Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
zai sake ni ai ban ce maka ya sake ni ba. Wanda yake ma tunanin zai sake ni to ya daina bayan sallah zan koma gidan Mijina."
Tana gama faɗin haka ta wuce fuu,Sai ya bita ya na ƙara kiran sunanta kawai sai ta juyo a fusace cikin tsawa tana faɗin" Don Allah ka kyaleni, wannan bala'in da me ya yi kama! Kai ba ka ga abin da ka ja min ba ne? In ba so kake yi ka kashemin aure ba ka fitar mana daga gida"
Cikin mamakin kalamanta Jaheed ya nuna kansa yana faɗin" Ni yau kike kora daga gidan nan Mimi?.
Kai tsaye ta ce"Eh In dai alheri zai kawo ka ba. Ni ce kuma na gaya maka ina da aure kaai na bibitayata Allah ya baka wata wacce ta fini."
Daga haka ta yi wucewarta ta bar sa nan tsaye baki buɗe Baba Uwani ne ke ta jinjina kai, Hajiya kuma sai ta koma ta zauna ta yi shuru ba ta yi mgana ba. Jaheed ya kaɗa kai kamar ya yi kwallah kafin ya juya yana faɗin" Sai da safe Hajiya.". Ba ta ma amsa masa ba, Baaba Uwani ce ke ce masa bai ko ci wani abu ba ya tsaya mana ya sha ruwa anan ko sauraranta bai yi ba ya fice daga falon da sauri.
Baaba Uwani ta kalli Hajiya kafin ta ce"Hajiya ba ki tsaida shi ba?
Hajiya ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce" ƙyale shi kawai."
Baaba Uwani ta yi shuru kafin ta ce" Shike nan Hajiya" daga haka ta wuce ta shiga Kitchen ita dai har ga Allah tana tausayin jaheed sannan ya fi mijin Binta fara'a da son mutane, kuma ga na gida ai gwara na gida da wani bare.
Hajiya ta haɗo ma kayan shan ruwa ga abincin da a ka shiryama Aji nan a kamalle waje ɗaya, Mimi kuma na cikin ɗakinta ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta kira wayar Aji kamar ba gobe amman bai ɗaga ba.
Gajiya ta yi ta hakura ta koma ta zauna Gefen gado kamar ta yi kuka, kanta ta dafe lokaci ɗaya tana fitar da huci daga bakinta.
Wannan wani irin kishi ne. Wannan kishin na Aji ya na bata tsoro kada ya zame mata wata matsala anan gaba, tunanin kiran Mu'azzan ta yi, Sai ta ga ya na nesa ba amfanin kiran shi. Har Nasir ta yi tunanin kira sai ta fasa. Sai daga baya tunanin kiran wayar Inna Meri ya faɗo mata amman kuma ta na jin Kunya tun bayan barowanta gidan ba ta ƙara kiranta ba sai yanzu ta kira ta ce ta na neman ɗanta. Abun da kunya kamar ta fasa amman kuma ta kasa hakura ta riƙa Allah yasa wayar tana hannun Walida Allah kuma ya amshi addu'arta, tana kiran wayar Inna Walida ta ɗauka ita kuma damab wayar na hannunta, pokacin da ta ga Binta ta ɗauka Bintu ne ba ta ma tsayawa dubawa ba ta ɗauka sai ta ji muryan Mimi tana faɗin" Walida ce?
Sai walida ta sake ɗago wayar tana ganin mai Kiran sai kawai ta daga tsalle tana faɗin" Anty Mimi".
Ta faɗa cikin tsananin murna. Daman wayar na hannunta a cikin ɗakinta tana faman latse latse.
"Walida Yayanki na gida?
Haka kawai Mimi ta faɗa.Sai walida ta ce"Anya? Ba ya nan me ya faru?
