Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
ya nuna mata ta ce sun gasu ta karɓa ta ƙara sakaa wasu buredin da butter ta maida, ita kuma tana cigaba da soyan ƙwan suna hira sama sama.
A tare suka gama sannan Mimi ta gyara kitchen ɗin dakyar Aji ya taya ta ɗaukan Kayan karyawan nasu zuwa Dinning suka zauna saman karyawa, a lokacin ne yake ce mata mganar zuwan su kwami ba ta sai dai zuwa gaba.
Cikin mamaki ta kalle shi lokacin tana tura Buredi da ƙwai bakinta sai da ta kurɓi Tea sannan ta ce"Me ya sa?
Kai tsaye ya ce" Nima tafiya ce ta dole ta kamani zuwa Abuja."
Sai Mimi ta washe baki kafin ta ce"Gaske? Me za ka je yi?. Nan ya ke gaya kata yadda suka yi da Coach ita kuma ta ce"Gaskiya bai kyautu kace ba za ka je ba. To ya kenan?
Ya na kallonta kai tsaye ya ce" Tare za mu tafi Abujan sai ki je gida ki yi adadin kwanakin da zan yi, domin ba zan barki can ba tare za mu dawo."
Cikin gamsuwa ta ce" To can Bauchin fa?
Sai da ya kurbi Tea shima kafin ya ce"Sai dai zuwa bayan sallah tunda kinga yau sallah bai fi saura kwanaki goma ba."
Sai ta jinjina kai kafin ta ce" Allah ya kaimu da rai da lafiya."
Ya amsa mata da Amin Amin, suka cigaba dahiiran su, ba kasafai ya cika faɗa mata wasu abubuwan da suka danganci aikinsa ko iyayensa ba, sai in yan hiran na shi suna kusa. Kamar daga sama ta ji ya ce"Fatima kinsan burika na guda uku ne anan duniya?
Sai ta girgiza kanta amman ta maida hankalinta a kansa tunda dukkansu sun gama ƙaryawan.
"Burina na farko shine Inna ta kasance cikin farincikin da kowacce uwa ke fata, Sannan burina shi ne na kai ta kasa mai tsarki ta sauke farali, na biyun kuma na mallakeki shi na cika wannan burin tunda na same ki, sannan na cika burin inganta rayuwar Inna abu ɗaya ya ragemin na kaita kasa mai tsarki ta sauke farali, ɗayan kuma zan faɗa miki daga baya."
Mimi ta yi shuru tana kallonsa kafin ta ce"In sha Allahu za ka cika burin ka, inna za ta je ta sauke fqrali ƙila ma ba sau ɗaya ba."
Mirmishi ya yi kafin ya ce"Ba ni da kuɗi yanzu duk na yi amfani da su Wajen hidindimu, ga kuma sallah na matsowa akwai sauran hidima amman ina so a wannan shekaran Inna ta je ta sauke farali In sha Allahu."
Mimi cikin jin daɗi ta ce"Allah ya amince,in kana bukatar kuɗi, akwai kuɗi a hannuna sai ka yi amfani dashi in ka samu sai ka maida min."
Bai ce mata komai ba, sai ta cigaba da faɗin" Kuma ga shi ma za ka je wannan taron na ji ana ta zuzuta ka iya taka leda nasan za ka iya kaiwa matakin kaiwa A kungiyar kwallon kafa ta Nageria."
Sai a lokacin ya ce"Ni fa ba ruwana da wannan, in da na ke ma ya isheni Fatima a baya ban taɓa tunanin zan kai haka ba, Shi ya sa ban cika son tusa kaina ba, matsayin da na kai a yanzu ma Ubangiji ne ya kai ni, ina kuma gode masa ban sani ba ko nan gaba Ubangiji ya ƙara dagani amman yanzu ni dai ba zan tusa kaina ba. A hakan ma Alhamdulillah."
Mimi ta na so ta kara mgana amman sai ya dakatar da ita miƙewa ya yi lokaci ɗaya yana na faɗin" Zan yi wanka Fatima."
