Idan An Ciza Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   2 / 49

3K to 6K   out of 146.6K words

a gidan tsoho ba"
Hibba ta kalli Walida itama ta kalleta domin dai kalaman sun yi girma.
Magajiya haka take ta masifa tana faɗan maganganu tana zagin Inna Meri a fakaice sannan kuma Baba Ɗanjuma ya kasa tsawarta masu daman ko a baya Magajiya ba ta jin mganarsa ballantana su Baba Sanin. Ana cikin haka sai ga Bintu ta shigo gidan ita da su yara har da Junior.

  Ta iske an tasa uwarta gaba ana gaggaya mata mganganu. Daman kuma tun da asuba Walida ta saci wayar Inna ta tura mata saƙon abin da ya faru, shi ne tun safe ta zo gidan amman ta iske ana ta cin ma Inna mutumci har magajiya na faɗin tana takama ɗanta na da arziƙi zaman me ya ke a gidan da ba shi da gado? Ina kuɗin?
Baba Sani ya ce ko akwai kuɗin zuciyarsa ta mutu mganganu dai marasa daɗi.
Inna Meri ta kasa mgana Baba Danjuma kuma na daka musu tsawa amman ba wanda ya saurareshi Sai abin da suka manta ba su faɗa ba.

  Idon su ya rufe ba wanda yasan Bintu ta zo gidan sai da ta kwaɓe hijabi ta ci ɗamara ta sha gaban Inna tana nuna Magajiya da yatsan hannunta lokaci ɗaya tana faɗin" Ya ishe ki fa magajiya kul ɗin ki, Innar mu ta fi karfin reni daga gareki, yayanmu ya fi karfin ku kirashi yana hango wani abu me zai hanga? Me kuke da shi? Miye a wamnan gidan ban da tsiya? Na rantse da zatin Allah ban ga wani abun arzikin dake gidan da Yayanmu zai nace sai ya zauna ba sai dai can wani ra'ayi na shi ,kuma  dukkan nan kunsan ya fi karfin zaman a wannan a kurkin ɗakin da kuke rigima a kan shi."
Ta faɗa cikin bacin rai, Magajiya sai ta saki baki ta na kallon Bintu, haka ma su Baba Sani Baba Ɗanjuma kuma sai ya yi mirmishi a kallah dai yasan yanzu za su saurara.

  Baba Sani ya nuna kansu yana faɗin" ke ke, wai mu kike kira matsiyata don uban ki? mu sa'annin ki ne?
Magajiya ta saki shewa tana faɗin" Lalle, to in har ana da arzikin a tashi a bar ma masu gado gida ehe."
Saddiqu ya harzuka ya faɗo tsakiyar wajen kamar zai kai ma Bintu duka Inna Meri ta tare gabanshi tana faɗin" Kul kar ka  sake ta taɓa ta, matar aure ce kuma sannan ƴaƴanta na kallon ka."
Sai Baba ɗanlami ya fara Kumffar bakin ta na kare mata amman tana gani tana yi musu rashin kunya. Saddiqu kuma yana haƙilon sai ya yi kasa kasa da Bintu ita kuma ta na bayan Inna ta na faɗin Uban da ya fasa wlh in ya taɓa ta sai ya yi kwanan cell.

  Inna Meri ta kalleta kamar ta make ta tana faɗin" Rufe min baki me ya sa baki da kunya ne?
Bintu ta tura baki tana faɗin" Inna to ba ki ji abin da yake cewa ba ne, ni zai da ka? To wallahi kar ya fasa."
Inna Meri ta ja Bintu ta turata cikin ɗaki har su Hibba ta ce su shige da yaran kar wacce ta sake fitowa, itama sai Baba Danjuma ya riketa ya na neman tura ta cikin ɗakin yana yi mata magiyan ta yi shuru lokacin fa har su gaje sun jiyo hayaniya sun shigo gidan.

