Idan An Ciza Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   37 / 49

108K to 111K   out of 146.6K words

take kiranta.

  Inna Meri ta kalli Mimi da ta farka ta janyen bargo daga jikinta saboda zazzabin ya sauka zafi ma take ji, cikin tausayawa Inna ta ce" Sannu Binta ya jikin?
Mimi kamar mai ciwon baki ta amsa ma Inna da sauƙi, Walida ma ta karisa kusa da ita ta zauna lokaci ɗaya ta na faɗin"Anty Mimi Allah ya baki Lafiya.".
Ta amsa da Amin idanuwanta sun tasa abun ka ga farar fata duk fuskarta ta bayyana halin da take ciki.
Walida Inna Meri ta kallah kafin ta ce"ki je kicthen na saka mata ruwan zafi ki sake ki kai mata bayi ta samu ta yi wanka ko jikin nata zai saki."
Daman abin da Mimi take bukata kenan wanka, da sauri ko Walida ta mike ga aikin da Inna ta sakata. Sai falon ya yi shuru Inna sai ta maida hankalinta kan laziminta amman tana ganin Bintar na share ƙwalla, tausayinta ya kamata wai har yaushe ne Baban Inna zai bar rayuwar ƴar mutane ta zauna cikin salama ne? Ta san wlh tsiyar shi ce amman bari Bintar ta natsa ta ji abin d kuma ya sake aikatawa wannan karon.

  Bayan Walida ta kai mata ruwan zafi saboda jikinta ba karfi, ta mike Walida ta riketa hannun da a ka yi mata karin ruwa har ya kumbura da walida ta taɓa wajen sai da Mimi ta yi wash, cikin sauri walida ta saki hannu kafin ta ce"Sannu ƙarin ruwa a ka yi miki?
Mimi ta gyaɗa kanta kafin ta ce"Daga wajen aiki ne na fara ciwom sai Rukayya ta kaini asibiti can na yini aka sakamin ruwa da Allurai." Inna Meri da Walida suka haɗa baki wajen faɗin Allah ya ƙara lafiya.

  Cikin kayan Walida. Walidar ta zaɓo mata wata doguwar riga, da yake daman rigar ta mata yawa ta kuma san za ta yi ma Mimin,Ai ko ta ji daɗin gasa jikinta sosai sannan ta ɗauro alwala salla tun ta asuba rabon ta da yi, rigar ta saka ta yi mata sai dai tsawon ne ya yi mata kaɗan sai ta ce Walida ta bata zani ta ɗora saman rigar ta yi salla kuma Alhamudulillah a tsaye ta yi sallar tunda ta samu sauƙi tana idarwa Walida ta kawo mata Tea mai ƙauri da buredi ta sha, sai ta fara dawowa daidai, bayan tea ta  dafa mata Indomie da ƙwai taci ta yi kat sannan ta sha ruwa, ba ta da alwala ya sa ta koma Tiolet ta yi alwala ta zo ta yi sallar Isha'i ta sha mganinta sannan Walida ta gyara mata gado ta hau ta kwanta, Inna Meri ta zo ta dubata ganin har ta kwanta ya sa ta kyaleta ta huta zuwa da safe.

  Walida ce ta kasa hakuri ta koma falo tana faɗin" Inna wai anan Anty Mimi za ta kwana? Inna ta amsa mata da eh, cikin ƙarim mamaki ta ce"To ko Yaya Mansoor ya yi tafiya ne?
Inna ta kalleta kafin ta ce"Ban sani ba, ba na son tambaye tambaye mara amfani, ki je ki kwanta ki kula da ita tunda ba ta da lafiya." Ganin Inna ta haɗe rai ya sa Walida ta kama bakinta ta yi shuru, ta yi ma Inna sai da safe ta koma ɗakin ta shimfiɗa bargo a kasan cafet ta yi shirin kwanciya sannan ta kwanta ta ɗauki wayarta tana danne danne. Ba su farka ba sai asuba Mimi ta ji daɗin barcin nan ta kuma ta shi kamar ba ita ba. Bayan sun idar da sallah Walida ta fita gyaran gida tunda da wuri take fita, Mimi ba ta san wayarta ta mutu ba sai da ta ɗauko domin kiran Rukayya ta gaya mata ta cike mata takarda za ta ɗauki hutu ba ta da lafiya sai ta samu wayar a kashe, da chazar Walida ta saka chaji sannan ta koma ta zauna a wajen har ta ɗan farfaɗo ta kunna wayar ta na gama saituwa sannan saƙo ya shigo wayar daga Aji tana gani ko dubawa ba ta yi ba, tana shirin kiran Rukky sai ga kiran jaheed ta san yana ta neman lambarta bai samu ba.

