Idan An Ciza Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   17 / 49

48K to 51K   out of 146.6K words

yi mishi daɗi ba haka ya duka yana ba ma Inna da Walida haƙuri, Baba Sani ya juya ya na kallon Mansoor dake tsaye har lokacin hannunsa goye a bayansa yana cije leɓensa na ƙasa Ya ce"Kai kuma tsayuwar me kake yi, ka zo ka lallashi ita Merin ta koma ɗaki lamarin bai yi daɗi ba sai hakuri."

"Akwai wanda na ke jira ne."

  Amsar da Mansor ya bashi kenan a kausashe kafin kuma ya kalli Walida kukan ta ma ɓata masa rai ya ke tsawa ya daka mata kafin ya ce"Ki yi min shuru anan wajen," haka ya faɗa yana kokarin saisaita fushinsa a lokacin ji yake yi kamar ya mutu sai wajen ya yi shuru har mai kukan ƙaryan ta natsu Bintu ya kallah daga baya yana faɗin"Bintu kama Inna ku koma ɗaki."
Yana gama faɗin haka dai dai da shigowar Saddiqu da sauri yana faɗin" Magajiya ki kamota ga mai adaidaitan na samo."
Gadan gadan kawai ya nufo bangaren shi kuma Mansoor daman shi yake jira Kawai sai suka haɗe. Ya saka hannu ya ture Saddiqu sai da ya kusa faɗuwa kasa ya dago cikin mamaki domin ya ga waye ya yi masa haka kawai Mansoor ya daddage iya karfinsa ya tsinke Saddiqu da lafiyayyan marin da sai da ya ga hasken taurari, bai gama dawowa hayyacinsa ba ya ƙara masa wani, da sai da ya faɗi kasa ya bi shi ya saka hannu ya damƙo ƙwalan rigan shi ya ɗago shi sannan ya ƙara masa wani marin mai shiga jiki sannan lokaci ɗaya ya ture shi da ƙarfin da sai da ya faɗi kasa. Kowa sai ya buɗe baki yana kallon ikon Allah Baba Ɗanjuma kuwa saboda jin daɗi da karfi ya ce"Na gode maka mansoor, kayi masa dukan tsiya."

   Harira ma ta ji daɗin hukuncin Gaje dai ba wanda ya gane yanayin ta, Baba Sani da Baba Danlami sai faman subhanallahi suke faɗi kawai domin Saddiqu ya maru lokaci ɗaya har shacin hannu ya bayyana a dama da haunin fuskarsa sannan jini na bin hancinsa kenan haɓo ya yi. Zuwaira ta kira sunan Mansoor cikin tsawa tana faɗin kada ya kara taɓa mata kaninta Auwalu na gefe ya ce"Wlh ya yi min dai dai gwara ya kara masa tunda ba shi da mutumci."
Bintu ko kamar an sakata a Ajannah har Walida mai kuka ta ji daɗi, yau kam Inna na zaune amman ba ta hana ba. Lalle tura ta kai vango magajiya kuma tsaabar ruɗewa ba ta san ma ta saki mai ciki ba tana mamakin wai Agola ne ya kama ɗanta da duka ita kuma Maeesha ba ta san ma ta tsaya da kafafunta ba jikinta ba inda bai rawa ganin Mijin nata da take taƙama da shi a gabanta ya maru, to ita fa? Tuni ta manta da an dake ta a ciki ta mike ga jikinta tana wani fiƙi fiƙi da idanuwa.

  Saddiqu kuma cikin ɓorin kunya ya lakato jinin dake saman hancinsa ya gani. Sai kawai ya taso yana faɗun" Ni ka mara. Wallahi sai na rama." Ya nufi Mansoor gadan gadan sai Auwalu ya riƙe shi amman yana fizge fizge kamar zai iya wani abun, Mansoor ya kalle shi cikin fushi kafin ya nuna shi da yatsa lokaci ɗaya yana faɗin" Mari na farko na Junior ne, mari na biyu na Walida ne mari na uku saboda Inna ne. Kai har ka isa uwar tamu kake son ka kashe mana?. Wallahi ka ci darajan Baba da yau sai ka raina kanka banza kawai sakarai wanda ba namiji ba."
Ya gama faɗa lokaci ɗaya har yana hambari sa shi da kafafunsa shi kuma Saddiqu tana hakilon nanza.

