Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
Kuma da ta dawo ko a zencen ba ta taɓa faɗan cewa Mommy ce ta yi aure ba.
Ko Inna ba ta gaya mawa ba ta kuma san Aji ba shi da surutu daman dai Mu'azzam ne, Rukky dai ta samu labari ta bangaren Jaheed da ta kira ta ta na tambayanta ashe kuma Mommy ta yi aure sai kawai ta ce"Uhm" daga nan ta sauya mganar har Rukky dai ta gano Mimi ba ta son mganar. sannan da kanta ta kira su khadi ta na gaya musu abin da ya faru sanda Alƙali ya zo tana gaya musu Mommy ta ba shi labarin kowa ya san shi ya sunan sunan shi.
Madiha bakin ciki kamar ta mutu sai ta ce" Wai mommy yarinya ce? Ji fa wannan aikin da take yi mtswww.."
Ta yi tsaki duk suka ƙara saka Mimi a tafiyarsu na ba su amince da auran ba shi ya sa ko da ta dawo ko sau ɗaya ba ta kira Mommyn ba sai ita ce ta kirata tana cewa ba ta kira ta ba kada bakin Mimi sai ta ce"Ina zan kira na takura miki Mommy, na baki lokaci ne ki ci amarcin ki.'
Mommy sai ta kasa mgana jiki a sanyaye ta ce"Ke ma kin kasa fahimtata ko Fatima.?
Da Sauri Mimi ta ce"Na fahimta kina son aure kuma kin yi, Allah ya ba da zaman lafiya. Daga nan ta kashe wayarta daga ranar ba ta ƙara nemanta ba, itama Mommy sai ta ba ma zuciyarta haƙuri ta tsaya ganin in da suka dosa. Matar alƙali da yayansa sun karɓeta sosai sai ita ce ke da yayan da ke yi mata barazana in ka cire Sulaiman Asma'u sai murna take yi ta samu Abba amman ban da su Madiha da suke kishin Abi sannan suna ganin kamar abun kunya ne.
Hibba ta saamu labarin auran da Mommy ta yi ta bakin Jawahir tunda sanadin Mimin suna zumunci ta je gidan shi ne ana hira labari ya kawo ta faɗa mata, tana komawa kuma ta faɗama mijinta shi kuma sai ya xe bai ji ba, bayan ya kira yayanshi ya tambayeshi sai ya ce eh da gaske ne. Ke Hibba sai ki ka ga Mimi a chart sai kika ce mata" Matar Yaya ashe kuma Mommy ta yi aure? Allah ya sanya alheri."
Sai ta tura emojin dariya har da na rawa, wannan abun Mimi ta gani sai ranta ya ɓaci kawai sai ta yi ma Hibba vioce da cewa miye take mata dariya saboda Mommy ta yi aure? Abun dariya ne ya faru da za ta riƙa mata dariya? Tun Hibba na ganin wasa har Mimi ta maida mgana faɗa ta kira Hibba a waya tana gaya mata mganganu marasa daɗi har tana faɗin in abun dariya ne to ta bari in nata Baban ya rasu mamanta ta sake wani auren za ta yi mata dariya ta ji in da daɗi. Ran Hibba ya ɓaci sukavyi ta gayama juna mgana ita da Mimi a ka rabu ba daɗi har da su blocking ɗin juna.
Hibba ta nata kuka haka Mu'azzam ya dawo ya ssme ta da ya tambayi ba'asi sai ta gaya masa abin da ya faru tun farko sannan ta kunna masa Vioce ɗin Mimi da wayar da su ka yi domin ta yi recording abun dai duk ba daɗi ya yi ma Hibba faɗa me ya sa ba ta ba ta hakuri ba? Ita kuma sai ta ce ita fatan alheri ta yi ba na tsiya ba, saboda dai a kashe mgana ya sa ya kira Mimi da kansa domin ya ba ta hakuri shima ta shafe su ba ta ɗaga wayarsa ba sai ya kira Inna Meri ya gaya mata abin da ya faru, ta ce itama ba ta ma san Mommyn ta sake aure ba tun da daga Binta har Mansoor ba wanda ya faɗa mata sai ta ce ya bar mganar a hannunta Mansoor shi zai kashe wannan fitinar.
