Idan An Ciza Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   43 / 49

126K to 129K   out of 146.6K words

Naguda ita ai sai dai ta yi ma Allah godiya domin ta samu ciki cikin sauki ba ta yi wahalan laulayi ba sannan wajen haihuwa ma Ubangiji ya saukaƙa mata, in a ka cire ƙarin da ta samu suka yi mata ɗinki sannan ba ta yi doguwar naguda ba, ko da yake Inna Zainaba tace irin Mommy ce itama haihuwan ta cikin sauƙi ne kafin ma a tafi asibiti wani lokacin ta haihu, har ita kanta Mimin a gida ta haifeta sai daga baya suka je asibiti a ka duba su. Rukky ce ta fara kiranta lokacin da ta fara amsa waya suka yi mgana bayan kuma sauran wayoyin da ta rasa ba ta amsa ba, ta yi mgana da duka ƴan'uwanta har Mommy suna yi mata barka da arziki har da Madiha da megidanta domin ita kai tsaye ta ce"Congratulation Fatima Kabir Dabo, Za mo wa uwa ba abu ba ne mai sauƙi. Allah ya raya abin da kika samu ke kuma ya baki lafiya da ƙwarin jiki wajen shayarwa tare da tarbiya."

Sai ta ji daɗi da abin da ya kai ɗan'uwa daɗi a wannan duniya ko da kuwa kuna da tarin bambamcin hallaya ne a tsakanin ku.
Haka ma Dr ya ce ya yi ta mata addu'a sannan da faɗan ta kula da kanta, shi da Jawahir sau biyu suna kiranta haka ma Hibba da Mu'azzam ta samu wayarasu ita dai ba ma za ta iya kirga waɗanda suka kirata ba amman dai abu mafi soyuwa shine babban kyauta ne na Ubangiji ace yau ka na amsa sunan uwa wani farinciki na dabam ne. Farincikin da take ciki ya sa ta kasa daina kallon jaririyar da Aji ya yi mata huɗuba da Maryama ba. Mamaki take yi yau itace ta haihu? Haihuwan ma tare da Aji abin da ba ta taɓa tsammani ba, har ta cire tsammani kuma sai Ubangiji ya kaddara za su zamo abu ɗaya.

Sanda ya shigo gidan ɗakinsa ya wuce ya yi wanka ya sauya ya tsaya ya amsa wayar Coach na su in da ya ke yi masa barka, ya kira shi da safe suna asibiti sai ya tura masa saƙon ba zai shigo Camp ba saboda mai ɗakinsa ta sauka shi kuma Coach na jin haka ya gayama sauran ƴan Team da cewa matar Capatin ɗin su ce ta haihu so ranar shi ya jwgoranci morning traning ɗin, abinci da komai da zai bukata Mimi ta faɗa ma Inna Zainaba a ka tanadar mishi a saman Dining bai duba abincin ba sai da ya leƙa ɗakin Mimi ya gaida da Inna Zainaba sannan ta fice falo ta ba su waje, gefen gado ya zauna lokaci ɗaya ya na faɗin"Me jego."
Mimi na mirmishi ta ƙara kishingiɗa lokaci ɗaya tana faɗin"Na'am Angon ƙarni."
Mirmishi suka yi ma juna, sannan ya leƙa jaririyar dake kwance gefenta tana tasharan barcinta na wani lokaci sannan ya dawo ya daidaita zaman shi.

"Sannu da koƙari Matar Aji.."

Mimi na mirmishi ta ce"Yauwa Mijin Mimi.".