  Ta ɗauka a sanyaye suka gaisa ya ce ya jikinta ta ce masa ta ji sauƙi. Kai tsaye ya ce"Ina fatan ba matsala? Kai tsaye itama ta ce"Da Sauki dai, za mu yi mgana daga baya." Da ga haka suka yi sallama bayan ya ce ta kira Rukky tana ta neman wayarta itama a kashe.
Suna gama waya Rukkyn ta kira nan take gaya mata Bibi ta haihu aiki a ka yi mata ta samu mace suma asibiti, Mimi ta yi mata Allah ya raya sannan ta ce in ta shiga ma'aikata ta rubuta mata takarda sai ta ce mata eh za ta je. Daman Manaja ya san ba ta jin daɗi amman za ta je ta yi rubutun ta ba da, ko alama Mimi ba ta nuna ma Rukayya wani abu ba itama ba ta sani ba tunda Jahedd ya rike alƙwari bai faɗa ma kowa ba .

  Tana gama abunda za ta yi da wayar ta sannan ta kashe wayar ta maida ta chaji, ta na shirin komawa ta kwanta Inna Meri ta shigo cikin ɗakin sanye da hijabin da ta yi salla. Mimi na ganin ta da sauri ta duka ta na gaisheta Inna Meri ta zauna gefen gado lokaci ɗaya tana faɗin" Tashi ki zauna Binta ke da ba ki da lafiya? Sannu ya karfin jikin na ki? Ta amsa mata da sauƙi kanta na ƙasa, Inna Meri ta yi mata fatan Allah ya kawo afuwa, shuru na wani lokaci sannan Inna Meri ta gyara zama lokaci ɗaya tana kiran sunan Mimin.

"Fatima.."

Mimi ta ɗago tana kallon Inna Meri bayan itama ta daidaita zaman ta a nan gefen gadon na Walida ta amsa mata cikin ƙanƙantar da kai.

"Kin ɗauke ni a matsayin uwa Ko Fatima?
Mimi ta gyaɗa kanta sannan Inna Meri ta cigaba da faɗin"Na kuma ga haka, tunda ki ka zo wajena ba tare da kin tafi ga Hajiya ko Mahaifiyarki ba  na ji daɗi da kika mutumtani Binta, ki faɗamin abin da ya faru kika zo gidan nan cikin wani yanayi kuma har kika kwana ban ga megidan ki ya zo bin bayan ki ba? Me ya faru? Ki faɗa min kada ki ɓoyemin komai domin Allah Fatima."

  Inna Meri ta ƙarishe faɗa tana kallonta Mimi kuma sai ta ji idanuwanta sun cika kwallah, ta kasa mgana jikinta har ya fara rawa Da sauri Inna ta matsa kusa da ita ta na mai dafa kafaɗanta kafin ta ce"Kada ki damu ni uwace, mai jin damuwar ƴaƴanta ta kuma taya su addu'a ko kuma in tana da hanyar mangancewa ta yi musu mganin damuwarsu, ki sanar da ni abin da ke faruwa nayi miki alƙwarin yi ma duk abin da ya faru adalci in sha Allahu."
Mimi sai kawai ta fashe da kuka har da shessheƙa Inna kuma na faman lallashinta da kalamai ma su sanyaya zuciya lokaci ɗaya tana bubbuga kafaɗan ta da hannayenta.