Sai ta miƙe suka jera zuwa cikin Bedroom ɗin su kowanne na sake sake a cikin ransa.
Yinin ranar yana gida bai fita ko'ina ba sai dai waya kawai.Sai bayan mangariba ya fita ya je gidan Inna suka gaisa, ta yi masa mganar zuwa Kwami nan ya ke gaya mata cewa sai dai bayan sallah tafiya Abuja ta kama shi daman kuma ya yi ma Mimi alƙwari za su tafi tare ita sai ta sauka a gida Inna tace hakan ma ba laifi, yana gida har a ka yi sallar isha'i kuma sai da ya ci yuwo da miyar kuɓewa, da su ka yi waya da Mimi ya gaya mata ga shi ya na cin tuwo sai ta ce itama don Allah ya ce ma Inna za ta ci, kai tsaye ya ce"Ni ɗan aiken ki ne? Ba zan iya daukan tuwo ba."
Ta san halin shi ya sa ta kira wayar Inna ta gaya mata tana son tuwo nan da nan inna ta ce a saka mata a Kula Baban Inna ya wuce mata da shi, ya na zaune kai tsaye ya ce"Ni kuma Inna? Daga nan ba gida zan je ba fa."
Inna ta harareshi kafin ta ce"Ko ba gida za ka je ba sai ka ɗauka ba na son iyayin banza."
Shuru ya yi bai kara mgana ba har Walida ta zubo tuwo da miya a kula sai yake mata mganar yaushe za ta gama Traning ɗin ta?
Kai tsaye ta ce"Wata mai kamawa yayanmu., Amman mai shagon ya ce zai rikeni na riƙa zama masa kafin lokacin zana jamb ɗin ya yi." Da sauri ya ce"A'a ba za ki zauna ba, ki dawo gida ki cigaba da taya Inna zama."
Inna ba ta yi mgana ba daman itama tunda ta gaya mata ta ce ba ta amince kuma daman tasan shima Baban inna bazai amince ba.
Inna ce ta ga Walidan ta ɓata rai sai ta ce"Nima na ce mata ta yi hakuri ita mace ce, ko wannan ɗin ma da ta yi saboda Kun matsa ne. Ni da har shawaran ta fara zuwa can anguwan da muka taso wajen Bahijja yar wajen Dije ta fara koyon ɗinki kada ta yi ta zama ba ta wani abun."
Mansoor ya mike lokaci ɗaya yana faɗin" To gwara ma can ɗin, ki yi mata mgana Inna abin da a ke bukata sai a sanar da ni."
Shike nan ma har ya zartar da Hukunci Dole Walida ta yi shuru, amman ita har ga Allah ba ta son koyon ɗinki yana da wahala, Inna kuma Daman shawara ce nata abin da Baban Inna ya ce shike nan ballantana Baba da duk abin da ya zartar sai ya ce mata ya yi, gwara Mariya auranta za ta yi, itama ta na da samarim amman kuma tunda ta ce karatu za ta yi ba ta da ikon sauya wata mgana daga baya.
Tana ji ta na gani Baban Inna ya bar gida bayan inna ta ce za ta kira Dijen su yi mgana ko ita Walidan ta je ta samu Bahijja su yi mgana.
Abu kamar wasa ƙaramar mgana ta zama Baba Inna ta kira Dije ta ce ai bakomai an zama ɗaya, ta ce Walida ta fara zuwa gidan Bahijja ita a Tunferre take zaune kuma babbar Tela ce gidanta cike da yaran mata har da matan aure ma ba'a bar su a baya ba, Walida ba ta da ra'ayi amman tunda mai gayya mai aiki ya zartar shikenan
Kuma duk abin da ake bukata Aji ya ba ma walida kuɗi ta siya, kenan ba ta da iko da ta ce ba za ta je ba, an gama mgana da cewa da zaran an yayeta a computer Traning za ta fara zuwa, da ta gayama mariya abin da Yaya Mansoor ya ce itama ta ce ta na so za ta yi kafin auran ta ya zo, tunda wani Lokacin Walida na biyawa ta gidan Magajiya ta yi laushi kamar ba ita ba wani ookacin har cewa ta ke yi, Walida ta gai da Inna amman kunya ya hana ta zuwa gidan innar da kanta.