Hannunta ya kama ya riƙe yana kallonta kafin ya ce"kin ƙara kyau, yau kaɗai jego nan ya karɓe ki."
Dariya ta yi amman ba ta yi mgana ba sumbatar hannun nata ya yi kafin ya ce"Ina fatan komai lafiya ko? Ta fara shan nono?
Haka ta faɗa ya na rike da hannuwanta. Sai Mimi ta girgiza kanta kafin ta ce" Ruwan zamzam kaɗai a ka bata, ruwan Nono dai kaɗan ya fara zuwa kila sai da zuwa gobe haka."
"To ba matsala zuwa goben? Ba za ta ji yunwa ba?
Mimi na dariya ta ce"Yunwa kuma? Ba za ta ji ba kada ka damu, na sha tea,kuma Inna Zainaba ta damamin kuni na sha zuwa Gobe ruwan nonon zai zo in sha Allahu "
Sai ya jinjina kansa alamun gamsuwa, sai kallon Mimi yake yi itama ta na kallonsa ta na nasa mrmishi, ita ta ɗauko yarinyar ta ɗora ta saman jikinsu dukkansu biyun a tare suka rike ta, sannan ɗayan hannun Mimi ta saka ta sakalo bayan Aji da shi, sun haɗe yarsu waje ɗaya sun rike. Ya riƙe hannun jaririyar ya haɗa da na Mimi ya damke kawai ya na mirmishi ya kasa mgana.

"Ka ga Kyautar da ubangiji ya yi mana ko? Yau mun zamo iyaye ma'ana mun zamo uwa da uba daga yau, nauyi ya same mu mun zama iyaye akwai haƙƙin ƴarmu a kan mu na tarbiya da kula da ita."

Ƙura ma jaririyar ido ya yi ta na ta barcinta sai kawai ya yi mirmishi kafin ya ce" Allah ya raya ki Inna ta, "
Haka kawai ya faɗa ya na cigaba da kallonta In Mimi ta na mgana sai dai ya ɗaga kai ya kalleta ya yi mirmishi kamar yau sauran kalaman bakinsa nasa sun ɗauke.
Ya dai kalleta cikin wani yanayi ya ce" Na gode sosai, na gode da kika yi dalilin jin wannan farinciki a matsayina na Uba na gode kwarai da kika kasance a cikin rayuwata Fatima kika kuma bani dukkan farincikin da gata a zamantakewar mu na aure. Na gode miki bisa yardan ki, haƙurin ki, Koƙarin ki a kaina Allah ya shirya mana Maryama ya ba mu ikon yi mata tarbiya ita da sauran ƴan'uwanta da suke tafe nan gaba."
Kanta ta ɗora saman kafaɗansa lokaci ɗaya tana faɗin"Amin Amin Mera. Nima na gode da ka yi sillar zamowa ta Uwa. Allah ya bar mu tare Amin."

Shima kansa ya jinginar saman kanta yana amsa mata da Amin Amin, sun ɗauki lokaci a haka sannan Mimi ta ɗago da kanta tana faɗin" Na manta ka ci abinci kuwa?.
Sai ya girgiza mata kai da sauri ta karɓi Jaririyar daga hannunsa lokaci ɗaya tana faɗin"Yana can saman dinning."
"Me kuk dafa ne?

"Jallop rice ne Bintu ta dafa ɗazun nan kafin su tafi, sai na ce su saka maka Food Flaks kada ya yi sanyi kafin ka dawo"

Kai ya jinjina kafin ya miƙe lokaci ɗaya yana faɗin"Kuma sai da kika yi mgana na tuna ina jin yunwa tun tea da na sha da safe ban kara cin wani abu ba."
Mimi na mirmishi ta ce"Na sani, na ga duk ka fara rama ne."
"Zo ki rakani mana, ni kaɗai za ki bari naci abincin?
Ta na yar dariya ta ce"Jego fa na ke yi Mera, ba'a son na zauna wajen sanyi Inna ma ba za ta barni na fita falo na bar yarinyar nan ita kaɗai ba.
Da sauri ya ce"Tare da ita za ki taho, ina cin abinci ina kallon ku ina jin ɗadi."
Mirmishi ta yi masa kafin ta ce"Haihuwa fa na yi jego nake yi, in na fita Inna za ta min faɗa sai ka yi hakuri fa."