  Sai da Mimi ta samu natsuwa sannan ta iya warware ma Inna Meri abin da ya faru, wannan karon ba za ta iya rufa masa asiri tun da har ya saka zargi a zaman auran su, ta karishe da faɗin" Inna abu ɗaya ya fi min zafi yadda Mansoor ya kasa shaidata ya ce tabbaci gare shi ina cin amanarsa da ɗan'uwana, ya saka zargi a cikin ransa kinga kenan ya na so ya ɓata auran mu, sannan da bakinsa ya ce na fitar masa daga gida na koma in da na fito daga yawon iskancin nawa." Ta faɗa ta na kuka da karfi saboda yadda in ta tuna abun ta ke jin kamar bakin ciki zai kasheta.

  Inna Meri ranta ya yi mummunan ɓaci ba ta san lokacin da ta ja wani dogon salati ba" Innalillahi wa'inna alaihirraju'un na shiga uku ni Meri, a she Baban Inna dabba ne jaki ne kuma ni ban sani ba? Haka ta faɗa saboda ranta ya ɓaci ta rasa ma wani suna za ta kira Baban Inna da shi.
Cikin harzuƙa ta cigaba da faɗin"Sakarai ne ashe mara tunani ya na abu kamar jahili wanda bai je makaranta ba? Da kansa zai lalata auran shi? da kansa zai kalle ki ya ce ya na zargin ki? Ashe shi jaki ne ban sani ba.? Inna Meri ta ƙarishe faɗa itama baƙin cikin duniya ya ishe ta.
Me ya sa Mansoor ba shi da hankali ne ba ya tunani in zai aikata abu? Shi ya sa ta sha faɗa masa in dan an ciza a hura saboda gudun nadama wata rana.

Kafaɗan Mimi ta dafa lokaci ɗaya tana faɗin" Ki yi hakuri don Allah Binta ki daina kuka, na kuma gode ma Allah da kika yi tunanin zuwa wajena, ni kuma zan ɗauki matakin da ya dace kuma sai ya raina kansa zan saita masa tunani tunda na lira shi ɗin dabba ne mara hankali ai ko Mu'azzamu da yake ƙaninsa wlh ba zai yi abin da ya yi ba. Shashasha kawai ki yi kwanciyarki kada ki sake ki ɗaga wayarsa balle ki faɗa masa kina nan barsa zai zo da kafarsa tunda yana zargin ki kenan ba amfanin zaman ku tare sai ya zo ya sake ki ya auri wacce zai riƙa saka ta a riga yana yawo."

  Dole Mimi ta yi shuru ganin Inna Meri ta fita ɗaukan zafi amman ba ta bar ɗakin ba sai da ta tattabar da Mimin ta daina kuka ta kuma share hawayenta sannan ta koma ɗakin ta  sai faɗa take yi ita kaɗai wannan karon sai ta ci ma Baban Inna mutumci tunda ba shi da tunani. Walida ta gama gyaran gida sannan ta yi musu abin karyawa itama ta karya sannan ta yi wanka ta ta fi wajen koyon ɗinkinta, Mimi kuma sai da ta yi wanka sannan ta karya ta sha mgani ta kwanta Inna kuma na zaune a falo tana jiran ta ga idon mara mutumcin.

******

*MANSOOR*

Barcin kirki ma bai samu ba. Shi ya sa har ya na makara sallar asuba sai dai a gida ya yi ta shi, ga yunwa yana ji amman ya kasa ma kansa wani ƙokari har kuma da wayewar garin yana ta kiran wayar Mimi a kashe shi ya sa karfe bakwai ya bar gidan zuwa Camp sun yi morning traning bayan sun gama Daga nan ko gida bai je ba ya tafi gidan hajiya. Sai dai daga yanayin tarban da kuma zolayan Hajiya ya san Mimi ba ta zo ba domin Har Hajiya sai da ta ce"Yau kai kaɗai ka zo kenan? Ina ga ka zo dai mu sansanta ne shi ya sa ka baro ta a gida."
Daga nan ya san Mimi ba ta zo ba sai kawai ya fake da ya zo gaida Hajiya ne  ya ijiye mata kuɗi bai daɗe ba ya bar gida.