   Juyawa mansoor ya yi ya isa ga Inna ya saka hannu ya ta da ta tsaye lokaci ɗaya yana faɗin" Ki yi hakuri Inna komai yau ya zo karshe." Bintu ya kallah kafin ya ce"Ɗauko ma Inna hijabi ta saka, ke ma ki shirya Walida ta ɗauko mayafinta mu je mota ki riko hannun Junior."
Ya faɗa Lokaci ɗaya yana rumgume Inna ta gefren kafaɗanshi da sauri ko Bintu ta shiga ɗaki ta ɗauko masa hijabin Inna ya taimaka ya saka mata, Inna hawayenta sun ƙi tsayawa abin da ya faru yau ya ba ta tsoro matuka da mamaki. Walida ma ta sako hijabinta ita da Bintu, Inna Mero kuma Mansoor ya saka mata takalmi da kansa sannan ya Juya yana kallon Baba lokaci ɗaya yana faɗin" Baba ka yi hakuri amman Inna ba za ta cigaba da zama a gidan nan ba tunda har oamarin ya kai ga duka bamu san abib da zai faru a gaba ba kuma, kada ka ji a ranka kamar ka gaza kawai dai ba zan iya hakurin na barta ba ne gwara ta bar gidan sai waɗanda basu san zamanta a gidan su haɗa da ɗakinta suyi ta zama zauna."
Baba Ɗanjuma ya jinjina kai kafin ya ce"Bakomai Mansoor, nima a yau ina goyan bayan ka, Mahaifiyarka ce kana da Ikon kare martabanta tunda ni na kasa, ku je duk inda ta koma ni a matsayina na mijinta zan bita ko'ina ne."

  Sai a lokacin Magajiya ta samu bakin mgana sai ga ta, ta yi wani tsalle ta sha gaban Mansoor da Inna Meri lokaci ɗaya tana faɗin"Ina za ka?. Wallahi baka isa ka dokar min ɗa kuma ka juya ka yi tafiyarka kamar ba abin da ya faru ba. Ba ka isa ba domin ban taɓa ganin inda Agola ya daki ɗan ma su gida ba, Ko ka ɗauke ta daga baya kenan bayan kun gama zama kun gama more komai, nan gidan dai shi ya yi muku komai dangin uban naka me suka tsinana maka?  tunda ka shigo rayuwarmu kai da mahaifiyarka kuka rugumin gidana a da ina zaune da gani sai ƴa'yana da mijina amman zuwan wannan matan da zuwan wannan Agolan gidan nan komai ya sauya. Yanzu Danjuma ya fi fifita Agola sama da ƴayansa, in ba lalacewa ba a gaban idon ka a ɗaki ɗanka amman ka kasa mgana sai ma munawa da ka yi abin da aka yi dai dai ne to ni wallahi ban yarda ba sai an bi ma ɗana haƙƙinsa"

