Idan An Ciza Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   41 / 49

120K to 123K   out of 146.6K words

sai ta ce baza'a bar gida ba kowa ba ga Zuwaira ta ce za ta je, to fa tunda a ka ji Mansoor zai yi tashan mota sai kowa ya miƙe yace zai je Harda Jummai da matar Auwalu ga matar Saddiqu ma Walida da Mariya ma sun ce za su je. Sannan a gidan su Baba Ɗanlami Inna ta ce ko Gaje ko Harira ga kuma can gidansu Hibba ko mutame biyu ne za'a ɗauka.

  Ranar Alhamis daga camp Mansoor gidan Inna ya sauka kan mganar motar, dama sun yi mgana da ƴaron Baba Ɗanlami mai jan motar sharon, shi zai kai su sannan ya koma in an gama suna ya ɗauko su tunda daman yana zuwa kano kaduna ne daga nan Gombe. Mansoor ya sha mamaki da Inna ke yi masa lissafin masu zuwa cikin nuna mamakin sa ya ce"To ai motar ma ta cika Inna? Haba abu sai kace biki? Sun yi yawa ya kamata komai a yi shi da tsari ne.
Inna ta gyara zama ta na faɗin"  Bakomai arziƙi ne, kuma dukkansu ba su san gidan ba. In ba domin haihuwan ba wa zai ta shi yace zai je Baban Inna? Kuma wa kake ganin a cikin su bai cancanci zuwa ba? Daga ƴan'uwanss sai yan uwan matarsa sai ƙannensa a ciki wa kake ganin za'a ce ba zai je ba?. Tun da ya ji Inna ta fara magana ya yi shuru ya san daman karatun za ta ɗora masa kenan amman sai da ya kaɗa kai kafin ya ce" Duk da haka dai Inna a yi abin hankali mana, shima Mu'azzam ɗin wata ɗawainiyar za a ƙara ɗora masa kada ki manta haihuwa a ka yi masa ya yi hidima Inna." Inna ta na mirmishi ta ce"To duka duka kwana nawa ne? In sun daɗe fa kwana huɗu."

  Da sauri ya ce"A'a kwana biyu za su yi Inna, zan ma gaya ma su Yaya Halima kada wacce ta fi haka."
Inna sai kawai ta kaɗa kafin ta ce"Allah ya sa su je lafiya su dawo lafiya."
Ya amsa mata da Amin, suna zaune ne daman dukkansu a saman kujerun falon, ita ta na daga gefe shi kuma ya na zaune saman kujera mai zaman mutum biyu yana danna wayarsa suke wannan mganar da Inna..

"To ita Bintar za ta samu zuwa ko?

  Kai tsaye ya ce" Eh za ta je, amman Inna kina ganin ya kamata Walida ta tafi? Sai a bar ki ke kaɗai?
Inna ta balla masa harara kafin ta ce" Yarinya ce ni da za ka ce a barni ni kaɗai? Ta je abun ta Allah ya dawo su lafiya kafin na haife ku ai ni kaɗai nake zaune miye a ciki?
Sai kawai ya kaɗa kai kafin ya mike yana mata sallama sai ta ce ya tsaya ya ga kayan da suka tara dole ya koma ya zauna Walida ta kwaso masa kayan, bai ko ɗaga ba amman ya kallah kafin ya yi mgana Inna Meri ta yi masa bayanin abin da suka hada sannan ta ce ɗazu da yamma Matar Auwalu ta kawo turmi da omo da sabulai ta ce na ta da na Magajiya Auwalu kuma dubi biyar ya ba da gasu a hannu.

  Kai tsaye ya ce Allah ya saka albarka. Sai a lokacin ya tuna da ana ma fa wani abun in an haihu duk da ya turama Mu'azzam ɗin 100k ya kara amman sam hankalinsa bai kawo masa Mimi ma ba haka ya kamata ta je ba. Amman ganin kayan da Inna ta nuna masa sai ya farga daga nan gidan Inna sallar isha'i ya tsaya ya yi a hanya sannan ya shiga gida ya iske gida sai ta shin kamshin turaren wuta, ga kamshin girki ga kanshin matar gidan da ta chaɓa ado ta ci kwalliya domin farincikin mijinta.
Tarba ta yi masa kamar yadda ta saba, suka makale juna kamar wani zai raba su. Bayan ya yi wanka suka zauna saman dining suna cin abinci jefi jefi suna hira.