Dakuna fuska ya yi kafin ya ce"To shi ne me? Jegon dai ba a haihu a taru a yi suna aci abinci ba ne? Ina ce shike nan an gama jegon.?
Ta na dariya ta ce"A'a sai na yi kwana arba"in ina jego a na kula da ni tare da mai sunan Inna, akwai dokoki ciki har da zama a ɗaki mai ɗumi."
Sai ta faɗa ya ji zafin ɗakin tunda ba fanka sannan an kashe Ac. Har gumi ya fara ma bai sani ba abun sai ya ba shi mamaki har sai da yace Topha, ya na koƙarin sake mgana ne Inna Zainaba ta yi sallama a Kofar ɗakin suka amsa mata sai ta shigo
Kai tsaye ta kalli Aji ta ce"To Baban Maryam mu kwana lafiya ko?
Kallonta ya yi cikin mamaki bai yi mgana ba,a gabansa ta kalli Mimi ta na faɗin"Za ki kara shiga ruwan ɗumi kafin ki kwanta.".
Sai ta gyaɗa mata sai kuma ta ƙara cewa"Ga Kunin ki nan a fulas anjuma ki ƙara sha, Sannan wankan towel ɗin nan zuwa sati zai tsaya, ganye za'a samo min na daki jikin ki da shi."
Mimi ta zaro Ido haka ma Aji da bai bar ɗakin ba. Inna Zainaba ko a jikinta ta shige toilet domin haɗa ma Mimi ruwan dumi ba ta ciki da iskacin yaran zamani na fahimci Mijin nan na Mimi ɗan gadara ne, ta gama masa kara in ta masa lamunin ganin matarsa da ƴarsa minti goma ne za ta riƙa shigowa tana ganin abin da ke faruwa.

Aji ya kalli Mimi kafin ya samu damar magana ta masa alama da hannu alamun ya yi shuru sannan ta ce ya fita amman bai fita ba sai da ya dawo ya sumbaci yarsa da matarsa sannan ya fice yana faɗin"Sai da safe Ummu Maryam."
Amman har ya gama cin abinci ya na mamaki shi fa ya ɗauka wani ɗaki mai kula da Mimi za ta kwana shi kuma ya kwana tare da matarsa amman kuma sai yake jin wani karatu na dabam, da ya koma ɗaki ya saka kayan barci ya kwanta ya kira Mu'azzam ya na masa ƙorafi Mu'azzam na danne dariyan sa ya ce"Ai hakuri za ka yi Yaya sai in Anty Mami ta yi kwana arba'in sannan komai zai dawo dai dai.".

Aji ya ce" Haka ta ce, wai daman da gaske take yi? Ni kaɗai zan rika kwana kamar wani mara gata, addini ne ya ce a yi haka ne?
Mu'azzam ya ce A'a nan take Aji ya yi tsaki kafin ya ce"To saboda wata al'ada sai a ware ni, ana gama taron suna zan ce kowa ya tafi a barni zan iya kula da matata da ƴa ta." Mu'azzam na ta danne dariyansa amman ya san tunda yayansa ya faɗa zai aikata shi ya sa da asuba yakira Inna da shawaran Hibba saboda ta ce gwara a kwabe sa tun yanzu kada ya aikata ya bar mutane da jin kunya.

Inna na jin abin da Baban inna yake shirin aikatawa ta yi yar dariya kafin ta ce"Bar ni da shi, shi ya sa ya ce ba za ta je gida ba saboda ya yi wannan diɓar albarkar ko? To zan ce bayan suna ta koma gaban Hajiya sai naga karyan tsiya fitinannen yaro kawai sai kace a kansa a ka fara haihuwa."
Mu'azzam na jin haka da sauri ya ce"Kada ki yi haka Inna ki dai yi masa mganar don Allah kada ya yi wata mgana ya bar ƙanwar mamanta da kika ce tana wajen ta ta zauna ta kula da ita kin ji ko Inna? In ta koma gidan Hajiya an ƙwari yayana tunda shi baya ra'ayin ta koma can in kika matsa masa kamar an shiga haƙƙin sa ne."
Da waɗanan kalaman ya lallashi Inna Meri ta bar mganar cewa bayan suna Binta ta koma gida, amman da safiyar ta je can gidan duba Binta da takwaranta ta iske tuni sun sha wakan har sun karya ta samu Mimi na cin ferfesun kayan ciki ta iske su Mama a gidan su suka taho mata da shi.