  Amman Inna ta kafe ta ce ita ba faɗa za ta yi ba mgana za ta faɗa musu sai ya sake ta.
Kallonsu ta yi dukkansu kafin ta ce" Ku kwantar da hankulanku zaman Binta a gidan nan tun jiya ya ƙare, ga ɗaki nan ku yi yadda kuke so da shi.Ɗan yau ne ka haife shi ba ka haifi halin shi ba, in da ace Baban Inna mai jin mgana ne wallahi da yau ba ta zo ba, amman ku yi hakuri ga ɗaki nan in kuma nan ma bai isa ba, ni ma kuna son na tashi na bar ma shi Saddiqun shashen ne gabaɗaya sai in ta shi, miye a ciki? Ai ba wani damuwa tunda gidan ubansa ne, ni kuma matar babanshi nake  kuma ya fini iko da gidan gabaɗaya"

  Da sauri Baba Ɗanjuma ya ce" Ki fita ki bar musu shashen? To ban animce ba, ba ke ba ko Manaoor ba in da zai je."
Inna Meri ta ce"Magana ai ta kare kuma, ga ɗaki nan zan kira Hajiya su zo su kwashe kayan su, abin duk bai kai na faɗa ba."
Sai mamaki ya kamasu Baba Ɗanjuma cikin mamaki ya ce"Ban gane ba, ina ita Bintar?
"Ta na gidan su tun jiya.?
"Me ya faru?
Inna ta kalle shi lokaci ɗaya kafin ta yi mirmishi tace" Ina ga sun rabu ne."
Gabaɗaya su Baba Sani suka zaro ido, ita Inna Meri ɗaki ta shige da sassarfa Baba Ɗanjuma ya bi bayanta cikin mamaki.
A ka bar su Magajiya a tsakar gida suna ta magana ƙasa ƙasa.
Magajiya ko har dariyan mugunta ta saka da karfi ta ce"To daman ina wannan auran zai yi karfo? An gama karyan arziki ya auro wacce ta fi karfin shi, ai daman hausawa sun ce kwarya ta bi kwarya in ta hau akushi sai ta fashe fasss."

Ita dai tunda an ba da ɗaki ta yi wucewarta shashenta tana waƙe waƙe  Ta bar su Baba Sani na mganganun su, Gaje ta bi bayanta Harira dai duk ba ta ji daɗin abin da ya Faru ba,.Haka suka fito suna ta dariyan cewa Daman ai tun farko ya kai kansa in da aka fi karfinsa , Saddiqu ma sai dariyan mugunta yake yi domin ya ce ya na jin haushin Mansoor ya yi ta nuna yafi kowa sa'an rayuwa.

  A can ɗaki kuwa Baba Danjuma ya tsare Inna Meri sai da ta maida masa abin da duk ya faru a daran jiya.
Cikin tashin hankali y ace"Innalillahi! Ban san duk haka ya faru ba, jiya na gaji sai na kwanta da wuri amman Meri me ya sa kika barta ta tafi?
Inna Meri ta bar gaban Baba Ɗanjuma sai ta koma gaban tibin dake ɗakin tana neman Sigan da za ta saka ma Kuni lokaci ɗaya tana  faɗin"me ya sa kuke tunanin zan hana ta tafiya? Shi wanda ya ijiyeta da kanshi muna ji ya ce ta tafi ɗin zai fi, ni kuma a wa da zan ce kar ta tafi,? wallahi  na ɗauki Binta a matsayin ƴata kamar Bintu ko itace Bashir ya yi mata wannan wulaƙanci sai na dawo da ƴata gabana sannan na saka ya sake ta tunda ba a zaman aure dole ko domin alfarma."

  Baba Ɗanjuma da ya fahimci ranta ya ɓaci sai ya ce"Yanzu Shi Baban Inna yana ina?
Inna Meri ta yi masa banza ta duka tana saka ma kuninta siga,  sai ya shiga ƙwalama Walida kira sai ga ta fito ita da Bintu su yake tambaya Mansoor walida ta ce tun jiya da ya fita bai dawo ba sannan Yaya Mu'azzam ya ce yana ta kiransa bai same shi ba.
Baba Danjuma ya fice yana faɗin bari ya neme shi ya gani ko zai same shi.
Ya na fita Bintu ta ce" Yaya Mansoor bai  kyauta ba, ga shi yanzu saboda shi  an zo Anci mutumcin Inna"
Nan suka zauna suna mai da yadda akayi Inna ba ta saka musu baki ba tana dai ta hidima da yara abin ta, Bintu ce ta kira Yaya Amina da Yaya Halima ta ce su zo gida su dai sun ce in Inna ba za ta saka baki ba su za su saka, in ta kama sai su je su ba ma Mimin hakuri da kansu, tunda Hibba nata kiran wayarta ba ta ɗauka ba,daga baya ma sai su ka ji wayar a kashe.