  "My Jan me za mu siya na sunan mai sunan Inna?

  Kamar daga sama ta ji tambayar na shi, lokacin ma nama ne a bakinta sai da ta hadiye ta sha ruwa sannan ta kallesa kafin ta ce"Kamar me kenan?
Sai kawai ya ce"Kaya mana, ba na ga wai ana siyan atamfa ko kayan jarirai ba."
Sai Mimi ta saka dariya kafin ta ce"Ashe ka sani, ko gaya maka a ka yi?
Kai tsaye ya sanar da ita a gidan Inna ya gaani mirmishi ta yi masa kafin ta ce"Ni ai ban jira ka ba, mu gamaccin abinci mu shiga ciki ka gani."
Sai da su ka gama cin abincin ta kwashe komai ta kai kitchen. Sannan ta gyara wurin ta rike masa hannu zuwa ɗakinta a saman gado ya ga akwatinta ƙarama.
Gefen gado ta zaunar da shi sannan ta buɗe wardrpe ta ɗauko wata katuwar leda, ta sauke a gabanshi shi kuma dai dai lokacin ne ya kalli akwatin nata kafin ya ce"Wannan akwatin fa? Ko shima kayan sunan ne a ciki?

Mimi na dariya ta ce" Kayan dai mai zuwa suna, kasan sati fa zan yi ina so ka bar ni zan je kofar soro na gaishe su sai kuma na leƙa gidan Dr."

CBai samu ma bakin mgana ba, ya ga kawai ta zazzage ledan hannunta kaya sun faɗo, Atamfa da less sai rigunan Jarirai masu kyau guda uku sai katon pampers guda ɗaya sai wifer, sai wasu huluna na jarirai da safa a kalayensu masu kyau sai over roll shima na kwali masu kyau guda uku sai saitin man shafawan yara mai haɗe da hoda da olive. Ta gama ɗaga masa kayan ya gani sannan ta maida a leda lokaci ɗaya tana faɗin" Ni na gama mawa saura naka uban Maryama."
Mirmishi ya yi kafin ya ce"Duk yaushe kika yi wannan siyayyar ban sani ba?.
Gira ta ɗaga masa kafin ta ce" Zauna nan, kasuwa na je ni da Rukkayya."

"Da izinin waye kika je kasuwan?

  Haka ya faɗa yana tsare ta da Idanuwansa sai kawai ta saka masa dariya kafin ta ce"Da izinin mijina mana, ka manta ranar na ce maka Rukky za ta rakani anguwa? Ka ce sai na dawo kada na yi dare? To ai kasuwan ne anguwan"
Sai kawai ya jinjina kai kafin ya ce"Na ji kin yi naki, ni me ya kamata na yi?
Sai da maida ledar in da ta ɗauko sannan ta zauna gefensa kafin ta ce" To me ya kama ta ka yi? Tunda ni na siya waɗanan kayan me zai hana kai sai ka ɗora mata da Kuɗi?
Kai tsaye kuma ta cigaba da cewe" Kuɗin zai fi, tunda ka ga ni na siya kayan sai mu ɗora da kuɗin zai fi."
Sai ya jinjina kai kafin ya ce" Shike nan amman kamar nawa ki kke ganin zan ɗora na kuɗin?
Kai tsaye ta ce"  Duk abin da Allah ya hore maka Merapyaarr"
Sai ya gyaɗa kai kafin yace bari da safe in Allah ya kaimu.

  A daran bai mata mganar satin da ta ce za ta yi ba sai da safe tunda tun asuba ta tashi tana aiki. Daman tun a daran jiya ta yi masa miya saboda tasan shi ba ya son aiki.
Sannan ta saka an yi masa snak cake da cincin da samosa ya riƙa shan Tea da shi kafin ta dawo duk kuma ta kaisa kitchen ta nuna masa, har tana cewa ya riƙa dafa farar shinkafa ko taliya ya na ci da miya.
Kallonta ya yi a karkace kafin ya ce"Wai wata za ki yi ne a can?
Mimi ba ta ba ma tambayansa muhimmanci ba ta ce"Ka manta, na ce maka zan yi sati ɗaya."