Sai kawai Mimi ta ce"Bakomai ki gaida Inna." Sai kawai ta katse kiran, abin ya ba ma Walida mamaki ta bi wayar da kallo, to kuma me ya faru? har ta shi ta yi ta fita falo ta iske Inna na zaune daga kallo ta fara gyangyaɗi haraban gidan ta leka ta ga motar ba sai mashin tabbacin Yaya Mansoor ba ya gidan kenan sai kawai ta koma ɗakinta, Ita da Junoir wanda tun ɗazu daman ya yi barci amman sai da ta kashe tibin dake ta yi shi kaɗai, domin Inna na zaune sai faman gyangyaɗi take yi.
*****
Mimi na jin cewa Aji baya gida tunaninta ya ba ta yana Camp ɗin su, duk da ba ta taɓa zuwa ba amman tasan wajen yana cikin gari ne. Sai kawai ta ɗauki mayafi ta yafa ta zura wani saukakƙun takalma ta fita falo ta iske Hajiya na shan kayan marmari ita da Baba Uwani ba ta ma tsaya ta kansu ba ta faɗa Kitchen, ta kwashe abincin da ta yi ma Aji ta zuba acikin kwando mai zif ta zage sannan ta fito falon a gaggauce tana faɗin" Hajiya zan je na dawo."
Cikin mamaki Hajiya ta ce" Ina kuma za ki Binta? dare fa ya yi kuma kin yi Azumi amman komai ba ki ci ba."
Kawai wucewa ta yi tana faɗin" Hajiya sai na dawo zan iya cin wani abu."
Kafin ma Hajiyar ta sake wata mgana ta fita, Sai da ta fita ta tuna ba ta ɗauko Key ɗin Mota ba sai ta dawo da gudu gudu ta koma ɗaki ta ɗauko Key ɗin motar ta fice ta na jin Hajiya na faɗin"Binta dare fa ya yi"
Ita dai ta fice tana faɗin" Hajiya ba zan daɗe ba. In sha Allahu"
Ko ba ta faɗa ba tunda Hajiya ta ga ta kwashi abinci ta san in da za ta je. Sai kawai ta kaɗa kai ta cigaba da shan kankanarta, Duk Binta ta jaa ma kanta da ba ta baro ɗakinta ta zo gida ba da duk haka bai faru ba, Baaba Uwani ko mgana ce a bakinta amman yadda Hajiya ta kame fuskarta ya sa ta kasa furta wani abu.
Megadi ma ya yi mamakin fitar Binta da daddare abin da ba ta yi, duk tsiya ana mangariba take dawowa gida. Amman yau bayan mangariba wajen takwas saura ta shiga mota ta fita sai dai ya bi ta da fatan dawowa Lafiya, ita kuma tana tuki amman hankalinta na kan wayarta tana ƙara kiran lambar Aji anman bai ɗauka ba. Kusan ɓacen hanya ta yi ma sai da ta sake komawa tunda ta manta wajen daga karshe sai da ta tsaya a bakin hanya ta yi tambaya sannan a ka yi mata kwatance kai tsaye sai ga ta a bakin get ɗin Gombe United Camp. Akwai Security masu kula da shiga da fita domin tana zuwa sai suka hana ta shiga tun da ba su taɓa ganinta ba.
Sun tambayeta wa take nema?
"Mansoor Aji.."
Kai tsaye Mimi ta faɗi sunansa. Security ɗin guda biyu ne suna sanye da uniform da kuma manyan fitilu suna haske motar Mimi da ita kanta tunda kamar cikin Camp ɗin ya yi duhu ba wuta.
Dukkansu suka kalli juna kafin bahaushen ciki ya kalli Mimi lokaci ɗaya yana faɗin" Captain kike nufi?.
Sai ta gyaɗa musu kai lokaci ɗaya tana faɗin" Yana ciki ko?
Sai ya ce"Eh bai daɗe da shiga ba, amman ya san da zuwan ki?
Sai Mimi ta girgiza kanta lokaci ɗaya tana ɗaukan wayanta a hannunta.
"Bai sani ba, ina ta kiran shi bai ɗauka ba."
Tana faɗa tana rubuta masa saƙo.
"Ina bakin get ɗin Camp ɗinku.."
