Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
Mu'azzam sai kuma ya fasa, yac e sai ya gama rigimarsa da Mimi sannan zai neme sa.
Dr. Sulaiman kuma na shiga cikin gidansa ya iske Jawahir a falo turus tana zaune da tsininin cikinta a gaba. Yara duk ba sa nan suna Mandawari sun je gidan kakanin su..ta na ganin shi ta sakar mai mirmishi lokaci ɗaya tana faɗin"Ka dawo da wuri yau."
Yana zama gefenta yac e"Kinsan ba aiki na je yi ba, duba Patient ne kawai."
Sai ta gyaɗa kai ta yinkura ta mike dai dai lokacin yake faɗin" Kun yi mgana da Mimi tun bayan tafiyar su Umra?
Jawahir ta ce"Sau ɗaya muka yi mgana lafiya dai ko?
Sai kawai ya miƙe yana faɗin"Bako gare ta. Mijinta ne ya zo."
Jawahir ta zaro ido kafin ta ce"Yana ina?
Sai ya nuna mata falon baƙi yana kora mata jawabin yadda aka yi ya ƙarishe da faɗin", na rasa me zan ce masa."
Jawahir ta ce"Gaskiya ba daɗi, tun zuwansa Abuja na yi ma Mimin faɗan ta yi hakuri ta koma gida ta saurare shi a kallah dai ai ya nemata, ina amfanin wannan abu kuma? Ai sai ya ɗauka kuma mutanen banza ne."
Dr ya mike lokaci ɗaya yana fadin"Daddy ne duk ya ke biye mata, amman yanzu dai haɗo min ruwa da lemu akwai abinci?
Sai ta ce sai da miya amman bari ta dafa ko shinkafa ne da Ssauri sai ya ce ta hanzarta, Ta wuce Kitchen duk da cikin ta ya girma amman matar likita ce motsa jiki a wajenta na da matukar amfani.
Shi kuma Dr. Sulaiman sai ya kira Daddy bai dauka sai da ya ƙara gwada kiran shi sai ga shi ya ɗauka sai daga baya ya tuna yau oahadi ne, bayan sun gaisa sai ya ke gayamasa zuwan Aji tare da cewa"Daddy ina jin kunya me zan gaya masa?
Kai ya ce"Ka gaya masa gaskiya mana, miye abun ɓoye ɓoye."
Dr Ya yi kasaƙe bai yi mgana ba jin haka ya sa Daddy ya ce"Ka ga kada ka damu, in har yana da hankali ya san in da zai zo komai ya warware."
Ya kashe wayarsa ya na yar dariya ɗan tselen uwa ashe dai ƴa na son fiyar ta shi har yanzu, in gaji da zagaye zagaye zai neme shi, a lokacin shi kuma zai gaya masa matsayarsa.
Jiki a sanyaye Dr. ya kwashi farantin ruwa da Lemu ya kai ma Aji dake zaune a falo har ya fara auna Mimi ta shigo falon nan ya fara balbaleta da faɗan sa amman maimakon ita sai Yayanta ya kara gani. Da ya ce ba zai sha ruwan ba sai ya nuna bai ji daɗi ba shi ya sa sai ya tsiyaya ya sha kaɗan shi da Babban shan ruwan shi ya ga Mimi a gabansa.
Amman sai ya ga ba ta zo ba,.Sannan Dr na zaune bai yi masa wata mgana ba sai ya gyara zama yana faɗin" Mimin ba ta nan ne?
Dr ya sauke numfashi kafin ya ce"Eh. Ba ku yi waya ba ne?
Aji ya maimaita E, cikin mamaki kafin ya ce" Ba ta nan? To ta na ina?
Ya faɗa cikin mamaki sannan lokaci ɗaya ya na ɓoye takaicin sa.
Cikin ɗan jin nauyi Dr ya ce"Tana Umra. Ta je Lagos wajen Madiha to ita da mijinta za su je Umra sai ta bi su suka tafi tare daman tana tare da Internationl ɗin ta, na ɗauka ma ko kun yi waya ne ta sanar maka?