  Yana fitowa daga gidan ya kira Mommy a waya itama dai suna gaisawa ya ji ta ce" Ya wajen Mimi? Fatan duk kuna lafiya? Daga nan ya tsuke bakin shi suka gaisa ya katse wayarsa shine har Dr. Sulaiman ya kira shima ɗin dai ba wani bayani alamun dai Mimi ba ta je can ba, sai kawai ya saka ma ransa tana gidan su Rukayya daman ya san gidan sai ya kaɗa kan mota sai gidan su Rukayya, ya iske ba ta a gida sai ƙanwarsu karama ita ke gaya masa Anty Bibi ce ta haihun Mama na wajenta a sibiti Anty Baby kuma ta dawo amman ta shirya ta tafi wajen aiki. Sai a lokacin ya tuna ya ga kiran Makama jiya da daddare bai ɗauka ba kuma bai bi baya ba, kenan haihuwar matarsa yake son gaya masa.

  Daga gidansu Ruƙayya ma'aikatansu na Karamchi Tv ya wuce, Rukky na can ma bangaren su Mimi ne suna mgana da Manaja, a ka ce tana da baƙo a waje ta yi mamakin ganin Aji,sai da gabanta ya faɗi ta ɗauka wani abun ne ya faru da ƙawar ta ta.
Cikin ruɗewa ta ƙarisa gabansa cikin ruɗewa take faɗin" Me ya samu Mimin? Ko dai jikin ne ya tashi, na shiga uku ni Ruƙayya"
Haka ta faɗa tana dafe ƙirjinta  Cikin mamaki Aji ya kalleta kafin ya ce"Ban gane ba. Daman ba ta da lafiya ne?
"Ba ka sani ba?
Itama Rukky ta maida masa martanin tambayansa cikin mamaki.

  Sai ya ji kunya ta kamashi cikin wani yanayi yacce"Rukayya me ya faru? Don Allah ki gaya min ina Mimin ta je jiya?
Rukayya cikin mamaki ta ce"Jiya ta zo wajen aiki ba ta da lafiya na kira wayarka baka ɗauka ban Sai na kira Jaheed ya zo ya kaimu asibiti a ka yi mata allurai da karin ruwa bayan an sallamo ta, za mu kai ta gida na samu waya cewa Bibi na asibiti. Sai na bar Jaheed ya kai ta gida ni kuma na wuce asibiti, ban gane duk ba ka san abin da ya faru ba?
Yana kallon Rukayya cikin wani yanayi ya ce" Ina Fatiman take yanzu?
Rukky fa ta fara tunanin akwai wani abu cikin karin mamaki ta ce" Ah ikon Allah kai zan tambaya ba tana gidanka ba l? Mun yi waya da ita da safen nan har ta ce min na zo cike mata takarda, za ta zauna a gida na kwana biyu sai ta ƙara warwarewa."
Aji ya yi shuru kawai kamar ruwa ya ci sa, innalillahi kawai ya ke maimaita a cikin ransa. Me ya aikata? wani irin shirme ya tafka? Me ya yi ma kansa ne?
Kawai sai ya juya zai shiga mota da sauri Rukayya ta ce"Mimin ba ta kwana a gida ba ne?Sai kawai ya kaɗa kai kafin yace" Kada ki damu ba matsala."
Daga haka ya koma mota ya kunna ya bar haraban ma'aikatan.

  Rukayya mamaki ya kamata sai kawai ta ɗaga waya ta kira Jaheed tana gaya masa abin da ya faru da kuma tambayan ko wani abu ya faru ne jiya? Bai gaya mata sai kawai ya ce"Ban sani ba, a waje na sauketa jiya nan." Da sauri Rukky tace"An ya? Ina zargin da wani abu. Mimi ba ta kwana a gida ba, Bari na sake kiranta."
Da sauri ya ce" A'a Ruƙayya kyaleta. Shi aure daman ya gaji haka tunda ba ta faɗa miki ba to ba ta son ki sani ne, ki yi musu addu'an Allah ya daidaita su kawai."
Shi ya hana Rukky sake kiran Mimi amman abun ya dameta tana tunanin me ne ya faru haka,? Jaheed kuma bai ba ta damar da za ta gane ya san wani abu ba, yana  ma faɗa mata Jirgin karfe uku zai bi zuwa lagos su haɗu a asibitin da a ka yi ma ƙanwarta aiki su yi sallama.