Ta fahimci Binta dai tana kishin Babanta ba ta so auran Mommy ba. Shi ya sa duk rayuwaka suka ɓaci itama kuma Hibba ta na ganin ba wani abu ta faɗa ba sai a ka kasa samun fahimtar juna gabaɗaya.
Inna Meri da kanta ta kira Mansoor ta faɗa masa abin da ke faruwa ta ƙara da cewa" Ba ina goyon bayan Hibbatu ba ne, amman zencen gaskiya ta fi matarka gaskiya saboda ita ba ta san abin da ke faruwa ta yi mata fatan alheri, daga karshe sun kasa fahintar juna har abubuwa suka lalace, na so na je na bata hakuri amman sai na yi tunanin ba hurumina ba ne tunda ba ta gaya min ba, ba na so a fara samun baraka daga matayenku saboda in hakan tana faruwa wata rana kuma ɓaraka za ta iya bayyana daga bangaren ku, kai ka yi ma Binta mgana ka fahimtar da ita shima Mu'azzamu na gaya masa ya fahimtar da matarsa in an samu daidaito sai su kira juna Hibba ta ba ma Binta hakuri magana ta wuce."
Sai Aji ya ce cikin satin nan zai zo gida zai yi mgana da Mimin shi ya ɗauka Fatima na da tunani ashe dai da sauranta.
Mu'azzam suna waya amman bai gaya masa ba. Sannan ko Walida da ke gidan ta kwana ta tashi ba ta san wani abu ya faru, sai ya bari kawai sai ya dawo gidan ya samu lokacin da zai yi ma Mimin faɗa sosai ko ta dawo cikin hayyacinta ya je ma ya kara ganin Mommy tana hawaye ta na gaya masa duka yaran sun juya mata baya harda Mimi sannan ta hada shi da Alƙali har ga Allah bai ga illan shi ba, kamili mai mutumci sun samu uba amman suna haukan banza.
Ranar jumma'a ya dira gombe, ko a fuska bai nuna ma Mimi wani abu sai da ta gama bikin tarbansa bayan ya yi wanka ya ci abinci ya so ya yi mata mgana amman sai kewarta ta hana shi a ka kwana ba ma juna Soyayya da asuba ya tafi masallaci bayan ya dawo ya koma barci asabar ne ba ta fita aiki bai tashi ba sai goma na safe yana fita falo ya iske ta, tana goge goge ga Ummi saman kujera an jinginar da ita alamun an fara Koya mata zama. Ita kuma matar gidan tana ta gogen tibi wayarta na saman kujera ta saka speaker suna mgana da Madiha abun da kunnuwansa suka jiye masa shi ne Madihan na cewa" Ni fa na gayama Khadi in har Mommy na son mu sai dai ta zaɓa ko auran ta ko mu."
Mimi ta ce",Wlh nima fa ko kiranta ban sake yi ba, in har tana son mu sai ta zaɓa ko wannan mijin ko mu ƴayanta."
Yana tsaye ya ji Madiha na zuga Mimi da kada ta ƙara kiranta ta bar ta in suna da amfani za ta neme su.
Saboda haushi ko Mimi ba ta san ya shigo falon sai da ta ji muryansa yana faɗin" Ko shekara ɗari ta yi ba ta neme ku ba, ba abin da zai sameta amman ku sami ko wata uku kuka yi ba ku neme ba ta tsinuwan Allah da ta mala'iku sai ta tabbata a kan ku, sannan ku sani ita ce ta haifeku ba ku ne kuka haifeta ba, aure ta yi ba zaman zina take yi ba, ko da saka albarkan ku ko babu za ta zauna lafiya.Ku ne in ba ta yafe muku ba ku ke cikin bala'i da masifa, sannan zan miki gargaɗi na karshe in har ba alheri za ki kira matata ki gaya mata ba, to don Allah kada ki sake kiranta ina son ta samu rabauta a duniya sennan ta samu lahira ke da kika juya ma Albarka baya je ki ki yi ta fushin ki ki jira ranar da mahaifiyarki za ta zabi sunnar ma'aiki a kan ki, ga ki kamar mai hankali maimakon ki zama jagoran ƙannen ki wajen faɗa musu gaskiya sai ke ce ke ƙara zugasu kuna kauce hanya, girman banza gareki sannan takmar ilimin ki bai yi miki wani amfani ba, ki je can ki yi ta sakarcin ki amman na gaya miki wlh tallahi ka da ki kara kiran matata kina zugata."