  Bai ƙara mgana ba. Sai da suka karya har Mimi ta yi wanka tunda Bintu ta kira ta ce suna gidan Inna ita a ke jira mai motar ya ce karfe tara na safe za su tafi, Aji ya riga ya biya kuɗin motan na zuwa da na dawowa.
Sai da suka zo sallama duk da shi zai kaita gidan Inna a motarsa, ya rumgumeta yana shafa cikinta da ya fara tasawa lokaci ɗaya kafin ya ce"My jan.."
"Uhm Merapayaar."
"Bai kamata ki je ki yi sati ba. Saboda kina da juna biyu ni ya kamata na riƙa kula da lafiyarki, don Allah ki yi kwana biyu ki biyo su Yaya Halima ku dawo"
Da sigar lallashi ta faɗa, da yasa ta yi shuru ta lafe a jikinsa.
Ganin ta yi shuru yasa ya ƙara sausauta murya kafin ya ce" Na saba dake, ba zan ji daɗin zama ni kaɗai ba, ba ki tausayina? Wa zai rika ba ni abinci yana min hira? Ki bari daga baya ko bayan kin haihu ne sai ki je ki gaishesu. Ni sai ma mu tafi tare na rakaki amman na roke ƙi da Allaj ki dawo tare da su Yaya Halima.".
Nan ma shuru ba amsa, Idanuwanta ya ciko da kwallah. Domin har ta faɗa ma Mommy za ta je soron ɗinki, sannan kuma yanzu sai ta ce ba za ta samu zuwa ba?
Ganin yadda ta nuna ne ya sa sai ya raba ta da jikinsa lokaci ɗaya yana faɗin"Amman kin kin ga da takura ba zan hana ki ba, ki yi satin sai ki dawo daga baya."
Sai kawai ya juya zai fita daga ɗakin da sauri ta riƙo hannunsa kafin ta rumgumeshi ta baya lokaci ɗaya tana faɗin" Umarni kawai za ka ba ni ba alfarmana za ka roƙa ba, ai zaman ka nake yi, Kada ka damu zan dawo in sha Allahu tare da su."

  Kamar zai yi kuka  ya juyo yana faɗin "Kwana biyun za ki yi ko? Sai ta gyaɗa masa kai, rungumeta ya yi cikin farinciki lokaci ɗaya yana faɗin" Allah ya miki albarka My Jan, na yi miki izinin ko Walida ko Bintu su raka ki ki je ki gaishe su kin ji ko? Sai ta gyaɗa masa kai, Ita da kanta ta yi ɗage ta sumbaci kumatunsa. Shi kuma ya yi saurin damƙe kanta ya rankwafa yana sumbatar bakinsa, ita kuma sai ta zagaye hannayenta daga bayansa ta rumgumosa sun daɗe a haka kamar ka da su rabu gani ta yi zai ɓata mata kwalliyarta yasa ta ƙwace jikinta lokaci ɗaya tana faɗin" Suna jira na fa."
Ƙara riƙota ya yi lokaci ɗaya yana faɗin"Minti biyar to."

  Dole ta kyaleshi ya rumgumeta kawai ya na shakan kamshinta. Sannan ya sake ta lokaci ɗaya  yana riƙe mata hannu ɗayan hannun kuma ya rike akwatinta, sai ta karɓa Lokaci ɗaya tana cewa"Sai na sauya shiri."
Shi taya ta ta rage wasu kayan, kayan sunan ma da za ta kai ma Hibba duk a ciki ta tusa kafin su fito har Yaya Amina sai da ta kira shima Kuma Mansoor Auwal na ta kiran shi Mu'azzan tun asuba ya kira baki ya ƙi rufuwa yan'uwansa suna hanya.
Shi ya rike mata akwatin har jakarta sannan ya saka mata mayafinta a saman kanta ya rike mata hannu ya kai ta har mota, sannan shima ya zagaya ya shiga a hanya suka tsaya ya cire kuɗi 50k yace ta haɗa ta kai ma Hibba ta amsa lokaci ɗaya tana faɗin. "Mungode Baban Maryam Allah yasa ka ma nema albarka."
Yana mirmishi ya ce"Amin Amin Ummu Maryam."
Suka haɗa ido suka yi ma juna mirmishi, ya rike mata hannu da hannunsa guda ɗaya, ɗayan kuma ya na tuki dashi, kewarta yake yi tun kafin ta tafi, ganin yadda ya matse mata hannu yasa ta rike hannayensa da hannunta guda biyu ta jimke kafin ta kallesa cikin shagwaɓa Ta ce.

