Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
ma a hannun masu aiki suka yi wayau
Har dare Mommy ba ta ce musu komai ba, Sun dai ga sun shige ciki ita da Daddy da Hajiya sun jima suna mgana sannan ya fito, shi a ranar ya koma daman ba kwana ya ce zai yi ba. Hankalinsu ya kwanta ganin Mommy lafiyanta ƙalau ta na ta zirga zirganta suna da tabbacin ba ita ce wani abu ya same ta ba. Har Asma'u sun ma mgana ta ce itama ba ta sani ba, sannan sun yi ma Inna Zainaba mgana ta kalli Khadi da ita ce ta tsarete da tambayan abunda ya sa Mommy tace ta na son ganinsu."
Inna Zainaba ta ce"Ban sani ba,ko jira ita uwar taku ai tunda ta kira ku za ku ji abin da ke faruwa." Sai suka yi shuru ba su kara mgana ba ko Dr da yake namiji bai damu ba. Harkan gabansa kawai yake yi sai su ne duk suka damu barin ma Khadi da Madiha.
Madiha ba ta hakura bq sai da ta je har ɗakin Mommy a daran ta ga ta na waya amman ta na ganinta sai ta ce"Zan kira, yanzu zan yi mgana da yaran nawa."
Daga nan ta juya tana kallon Madiha cikin Mirmishi kafin ta ce" Madiha Kabir Dabo,."
Haka ta kira sunanta sai itama ta yi mirmishi kafin ta ce" Barrister me ke faruwa ne? Kin kiramu kuma kin ƙi ce mana komai? Kin san gobe zan koma ga Dr ma ya na da Tiyata jibi ya ce."
Sai Mommy ta dafa kafaɗanta kafin ta ce"Ina sane da abin da nake yi, mu je ɗakin da Hajiya ta sauka sai mu yi mganar gabaɗaya.
Tare suka fito da Mommyn da Madiha Dr ya na ɗakin da yake sauka Mommy ta kira shi a waya ta ce ya shigo cikin gida. Mimi kuma tana ɗakinta suna waya da Aji, yana gaya mata gobe zai zo su haɗu daman ya yi kewarta sosai, itama Khadi ta zo ta kira ta Ummi dqman tana goyo bayan Inna Zainaba ta na barci bayan mangariba ta fara rigima ana yi mata mata wanka sai ga shi ta yi barci bayan ta goyata.
Gabaɗayansu sun haɗu a ɗakin da Hajiya ta sauka amman kafin nan inna Zainaba ta faɗi wata mgana da ya jefa su a duhu domin kallon Mommy ta yi kafin ta ce" Murja kina ba ni mamaki sai wani tare tare kike da yara? Ba fa saɓon Allah za ki yi ba sannan ke ce wwarsu ba su ba, ballantana ki ce yardan su kike nema ai ya kamata daman tuntuni ki yi ma kanki faɗa tunda zaman haka gare ki da sauran kuruciyarki ba zai miki kyau ba."
Ga shi dai ba ta faɗa kai tsaye ba amman dukkansu sun sha jinin jikinsu, ai ba su ƙara firgita ba sai da Mommy ta warware musu mgana ce ta aurenta ya ta so, wani Alkali a ya ganta ya na so tun daɗewa amman dai ba ta bashi fuska ba, yana ta bin ta sai yanzu ne ta bashi daman a takaice tana so ta yi aure kuma ba har ya je kano ya ga ƴan'uwanta yanzu ma haka gobe a ke son a je can kano a ɗaura auran amman ta ce a dakata mata sai ta yi magana da janin mijinta da wwar mijinta da kuma Yayanta, to ɗazu ta yi mgana da Daddy ya ce abu ne mai kyau daman zamanta haka ba daɗi, Hajiya ma ta ba ta dukkan goyon baya, ita ta ma yi garaje ne tana ganin kamar in ta kawo maganar Murja ba za ta amince ba, amman har ga Allah taso Hamza ya auri murja amman tunda har ta daidaita da wani sai ba ta kawo mganar Hamza ba, ta ba ta dukkan goyon baya. Ita yanzu tana son jin ta bakinsu ba, su ɗin ƴaƴanta ne suna da haƙƙin ta sanar da su kafin auran ita ta ce ma adakata amman in ta waliyyanta ne da tun zuwan farko an ɗaura mata aure da Alƙali Mustapha Tafida, matarsa ɗaya yayansa biyar amman duka sun yi aure kawai shi dai ya na son Barrister Murja ne amman ƙarin aure ba shi cikin tsarinsa matarsa likita ce tana aiki a wani babba asibiti anan garin Abuja.