******

*MANSOOR.!*

Tun a daran jiya da ya bar gidan ya isa camp ɗin su domin a tunanin shi anan zai samu natsuwa. Sai dai Ina! wannan natsuwar da ya ke fata ya kasa samun shi, gaɓadaya ji ya yi kamar ya na cikin nadama wata zuciyarsa tana faɗa masa abin da ya aikata ma Mimi bai kyauta ba? A ƙasan ran shi ya ke jin radaɗin maganganun da ya gaggayamata sannan a cikin kunnuwansa ya ke jin sautin kukan ta, me ya sa? me ya aikata? Menene laifin Mimi da ya riƙeta a cikin ransa? In har zai yi adalci da ita da shi duk suna matsayi ɗaya ne a lokacin.

  Amman sai wata zuciyarsa ke faɗa masa abin da ya aikata shi ne dai dai domin duk abin da ya faru Babanta ne sila, kuma ya san duk barazana ce ba za ta iya tafiya ko ina ba saboda ta na son shi, bai taɓa tunanin da gaske Mimi za ta iya tafiya ba in da ace yasan za ta suɓuce masa da bai tafi ba da ya tsaya ya bata hakuri.
Ko ya yi tunanin kamar ya tashi ya koma gidan ya ba ta hakuri amman sai zuciyarsa mara kyan ta hana shi, sai yake ganin kamar shi za ta ba ma hakuri domin shi aka fi Saɓamawa da wannan tunanin ya sa ya kasa dawowa amman barcinsa rabi da rabi ne gabaɗaya sai yake jin sa kamar wani mai laifi, yana ji kamar ba shi da gaskiya sannan yana jinsan kamar wanda ya ɗauki wani irin nauyi mai girma a saman kansa.

  Uwa uba ga kallon da Inna ta yi masa a jiya nan yasan ba shi da bakin kare kan shi, sai kuma ya yi tunanin bai kyauta ba ya fara nadama sai wannan baƙar zuciyar tasa ta rinjayeshi ya ji kamar abin da ya aikata daidai ne, amman kwana ya yi da ya runtse ido sai ya ga Mimi ta na wannan kukan.
Da asuba ya kashe wayarsa saboda wata  zuciyarsa na zuga shi akan ya ɗaga waya ya kira wayar Mimi ya ji lafiyanta ita kuma wacce baƙar zuciyar nasa na nuna masa shi ne akan dai dai. Saboda kar ta  rinjayesa ya kira ne ya sa ya kashe wayar gaɓadaya.

  Ranar morning traning gare su sai dai ya wakilta Zinder ya tsaya da su, ya ce ba ya jin daɗi ɗakinsa dake cikin camp ya koma ya kwanta saman ƙaramin gadon yana faman tunani ya yi juyi ya fi sau goma amman Mimi ce a cikin ransa! Ko ya koma gidan ne ya ga halin da take ciki? Ko kuma ya kira ta a waya ne? Haka yake ta wannan tunanin sai ya ji kamar ya amince ya ta shi ya je ya ganta sai wata zuciyar ta ce"Me kake shirin aikatawa? Ai ba ka yi mata laifi ba duk abin daka faɗamata gaskiya ka faɗa."
"A'a na na yi mata ƙarya, na yi mata karyan cewa ba na sonta ahalin duk duniya duk wata macen bayan uwata da ƴan'uwana su biyo bayan Mimi a zuciyarsa duk saboda ita ne ya koma haka saboda tsananin kishinta da yake yi ne ya sa a tsawon shekarun zuciyarsa ta kasa zama cikin salama a baya yana da tabbacin in da ace Mimi wani ta aura ba shi ba, to ko bai mutu ba sai ya Ta ggayara.