Ta iske suna ta maganar yau da safe an samu ruwan nono har yarinyar ta samu ta sha, amman sai barci ta ke yi Mama ta ce" Daga gani rigiman dare za ta riƙa yi."
Inna Meri ta ce"Shima ai haka ya yi, na fi wata takwas da haihuwa Baban Inna bai daina kukan dare ba."
Ana ta dai raha ana dariya. Baya gidan tun safe ya fita zuwa Camp, dawowarsa kenan ya shigo yana gaishesu sai ya ga Inna bai ma san ta zo ba.
Daga nesa ya kalli Mimi ta kalleshi suka yi ma juna mirmishi, Sai a ka bar shi da tambayan Inna Zainaba yana faɗin" Ba wata matsala ko inna? Ko akwai wani abu da kuke bukata?
Cikin mirmishi ta ce"Ba ma bukatar komai, ai komai ai akwai shi sai godiya Allah ya ƙara buɗi na alheri."
Ya amsa da Amin kansa a kasa sannan ya miƙe ya fita sai Inna Zainaba ta ce Mimi ta ɗauki yarinya ta je su gaisa jikinta na rawa ta mike ta sunkunci yar amman sai da Inna Zainaba ta saka ta ta saka mayafi da takalmi daman kafar nan da safa tun da ta haihu ko'ina na jikinta ya na rufe Inna Zainaba jegon mutanen da take yi mata..

Aji har ya fara ƙorafin mutum da matarsa an barshi da kallo daga nesa sai ga Mimi farinciki yasa sai da ya rumgumeta yana sauke ajiyar zuciya. Ba ta daɗe ba tunda tasan halin Inna Zainaba amman sai da ta ɗauko masa abun ƙaryawansa ta jera mai sanan cafet a cikin Bedroom sannan ta koma ɗaki har magiya ya yi mata ta tsaya ya gama ƙaryawa tace a'a in ta daɗe za ta yi mata faɗa, daman bayan fitan ta sai da Mama ta ce" Yaran zamani jikinsu na rawa za'a je wajen miji."
Inna Zainaba ta ce"Su ko tausayin kansu ba sa ji."
Inna na gefe ba ta ce komai ba, ta san halin Baban Inna bai son kara ba.

Sai da ya yi wanka ya sauya kaya sannan yace Inna Meri ta fito ya kaita gida, Itama daman tana son mgana da shi, ta yi musu sallama akan anjuma Walida za ta kawo garin kuni, a hanya ne ta yi masa mganar ya rika kawaici sannan kada ta ji ya yi mganar bayan suna a watse in an barshi da matar da yarinyar zai iya kula da su ne? Ya na jin haka yasan Mu'azzam ne ya kai mgana wajen Inna bai ce komai ba, illah tura baki kafin ya ce" To Inna mutun da matarsa sai a hana shi ganinta."
Inna ta yi masa wani kallo kafin ta ce" Ka dai ji abin da na gaya maka, in ka ce ba za ka yi kawaici ba wlh zan ce a maida Binta gaban Hajiya sai bayan wata biyu sai ta dawo " Yana jin haka da sauri yavce"Allah ya baki hakuri Inna, In sha Allahu ba zan ƙara mgana ba"
Amma bayan ya sauke Inna, bai shigan ba ya juya a hanya ya kira Mu'azzam yana ce masa"Kai ba'a sirri da kai ko? Ban ƙara gaya maka wata mgana."
Tunda yaji haka ya san kan mganar yana koƙarin mgana yayan nashi ya katse kiran sannan ya kira shi daga baya bai ɗaga ba sai kawai ya ƙyaleshi za su daidaita daga baya.

