunan? Tana cikin tunanin ya ɗago kanta ya ɗora saman kirjinsa ya kamkameta yana faɗin"Kina mamakin a ina na san wannan sunan ko?
Bai ba ta damar mgana ya cigaba da faɗin" Na san ki, na san ke kike amfani da sunan Miaj da boyayyen account ɗin da kika buɗe saboda ni."
Mimi ta zaro ido kafin tac e"Ka sani ka ce fa? To ta ya ya?
Mirmishi ya yi kafin ya ce"Mun zama ɗaya lokaci ya yi da za ki san wasu abubuwan da yawa waɗanda ba ki sani ba Fatima."

Goshinta ya sumbata kafin ya ce"Ina son ki, na yi miki wani irin so mai tsananin da na kusa mutuwa saboda soyayyarki Mimi, bayan dawowata daga gidanku da faruwar abin da ya faru kaɗan ya rage ban hqkura da rayuwa ta ba. Sanadin ki na sallama Komai ina tunanin in ba ki cikin rayuwata mafarkina bai cika ba, ciwon rasaki sama da shekaru goma ya ke damun zuciyata bayan ke ban ñara ganin wata mace da sunan so ko vurgewa ba. Shi ya sa na sha gaya miki ke ce a jiya da gobe da shekaranjya da jibi a cikin zuciyata ba ki da kishiya ke ɗin da na zaɓa tun farko na kuma ƙasa sauya ki Fatima. Soyayyarki ce duk ta wahalar da ni ta sakani na riƙa rayuwa dabam da na sauran mutane, gani nake yi duk abin da ya faru babanki ne ya yi sanadin faruwan shi da farko ba na bibiyanki saboda Ina so na manta dake amman daga lokacin dana fahimci ina sonki ba kuma zan taɓa daina sonki ba sai na fara bibiyan ki a lokacin kina Univesity of Ibadan har ranar graduation ɗin ku ina cikin makarantar ku, na ganki amman ke ba ki ganni ba."
Mamaki ya kama Mimi cikin alj'abi ta ce"Ka je har ibadan?

Aji ya gyaɗa kai kafin ya ce"E. mana, na je har hoton ki na ɗauka a lokacin zan nuna miki da safe, ina bibiyan duka motsin ki saboda ina so na gani ko kin manta dani sai na samu tabbacin ke ma ba ki manta da ni ba. Dawowarki Abuja ya sa na cire rai dake saboda na san mahaifinki ba zai bani auran ki ba,nima kuma na haramta ma kaina ke a lokacin na fita batun ki daga bibiyanki amman kin kasa fita daga rayuwata faɗawata harkan kwallon kafa ya sa lokacina ya zama ragagge. Sai ya riƙa ɗauke min hankali daga tunani da shiga damuwa amman na kasa mantawa dake, a cikin kirjina na ke jin kuna amman ina samun salama in nasan ke ma ba ki yi aure ba, kamar yadda nima ba wata ƴa mace a gaba na.Nasan ke ce mai accuout ɗin Miaj kuma ba wani ya gaya min ba a jikina na ji hakan ko daga yadda kike yawan bibiyata, amman ban tuna nuna miki na gane ki ba. Na dawo da sanin komai na rayuwarki ne daga fara aikin da gidan Tv hankalina ya tashi kin san ina da bala'in ki shi ba na so na ga wasu mazan suna yabon ki, ko suna ambaton kin birgesu, kuna nake ji in na tuna kina can kina birge wasu mazan, na kalli hiran da kika yi a gidan talabijin ɗin ku kina ba da labarin ki da yanayin yadda a ka riƙa comments na yabawa gare ki, kwana na yi ban yi barci ba sai na fahimci duk ɗauriyata ba zan iya ba Na fi ki farincikin haɗuwata dake a Dinner bikin Makama domin ganin ki ya sa na ji kamar zan iya samun ki. Sai dai na kasa ba ma zuciyata dama kan abin da take so saboda tunanin abin da mahaifinki ya yi min.