  Duk yadda da ya so ya manta da abin da ya faru ya ƙasa, sai ya yi tunani ya bari ta huce, amman a ransa yata ta addu'an Allah ya sa ta daina kuka, sai kuma gefen zuciyarsa ta faɗa masa Inna za ta lallasheta sannan ga Walida ga matar Mu'azzam ya tabbata ba za su barta ta yi ta kuka ba.
Ya yi tunanin ko ya Kira Mu'azzam ne saboda halin da yake ciki a karon farko yana son ya tattauna da wani na kusa da shi
Amman sai ya ji ba zai iya yin wannan maganar da Mu'azzam ba, har gobe ƙaninsa ne kuma shi a ƙarami na ƙasa da shi yake kallon sa.

Duk wanda tunaninsa ya kawo masa sai ya ga ba haka ba ne. Daga karshe sai ya yi tunanin kiran Ahmad sai kuma ya fasa tuna ya yi nisa, kuma shi ba shi da wasu abokai bayan su, ko zamanin da ya yi karatu ban da gaisuwan nutumci har ya gama bai yarda ya yi aboki ba rayuwarsa kawai yake yi a bangaren kwallo ma sai da yaran dake ƙasan shi da Caach ɗin dake saman shi suma maganar aiki ce kawai a tsakaninsu ba shi da wani sakewa da nutane kuma a wannan halin yana son ya yi mgana da na kusa da shi wanda ya san shi sosai domin yana bukatar ya amsa masa wasu yan tambayoyi.

  Ya yi tunanin Makama sai ya ga bai san gidan shi ba sai dai gidan Nasir shima tunda da daɗewa lokacin ana ginin gidan suka je gidan  yanzu ma baya tunanin zai  iya gane gida. Duk da ya san iskancin Nasir amman a yanzu ba shi da mafita tunda yana bukatar shi. Jaket ɗin sa ya ɗauka da wayarsa sannan ya ɗora saman riga da wandon jikinsa ya dora P. cap a saman kansa, ya dauki key ɗin motarsa ya fice yana fita can haraban Studio din su ya nufa in da suke traning suna ganin shi suka bar abinda suke  yi s ka taso zuwa gaban shi suna kiran sunan shi da "Captain"
Cewa kawai ya yi su kula da kansu sannan in caach ya zo su faɗa masa ya ɗan fita amman ba zai daɗe ba.
Yana ma tunanin za su ba su hutun sati biyu su je gida tun da ƙarshen shekara ba su yi hutu ba saboda wasannin da suka yi ta bugawa.

  Bai yi tunanin zai ga ne gidan Nasir ba sai ga shi ya gane, a kofar gidan ya tsaya sannan ya kunna wayarsa ya lalubo lambar Nasir da ba zai iya tuna ranar karshe da ya kira shi da kansa ba ma ya doka masa kira.
Nasir na tare da matarsa Nafisa da ƴaƴansu suna karyawa wayarsa na gefen nafisa ta fara kukan ana kira sai ya ce ta ɗauko masa wayar lokaci ɗaya yana faɗin" Waye ne hala?
Ta kalli Screen din wayar lokaci ɗaya tana faɗin" Wai AJI..'"
Nasir ya dakata da cin buredin dake hannunsa lokaci ɗaya yana maimaita sunan.

"Aji.."

Da sauri ya karɓi wayar lokaci ɗaya yana miƙewa. Shafa wayar ya yi ya ɗaga kiran ya na mai karawa a kunnensa bakinsa da alamun cikar buredin da ya tusa.

"Nasir kana gida ne?

"Eh ina gida,."

  Nasir ya fada lokaci ɗaya bakinsa cike da abu, sai da ya ɗauki kofi ya kurbi tea ya wuce da shi dai dai lokacin da Aji ya ce" To ina kofar gidan ka."
Nasir ya zaro ido kafin ya ce"Kai ɗin? wani gidan? Ka yi ɓatan kai ne?

"Mallam ina jiran ka, kar  ka ɓatamin lokaci."

  Daga haka ya katse wayarsa, Nasir na jin haka bai koma kan datarsa dake faman tambayan shi ina zai je, bai juyo ba ya ce nan waje zai fita yanzu zai dawo.
Da sauri ya zura takalmi ya fita sai kofar guda mamakinsa ya kare da ya hangi motar Aji a fake sai ya riƙe baki a ranshi yana mai ɗimbin mamakin ganin Aji a fofar gidansa yau.