"Ina sonka, ina matukar kaunar ka.."

  Wani kayattacen mirmishi ya saki kafin ya ce" Kin san dai na fi ki son ki ko?  Ina sonki, ke ce komai nawa Fatima."
Sai suka ƙurama juna ido, ganin kamar hankalinsa na kanta yasa da sauri ta ce"Tuki kake yi, ka kula Merapayaar"
Sai ya maida hankalinsa kan hanya Allah yasa ma titin ba motoci sosai. Suna tafe amman suna ƙanƙame da hannuwan juna
"Ki kula da kanki, kin ɗauko magungunan ki?  Sai ta gyaɗa masa kai kafin ta yi mgana ya yi saurin cewa"Ka da ki ci wani abun da cikin ki ba ya so, ina son cikin nan Mimi nima na ƙosa ki haifamin wata Maryama ɗin"  mirmishi ta yi masa kafin ta ce" In sha Allahu kada ka damu."
Sai ya jinjina kansa, sun shigo anguwan Tunfere kenan ta ji yana faɗin" Na ma gayama Mu'azzam ya kula da ke, kina da juna biyu."
Mimi ta kalleshi cikin jin kunya ta ce"Kai, wai kai baka jin kunyar gayama mutane ina da juna biyu?
Suna tsayawa ƙofar gidan Inna dai dai lokacin da ya kalleta yana faɗin" To miye a ciki? Ai ba abun kunya ba ne na ga abin farinciki ne kowa kuma na son matarsa ta samu ciki."

  Mimi ta ce"Duk da haka dai ba a faɗa sai dai a gan shi ya fito, haka fa da muka je gaida Daddy ka faɗa masa wai ina da juna biyu."
Dariya ya yi mai sauti kafin ya ce"Kin ji ki da wata mgana? Abun kunya ne?  Na ga dai abun alhafari ne, kuma ke ba ki san masu shege ma suna nuna ma duniya ba? Ballantana ni da ɗan sunna zan haifa"
Dai dai yana buɗe mota ya fito sannan ya zo ya buɗe mata ya rike hannunta ta fito daidai lokacin da ta ce"Amman ai da kunya tun da kowa ya san abin da muka yi a ka samu cikin ko?
Aji ya kalli Mimi ganin har ta na wani ɓata fuska. Dariya ta kamashi ya kama yi tun da Mimi take da Aji a sanin da ta yi masa a baya da yanzu ba ta taɓa ganin shi yana dariya haka ba.

"Shekaran ki nawa wai? Ai daman kowa ya san sai da muka haɗu a ka samar da saduwa sannan kika samu ciki, tunda ba a ruwa za ki sha ba."

  Haka yake faɗa yana mata dariya, kamar za ta yi kuka ta dake shi a kirji shi kuma ya na riketa yana dariya dai dai lokacin sai ga mai motar tare da Auwalu da Gaje a ciki ita ce za ta je. Sai matar Auwalun da Maeesha da Mariya, da Jummai da Zuwaira kowa cikin shirinta, Auwalu ne ya sauko suka gaisa yana gaya masa yaron mai motar ne zai kai su kanon shi yana gida baya jin daɗi, Aji ya kalli direban kafin ya ce"Ka tabbata ya iya mota?  matata ciki gare ta ban shirya ɗaukan wannan kaddaran ba yanzu."
Ai Mmi na jin haka ta ja jikinta zuwa wajen su Yaya zuwaira tana gaishesu domin in ta cigaba da tsayawa saita ji abin da zai saka ta ba za ta ƙara kallon Yaya Auwaln ba.

