Idan An Ciza Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   5 / 49

12K to 15K   out of 146.6K words

sai ya ce gaskiya daman wannan auran na Mimi sai a hankali.

  Jaheed ya fi kowa murna da faruwar haka, Tun bayan auran Mimi yake cikin garari, sai dai kule kulen ƴanmatan zamanin nan da ba ka raba Mazan zamani da shi, bai san Yaddiko ba ta sani ba sai da ya kirata ya gaisheta kawai ya faɗa mata saboda ya san tana goyon bayansa ko a baya aiko nan da nan ta ce ba ta sani ba amman anjuma za ta leka gidan Hajiyan ta ga abin da ke faruwa, Lamarin ya daure mata kai, ita fa ba ta son ta ga mace da ƙuruciyarta tana bin ɗakuna in ya zama jiki bshike nan duk in da ta yi aure ba za ta zauna ba.
Da daddare ta saka ƴaron makotan su ya kawo ta gidan Hajiya, Ta kuma gasgata abin da Jaheed ɗin ya faɗa mata tunda ta ga Mimi a gida sannan da ta yi mganar ba'asi Domin sai ta nuna Kamar ba ta san abin da ke faruwa ba.

  Nan Hajiya ta yi mata bayani da zuwan Daddy jiya da maganar da ya yanke a kan Mimi ɗin, Yaddiko ta gyara zama lokaci ɗaya ta na faɗin" Haba Hajiya me ya sa za ku biye mata? Tun farko sai dai a ka nuna mata ga Ɗan'uwanta ta dage sai abin da take so an kuma yi auran nan amman kawai sai ta kamo kafa ta dawo ta ce ta hakura da zaman aure? Haba dai Hajiya ai ya kamata ku ma ku zauna ku yi tunani kar ta maida mi kananun mutane mana"
Hajiya ta kalleta kafin ta ce" To yanzu tunda mu ba mu iya ba, ya kike son ayi?
Kai tsaye Ta ce" A kira shi mijin nata Yaya ya zauna da shi sai a ji shima ta bakinsa."
Hajiya ta gyaɗa kai kafin ta ce"To kuma har yanzu bai zo kuma bai kira waya ba, shi kuma Hamza ya ce ba wanda zai neme shi."
Sai Yaddiko ta yi shuru ta kasa mgana Hajiya ta cigaba da faɗin" Ba na nufin Auran Binta ya ƙare har ga Allah Yaddiko.  Amman mu ba su lokaci mu gani ina ji a jikina ko ba yanzu ba nan gaba kaɗan za su daidaita in sha Allahu."
Yaddiko dai ba ta kara mgana ba saboda ta ga Kamar wannan karon ma Hajiya tan goyon bayan Bintar ne.

  Kuma ba ta hakura ba da za ta tafi, sai da ta leƙa har ɗakin Hajiya ta na ce ma Mimi" Binta rayuwar nan ta aure duka fa hakuri a ke yi, ke shaida ce irin hakurin da Murja ta yi da Yaya Allah ya jikansa da ba ta yi haƙuri ba,da ba ku ta shi kun ga iyayen ku waje ɗaya ba, kowa ki ka gani a gidan auran shi ya na zaune to karki so ki ji irin haƙurin da yake yi a zamantakewarsa, in ka ji na wani sai ka ce naka nafila ne, auran dai kika na ce kina so kuma a ka bi abin da kike so a ka baki shi sai kawai aure ko shekara bai yi ba sai ki dawo gida ki ce ba za ki koma ba? Kar  fa saboda kin ga ana bin abin a kike so ki riƙa zuwa mana da renin hankali aure ibada ne ba wajen wasa ba."
Har Yaddiko ta gama maganarta Kan Mimi na ƙasa ta kasa mgana sai dai Idanuwanta sun tara ƙwalla ai ba ta da wani ikon kare kanta yanzu shiyasa ta yi shuru.