Haka kawai ta rubuta masa. Dai dai lokacin taji wani cikinsu na faɗin" Bari mu kira wayar ɗakin sa, wa za'a ce masa? Tun da akwai telephones a cikin Camp wajen guda uku da na reception da na ɗakin Aji da na meeting room ɗin su.
"Mimi.."
Sunanta ta faɗa musu. Sai ta jira a cikin mota ta na ji suna mgana a Telephone amman ba ta jin me su ke faɗa ba.Ta ga dai ɗaya daga cikinsu ya zo ta gefen tagar motarta dake ke buɗe yana faɗin" Ki shiga ciki Hajiya.".
Sai ta amsa masa da kai dai dai lokacin dayan ya buɗe mata get ɗin ta shiga ciki saboda ba ta san yanayin wajen ba sai ta rasa ina za ta yi fakin. Dole ta tsaya a bakin ginin wajen da aka sake rubuta GOMBE UNITED CAMP. Ta Fara waige waige kenan kamar suna jiranta sai kawai a ka kawo wuta wajen ya gauraye da haske, sai kawai ta fito daga cikin motar da wayarta a hannunta sai dai wajen tsit sai kukan tsuntsuye haka ta rika juya ido tana bin cikin wajen da kallo. Kai wajen fa ya haɗu dole Aji ya riƙa zuwa nan domin za ka ssmu cikakken natsuwa.
Ba ta san daga ina ya fito ba kamar dai Kila ta bayanta ne ta ji dai mgana kawai a saman kanta.
"Me ya sa kika zo nan?
Da sauri ta juya yana tsaye daga bayanta yana sanye da riga da wando saukakku, fuskar nan tasa a haɗe kamar bai taɓa dariya ba, tana ganinsa ta sauke Ajiyar zuciya sai kawai ta buɗe mota ta ɗauko kwandon abincin lokaci ɗaya tana faɗin" Ga abin da na kawo maka."
Ta faɗa tana ƙarisawa gabanshi. Juyawa ya yi kawai ya fara tafiya yana mai faɗin" Me yasa ba ki ba ma saurayin na ki ya cinye ba?
Ba ta yi fushi ba haka ta bi bayan shi da sauri tana faɗin" Aji mana. ka Saurare ni ne mana, Yayana ne fa"
Bai juyo ba ya ce" Yayanki guda ɗaya na sani. Dr Sulaiman bayan shi ban san kina da wani Yaya ba."
"Cousin Brother ɗina ne. Jaheed ne Son ɗin Daddy."
Cak ya tsaya. Har ta kusa cin masa kafa fuskarta ta daki bayansa yana juyowa ya ga
ga kwandon hannunta na neman faɗuwa da sauri ya saka hannu ya karɓa lokaci ɗaya yana faɗin "Oh muharraminki ne da zai riƙa taɓa jikin da ni kaɗai ne nake da ikon taɓa shi? Ko kuma ya dace ki tsaya da shi ba mayafi a jikin ki duka suran ki ya bayyana wanda ni kaɗai ne shari'a ta ba ni damar ganin ki a haka. Wato shi kin yarda ya ganki a haka ya kuma taɓa jikin ki ni kuma da shari'a ta ba ni wannan damar ba ki taɓa yarda wani abu ya shiga tsakanin mu ba ko? Me ki ka mai da kan ki ne Fatima? So kike yi ki kasheni lokaci nq bai yi ba ko? Kin san yadda zuciya take yin kuna? Kin san cewa hoton ku ya kasa ɓacewa daga tunanina? To in ma ya na tunanin zan rabu dake ne ya aura to ki gaya masa ya farka daga wannan nafarkin nasa domin ba zai taɓa zama gaskiya ba, ke ko mutuwa na yi ki ka sake aure Allah ya isa ban yafe ba."
Haka ya faɗa cikin fusata Idanuwansa sun kada sun yi jajir, Mimi ta zaro ido tana kallon shi jin mamakin kalamansa a ina yasan cewa Jaheed na sonta.? Kuma wai Allah yas a ko bayan ransa in ta ƙara aure.