Gabaɗaya sun kasa mgana saboda lamarin ne ya zo musu a bazata. Ban da Dr da ya yi mirmishi kafin ya ce"Haba Mommy don za ki yi aure sai ki ce sai kin nemi yardan mu? Mun san cewa tunda Abi ya rasu wata rana za ki yi aure tunda ke ma kina bukatar Kyakyawan rayuwa anan gaba, mu ma a matsayin mu na ƴaƴanki hankali mu zai kwanta sanin kina ƙarƙashin wanda zai kular mana da ke, sannan a kallah bayan Abi ƙin kara samar mana gurɓin ƙara kiran wani da sunan uba."
Mommy sai kawai ta fashe da kuka, Hajiya ma sai da ta share kwallah tana fqɗin"Allah ya yi maka albarka Sulaimanu, ban taɓa ganin mai hankali kamar ka, kaf cikin Ƴayan Murja ba kamar ka, Allah ya raya maka zuru'a shi kuma babanku Allah ya jiƙansa da rahama."
Ya amsa da Amin ya na mirmishi kafin ya tashi ya ƙarisa kusa da Mommy ya zauna ya na lallashinta, Mimi ta ji abun a ranta domin Abi kawai ta tuna amman ba ta jin za ta iya cewa kada Mommy ta yi aure, amman har ga zuciyanta sai ta ji zafin auran da Mommy za ta yi.
Bangaren su Khadi kuwa ba wanda ya san abin da ke ransu sai da Hajiya ta kalle su kafin tace" Ku ba ku ce komai ba? Ba yardan ku ta ke nema ba, kawai dai ta gaya muku ne saboda kuna da haƙƙin ku sani ku saka mata albarka mahaifiyarku ce ba ku da kamarta, kun dai ji kalaman yayan ku? To kuma ku yi ko yi da shi."
Madiha ce ta girgiza kanta kafin ta ce"Tsaya tsaya Hajiya ni fa ban gane ba, shin Mommy za ta yi aure gobe? To menene amfanin gaya mana ba yardan mu take nema ba, tunda ko mun ce a'a ba abin da za'a fqsa. Maganar gaskiya ni ban goyo bayan wannan auran na Mommy ba, me ta nema ta rasa? Me take bukata? Abi ya rasu ko shekara biyar bai yi ba Mommy kin manta da shi za ki je ki auri wani, kuma ki sakamu mu kira shi da sunan Baba, gaskiya Mommy ba zan iya miki wannan biyayyar ba, ba da yawun bakina a wannan auran na ki ba sannan ni uba na ɗaya ne ya rasu bayan shi ba ni da wani uban kuma."
Daga haka ta mike ta fice t na kuka, Khadi ma ta na sharan kwallah ta ce" Gaskiya ba ki kyauta ba, wani irin aure kuma? Da girman ki gotai gotai da ke kice za ki yi wani aure? duka duka yaushe Abi ya rasu da har kin manta da shi za ki yi wani auren? Ni ma gaskiya ban yarda ba kuma ban amince da wannan auren ba."
Itama tashi ta yi ta fice ta na kuka Sulaiman na kiranta amman ta ƙi sauraran shi, Hajiya ta girgiza kai ba ta ce komai ba, daman ta san haka zai faru, Momny kuma tana ta kuka Mimi kuma ta kasa mgana kanta na ƙasa amman a cikin ranta itama ba ta son auran da Mommy za ta yi amman ta kasa mgana, Hajiya ta kalli Mommy lokaci ɗaya tana faɗin" Murja ki daina kuka, su ai ba su isa su hanaki aure ba, in kika biye ma yaran nan marasa jin mgana sai dai ki ƙare a haka, su ba'a aure suke zaune a gidan mazajasun? Ba na son iskanci da wawanci."
Mommy ta ɗago ta na kallon Mimi kafin ta ce" Mimi ba ki ce komai ba? Ke ma kina ganin na manta da babanku ko na ci Amanar sa ne?
Ganin yadda Mommy ke hawaye ya sa Mimi ta girgiza kanta kafin tace"A'a Mommy. Ni ban san me zan ce ba. Amman dai ba zan hanaki aure ba tunda kina so Allah ya sanya alheri, amman ina so ki ba ma su Khadi lokaci za su sauko daga baya.."
Ta na gama faɗin haka itama ta fita Mommy ta ta shi za ta bisu Sulaiman ya hana ta ya ce shi zai je ya same su, nan ya ta shi ya fita ya bar ta da Hajiya tana ba ta baki.
A ɗakin da Madiha ta sauke ya iske su sun haɗa kai suna kuka har da Mimi nan ya zauna ya na jawo hankalinsu da nuna musu falalan auran da Mommy za ta yi amman Madiha cikin ƙaraji ta ce" Ban amince ba, domin ban ga wata falala a auran Mommy ba, da girmanta ne sai ta yi wani auren? a she ba ta son Abi tunda har da mutuwansa ba daɗewa take tunanin sake auran wani Nlnamijin."