  Yaddiko na fita ta koma ta kwanta tana kuka, Mommy ma da safe ta kira ta tana yi mata faɗa akan wannan abin da ta yi har ta na cewa ta shirya ta koma gidan Mijinta,  ita kuma ta saka mata kuka cewa ba za ta koma ba ta yi ma Daddy magana kuma shi yace ta zauna. Da Mommyn ta kira Daddy bai saurare ta ba ya ce in ta samu lokaci ta shigo Gombe su tattauna da haka suka rabu da juna, Mommy da kanta ta sanar ma Khadi, ita kuma khadi ta sanar ma da Dr . Sulaiman da Madiha a bakinta suka ji L
labarin abin da ya faru tun daga lokacin suke rige rigen kiran wayarta amman ba ta ɗauka ba, Madiha ma ba ta kira ba cewa ta yi daman ta faɗa ma Mimin ba abun kunya ba ne in ta dawo gida ta nemi Saki, ita kuma Khadi kanun zencen ta ke so ji.
Dr. sulaiman kaɗai ta daga kiransa suka yi magana shima dai bakinsu ɗaya da Mommy in ma wani abu take so ta yi mgana a yi mata amman ta bar mganar kashe auranta gwara ta koma zai fi mata alheri.

  Shima kuka ta saka masa tana faɗin ita ba za ta koma ba. Saboda ai shi Ajin ya san tafiyarta kuma da kanshi ya ce ta tafin, kuma har yanzu bai zo kuma bai kirata ba kenan shima ya gaji da auran nata.  Jin haka yasa bakin Dr  ya mutu amman shima ya ce a cikin ranakun weekend in ya samu lokaci zai zo Gomben.
Shima ya kira Daddy sun yi mgana  ya ɗan dai yi masa bayanin Mimi za ta koma matuƙar Mijinta ya zo biko a ka zauna a ka ji inda suke da ɓaraka a yi gyara amman matukar bai tako ba shi ba zai maida masa Mimi ba tunda ba ƴar sadaka ba ce. Ta nan kuma Dr ya ga gaskiyan Daddy ko ya ya ne a nuna masa Mimin tana da daraja, amman matarka ta biyo dare ta dawo gida amman baka kira ba, sannan ba ka zo ba, sannan ba ma tunanin ko wani abu ya faru da ita bayan fitar ta ba, shima ta wannan bangaren ya ga wawancin mijin na Mimi a haka kuma a fuska kamar mai hankali da Tunani.

  Ita Hajiya sai fakewa take yi da ƙannensa suna kiran ta wayarta ba ta ɗauka Daddy ya ce ƙannensa dabam shi dabam, ba ƙannensa ke auranta ba shi ya ke auranta kenen bai ma san darajanta ba kenan.
Kan kuma maganar kwaso kaya ne domin Maman ta zo a daran ta ce gobe da safe za su je tare da Turai su kwaso kata kayanta da umarnin babanta.
Hajiya ba haka ta so ba, ta so a dakata ba ta san vaggawa amman Daddy ya ce sai an kwaso saboda shi kaɗai ya bar ma kansa Sanin dalilin shi na cewa a kwaso kayan da gaggawa.

  Washegari misalin ƙarfe 10:20am na safiya ranar jumma'a Mama ta isa gidan Wanzamai, ita ta fara yo gaba Hajiya Turai za ta zo da mai motan ɗaukan kaya, Inna Meri na ayyukanta a tsakar gida Mama ta shigo ta gane ta sai ta karɓe ta hannu bibbiyu ta shigarta da ita har cikin ɗakinta ta saka Walida ta kawo mata ruwa, Inna Meri kunya duk ya kamata a tunanin ta ko Maman ba ta san Mimi ta koma gida ba ne, Tana shirin ce mata ai Bintar na gidan Hajiya sai kawai ta ji Mama tana faɗin" Key ɗin ɗakin Mimi nake so don Allah."
Sai Inna Meri ta kasa magana saboda jikinta ya yi sanyi amman sai ta yi yaƙe kawai ta tashi sda kanta ta shiga ciki ta ɗauko daman ita da kanta ta rufe ɗakin ta riƙe key ɗin a hannunta. saboda jatsari ne barin ɗakin a buɗe tunda akwai kayan kudi a ciki.