"In ta sanar da ni ai da ba za ka ganni ba., Ni ba ta kirani ba asali ma na ɗaɗe ba na samun ta waya, kenan ka ga tafiyar da take yi ba da izinina ta ke yin su kuma, tunda har gobe ina matsayin mijinta ban ce na saketa ba, sannan ban ce ta yi yaji ba ganin damanta ne sai na kyaleta saboda ita mace haka t ke in ta gaji da abu sai ka bata iska, Amman ace da yau sakinta na yi da iddata ne akanta kuna Iyayenta za su barta ta riƙa yawo gari gari? Yanzu ma wata kasar ta fi ba tare ni Mijinta na sani ba tsakanin ga Allah hakan da ta yi ya dace ko a bangaren zamantakewa kafin ma a shiga mganar Addini.?
Aji ya karishe faɗa yama mai ƙura ma Dr Ido shi kuma sai ya jinjina kai kafin ya ce"Tabbas bai kyauta ba amman ka yi haƙuri, ni kaina ban san da tafiyar ba sai ana gobe tashin su amman zan kira wayar Madiha tunda kamar Mimin ta kashe wayarta zan gaya mata ta dawo akan lokaci."
Mansoor Aji miƙewa kawai ya yi lokaci ɗaya ya na saka wayar a cikin aljihun gaban Rigarsa kafin ya ce"A'a ku ƙyaleta kawai."
Takaici ne da ɓakin ciki suka hana shi mgana Dr na roƙomsa ya tsaya ya ci abinci ya ce ba zai tsaya ba.
Cikin jin nauyi Dr.Sulaiman ya ce"To haka za ka koma baka ci komai ba?
Sai kawai ya samu kanshi da Cewa"Ba wani damuwa, da yake ma kasan kanina SP ne a nan garin zan je gidansa mu haɗu."
Haka nan kawai ya ji yana faɗin haka, Dr Sulaimam duk bai ji dadi ba hakanan suka yi sallama ya rako shi har waje yana kara bashi hakuri shi kuma ya ce bakomai Saboda ya raunana Allah Mimi ta kure hakurin shi zuwa yanzu ya rasa matakin ɗauka a kanta duka matakan ƴakinsa sun rushe da gaske take yi abij da ta faɗa ba za ta bari su yi mgana ba, kuma da gaske take yi ta hakura da auran shi.
Sai yaji duk ya damu wata zuciyar na gaya masa duk laifinsa ne me ya sa a daran bai tsaya ya bata hakuri ba? Sai ya fara jin Tsoro kada Mimi ta suɓuce masa a karo na biyu in wancan karon ya sha wannan karon ba zai iya sha ba kam.
Sai dai kawai Mu'azzam ya samu wayar Yayan na shi ya na tambayan shi yana ina? Shi kuma lokacin ya na Office ya zo saboda mganar Cases ɗin wani maraya da dangin babansa suka cinye ma gado.
Sai ya ce masa yana Office abun mamaki Ranar da ta zama ranar tarihi ga Mu'azzam kawai sai ji ya yi Aji ya ce ya tura masa adireshi ga shi nan zuwa.
Ko kafin ya kariso ya fito haraban Division ɗin na su ya na jiran shi,.Yana sanye da kakinsa ya fito a matsayin SP M.G ƊANJUMA, wato Mu'azzam Gaddafi Ɗanjuma.
Bakin nan yaƙi rufuwa karon farko da Mansoor zai kawo masa ziyara wajen aikinsa,.Sannan a karon farko za su haɗu da kaki a jikinsa.
Sun kuma haɗu, Mansoor sai da ya ji wani iri ganin ƙanin nasa cikin uniform Rumgume shi ya yi kamar ya samu karin girma zuwa DPO tsabar murna da zumuɗi.
Sai ga Mansoor a kayattacen Office din ƙanin nasa gwanin burgewa.
Ba wani takarce bayan wajen zama sai daga can haka wasu kananun kujeru.