Ba ta samun zarafin mgana ba ya kuma juya kawai ya fara tafiya zuwa wajen motar ta lokaci ɗaya yana faɗin"Ki koma gida dare ya yi"
Tura baki ta yi kafin ta ce"Ni a'a sai ka ce ka haƙura." Banza da ita ya yi har suka karisa wajen motar ta ya buɗe baya y sakaa mata kwandon abincin lokaci ɗaya yana faɗin" "Ba na son gaddama, ki shiga mota."
Yadda ya yi mganar ya sa ta san ba wasa Idanuwanta suka tara kwallah a sanyaye ta ce"Ka yi hakuri ba abin da kake tunani ba ne.' Wani kallo ya yi mata da yasa ta buɗe bangaren direba ta shiga ta zauna kafin ta kalle shi a marairaice tana faɗin" To ka yi hakuri ka ɗauki abincin"
Kansa ya kauda da sauri kamar za ta yi kuka ta ce"Ni na girka fa da kaina don Allh kada ka ce a'a ka ji."
Sai ya ɗan kalleta da sauri ta ƙara shagwabewa kafin tac e"Don Allah na ce fa"
Tana gani ya sauke numfashi sannan ya buɗe bayan motar ya ɗauko kwandon abincin dai dai karisowam wani matashi ya na tafiya ne da alama dai ya fito shan iska ne sai Aji ya kira sunan shi.
Da sauri ya ƙariso Cikin ladabi yana faɗin" Barka da dare Captain"
Kwandon kawai ya mika masa lokaci ɗaya yana faɗin" Ka saka min a cikin ɗakina."
Da sauri ya amsa amman yana leƙen Mimi a mota akwai haskem wuta ya gane ta tabbas Matar Captain ce ma'aikaciyar gidan tibi ya na tafe yana faman waige ya ƙosa ya je ya kai sakon ya shiga group chart ɗin su ya kai ma su Zinder labarin yau matar Captain ta kawo masa ziyara a cikin Camp. Shi ko sai da ya ga kabiru da suke ma laƙabi da pele ya wuce sannan ya zagaya ta bangaren Mimi kai tsaye ya ce"Fito.."
Ba musu ta fito, shi kuma ya shiga mazaunin direba ya zauna lokaci ɗaya yana faɗin" Sai na ce ki zagaya ki zauna?
Da gudu Mimi ta zagaya tana mirmishi ta shiga bangaren mai zaman banza ta zauna
"Seat belt"
Da Sauri ta saka nata, shi daman ya zura na shi sannan ya ta da motar tunda daman key din na jiki. Tun da ta fahimci gida zai kaita ta ke ta faman mirmishi a sannu sannu har zuwa bakin get shi ya leka ya yi mgana da Security suna ganin shi ne suka buɗe mishi get suka fita suma suna gulmar kila madam ɗinsa ce domin tunda suka fara aiki a wannan wajen ba su taɓa ganin mace ta zo wajensa ba sai dai maza, suna tafe a hanya amman ba wanda ya yi ma wani mgana Mimi ce ta ga kamar ya na fushi da ita har lokacin ta kara narke murya tana ba shi hakiri kanzil bai ce mata ba har ya kai ta gida har cikin haraban gidan sai da ya yi parking Sannan suka fito a tare.
Key ɗin motar ya mika mata ookaci ɗaya ya na faɗin" Kada ki ƙara cewa za ki tuka mota da daddare, in kika haɗu da miyagu fa?
Kanta na kasa ta ce" To ba kai ba ne ka tafi kaba fushi da ni ba"
Kamar za ta yi kuka. Kallonta ya yi kafin ya tura mata key din motarta ta saka hannu ta karba sannan ya juya kawai ya wuce ta bi shi da kallo, da sauri ta bi shi tana faɗin" Kana da kuɗi a hannunka ne?
Juyowa ya yi ya kalleta kafin ya nuna mata hqnnu cikin kaushinsa yana faɗin" Ki koma ciki gida Fatima."
Yadda ya yi mganar ya sa dole ta juya tana tafiya a sannu har falon Hajiya amman sai da ta laɓe tana lekensa su ka yi mgana da Megadi sannan ya fita ya bar gidan.