Mimi wlh tallahi lokacin da Hajiya da Momny suka zo min da mganar auran ki kaɗan ya rage ban suma saboda daɗi ba na kwana farinciki da godiyar ubangiji na yi ta sadaka sannan bayan azumin Kaffara na yi azumi bakwai wanda na yi alƙwari tsakanina da ubangiji a kan duk ranar da na same ki zan yi wannan azumin. Na saka miki waɗannan sharuɗdan ne saboda ina tunanin zan iya rama kwatakwatancin zafin da na ji a zuciyata saboda rashin ki, Mimi saboda ke nake son shiga bangaren Inna in na ganki sai naji damuwata ta yaye, in na zo ban ganki ba sai na ji ni cikin kunci, ina tsokanarki Ssboda na ga fushin ki saboda kina yi mini kyau sannan ina so ki rika biyemin muna mgana a tsakanim mu, Mimi in na saka ki kuka ji na ke yi kamar zan mutu yadda na tsani kukan Inna haka ma tsani na ji kina kuka, lokacin da kika fara sakarmin fuska muka fara zama na fi kowa farinciki in da za ki tona zuciyata a Lokacin kamar farar takarda, ba a son raina na gayya miki mganganu ba Fatima har ga Allah zuciyata ne na ƙasa iya sarrafata ta manta baya shi ya sa na kasa ba ta haɗin kai ko dama kan abib da take so. Sai na yi yunkurin mu gyara zaman su sai wata zuciyar ta hana ni, sheɗan ya yi tasiri a kaina na so na yi ma kaina saken da zan ta nadama har na koma ga Allah.

Har ga Allah ban ɗauka za ki tafi ba na ɗauka kamar yadda na ke sonki kina min son da ba za ki iya bari na ba bayan tafiyata ranar ban yi barci ba na yi ta nadaman abunda na aikata, a lokacin da baki nan na shiga tashin hankali kawai ina daurewa ne ina cikin zullumin da tunanin kada na rasaki a karo na biyu , ko ba ki zo min da wasu sharuɗɗan ba da addu'an iyaye da abokai na suka na gane gaskiya riko ba shi da amfani gwara na bar komai ya wuce domin nima na zauna lafiya cikin rayuwa mai kyau kamar kowa, abin da ya sa na gaya miki haka ina so yau ki sani tun bayan rabuwar mu da shekaru goma har yau har gobe matsayin ki bai taɓa sauyawa ba, I love u so much, ke ce mahaɗin farincikin rayuwata Fatima"

Kafin ya gama magana Mimi har ta fara shessheƙan kuka. Saboda mganganun sun shige ta, ƙara wani kamkame shi ta yi kamar za ta maida shi ciki ta ƙara fashe masa da kuka lokaci ɗaya tana faɗin" Shi shi ne ka yi ta ba ni wahala haba mana."
Haka ta ke faɗa ta na dukan sa a kirji shi kuma ya na jinta amman bai hanata ba haka ya ƙara rumgumeta kamar zai maida ta ciki lokaci ɗaya yana faɗin"Na sani, na sani amman yanzu komai ya wuce."
Kuka mimi ta riƙa yi kafin cikin kukan ta ce"ka sa na kasa kallon wani ɗa namiji da sunan so, na kasa ganin kowa sai kai. Kowa ni yake kallo an ce naƙi aure kai na ke jira ba ni da tabbas a kaina kowa sei yace ka daina sona ni kuma ina da yakinin kana sona har gobe, aji ina barci da hotonka a saman kirjina, ina kuka a kan hoton ka saboda ina tunanin ka yi min nisa!. Me ya sa ka bani wahala!.? Ka bar ni ina zaman jiran ka shekaru sama da goma bayan kuma ma same ka ka yi ta ba ni wahala, me ya sa ka min haka? Kasan yadda n ke kwana kuka saboda kai? Ta faɗa tana kara fashewa da kuka lokaci ɗaya ta na dukansa da hannunta sai da ya bari ta yi har ta gaji sannan ya kamata ya sake rumgumeta ya haɗe bakinsu wake ɗaya na tsawon lokaci ɗaya sannan ya sake ta, ta lna haki ta ce"Da na rasa ka da bansan wani hali zan shiga ba, ina sonka, da ban same ka ba da na shi."
Bai barta ta ƙarisa ba ya ƙara haɗe bakinsu waje ɗaya bayan ya maida ta kasa shi kuma ya zama yana samanta daga nan sai zencen ya sha bamban Mimi ta kamkame Aji tana sakin masa kukan farinciki shima ji ya yi kamar ya yi mata kukan saboda yanayin da yake ciki, ji ya ke yi kamar ya buɗe zuciyansa ya saka ta a ciki domin ta fahimci soyayyarta ta wahalar da shi.