Mariya Auwalu ta yi ma mganar itama tana son koyon ɗinki tunda ga Walida ma za ta fara zuwa da ta ce za ta yi ma Yaya Mu'azzam magana sai ya ce ta bari shi zai ba ta kuɗin abin da za ta bukata, ba zai zama lalle sai komai Mu'azzam ko Mansoor sun yi musu ba, suma ya kamata su riƙa taimakawa da wani abun, Saddiqu dai lagos ɗin ta gagare shi ya koma yana zaman shago, gida duk ya lalace ga dai ɗakin nan Inna ta bar musu amman ba kowa ciki sai tara tarkace Maeesha ke yi, can ma bangaren da Maeeshan ta tashi shima Mariya ce ke tara tarkacenta a ciki, tabbas dai Inna ita ce gida ko shiga da fitan jama'a babu kamar baya.
Shi kuma Baba tunda bayan abin da ya fqru ya daina ɓata bakin shi, ya bar Magajiya da Ƴaƴanta duniya ta koya musu hankali daman an ce indan an ciza a hura Saboda gudun ranar nadama kuma ga dukkan alamu nadamar ta fara shigar su.
*****
Ana sallah saura kwana shidda Mimi da Aji suka tafi a Abuja jirgi suka bi, ana gobe taron da Mansoor zai hallata. Har gida ya rakani Mimi sai da Mommy ma ta saka baki ya tsaya ya sauka nan ya yi sallah ya ci abimci kwana kuma ya ce ba zai kwana ba, Mimi ta san halin yan kayanta shi ya sa ba ta matsa masa ba, hotel ya kama ya kwana washegari kuma a ka yi taron a Eagless Squeare, An san da zuwan shi tunda ya na wakiltan Gombe United ne ya haɗu da shugabbanin Kungiyoyin kwallon kafa ta jihohin Nageria waɗanda ya sani, da ma waɗanda ma bai sani ba su sun san shi, ya haɗu da su Ahmad Musa shima sun gaisa sannan ya nuna masa sani da cewa yana kallon wassanin shi sannan hatta shuggaban Super Eegless ɗin sun yi mgana da Aji abin da bai sani ba Coach ɗin su ya daɗe yana kai mganarsa sama tare da video ɗin wasannin Aji fatan sa kafin Contart ɗin sa ya ƙare Allah ya ɗaga sa zuwa sama amman baya taɓa bari Ajin ya sani tunda yasan in ya sani zai ce shi baya bukata.
Kwana biyu a ka yi ana taron na ƙara ma juna sani ne kan abib da ya shafi ƙwallon Kafa ne, bai ƙara neman Mimi ba sai da suka gama taron gabaɗaya sannan ya memeta. Ranar da ya je gidan sun daɗe suna hira nan ya yi sallar mangariba da isha'i ya ci na rana da sare sai dare ya tafi washegari Mimi ta matsa masa sai da suka fita zaga gari, su ne wajajen shakatawa da kuma wajajen siyan kayan ƙwalama sun yi hotuna da Vedio sai dare ya maida ta gida. Washegari suka juya Gombe,sun koma saboda sallah saura kwana biyu ne. Tun yana Abujan sun yi mgana kan ragunan layya da zai siya. Daman duk salla Aji ke yi ma Inna layya Mu'azzam kuma sai ya yi ma Baba.
Akwai daman wani anan anguwansu mai safaran Rlraguna daga taraba daman wajensa suke siya, Mu'azzam ya turo kuɗin raguna biyu ya ce ɗaya na Baba ɗaya kuma Baba Sani tunda shi ne Babba in kuma shi ya yi layya naman gida biyu za'a raba Baba Danlami ya ja na shi, shi kuma sai ya siya guda biyu na shi ɗaya na Inna guda ɗaya, Mimi ma za ta yi amman ita Daddy ne yake siya mata ita da Hajiya.