Sannan ta sauke ajiyar zuciya tana juyowa ta ga Hajiya zaune taba gyanyadi ta kuma san zaman jiranta take yi. Sai ta yi mirmishi sannan ta ƙarisa wajenta tana tashinta Hajiya ta farka sai ta ga Mimi da sauri ta ce"Binta kin dawo?
Sai ta riƙe Hannun Hajiya ta miƙar da ita tsaye lokaci ɗaya tana faɗin" Na dawo Hajiya, ki kwantar da Hankali Aji ne ya dawo da ni gida."
Hajiya ta jinjina kai ba ta yi mgana ba. Sai Mimi ta riketa har zuwa cikin ɗakinta ta kwantar da ita kan gado Hajiya na faɗin, ki samu wani abi ki ci Binta kin yi azumi ba ki ci komai ba."
Sai ta amsa mata. Nan ta bar Hajiya ta koma ɗakinta ta cire kaya ta yi wanka da sallar Isha'i sannan ta fita falo zuwa Kitchen ta diɓo abinci da kayan marmari Baaba Uwani ta jima da shiga ciki, sai da ta gama cika cikinta ta sha zobon da ta yi sannan ta koma ɗaki ta ɗauki waya ta kira Aji amnan bai ɗauka ba, so take ta ji ya koma gida lafiya?
Sai ta kyale shi gajiya ne a jikinta saboda ta wahala yau ga azumi ga aiki, amman ɗazun nan ba ta ma jin yunwar. Sai yanzu da ta kwanta gajiyan ya taso mata, har ta fara barci ta ji karan wayanta tana dubawa ta ga Aji ne da sauri ta ɗaga kiran na shi tana tambayansa ya ya koma gida? Ya amsa mata a dakune lokacin fa ya gama cin abincin da ta yi masa ne farar shinkafa da miyar naman rago da cowslow, sai zoɓo da kunu, daman bai ci komai ba amman kishi ya hana shi ya nemi wani abu da ba ta kawo masa ba haka zai kwana kuma ya tashi da azumi. Haka dai su ka yi wayar yana ta wani cin mgani ta na dai bashi hakuri. Shi bai ce ya haƙura ba shi kuma bai ce bai haƙura ba, Karshe ma barci ne ya kama idanuwanta ya sa ta yi masa sallama tace za ta kwanta, da asuba ma wayarsa ne ya tashe ta ya ce ta tashi ta yi Sahur ita kuma sai da za ta tafi wajen aiki ta kira shi yana barci sai bayan ta je wajen aiki ya kira ta daga jin muryansa ma ta san yana barci ne sai suka gaisa sama samma sannan suka yi sallama har a lokacin dai bai gama Hucewa ba sai bayan wajen kwana huɗu sannan ya warware ya daina fushi fushi. Amman da ta ce ta ƙara gayyatansa shan ruwa cewaa ya yi ba zai zo ba kada ya ƙara zuwa ya ga ta gayyato saurayinta.
Sai ta riƙe baki kafin ta ce"Ba ka hakura ba kenan? Kuma ni ai ba ni na gayyace sa ba."
Banza ya yi mata. Sanda suke mganar ya kaita ne kasuwa ta amso ɗinkunan hijabanta a ranar ta ba shi Atm ɗin sa ya kalleta kafin ya ce"Kin gama komai? Domin kika sake na karɓa in ma da wani abin sai dai ki siya da kuɗin ki"
Tana jin haka ta yi saurin maida shi jaka tana na faɗin" Ban cire na gyaran jiki ba."
Taɓe baki ya yi bai yi mgana ba, da ta ga kamar ya ƙara shaƙa sai ta ce"Ka zo gobe don Allah zan jira ka."
"Ba zan zo ba."
Haka ya ce kuma yanayin mganarsa ya sa ta san da gaske yake yi sai ta kyale shi.
Da ta gaya ma Rukky itama sai da ta ce Jaheed bai kyauta ba amman ta ba shi hakuri