Tana faɗa khadi na faɗa. Sun ƙi sauraran sulaaiman, Allah ya kawo Inna ZAINABA ta yi musu wankan tsarki ta karishe da cewa"Wato ita ba mace ba ne sai kada ta yi aure, ta zauna ta cigaba da takaban uban ku yana kabari ta ƙare rayuwanta a lalace ko? To ba ku isa ba tunda Allah ya ba ta wannan damar wlh sai Murja sai ta yi aure ta samu natsuwa, ku na gidan auran ku ina ruwan ku da auranta? In ba'a aure ku me ya sa kuka yi? Ai mace ba ta wuce aure in ba mutuwa ta yi haka namiji, ina laifi ta zauna tsweon shekara uku ba aure, in da ace yau ita ce ta raau na tabbata in uban ku ya yi mata hallaci ta yi shekara a ƙasa tuni zai ƙara aure sai mace ce a ke ganin laifinta bayan ta rasa miji ta ce za ta yi aure sai ace gotai gotai da ita ko? Shi amman namiji ko ɗan shekara ɗari ne ba mai damuwa da shekarunsa sai ma a aura masa budurwa ba wanda zai ce wani abu, to bari ku ji na gaya mu ku, ko da yardan ku ko ba yardan ku wlh Murja ta gama zama matar aure a gobe in sha Allahu wanda ya ji haushi ya yanke ta kada ya sake nemanta, ku ne za ku taɓe domin ita sha kudum ce tunda kuka bari ta haifeku ta zama uwarku."
Haka ta ke ta faɗa da Dr ya ba ta hakuri ne ta sassauta amman sai da ta ce"Raina ne yaɓaci Sulaiman, ku ba yara ba kowace da mijinta da yayanta amman kuma ku ce murja kada ta yi aure? To ta zauna zaman ubanku a cikin gida? Wlh ba ku da tsausayi, daman na san ko kowa bai ce wani abu ba sai kin ce baki yarda ba, tunda daman ba ki da zuciya mai kyau, To mu zuba mu gani shege ka fasa." Ta tafa hannu bayan ta gama nuna Madiha da yatsa, sannan ta yi tsaki ta fice Sulaiman kuma kalaman bakinsa sun ƙare sai tashi ya yi shima kawai ya fita. Mimi ce mai sauƙi sauƙi itama haka su Madihan suka gama saka mata na su tunanin a ranta har ta ji itama tana jin haushin Mommy, A ɗakin nan suka kwana ko Ummi sai da asuba Inna Zainaba ta kawo ta, ta ce ta ba ta Nono kafin ta yi mata wanka.
Suna cikin ɗakin nan ko karyawa ba su yi ba. Sai da Dr ya sake dawowa ya lallashe su amman ba su ji ba gwara Mimi ta sha tea sannan ta ci dankalin da Asmauu ta soya ko saboda goyo. Sannan ta saki fuska har ta je ta gaida Hajiya da Mommy da duk idanuwanta sun kumbura saboda kuka Hajiya ta kalli Mimi kafin tabce"Binta ka da na ji ko na gani kin biye ma sakarkarun yayyenki kin saɓa ma Murja, kin ji ko?.
Sai ta gyaɗa mata Hajiya sai faɗa take yi Inna Zainaba na wajen ta ce"Hajiya kyalesu sai dai su mutu aure kamar an yi an gama."
Mommy daman a jiyan ta ce ita ta fasa Inna Zainanba ta dira kanta da faɗa da cewa"Sai zauna ki koma baya kina bin ƴaƴa sai abunda suka ce aure fa ba mai tada shi na ce duk wanda ya ji haushi kada ya ƙara neman ki."
Khadi da Madiha suka fara shirin tafiya, Sai dai misalin goma sha ɗaya safe suka ji Inna Zainaba na sakin guɗan an daura auran Mommy da wani, gabaɗaya sai hankalinsu ya ƙara ta shi, ba yadda sulaiman bai yi da su su tsaya kada su tafi ba suka ƙi ba da asuba kafin ya wuce tunda shi ma jirgin karfe bakwai ya bi ya koma kano ya samu ɗaurin auran Mommy.
ita madiha ta samu jirgi amman Khadi motar haya ta bi zuwa Kaduna kuma ko sallama ba su yi ma Mommy ba ballantana Hajiya, Mommy ta damu Inna Zainaba ta ce kada ma ta saka a ranta su je, ma ji ma gani in sun isa su sauya ma tuwo suna. Mimi ce kaɗai a gidan itama sun yi da Aji zai zo bai kuma zo ba sai bayan azahar shima da labarin Mommy ta tare shi sai ya washe baki yana riƙe da Ummi lokaci ɗaya yana faɗin"Ma sha Allahu abun alheri madallah. Na yi ma Mommy murna Allah ya ba su zaman lafiya."