  Ba tare da ta tambayi ba'asin abin da Mama za ta yi a ɗakin ba ta damka mata makullayen ɗakunan, Ita kuma har ta amsa ta fita daga ɗakin ba ta ƙara cewa komai ba, Ta buɗe dakin ta shiga ciki Inna Meri ba ta taba tunanin za'a kwashe kayan Binta ba ne duk daman ko yau sai da Magajiya ta zo Kofar ɗakin ta ta tsaya ta na faɗin suna bukatar ɗaki domin Matar Saddiqu za ta dawo nan ne cikin gaggawa.
Walida ta same Inna zqune kawai ta yi tagumi, Hibba ta je gidansu Jiya ba ta dawo ba sai ta kwana a can, Junior kuma ya ƙi zaman nan sai gidan Bintu saboda su Husaini.

  "Inna ko dai an zo ɗaukan kayan sawan Anty Mimi ne?

  Walida ta faɗa tana zama kusa da Inna Meri, ita kuma sai ta girgiza kanta kafin ta ce"Ban sani ba, makullin ɗakin kawai ta tambaya."
Ita kanta Walida duk jikinta ya yi sanyi, Uban gayyar kuma tun ranar da suka zo da Nasir ba wanda ya ƙara ganin shi Baba Ɗanjuma har ya yi tunanin su je gidan Sanata Hamza shi da abokinsa Mallam Hashimu su ba da hakuri Inna ta hana ta ce shi wai mai auren bai damu ba sai su ne za su damu kansu? Ai abin da ya nuna ya nuna ma duniya shima hakan ya zaɓa. Cewa ma ta yi in dai ya je ita ba da yawunta ba, Shi ya sa sai ya dakata shi kuma gogan in an neme sa sai ya ce kar kowa ya saka baki yana tutiniyan duk in da Ma Mimin ta je a cewarsa za ta dawo ne ma. Har su Yaya Amina sun so su  zuwa har gidan Hajiya su Samu Mimi su ba ta haƙuri Inna Meri na ji ta ce kar wacce ta taka ta je, ba hurumin su ba ne.

  Su dai suna zaune sai gani suka yi wata mata ta shigo Hajiya Turai, Mama ita ta leƙo ɗakin Inna ta ce a gaya ma matan gidan Maza za su shigo su fita da kaya shike nan ta faru ta kare. Daman Zuwan Mama kayan Sawan Mimi ta gama haɗa mata duka a cikin akwatinta da duka kayan kwalliyarta da takalmanta, Inna ko iya fita ba ta yi sai Walida ne ta je ta gayama magajiya Maza za su shigo ɗaukan kaya. Tana jin haka ta san Dalili a ranta ta ce abin dai ya tabbata kenan Daman itama duk ita da gayama yaƴanta har Maaeesha dake gidan Zuwaira ta je ta kai mata labari sai ta ji daɗi ko banza za ta zama tauraruwa a wannan gidan.
Kuma ta ji daɗi da za ta koma ɗakin Mimi Saboda ya fi jin kayan gyara sannan ya fi kyau komai na fantin ɗakin da abubuwa Uniqui ne masu tsada da yarari.

Walida hankalinta ya ta shi ganin da gaske fa tunda ana ta fita kaya. Sai ta Lallaɓa ta saci wayar Inna Meri ta Kira Bintu ta sanar da ita abunda ke faruwa sai ta ce ga ta nan zuwa ta kuma ƙara kiran Hibba ita sai ta ce ta na kan hanya tunda sun yi waya da Mu'aazzanm tun asuba ya ce ya ta so.
Da Bintu da Hibba a kofar gida suka haɗu suka shigo gidan lokacin har gqdon Mimi an kwance an fita da shi Kujeru ne su kaƙi fita a na tunanin a haura da su ta garu kamar yadda dama suka shigo gidan tun farko.