A kwai hotunan gwamma garin sai na Sarki a saman teburin Mu'azzam kuma akwai hoton Junior sai a gefe hoton Mansoor ne da kayan kwallo a jikinsa ya yi ɗan mirmishin gefen baki.
Mansoor sai da kwallah ya tarun masa a ido, ya yi saurin basarwa, Mu'azzam ya rasa ina zai saka shi ya ji daɗi, nan da nan ya saka aka haɗo masa shayi ya na kuma rawan jikin tambayansa abin da zai ci kawai sai ya yi mirmishi kafin ya ce" Ka natsu, ai yanzu na zo ni da zan ƙarisa har gida in sha Allahu."
Mu'azzam ya ji kamar an yi masa bushara da gidan aljannah jiki na rawa ya kira Hibba ya gayamata suna da babban bako a tanadi abinci bai gayamata ko waye ba amman yanayin murnan shi ya sa ta san baƙon mai muhimmanci ne.
Ba su zauma ba sai da su ka yi sallar azahar Kowa kuma sai Mu'azzam ya nuna shi ya ce Yayansa ne daman ko da ya ƙariso mutanen da zai gani ba su kariso ba sai da Mansoor ɗin ya jira suka gama ya sallame su sannan suka natsu yaya da ƙaninsa domin tattaunawa.
"Allah ya sa dai kun gama mgana da Anty Mamin?
Aji ya yi shuru kafin ya ce"Ban ganta ba, bata nan wai ta je Umra?
Mu'azzam ya zaro ido kafin ya ce"Umra? Topha? Ikon Allah."
Shi kan shi lamarin ya ba shi mamaki kafin ya ce" To kuma ba ku yi mgana a waya ba?
Aji ya girgiza kansa kafin ya ce"Na gaya ba na samun wayarta kwata kwata.".
"To me take so ne?
"Ƙure ni take son ta yi mana? Kuma kamar ta yi nasara, Mu'azzam na fara jin tasoro, ina jin wani tsoro na shiga na tsoron da ban taɓa jin irin sa ba"
Ya faɗa cikin karyewan sauti, daga alamu kuma abin da ya ke faɗa daga karkashin ransa ne ganin yadda ya yi laushi lokaci ɗaya. Bai ma Mu'azzam damar mgana ba ya cigaba da faɗin.
"Mu'azzam kana tunanin Mimi za ta dawo mu cigaba da zama? Ko kana tunanin abin da ta faɗa da gaske ne?
Mu'azzam ya ji tausayin Yayan nashi cikin kwantar da murya ya ce"A'a ni fa ina ganin akwai abin da kake yi mata ne ba ta so, in za ku zauna ku samu daidaitu za ta dawo in sha Allahu."
Aji ya dafe kansa lokaci ɗaya yana faɗin" To ta ƙi ba ni damar haka? Allah ba zan mata faɗa ba zan saurareta wannan karon, sannan ina ji a zuciyata zan iya mata abin da ta ke so, mganar gida kuma sai in da take so za ta zauna na janye duka sharuɗda na a kan ta."
Ya faɗa lokaci ɗaya yana tagumi kafin ya cigaba da faɗin "Mu'azzam na taɓa ga ya maka ina son Mimi? Na taɓa ga ya maka itace rayuwata?
Ya faɗa yana mai kallon ɗan uwan na shi Mu'azzam ya yi ajiyar zuciya kafin ya ce" Na san kana sonta mana amman abin da ban gane ba me ya sa bayan ka same ta ka kasa nuna mata wanman son? Me ya sa kuma ka ga ya mata ba ka sonta?
"Ba ni da wani dalili Sai na jin hauahin abin da ya faru a baya. Sannan Allah ni fa ba gaskiya na faɗa ba, kawai dai na faɗa saboda ta ji haushi, kuma ita ta ja na faɗi haka saboda ita ta riƙa ja na da maganganu."