A Wannan daren masoyan sun raya shi ne wajen fallasa ma juna abin da ke cikin zukatan su, da safe Aji ya ɗauko hoton Mimi da ya ɗauka a ibadan a cikin wayarsa tabbas ko ya je, itama nan ta nuna masa Ajiyayun hotunansa na wayarta da kuma ma ajiyan sirrinshi in da hotunansa suke da ta saka a ka yi mata babban frame har da tsohuwarta wayar da tsoffin tasa tasan da suka riƙa yi ma juna a shekarun baya. Ya yi mamakin ganin har a lokacin ta na nan a jiye da duk abin da ya dangance sa.
Ranar kasa fita ya yi itama haka sai kawai ta zama ranar tuna old momory ɗin su. Su yi dariya su ji haushin juna sannan su kuma koma su ƙamkame juna kowa na faɗin da ya rasa ɗan'uwansa bai san halin da zai shiga ba, tunda kowa ya san ba ma ɗan'uwansa wahala barin ma Aji sai ya yi alkwarin ba ta dukkan wani farinciki a zamantakewar su itama haka ta yi masa alkwarin ba shi dukkan wani jin ɗaɗin rayuwar aure. Amman ya faɗa mata ta kiyaye masa kanta da auransa yana da kishi, in ta kiyaye sai su zauna lafiya har abada ba mai jin kansu sai dai in sun samu matsala su zauna su sulhunta kansu a tare.

Sun fara gudanar da kyakyawan rayuwa mai cike da abun sha'awa in Rukky ta zo gidan Mimi ta yi ta ba ta sha'awa tana tunanin Allah ya sa itama Nasir ya nuna mata so haka. Da gaske ne ta na son shi har ya shiga gida, Mimi ta fahimci mijinta mai son a yi masa biyayya ne sannan a bi ra'ayinsa sannan in ya ce abu to a yi masa cikin gaggawa sai ta zama mai danne bukatunsa a kan nata, sai a ka zauna lafiya tunda ya zama shugaba kuma wakilinta komai in za ta yi sai ta tambaye sa, ko shawaransa mota ma da za ta sauya sun yi magana sai ya ce ya so shi ya sauya mata mota amma ba yanzu ba. Ba zai tsaida ta ba in tana bukatar canjin yanzu ne shike nan jin abin da ya ce ne ya sa ta fasa siyan motan saboda ta girmama maganarsa kuma ya ji daɗin haka. Target ɗin shi na gaba Inna ta je ta sauke farali bayan nan komai wani irin buri ne zai cika shi daga baya, burin kai Mimi duk in da take so a faɗin duniya sannan ya yi mata komai take bukatan anan duniya domin shi take so ta kuma zauna da shi duk tsanani da wahala.

Duk in da ya ce kada ta tsallaka ba ta tsallakawa, ko gidan Hajiya in ya ce ba za ta je ba ko ba ta so ba ta nuna damuwa shi ya sa da kansa in

31 / 49