Ana gobe sallah a ka raba ma kowa ragon shi su Baba Sani suna ta godiya, Auwalu kuma ya siya ma Magajiya ɗan bunsuru ya ce ta yanka ta yi ta murna tana saka masa albarka, abin da ba ta yi a baya amman yanzu ta fahimci yadda duniya take.
Ana goben sallah a daran sai ga wata ɗiyar kanin Maman inna, suna matsayin yar mace da yar namiji ne, amman ubansu ɗaya ne da babanta. Lokacin da suka rasa mahaifinsu mahaifiyarsu ta kwashe yayanta sai bayan sun girma me suka nemi dangi, kuma shima ba'a nan sokoto ya ke zaune ba ya na tureta ne cikin garin Sokoto, Ita ce ta sauka a gidan wanzamai tunda wayar Baba Ɗanjuma ta kira.
An faɗa mata tana da wata uwa a garin Gombe shi Baban nata dake kwance ya na jinya ya ba ta lambar Baba Ɗanjuma da ita kaɗai gare shi ba shi da lambar Inna. Da ta fara biyawa ta can babban gidansu na Argugun ne ta samu tabbacin Inna Meri na aure a garim Gombe ne duk da ta kwana biyu ba ta je ba, shi ne ta shirya ta zo gombe sai ga ta a gidan Wamzamai ta sauka ɗakin Magajiya.
Inna ta san Tanimu ne kaɗai ya rage mata acikin ƴan'uwanta duk sauran sun rasu amman shi ba shi da zumumci sau ɗaya ta taɓa zuwa cqn Tureta, ko argungun sai ya fi shekara goma bai je ba.shi ya sa itama ta manta da shi kawai. Ta san yana da ƴaƴa amman ba za ta san su da adadin su ba..
A Daran salla Inna meri na zaune a falo tana na casbaha,Walida na kitchen tana ta suyan kajin da Yaya Mamsoor ya kawo musu sai ga Baba Ɗanjuma tafe ba bakuwa tun kafin ma ta yi mgana Inna ta ga kamar su da Ahalnta. Safiya da goyom yaronta namiji ta zo sai guda biyu yan biyu mata ma su takawa, Lokacin da ta ce ita ɗiyar Tanimu ce Inna ba ta yi mamaki ba domin taga kama bakinta yaƙi rufuwa Safiya ta ga tarba ɗakin mai katifa aka sauke ta a ciki Inna ta ce Walida ta ba ta duk abin da take bukata, a daran kwana suka yi hira nan ta ji ashe Tanimun na kwance ma ba lafiya shi ne ma yace ta je ta nemeta tana da wata Uwar a garim Gombe, Ita ma a can Tureta ta ke aure yayansu namiji ne amman ya rasu saura su mata biyar itace ta uku
Inna Meri tana ta faɗan shi ya yarda zumumci, ga shi yanzu ko can gida ba wanda yasan halin da yake cikim Safiya ta ce an sani amman ba wanda ya bi ta kansa Inna ta ce To tunda bai ɗauki kowa da muhimmanci ba wanda shima domin yanzu Lalura ta same shi a tsaya ta kanshi.
Nan da nan Inna tace ana fice sallah za ta bi Safiya ta je ta Duɓa Ɗan'uwanta, Washegari sallah ko Sabom kayan inna Ta ɗauka ta ba ma Safiya ta saka tunda sai a hankali daga ita har yaran nata daga gani suna cikin wahala. Halima ce mai yaran mata sa'anin yan biyu Inna ta kirata ta ce in za ta zo ta zo mata da wasu daga cikin kayan su zainab, yaran kuma na goyo Inna ta ce Amina tunda ta na da ƙaramin goyo.