Yana gama faɗin haka ya kashe wayar, Mimi ta dankare a tsaye tana kallon Aji cikin mamakin manya manyan kalaman da mijinta ya sauke ma yayarta, ta buɗe baki za ta yi mgana itama ya ɗaga mata hannu ya fara zazaga mata nata faɗan tas ya yi mata sai ta fara kuka tana faɗin" To koma menene sai ka gaya ma yayata mganganu haka? Kai tsaye yavce" An gaya mata in kuma za ki rama mata ne, bismillah ina ruwana da girmanta tunda girmanta bai mata amfani ba,.Mahaifiyarku ce fa amman saboda rashin tunani kuna neman saɓa mata saboda haukan banza in ba'a aure za'a haifeta? Ita ba tana gidan Mijinta ba ne? Sai ta hana ta auren ita? Ba ku da adalci ba ku ba yara ƙanana ba amman kuma kuna yin abin da ko yara suka yi sai an yi mamaki, har saboda haka Hibba ta yi miki murna ki ka bi ta da zagi saboda ke kin isa ina laifin wanda abun alheri ya same ka yace maka Allah ya sanya alheri? Sai ki zage ta?
Mimi na kuka wiwi ta ce" Ni fa ban zageta ba, ita ce ta min dariya to abun dariya ne?
Shima ya taso mata da cewa to abin kuka ne, ko so take yi ta ta ya ta haukan da take yi na faɗa da mahaifiyanta saboda ta yi aure. Mimi duk yadda ta so kare kanta Aji bai ba ta dama ba, ya yi mata faɗa sosai ya kuma bar ta, tana kuka ya ɗauki Ummi suka shige ɗaki ranar gidan yini ya yi ba daɗi ko abun kari ba ta yi ba ta shige ɗaki tana kuka shi kuma ya ɗauki ƴarsa suka fita zuwa gidan Inna ya karya ita kuma Inna ta yi ma Ummi wanka tunda Aji cewa ya yi Mimin ba ta jin daɗi.
Saboda nono ne ya sa ya maida Ummi gidan a mamakinsa sai ya ga Mimin ta tashi har ta yi abinci ta gyara gidan,ganin haka ya sa bai sake fita ba ya zauna ya na ƙara mata da nasiha, ita kuma ta baahi hakuri ta ce za ta,kira Mommy ta ba ta hakuri ita da Hibba.
A gabansa ta kira Mommy ta ba ta hakuri, Mommy kamar ta yi kuka farinciki ya cika ta, ta yi ta sakama Mimin albarka tana faɗin" Wlh Allah saboda ku na yi wanman auran saboda na kare muku mutumcin ku da na ƴayan ku." Mimi na hawaye tace"Hakane mommy ki yi hakuri, In sha Allahu ba zan kara ba suma su khadi duk za su daina." Mommy tace bakomai ita ba ta rike su ba ta yafe musu tun kafin ma su roke ta
Haka ta kira wayar Hibba bayan ta cire ta a blaklist ta ba ta hakuri itama ta ba ta hakuri shike nan sai mgana ta wuce. Amman fa Madiha sako ta turama Mimin da cewa ta gode tunda ta ba da damar da Mijinta ya zage ta har Dr ta kira ta gaya mawa shi kuma ya ce abunda Mansoor ɗin ya yi daidai nw in ita ba ta da hankali sai ta yi ta yi,Khadi ma ta kira Mimin ta mata surutun ta zaɓi namiji a kan su ƴan'uwanta tunda a gabanta ya zagi Madiha ta kasa mgana ita dai sai hakuri ta ba su, tunda ko ita ba ta tsira da faɗan ba kuma suna nan a kan bakansu na ba su som auren. Sai ga shi wata ɗaya da wani abu da auran mommy Khadi ta samu matsala da dangin mijinta sai ga ta gaban Mommy tana kuka, Mommy ita ta kira mijin khadi ya zo har gida suka yi mgan matsalace ta gida yayyensa ne suke son ya kara aure, karshen dai Alkalin da suka raina suke jin haushi ya tsaya mata tare da Mommy dashi suka maida ta kaduna suka kuma nuna ma mijinta ba ruwan Khadi da auransa amman ya kare mutumcin matarsa tunda yayyen nasa har gida suke zuwa su ci zarafinta, tun daga nan Khadi ta saduda itama Madihan ganin ba ta da abokin adawa yavsa ta fara saki amman ba duka ba. To ta na da wacce tafi Mommyn ne? itama Madihan kuɗi ya hado su da Mijinta tunda Kuɗin na su a waje ɗaya ne suna kasuwanci ti shekara ta yi kuma an zauna ana ta lissafi an gano dai shima yana karkatar da wasu kuɗi rigima har Abuja wajen Mommy. Sai ga shi Alkali Mustapha shi ya warware matsalan a ka samu sulhu, itama daga nan ta fahimci aure ga mace sutura ne komai tsufanta kuwa, ta saki suka rumgume alƙali a matsayin uba sannan akwai yarsa Batula dake aure a lagos Lakcara ce a Legal ya haɗa su suna zumumci itama Khadi akwai namiji a kaduna yana aiki da NNPC Shima tare da iyalansa sun zama ƴan'uwa tare da Khadija
akwai wacce ke kano, sunanta Badiyya likitan yara ce ashe ma asibiti ɗaya suke aiki da Sulaiman ya san ta ta san shi sai wannan dalilin ne zumuncin su ya ƙara zama na sosai Iyalanta na zuwa gidansa shima iyalansa na zuwa, ɗayan namijin Soja ne yana Abiya tare da iyalansa amman suna mgana a waya dukkansu.