  Tare suka shiga gidan suka iske su Yaya Amina tun ɗazu suna nan suna jiran su, nan a ka gaggaisa sannan sai ga su Auwalun sun shigo gidan tare da Mansoor suka gaida Inna sun shirya daman motan kawai suke jira, Yaya Halima ce ta kalli Aji kafin ta ce"Na ji ana zencen kwana biyu na ce mu fa huɗu za mu yi."
Kai tsaye ya ce"A'a kwana biyu za ku yi gaskiya." Haɗe rai ya yi kada ma ta kara mgana, Ita daman zolayanshi take yi, Bintu ce ta ce a hankali ita sati mijinta ya barta ta yi. Hararanta Mansoor ya yi kafin ya ce" Duk wacce ta ga kwana biyu ya yi mata kaɗan za ta iya ƙarawa amman litini da safe mota za ta koma wanda ya ga zai dawo shike nan.
Haka ya faɗa lokaci ɗaya yana ficewa Bintu ta tura baki ta ce" An ya in Anty Mimi ta haihu za mu je mu yi sati muna suna kuwa?
Yaya Amina ta ce" Kina da koƙari, in ma ya bari an yi sunan kenan tsab zai ce ba taron suna in dai Baban Inna ne."

  Mimi na gefe ta na jin su tana yar dariya, ba ta ce komai ba, Yaya Halima ta ce"Duk fa wannan muzurin saboda matarsa ne, kada mu kara kwana a barshi a gauro."
Gabaɗaya suka saka dariya Bintu har suna tafawa da Yaya Amina.
Mimi ta harare ta kafin ta ce" Har da ke ko? Zan gaya masa."
Bintu ta tsuke baki tana faɗin" Ni ban ce komai ba, ba ruwana."
Suna cikin mganan ne Auwalu ya leko ya ce su fito su Yaya Zuwaira daman suna tsakar gida Maeesha ne kawai tare da su, Mariya da Walida yan zumuɗi suna kofar gida wajen mota su Auwalu suka fiffita da kayan a ka saka a booth, sannan a ka tsara tafiyan Aji shi ya saka Mimi a gaban mota ita da Mariya tunda ba ta da jiki, Yaya Jummai ta kaɗa baki tana faɗin"To ai da baya ta dawo,  ko ka saka Bintu madadin Mariya."
Kai tsaye ya ce"A'a Bintu za ta matse ta, kuma ni ina so ku kula da ita ne, juna biyu gare ta fa"

  Kunya kamar Mimi ta nutse kanta ta sunkuyar Yaya Auwalu ne a ka bari da faɗin" ƙwarai kuwa, ku kula da matar yallaɓai dakyau."
Gaje ce ta ce" Kada ka damu Baban inna  zamu kular maka da matarka da abin da ke cikinta in sha Allahu."
Suna ta masa dariya shi kuma ya haɗe rai, Mimi ko kunya ta rufe ta wai har ya na ma direba warning cewa kada ya yi gudu ya bi a sannu matarsa juna biyu gare ta har yana cewa"Ita ce komai nawa, ka bi su a hankali don Allah ban da gudu.". Direba na dariya yace"In sha Allahu Yallaɓai "
Inna Meri ma har kofar gida ta rakosu,  tana musu fatan Allah ya tsare, baya mutum huɗu Gaje da Jummai da Zuwaira, sai Maeesha. Kujeran tsakiya kuma Yaya Amina da Yaya Halima sai Bintu, sai Walida da a ka gyara ma inji sauran kujeran za'a biya Tudun wada a ɗauki mutum ɗaya daga gidansu Hibba.

  Suna ɗaga musu hannu tare da fatan su isa lafiya, Tudun suka biya su ka ɗauko Zaliha ɗiyar ƙanwar Maman Hibba ne sai bayan sun dau hanyar kano Nafisan Nasir ta kira Mimi ta ce ba ta san sun shirya tafiya ba, Nasir ya barta da ta zo. Sai mimin ta bata hakurin itama ta sha'afa ne ba ta mata magana ba, amman wai Nasir ɗin ya yi

41 / 49