*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3002*

*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*


MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT

SHIN KINA DA LABARIN MACCE MAI GYARA DABAN TAKE GA ZUCIYA MIJIN TA, MUNA DA KAYAN MATA MASU ZAFI NA BUGAWA GA JARIDA

HAJIYA TA KUDI DA KUDI AKE NEMAN SU

INA MASU FAMA DA MATSALA RAMA BA GABA BA BAYA KINA ZAUNE ANA KWATANCI DAKE KINA CI BAKI KOSHI MUNA DA MAGUNGUNA DA ZUMA 3 IN 1 KIBA BRST HIPS TA CIKO MIKI KU INA KIYI FRESH MUNA DA KWAYOYI MUNA DA GARI DUK MASU CIKO JIKI NE KIYI DUM

INA MASU FAMA DA MATSALA BRST KU TSUHU YAFI SON YAGA NONO A TSAYE DUK MAI MAGANIN DA TACCE MIKI ZATA BAKI MAGANIN NONO KAI TSAYE YAYI MIKI KARYA CE MAGANIN BRST SAI KIN SHA ADADIN WANDA ZAI MIKI SBD DUK CIKIN GYARAN JIKI NA BRST YAFI WAHALA YI

INA MASU FAMA DA MATSALA SANYI MUNA DA MAGANIN SANYI ORIGINAL

INA MASU ZAMAN BANZA BABU SANA'A KINA KONE DATA KI GA BANZA WURIN TSEGUMIN KALLON STATUS DIN WASU GA DAMA TAZU MUNA HAR GIDA GA WAYAR HANNUN KI KI MALLAKE MOTA MILLION 8 HAR FIYE GA ALBASHI GA RIBA GA KYAUTA KAYAYA KI
08066726866.

Mamaki ya hana Nasir ƙarisawa kusa da motar Aji,  ya yi tsaye kawai yana kallon motar cikin tsananin mamakin ganin Aji  wai a ƙofar gidan shi yau.
Shi kuma Aji yana daga cikin motarsa abin duniya duk ya dame shi, tagumi ya yi fa abin da ya daɗe bai yi sai ga shi yau ya jinginar da kansa a jikin Kujeren da yake zaune ta bangaren direba amman fa ya zabga uban tagumi kallo ɗaya za ka yi masa kasan ya na cikin damuwa.
Bai ma san fitowar Nasir ba sai da ya sauke Ajiyar Zuciya ya waiwaya yana kallon kofar gidan Nasir ɗin sannan ne ya hango shi a tsaye ya harɗe hannayensa a kirjinsa yana bin motar na shi da kallo.

  Ƙaramin tsaki Mansoor ya ja, sannan ya danna ma Nasir hon har sau uku sannan ya ga ya fara takowa zuwa wajen sa, yana zuwa ya buɗe masa bangaren mai zaman banza lokaci ɗaya ya na faɗin" Ka shigo ciki."
Nasir ya leƙo yana faɗin" Na ɗauka za ka shiga cikin gida ne?
Aji ya yamutsa fuska cikin yar damuwa kafin ya ce" Cikin Ina? Malam ka shigo mgana na zo mu yi, me kuma zai kai ni shiga gidan matan aure ina magidanci?
Dariya ta kama Nasir domin a yadda Aji ya saka kalmar magidancin har yana wani gyara zama.
Shiga motar ya yi ya zauna lokaci ɗaya yana rufewa, Aji yake kallo wanda ya yi shuru kawai hannunsa guda ɗaya ya tare bakin sa.

"Ran Ajin Jihata ya daɗe wani abu ne ya faru?

  Ya faɗa lokaci ɗaya yana nazarin Ajin domin zai iya cewa ya daɗe bai gansa cikin yanayin sanyin jiki irin na yau ba. Shi ya sa yake ta kallonsa Aji kuma ya rasa ta ina zai fara sai faman sakin huci yake yi shi kaɗai.
Nasir ya gaji da zaman jiran shi sai kawai ya ce" Ni fa kaga zan koma cikin gida, karyawa nake yi da iyalai

2 / 49