A cikin satin da Mimi ta haihu kafin suna ko da yaushe gida cike da baƙi. Ba yan'uwanta ba na megidan ba, Khadi tun ana saura kwana biyu suna ta iso Madiha ma ta ce sai ranar suna za ta zo har da ƴan'uwan Mommy daga kano. Jawahir ma ana gobe suna ta iso ita da yara Rukky dai tana lagos ba za ta samu zuwa ba, amman har abokan aikinta mata sun zo mata barka sannan za su zo suna, mazan ma har gida suka zo su ka yi mata barka. Daman hutun haihuwanta sai bayan ta haihu zai fara aiki wattani uku kafin ta koma, kullum sai Magajiya da Gaje sun leka in da wani aiki su kama sannan Yaya Amina da Yaya Halima suna zuwa Bintu da ma Maeesha gwarama su Yaya Junmai suna fashin rana amman suma kan sun yi kokari Inna Zainaba sai yabawa take yi, ga uban gayyar kafin ma a bukace wani abun ya kawo shi.
Inna Zainaaba tana waya da ƴar'uwata lokacin da Mommy ta ce"Ina fatan ba wata matsala ko?

Inna Zainaba ta ce"Wlh babu Murja, Mimi ta yi dacen miji da danginsa masu karamci da mutunci komai da kika sani wlh sai dai ma mu yi kyautarsa. Mimi da Maryama ba abunda suka nema suka rasa waɗanan mutanen akwai karamci da kirki "
Mommy ta ji daɗi kwarai hakama khadi ta dinga faɗa, domin kayan Mimi da na jaririya duk safe Magajiya da Bintu ke zuwa su wanke sannan su dafa ruwan zafi su yi ma jaririyar wanka Mimi kuma Inna Zainaba ta yi mata. Bintu kuma da Maeesha suke gyara gidan su turarashi da kamshi.Su Yaya Amina kuma su zo su yi girkin rana da dare su Mama suna zaune suna hira ba abin da suke yi, duka yayyen Angon karni ne da ƙañensa ke yin komai yaddiko ma da ta zo sai da ta yaba musu, sannan Inna ma ta kan leko da safe, garin kuni haka ta yo shi da yawa ana damama Mimi har ruwan nono ga shi ya samu sosai.
Hajiya ma ta na gida labari ya zo mata Sai kawai ta yi mirmishi kafin ta ce" Meri basakkawata ce mai kirki, sanna yayanta sun samu tarbiya daga bangarenta, babu nadama ga haɗa zuru'a da ita."

duk da sunan ya zo ranar farkon azumi amman ba abin da aka fasa, komai an yi waina ce daman su Mimi suka yi da Sinasir aikatau a ka kai. Sai raguna biyu ɗaya na ta ɗaya kuma Aji ya raba abun ya ce a bama ƴan'uwansa, ya ba su komai na su a gidan Inna danginsa za su yi nasu taron tita kuma Mimi da na ta dangin a gidan ta.
Sannan sun haɗa ma Mimi kayan Atamfofi sama da guda biyar ga kayan Baby, Hibba ma ana gobe suna ta zo ita da Mu'azzam da Atamofi guda biyu sai na Bby sai 30k daga Mu'azzam.

Ranar azumin farko a ka yi shagalin suna duk da azumi ne Mimi ta ga taron mutane kaf yan'uwanta sun zo har da Madiha gida cike kuma isu isu tunda su Bintu suna can gidan Inna suna na su taron.
Mimi ta sha kunshi da kitso. Sannan ta shiga ta fita ita da Maryama wacce Mimi ta ce za su riƙa ma lakabi da Ummi tunda yar wajen Mu'azzam Ammi suke kiranta.
Sannan har Makeup an yi mata sannan sun sha hotuna, an yi tsire ga wanda ba za su tsaya a sha ruwa ba, a wata yar jeka sai a saka sinasir ko waina sai naman kaza ko na rago sai a saka maka cake ko samosa sai lemu da ruwa, duk sun yi zobo mai rai da lafiya da kunin aya amman zobon wannan na uban gayya ne za su yi walima da daddare a can Camp ɗin su.

Sinasir ɗin da waina Mimi ta ɗibar masa kula ɗaya sai fride rice da yasa Binta da su Yaya Amina za su yi masa, sai

43 / 49