  Ɗakin Inna suka faɗa cikin wani yanayi Bintu ke faɗin" Inna ke kika ce su zo su kwashe kaya? Inna Meri ta yi shuru ba ta yi mgana ba sai Walida ne ta maida musu abin da ya faru, Bintu ta ɗauko wayarta daga aljihun rigarta ta lalubo lambar Yayan na su ta kira shi amman wayarsa tana kashe ne so take yi ta sanar da shi abin da ke faruwa ƙila in ya ji ya zo ya dakatar da su.
Hibba faɗi take yi" Inna domin Allah ki dakatar da su mana.".
Inna Meri ta miƙe tana faɗin" Saboda wani Dalili Hibbatu? Ba ni da wannan hujjar."
saboda ma kar su dameta fita ta yi ta zuba ruwa a buta ta zagaya ta kama ruwa tana fitowa ta ɗauro alwala ta zo ta shige ciki ta shimfiɗa sallaya ta kabbarta salla.
Ganin ba mafita ya sa Bintu ta ja hannun Hibba suka fita lokaci ɗaya tana faɗin" Mu je mu yi musu mgana. Wlh makiyan gidan nan dariya suke yi mana."
Sun shiga ɗakin sun iske Mama da Turai suna maida wasu kayan Kitchen ɗin a cikin kwalayensu bayan sun gaishe su sai kuma suka kasa mgana har sai da Mama ta ce"Lafiya ko?
Bintu ta marairace kafin ta ce"Don Allah Mama ku yi hakuri da kwashe kayan nan, shi fa Yaya Mansoor bai ce ya saki Anty Mimi ba." Mama ta yi yar dariya tana kallon ƙanwarta Kafin ta ce" N ma yar aikace, umarnin Babanta ne ya ce Lalle lalle yau mu zo mu kwaso mata kayanta."
Turai ta ce"To tunda har ya ce ba ya sonta zaman me za ta yi da shi?
Mama ta ce" Babu kam, abin da yake so ne ta yi masa tunda ta ce za ta tafin ya ce gwara ta tafin."

  Da sauri Hibba ta ce"Sharrin sheɗan ne, sannan faɗan ma'aurata ne, in da an ɗan dakata za su iya sulhunta kansu."
Mama ta sake yin yar dariya kafin ta ce" To wannan kuma ban sani ba, amman ni dai yanzu Umarnin Babanta na ke aiwatarwa."
Duk iya ƙokarinsu amman su Mama ba su saurare shi ba. Daga karshe ma suna mgana sai suka yi musu kunnen uwar shegu.
Dole su ka fita jiki duk a sanyaye sannan sun koma suna ta kiran Mimi ba su sameta ba, abin da suka lura shi ne kamar ta rufe su ne ba za su ƙara samun ta a waya ba.
Suna ji suna gani aka kwashe kayan Mimi gabaɗaya tas kayan abinci kaɗai suka bar musu a kitchen da za su tafi suka ba su makullin ɗakin ba su ko ga Inna Meri ba ta na cikin dakinta.

  Makota ko sun cika ƙofar gida ana maida mgana, wanda ma bai sani ba duk ya san abin da ke faruwa Magajiya na tsakar gidan tana dariyan zuci burinta ya cika.
Mariya ba ta cika zama a nan ba ita ce gidan Zuwaira ko gidan Auwalu, Saboda anan ba za ta sake ta riƙa yin taɗe taɗe yadda ta ga dama ba sannan magajiya na takura mata kuma ba sa shiri da matar Saddiqu.
Sai ga ɗakin da Mimi ta yi rayuwa fayau ba komai a ciki haka su Hibba suka koma ɗakin inna suka yi jugum jugun abin haushi ma ba'a ɗade ba sai ga Saddiqu ya shigo Shashen shi da wani abokinsa ba sallama ba komai suka shige ɗakin suna dubawa baƙin ciki ya sa sai Bintu da ta yi kwallah ta ce ma Hibba bari ta je ta dawo ta fice daga gidan gabaɗaya tana jin magajiya na shewa ita da Gaje daman ai murna za su yi.
Daga nan Binta mashin ta hau zuwa gidan Yaya Amina domin ta sanar da ita halin da ake ciki ya kamata su san matakin da za su ɗauka kafin su zama abun dariya a cikin gida da maƙota.