  Shi kuma Aji daga ma'aikan su Mimi bulayi ya fara yi a gari duk in da ya yi tunanin Mimi na can ba ta je ba, to ta na ina? Ko dai tana gidan Bintu ne? Ya kira wayar Bintu ta ɗauka suka gaisa sai ya ji hayaniya sai yake tambayanta ta na ina ne? Sai ta ce masa tana  gidan su Bashir Hajiyarsa ba lafiya tunda ya ji haka ya san ba ta je bam Bayan Bintu har su Yaya Amina ya kira nan ma shuru suna ta tunanin yau Aji na jin zumunci duk ya kira su sun gaisa bai taɓa kawo tunanin tana wajen Inna ba  ganin ba shi da mafita ne ya sa ya yanke shawaran zuwa gaban Inna ya faɗi ya gaya mata duk abin da ya aikata ta taimake shi kada ya rasa Mimi in ya rasa ta ya shiga uku.
Yana tafe a Mota kamar mara lafiya duk ya faɗa saboda bai ci komai ba tun jiya da rana.

  A kofar gida ya bar motar, ya shiga gidan shima yana layi kamar zai faɗi, a tsakar gida ya ga Inna ta na shanya zogalanta ya yi sallama ta amsa masa a ciki ko kallonsa ba ta yi ba, tun bayan kallo ɗayan da ta yi masa bayan ya shigo ba ta kara ba.

"Ina kwana Inna.."

  Haka ya faɗa yana kokarin zama kan damdalin ƙofar ɗakin,  kamar ba ta jisa ba haka ta yi masa banza sai ya ƙara gaisheta sai ya ga kamar ma ba ta san yana wajen ba  Da ace ba ta amsa sallar masa ba sai ya ce ba ta san da zuwan sa ba, amman ta amsa kuma ta kallesa, tabbas wani abu na faruwa, Kafin ma ya samu bakin ƙara mgana ya ga Inna Meri ta wuce su zuwa cikin falon ta barsa nan kamar ma ba ta  gansa ba, baki sake ya bi ta da kallo kafin a ranshi ya ce" Me kuma na yi?
Ko dai Mimin nan ta zo?  tuna haka ya sa dai gabansa ya faɗi da sauri ya tashi ya bi Inna cikin falon lokaci ɗaya yana faɗin" Inna wai baki..."

  Sauran mganar ta sa ta maƙale ne a fatar bakinsa, ganin Mimi zaune a saman kujeran falon inna, sun kuma haɗa ido ta ganshi ya ganta, kafin ma ya samu zarafin mgana Inna Meri da ta fito daga kitchen ta kalleta lokaci ɗaya tana faɗin" Binta shiga ciki."
Ba musu Mimi ta mike tana tafiya a sannu sannu ta shige ɗakin Walida ta rufo kofa.
Amman an ce tsakanin miji da mata sai Allah sai ta tsaya jikin kofar kawai har ga Allah ta ji tausayinsa ganin rana ɗaya duk ya faɗa, jikinta a sanyaye ta karisa gefen gado ta zauna ta yi tagumi.
Inna Meri kuma Mimi na shiga ciki ta koma saman kujera ta zauna har t na jawo Radionta tana kunnawa kamar ma ba ta san da wanzuwarsa a falon ba.

  Ƙafafunsa suka yi sanyin da suka kasa ɗaukansa ba shi da mafita  Inna ba za ta saurareshi ba. Gwara ya bi ta hanyar Mimin kila ya samu ragowa tunda ta na son sh. Salau salau haka ya wuce zai nufi hanyar ɗakin da Mimi ta shiga. Cikin mamakin rashin kunyar sa Inna ta bi sa da kallo,gani ta yi zai shiga tana zaune bai ji kunya ba.
Sai kawai ta juya tana faɗin" Kai.."
Haka ta faɗa sai ya juyo yana kallon Inna cikin rashin madafa

  Inna ta nuna masa hannu kafin ta

37 / 49