Haka ya faɗa yana rike fuskarsa yana sakin huci Saboda tsoro ne ya shigesa tsoron rasa Mimi a wannan karon. Har ga Allah tabon dake zuciyarsa ya fara raguwa ga shi har ya zo Office ɗin kaninsa ya zauna suna mgana kai, ka ba ma zuciyarka aminci ma wani salama ne zama cikin kunci ba shi da amfani. Yau ɗin ranar sakin duk abin da ke damunsa ne haka ya riƙa yi ma Mu'azzan zan tuka na fita hayyaci da nadama.
Sai Kawai Mu'azzam ya ce"Ina da shawara me zai hana in ka koma ka nemi Babanta Alhaji Hamza? Tsohon Sanata tunda shine Waliyinta?
Aji ya yi shuru kafin ya ce"Da na ce ba zan je ba, amman yanzu ai ba ni da zaɓi. Zan je in sha Allahu da zaran na koma."
Sun ɗan tattauna Mu'azzam na kara gaya masa in ya je ya kwantar da kai tunda sulhu ya ke so, Bayan nan suka gangaro kan mganar gida Mu'azzam na faɗin Bintu ta gaya mai Inna wulakanci take kwasa tun bayan dawowar Matar Saddiqu bangarenta.
Aji ya yi ƙaramin tsaki kafin ya ce"Ka san Allah na kusa ɗauke Inna daga gidan, kawai dai ba na so Baba ya ga na nuna masa shi ya gaza ne."
Mu'azzam ya yi saurin cewa" Ni ma na yi wannan tunanin. Tunda Dai Magajiya ta fi ƙarfin Baba ba ya iya tsawarta mata, Inna kuma kasan halinta ko dukanta za su yi ba za ta taɓa mgana ba."
Mansoor ya koma ya jingina da Kujeren da ya ke zaune kafin ya ce" Kar dai a yi wani abin da zai ɓata min rai, zan ɗauke Inna gaskiya a wannan gidan."
Mu'azzam ya ce"Ko Yaya Amina abin da ta ce kenan gidan duk ba daɗi."
Sun cigaba da tattaunawa har kan batun su Walida Mu'azzam ya ce hakan ya yi dai dai, Aji yac e da zaran ya koma zai nemi Auwalu kan mganar ita Mariya.
Nan su ka shantake sai bayan oa'asar sannan suka ɗumguma zuwa gidan Mu'azzam d ke BUK old site. Sai dai Hibba ta ga Yaya Mansoor kamar daga sama itama bakinta kamar zai yage, faɗi take yi" Lalle muna da babba baƙo, sannu da zuwa Yaya Mansoor"
Ya amsa mata cikin sakewa abincin da ta yi sun fi kala huɗ nan suka baje suka ci suka sha suna ta hira kamar kada su rabu, Mu'azzam ya kira Inna ya sanar da ita ga shi ga Baban Inna itama kanta ta yi mamaki ta ce ya kyauta.
Sun ɗauka ma ko kwana zai yi ya ce ba zai kwana ba. Sanin halin shi ya sa Mu'azzam bai matsa masa ba wajen shidda da rabi ya kai shi tasha ya hau mota sai da suka tashi ya dawo gida tafiyar dare suka yi sai wajen sha biyu ya iso Gombe, bai je gidansa ba a Camp ya kwana kuma evening Traning suke dashi shi ya sa tun bayan sallar asuba ya kwanta barci ya kwashe shi. Bai ta shi ba sai da ya ji ana ta kiran wayar sa yana tashi ya Duba sai ga inna ta kira shi Bintu ma haka.
Sai ya bi bayan kiran yana duba Lokaci goma saura na safe,
Wayar Inna ta na ƙara ba'a ɗauka ba, yana cikin neman Bintu sai ga kiranta sai ya ɗauƙa da sauti gabansa na faɗuwa yana tunanin ba lafiya.
Kuka ya ji ta na yi masa, da sauri ya miƙe ya na laluban rigarsa.
Cikin fargaba ya ce"Bintu me ya faru ne?