  Take faɗa tana wani hura hanci, Mansoor ya yi niyar zagayeta su wuce ne amman Inna ta hana ta kalli Magajiya na wani lokaci kafin ta yi mirmishi ta ce" Kin ce wai dangin ubansa me suka yi masa ko? Ai ko sun yi masa komai tunda dai tun zuwan Baban Inna gidan nan abin naira biyar baki taɓa taimakon shi da shi ba kin ga baki da ikon faɗi wata mgana ba. Sannan na daɗe ina hakurin duk irin cin kashin da kike yi min a cikin gidan ki yi ta aibatana ɗana kina kiran shi da Agola Allah Sarki da ace Ibrahim ya yi tswon rai Magajiya na rantse ga Allah kila har ki koma ga Ubangiji ba za ki  haɗu da ni ba. Ba zan zo aure a wannan gidan har na zo da Baban Inna ba mutuwa ce ta yi ma shigar sauri ita ce ta maida shi mara uba amman ba Agolan da kake tunani ba, ni  ce nan na matsa sai na taho da shi saboda ba na son ya yi nesa dani amman ke kam shaida ce ba domin dangin Babansa sun gaza da ga riƙon sa ba. Na zauna da kowa bisa amana a wannan gidan ban taɓa tunanin cutar da kowa ba, ban sani ba ko tun zamana na taɓa yi miki wani abu na ɓacin rai da ya sa kika tsane ni. To yau ta kare ki yi hakuri ki yafe min Magajiya, Allah ya baki hakuri in dai laifina auran Mallam da kuma riƙon Yayan da ya bani to duk kiyi hakuri rayuwar nan duka duka nawa take? Wata rana ba ni ko ba ki a duniya nan? Ko kuma ba Mallam ko mu rasa wasu daga cikin yaran mu duka sanin gaibu sai Allah ki yafe min Allah ya kaddara saduwa."

  Inna Meri ta gama faɗa tana mai fashewa da kuka sai jikin Magajiya ya yi sanyi duka masifanta ta kasa magana, Inna Meri na kuka ta kalli su Gaje tana faɗin" Saboda zama da rayuwa in na taɓa saɓa muku ku yafe min, ni dai wlh ban taɓa rike kowa a cikin ku ba na yafe muku duniya da lahira, Sani da Ɗanlami ku ma ku yafe min ƙila zama na tare da ku na yi muku wani abu ni dai ba ku min komai ba wlh, ina rokon ku da yafe min saboda rayuwa."
Tana magana tana kuka  Gaje da Harira jikinsu duk a sanyaye su ka ce wlh ba ta yi musu komai ba ita ce ma suka yi ma laifi ta yafe musu ta ce bakomai su baba Sani sun kasa mgana Ɗanlami ne ya ce su kam ba ta yi musu komai ba.
Magajiya na ji da gani Mansoor na rike da inna Meri su k fice daga gidan su Gaje suka raka su har da Baba Danjuma aka bar mata gidan gabaɗaya amman kuma ta kasa farinciki Har Auwalu da shi a masu rakiya,  tuni makota sun fara taruwa,  su Gaje ke faɗin Inna Meri ne za ta bar gidan sai ga shi an fara cika wajen tuni Dije matan Mallam Hashimu ta garzayo, ta lna kuka tana faɗin Ina Inna za ta tafi ta barta Inna ta ce ba inda za ta je, amman ta san duk in da Baban Imna zai kaita in da za ta samu natsuwa ne amman ba auranta ba ne ya mutu gidan ne kawai ta fahimci alheri ne ta bar shi.

  Shi amfanin zama da mutane lafiya yana da kyau haka makota ke ta sharan hawayen barin Inna anguwar nan saboda kyawawan hallayanta wasu har suna faɗin ita ce Alherin gidan wanzamai wasu kuma su ka ce tunda Innar Mu'azzam ta bar gidan nan Sun daina shiga gidan daman saboda ita ce mace mai kirki da karamci mai zumunci duk abin da ya faru in dai ta ji sai ta je abun kaico kaico da abun Allah ya sanya alheri ga hannun kyauta ga son mutane da mutumci hatta da su Gaje sun koka wlh, Baba Danjuma duk jikinsa ya yi sanyi amman shima gwara haka ita kuma Magajiya ga ta ga gidan sai ta zauna.