******

Duka kayan Mimi gidan Daddy a ka sauke su,. Sai dai kayan sawanta ne Mama ta aika mata da su gabadaya gidan Hajiya.
Washegari Asabar Mommy ta biyo jirgi ta zo Gombe, can gidan Daddy ta je ta same shi suka tattauna bai fito ya nuna mata manufar shi ba amman ya ce sai ya nuna ma yaron nan Mimi yar gata ce, in yana sonta zai kawo kansa ya kuma ce kar ma wanda ya takuramata da Maganar komawa tukunna a ƙyaleta sai ta kara samun natsuwa da hutu.

  Dole Momny ta bar mganar shi ya sa ma kwananta ɗaya ta juya, sun yi saɓani ba ta daɗe da tafiya Dr. sulaiman ya zo garin shima, Duka dai bayanan da Daddy ya yi ma Mommy shi ya yi mishi ya ce kuma su taimaka masa wajen dawoma da Mimi darajanta a idon mijinta su cire bakin su su bar shi da shi da Mimin gabaɗaya.
Shima ɗin bai kwana ba a ranar ya bi jirgi ya koma kano amman ya je gidan Hajiya ya gaisheta sannan ya ga Mimi sun yi mgana shi dai ya ce ta kwantar da hankalinta komai zai wuce kamar bai faru ba.
Khadi kuma aiki ya hana ta zuwa amman Kwazzaba yasa sai da Mimi ta amsa wayarta.

  Har tambayan Mimi take yi wai daman ance baƙaƙen maza sun iya rashin mutumci tana so dai Mimi ta buɗe mata cikinta ita kuma sai taƙi, ce mata kawai ta yi i ta ta ce ta na so daga farko yanzu kuma ta ce ta haƙura ba dole sai an matsa mata anji dalilinta ba, itama tana da wayon ta san kowa na rufe siirin shi ita ba za ta bar na ta a buße ba, ko da ta zaɓi rabuwa da Aji har yau har gobe zuciyarta ba ta daina son shi ba. Kawai dai ta zaɓar ma kanta barin rayuwarsa ne saboda ƙimar iyayenta, Sannan kuma yana da hallaya masa kyau ɗin da ba za ta iya zama da shi ba, to wanda bai da kyakyawan zuciya ai zama da shi hadari ne. Mutumin da ba ya ganin ka da kai da Iyayenka a wata tsiya ai ba amfanin zama da shi.

  Madiha kam da suka yi waya ce mata ta yi" Zan yi supporting ɗin ki karo na farko Sisto, In bai sake ki ta arziƙi ba to za mu maka shi a Kotu alkali ya karɓan miki yancin ki, kin fi sa komai shi ne zai yi asaran rasaaki, ke kuma sai dai ki samubwanda ya ninka sa. daman abin da Abi ya guda kenan tun farko amman at last dai Hajiya da Mommy sun kasa ganewa ke ma wawanci ya rufe miki Ido, amman kar ki damu ba ki makara ba abin da kuma kika yi kin yi dai dai i support your Decession."

  Mimi dai ba ta ce mata komai ba. Daman ai madiha kowa yasan irin kalamanta kenan, ta kuma san za ta fi kowa jin daɗin abin da ya faru, amman ko da ita ba ta yarda ta furta mata wata mgana ba.
Ita yanzu wa za ta zauna ta faɗa ma tun auran su ko hannunta sai bisa kuskure Aji ya taɓa kamawa? Sai maganar ta kara girma sai daga baya ma ta fahinci kamar ba ya sha'awarta ne tunda ba ya sonta amman ko ita ta san tana

5 / 49