Kawai sai ta saka masa,kukan me ya sa zai yi murna saboda Momny ta yi aure? Ba ya kishin Abi ne me ya sa Mommy za ta ƙara aure? Cikin Mamaki ya kalli Mimi kafin ya ce"Ban gane ba? Saboda addini ya ba ta wannan damar gwara da ta yi auranta sai mutumcinta ya fi fitowa a idanuwan waɗanda suka santa, sannan kuma kwanciyar hankalinku ne ku tuna yau tana da miji kuma sannan kun kara samun wani abu a karo na biyu."
Kawai sai Mimi ta saki baki ta kasa mgana, Aji ba zai gane ba ne shi ya sa ba ta ma samu damar gaya masa abunda ya faru da su khadi ba sai da ya shiga suka gaisa da Hajiya ita ke gaya masa har ta na cewa" Ga ta nan duk da itama ba ta ce komai ba amman zuciyarta ba daɗi ka sake yi mata faɗa don Allah kada su saka ma Murja hawan jini."
Aji ya kalli Mimi da ke gefen sa kafin ya ce"Haba Hajiya, suma ɗin yarinta ne amman in su san ciwon kansu ai ba za su yi haka ba, sannan su mata tunanin su a karkace yake, shi Dr da yake namiji ne ai ya fahimta kada ki damu Mommy auran da ki ka yi masalaha ne ga rayuwarki da ta su gabaɗaya ba za kuma su fahimta ba sai nan gaba kaɗan."
Inna Zainaba ta ce" Ka ji maaganar masu hankali, itama sai ɓata rai take yi tunda ƴan'uwan sun yi fushi sun tafi."
Kuma da gaske nan ko fara'a Mimi ba ta yi Mommy ma duk ranta a jagule ga shi sai kiranta a ke yi masu yi mata murna, tunda acan kano aka ɗaura auran shi kan shi Alƙali bai je ba. Sai dai waliyyansa kuma da kan shi ya faɗa mata an ce babban ɗanta ne ya ƙarbi sadakinta wato Dr Sulaiman farinciki ya cika Mommy har sai da ta yi kuka a ranta ta yi ma Sulaiman fatan ya gama da duniya lafiya shi da iyalansa yadda ya ke faranta mata shima Allah ya faranta masa haka. Aji bai tsaya wani lallashin Mimi ba saboda ya ga kamar abun na su har da iskanci, bai nuna ma ya gane ta na jin haushi ba bai daɗe ba ya tafi sun rabu akan itama gobe za ta koma, cikin zolaya ya ce" Ki tsaya mana ko zuwa laraba ku gaisa da sabon Abin naku mana."
Hararansa ta yi sai ya yi shuru ya na dariya , har ya ci abinci ta tafi raka shi tana kumbure kumbure shine ma ya sa ta saki fuska tunda cakulkuli ya riƙa yi mata tana dariya.
Yana kuma tafiya ta koma yadda take, Mommy ba ta yi gayya ba amman ta gayyaci abokan aikinta sun zo mata murna tunda da ɗaurin auren da tariyan duk ɗaya ne ita a gidanta za ta zauna shi ne zai rika zuwa wajenta in ranar girkinta ya shiga, bai zo a daran ba sai washegari da safe da ta ce ya zo su gaisa da Hajiya da Mimi za su koma Gombe. Gaskiya a ido mutum ne mai kamala da dattako ba yaro ba ne domin zai iya yin sa'an Abin ma, sun gaisa cikin girmamawa da Hajiya, Mimi kuma tana gaisheshi ya kama sunanta da cewa"Mimi auta ko? Yau dai navga auta."
Ya faɗa ya na mirmishi ya miƙa hannu ya karɓi Ummi yana faɗin"Ga kuma Ummi maryama ko?
Sai Mimi ta gyaɗa masa kai a ranta tana faɗin su Mommy manya, ta sha kwaliyarta suna ta yi ma juna wani kallo.
Ba ta gama mamaki ba sai da ta ji ya na tambayan su Madiha tunda Mommny ta gaya ma sa dukkansu sun zo.
Da sauri ta ce Madiha za ta koma saboda yara ita kuma Khadi saboda aikinta sai ya ce bakomai wata rana ai za su haɗu Dr dai yana kano sun haɗu tunda shi ya ba da auran Mommyn tashi ya faɗa har ya na kashe ma Mommy ido, Mimi ta ji kamar ta make shi saboda haushi.
10k ya saka ma Ummi a jikinta sannan ta yi masa sallama ta bar falon zuciyanta na ɗaci saboda haka ta matsama Hajiya suka koma Gombe a ranar domin ba za ta iya zaman ganin wannan bakincikin ba Aji ma ya yi da ita ta zauna da Mommy ko na sati ne sai su koma tare amman ta ki sai ta fake da aiki shi kuma ya san dalili amman sai ya ƙyaleta.