  A gaban mota Inna ta zauna su Walida har da Mariya da tana kuka ta ce za ta bi su ta ga in da za su koma suka shiga baya, Sai Baba Danjuma ya ja mansoor gefe yana tambayan shi in da zai kai Inna?. Kai tsaye ya ce" Gidana za ta koma Baba."  Cikin mamaki ya ce"Gidan ka? To kai fa?
Mirmishi ya yi kafin ya ce" Kada ka damu Baba, zan iya siyan wani gidan ko na gina wani, Allah ya rubuta daman gidan zai zama na Inna nw wata rana.".
Sai kawai Baba ya dafa kanshi yana ta saka masa albarka. Makota kuma ma su jajen tafiyar Inna ta ce duk su yi hakuri in har ta ga in da suka koma za ta sa Bintu ta zo ta gaya musu sai su zo su ga in da take amman zumunci ba zai yanke ba.
Haka aka yi dafifi wajen motar Mansoor suna  ɗagama  makota hannu suma suna ɗaga musu, hatta su Baba Sani sun kasa motsi kamarin ya girgiza su, Magajiya na cikin gida ta kasa fitowa domin ta rasa me ke mata daɗi, Zuwaira na fadin daman ya san yana da in da za kai uwar tasa ya barta anan ta ce ma magajiya ai gida ya zama naki yanzu, Saddiqu kuma sai kumfar bakin sai ya ɗauko ma Mansoor yan daba sun yi masa dukan tsiya yake yi   Matarsa kuwa ta ja jikinta ɗaki ba ma wanda ya ƙara ganinta tuni aka manta da dukan ciki ballantana maganar zuwa asibiti.

  Magajiya ɗaki ta shige, tana zaune Zuwaira da Saddiqu suna mganganu amman ba ta sauraransu ita kaɗai ta san hqlin da Zuciyarta ta ke ciki. Kamar ta ɗora hannu ta rusa ihu. Ga shi dai Meri ta bar mata gidan amman ta kasa farinciki sannan ji irin yadda Mutane suka taru suna kukan tafiyarta wai har da su Gaje, sannan ita me ya sa ta kasa farinciki? Ina za ta koma? Ko dai gidan shi zai kaita? Ta na hasaso wanman katon gidan domin lokacin da aka gama ginin Danjuma ya matsa sai da su ka je gidan suka saka albarka, in dai Meri ta koma wannan gidan ai ta ci gaba ita kuma ta bar ta a gidan gado? Kamar ta saka kuka haka take ji Kallon Zuwaira ta yi Idanuwanta sun kala sun jajir kafin ta ce"ina Mariya?
Saddiqu ya ce"Kila ma ta bisu, tunda daman ba ta da kishi, duk irin su Auwalu ne." Sai Magajiya  ta yi  tagumi domin ta rasa kuma wani nazari za ta yi. Ga shi dai gida ya zama sai ita kaɗai amman kuma ba ta jin farinciki saboda tunanin in da Meri za ta koma ya fi in da ta ke sau ɗari da saba'in keman ita ta ci gaba ita kuma ta na nan a waje ɗaya.
Duk mganganun da su Zuwaira ke yi ko ɗaya ba ta ji ba, ta yi nisa cikin tunanin makomar rayuwarta a wannan gidan ga shi dai burinta ya cika gida ya zama nata amman kuma a kasan ranta ta kasa farinciki.

*****

Bangaren su Inna Meri kuwa daga nan ƙofar gidan Wanzamai sai gidan Mansoor, dake anguwan Tunfere, Ya nan a yadda yake kamar sabo tunda ba zama aka yi a gidan ba shi ne kuma regular ne wata rana ma ya na cinye satin shi a Camp.
Bintu ya ba ma Key din gidan ta buɗe shi kuma ya riko Inna Meri har tsakiyar falon gidan da ba komai sai katon tibi da cafet, Inma sai kallon gidan take yi, Bintu da Walida kamar za su suma saboda daɗi.
Gidan akwai kura saboda ba mutane a ciki amman komai sabo ne. Sannan gidan 4Bedroom ne, Sai daga waje haraban parking in da mashin ɗinsa take sai ɗakin megadi da wani ɗaki daga waje sai Fulaowin da ya shuka suka ƙarama gidan kyau a ciki akwai katon Kitchen sannan kowani ɗaki akwai Tiolet a ciki daman a cikin ɗaya yake zaune ɗaya kuma ya saka kayan motsa jiki. Sai ya ce ɗayan su share ma Inna ɗayan kuma Walida ta zauna a ciki kafin ya san in da zai kai kayan shi.
Su kam ai suna can suna faman zagaya gidab suna murna daman sau ɗaya suka zo gidan tun bayan an gama shi tun lokaci suke  santin gidan. Mariya ma ji ta ke yi kamar ta dawo nan itama su zauna tare da Walida.