Mansoor bai son da mganar zuwan wata bakuwa ba sai da ya zo ɗaukan Inna domin tafiya Idi ya ga bakuwar. Inna ta gabatar da ita a matsayin tubashiyarsa ita kuma ta sanar da shi Baban Inna kenan babban yaronta da ta haifa a can garin kwami Sauran yaran suna nan zuwa za ta gan su.
A mota Mansoor suka je sallar Idi, Inna sai Walida da Safiya sai Mimi a gaban mota can gida kuma Baba ya tafi a mashin ɗinsa tunda Aji ya ba shi mashin ɗinsa, bayan sun dawo sallar idi a ka yanka yanka ragunan layya masu fili da gyara suna aikin su, ita na Mimi a can gidan Hajiya za'a gyara a soya mata na shi kuma anan za'a gyara sai su tafi da shi can Mimi ta soya.
Suna gidan har azahar Safiya na ta yi ma Aji wasan dake tsakanin su amman ba ta ga fuska ba sai bayan tafiyarsu ne Walida ta ce mata"Wanman fa da kika gani bai son wasa ba, dama yaya Mu'azzam ne."
Ita ta zauna ta na yi ma Safiya bayanin iyalan Innar gabaɗaya.
Lokacin da Aji ya kira baba Yakubu domin gaisuwan sallah ne yake gaya masa bikin Yayansa guda uku bayan sallah da sati ɗaya, Inna ta sani domin ta taba gaya masa sannan Gwaggo Yalwa ta na can har yanzu ba ta koma gida ba sannan kuma da ya kira can kwami Sadi yaron baba karimu ke faɗa masa tautsuyi ya samu Babansu ya faɗi a mashi a hanyar gona ya samu karaya da raunika kenan bayan sallah tafiya kwami da Bauchi dole.
Ranar sallah na biyu Mimi na gida ta lna aikin nama su cincin kuma aikatau ta ba da, Ranar salla ta uku kuma gidan Inna ta yini, Safiya ta yi ta mamakin ganin yadda su Halima ke yi da Inna ta sha mamaki da Walida ta ce ba ita ta haife su ba. Bintu ce sarkin baki tana cacankarta itama tana ramawa, ranar salla ta uku Mimi ta je gidan Hajiya dagacnan ta biya ta gaida Daddy,har suka haɗu da Jaheed suka gaisa kamar wani abu bai faru ba.
A ranar ta je har gidan su Rukky daga nan ta rakata suka je gidan Bibi, gidan Nasir ne ba su je ba saboda Rukayya Ahmad kuma wannan sallar a kaduna suka yi.
Sai Dare ta dawo gida Aji kuma ya ce ta gama fita, ta yi zumumci gidan Nafisa bai samu ba sai dai ta kira wayarta suka gaisa Nasir din dai da makama sun zo gidan.
Mu'azzam da Hibba ba su zo sallah ba. Suna can kano amman suncji labarin zuwan bakuwar Inna, Safiya da tafiyar Inna, amman ba su tafi ba sai bayan sallah da kwana huɗu,.Tunda har gidan Wanzamai ta je ta yi ma Magajiya sallama abun mamaki har ta na ba ma Safiya 1k, ta yi ma Inna faram faram kamar ba ita ba.
Mansoor ya kai Inna tasha sun rabu akan cewa ta gaya masa Bintu da Halima da Mimi za su je bauchi biki shi kuma ya je ya gaida Babansa sai ya bar su su karisa Bauchi sai an gama biki sannan za su dawo.
Kai tsaye ya ce" Inna to ni fa? Da wa zan zauna?
Inna ta masa dakuwa kafin ta ce"Ban sani ba, da dawa kake zaune?
Sai ya sosa kai yana mirmishi. Safiya taga sha tara na arziki. Kaya na sawa haka su Bintu suka haɗa mata har da na yara sannan ga Atamfofi guda uku biyu Manoor ya siya ɗaya kuma Mu'azzam Innan ma ta ba ta kayanta sabbin ga Safiya sannan ga kuɗi ma su yawa da Mansoor ya ba su a hannun su wanda zai ishe