"Faɗa ake yi a gida saboda Matar Saddiqu ta dagi junior har sai da ta ture shi ya fasa goshi, shi ne shi ne Walida ta yi magana Meesha ta ja ta da faɗa suka kama Kokuwa sai ta faɗi, Saddiqu na zuwa kawai ya rufe Walida da duka Inna ta zo ta hana ya tureta har sai da hannunta ya goce."
Bintu ta faɗa ta na shesshekan kuka, Aji ya ji wani abu ya taso masa a ƙasan zuciyarsa. cikin maimaitawa ya ce"Ta goce? Ita Inna ce ya gotar don uban shi? Lalle ne ma."
Haka kawai ya ce ya kashe wayar daman ya saka riga kawai sai ya zura takalmi ya ɗauki key ɗin mota tabbas yau Saddiqu zai fahimci yana cin darajan mai daraja ne amman tunda har tura ta kai bango yau za'a buga final ɗin.
*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3005*
*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*
https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC
No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.
Cikin girmamawa suka gaisa da Hajiya, Ita kuma ta amsa masa cikin sakewa kamar wani abu ma bai faru ba. Har ta na masa irin zolayan da ta saba yi masa, tunda har ga Allah ba ta san da zuwan sa ba tunda Binta ba ta kira ta ba.
Kallon sa ta yi kansa na duke lokaci ɗaya tana faɗin" Ka makara da zuwa biko, Binta ba ta na nan shekaran jiya can ta tafi can Abuja wajen Murja. Hala ba ku yi waya ba ne?
Kansa na kass a cikin zuciyarsa ya maimaita" Abuja?
Lalle ne ma Mimi ta maida shi wani sakarai ya ga alama akwai kasawa ma ya ce ma Hajiya sun yi magana a waya shi ya sa kawai sai ya ce mata ya kira wayar ta bai same ta ba.
Hajiya ta muskuta kafin ta ce"Ai ko ba ta nan, amman tunda biko ka zo kuma ta karfe ta gudu, me zai hana ni mu daidaita? Ta fada cikin Sigar zolaya yar dariya ya yi yana shafa kansa kafin ya ce" Haka za'a yi Hajiya."
Shuru na wani lokaci, Hajiya ce ma take ɗan Jansa da hira tana tambayan shi aiki da mutanen gida.
Ya amsa mata da duk suna lafiya kai tsaye ta ce" Ka gaida min da Meri dakyau dakyau."
Ya amsa da In sha Allahu, ko ruwan da aka kawo masa bai sha ba ya yi ma Hajiya Sallama da cewa zai koma.
"To ko za ka ƙarisa gidan Babanta Hamza ne. Daman yana neman ka."
Hajiya ta ce tana kallonsa lokacin da ya miƙe shi kuma ba ya son wata doguwar mgana sai kawai yace mata Toh, amman shi ya san ba zai je ba wato ya kai kansa kenan tunda daman ana jiran shi.
Kuɗi ya ijiye ma Hajiya a nan ƙasa ta saka hannu ta ɗauka tana faɗin" Ai shike nan kana bikon dani tunda ka fara toshi, Na gode kwarai Allah ya ƙara ma rayuwa albarka."
Ya amsa mata da Amin Amin sannan ya yi mata sallama ya bar falon ta bi shi da kallo, Binta ta cika taurin kai sai da ta hana ta tafiyar nan amman ta haɗa ta da ubanta ya ce a ƙyaleta ta je ta gaida mahaifyarta ga shi megidanta ya zo ba ta nan, Baaba Uwani Hajiya ta kira ta Umarce ta da ta Dauko mata Wayarta a cikin ɗakinta.
Bayan ta kawo mata sai ta ce ta kira mata Binta tunda Baaba Uwani ta iya karatun Hausa ita ta nemo lambar Mimi ta kira ta sqnnan ta miƙa ma Hajiya tana ɗauka ta fara faɗin" Hajiya ta, kin yi kewata ne?
Hajiya ta ce" Kin san cewa yanzu mijin ki ya bar gidan nan yana neman ki?
Sai Mimi ta gyara kwanciyarta kafin ta ce"