  Inna Meri na tsaye ta kasa zama idanuwanta sun ciko da hqwaye, Mansoor ya zo ya riƙe ta yana faɗin"Inna ki zauna mana, an juma za'a kawo sabbin kujeru da sauram kayan amfani in sha Allahu."
Inna kamar ta yi kuka ta ce"Baban Inna wamnan gidan ya yi mana girma da haya ka kama min"
Cikin Mamaki ya ce"Haya kuma Inna? Wani irin haya kuma?  Ina da gida kuma sai ace mahaifiyata sai na ne man mata haya?
Inna na rike hannunsa ta ce" Kai fa? Ina Binta za ta zauna in  ta dawo?.
Mirmishi ya yi mata sannan ya kamata ta zauna saman Cafet shi kuma ya zauna a gabanta yana faɗin" Inna ina da kuɗin da zan iya siyama Mimi wani gidan ta zauna ko na gina mata wani, amman daga yau wannan gidan ya zama naki halas malak Inna."
Inna Meri ta fashe da kuka tana faɗin" Allah Sarki haihuwa mai rana Na gode kwarai Allah ya yi maka albarka, don Allah Baban Inna zan roƙe ka wata alfarma."
Ta faɗa tana riko Hannuwansa duka biyun da sauri ya ce"Faɗi koma menene ni kuma Zan yi miki  shi in har bai gagareni ba."
Inna na hawaye ta ce"Kukan farimciki nake yi Baban Inma ba na baƙin ciki ba. domin haihuwa ta min rana Ubangiji ya gama min komai. Ni kamin komai wlh na gode amman ina so kaima  na ga ka samu Farinciki Don allah ka manta komai ka je ku daidaita da matarka ka dawo da ita ku zauna domin kaima ka samu farinciki ka tara zuru'an da za ka yi alfahari da su sannan ka samu rayuwa mai inganci Baban Inna"

  Inna ta gama faɗa tana hawaye  Sai Mansoor ya share mata hawaye kafin ya ce"Ina sha Allahu Inna, ba saboda mganarki ba ni da kaina nake son na dawo da Mimi in sha Allahu."
Haka Inna ta ji daɗi ta rika saka masa albarka tana hawaye.
Su Bintu ya kira yac e ta bishi su je gida su kwaso kayan sawan su, Inna na zaune ta ce" Har da ma sauran kayan amfanin ai ba sai an siya wasu ba."
Shi kuma ya ce a'a ta bar musu gidan da abib da ke ciki kayan sawan su kawai sai abin da suke so za su ɗauko Inna ba ta da abin cewa sai fatan alheri kawai.

  Daman kuma tuni Bintu ta kira su Yaya Amina ta gaya musu abin da ya faru mamaki ya kama su suka ce ga su nan zuwa, Da Bintu kaɗai a ka koma can gidan ita ta haɗo duka kayan sawan su Inna da duk abib da za su bukata har da kayan amfanin gida su mopper da botikai da sauran su sannan ta saka key ta kulle ɗakin, daidai sai ga Yaya Halima daman sun yi waya ta ce tana gidan ta zo ɗaukan kaya gidan shuru ba motsin kowa kamar ba nutane. Bayan mota sai da ya cika da kaya da booth, sai Yaya Halima ta bi Mansoor ita kuma Bintu ta hau adaidata suka isa can gidan Yaya Halima ta samu Inna na ta sharan kwallah ta fara mgana sai ta ce ke ni kukan daɗi nake yi Halima sai dariya kuma gabadayan su nan da nan suka mike suka fara gyaran gidan ba daɗewa sai ga Yaya Amina ma ta ƙariso.
Mansoor kuma ya ce bari ya je ya dawo Junior na ta murna ya ga irin gidansu na Kano.

  Tun da mansoor

17 / 49