Bayan wannan ya wuce an samu daidaito zukata kuma sun samu natsuwa sai Mimi ta kara bijiro da mganar ta na son siya wata sabuwar Motar, Aji dai da ta nemi shawaransa cewa ya yi" Ni tun a baya na baki shawara,sannan na yi miki alƙwarin in na samu kuɗi da gumina zan siya miki mota amman na ga kamar kina sauri ne bazan hana ki siya ba tunda kuɗin ki ne amman da kin hakura da siyan wata motan ki cigaba da lallaba taki, ga tawa ma duk ki haɗa ki riƙa amfani da ita, in har Allah ya hore mana ko Jirgi ki ke so zan iya siya miki Mimi ba ma mota, gwara ki fara ko wani kasuwanci ne da kudin kamar zai fi,amman in ba ki ji shawarata ba shike nan ba zan hanaki yin yadda kike so da kuɗin ki ba."
Da ta yi mgana da Mommy da Hajiya suma dai shawaran da suka bata kenan sai ta amince da shawaran ta fara kasuwanci amman ta rasa ina zata fara tunda ba ta da Ra'ayi ko ido a kan kasuwanci da ta yi mgana da Aji sai ya ba ta shawaran ta yi mgana da Yayarta Madiha ai yar kasuwa ce za ta ba ta shawarwari amman shi da ita sun tsaida shawaran ta fara kasuwancin saida Abayoyo da jaka da takalmi in ta karɓu har shago za ta iya buɗewa.
Ta yi mgana da Madiha kuma ta yi na'am da shawaran Mimi ta ce za'a riƙa mata Oder jakunkuna wasu daga Lagos wasu kuma daga China ko India ko Italia,dogayen rigunan kuma daga daga Dubai, tunda ita tana harka da yan kasuwa daga kasashen waje tuni ta haɗa Mimi da su har ta tura kuɗi za'a fara kawo mata kaya kaɗan ta jaraba ta gani. Tunda tana aiki tallatawa ba zai mata wahala ba In ji mijinta Mansoor Ibrahim Aji.
******
"Maryama(Ummi) na da wattani goma sha ɗaya a duniya Mimi ta samu wani cikin, kuma har ya yi wajen wattani biyu da kwanaki a jikinta ba ta sani ba, kamar na Ummi ne, shima bai zo da laulayi ba in da ma ta fahimta ta na yawan ganin jiri da tashin zuciya sannan aiki kaɗan sai ta ji ta gaji kasala duk ya rufeta sannan sai ta fara,kwana da zazzabi mai zafi lokacin Mansoor Aji ba sa nan ya fita wasan shi na farko a kasar Ghana, amman ya bubbuga wasu anan Nageria ƙaananun wasanni wannan ne dai suka tafi wata kasa buga wasan.
Ba ta gaya mai ba ta da lafiya ba ta shirya ta je asibiti domin tafara zargin ciki gare ta sai ga shi gwajin farko a ka gani ciki ɗan wattani biyu da kwanaki a cikin jininta. Hankalinta ya yi bala'in ta shi Ummi ba ta shekara ba amman ta yi yawo tana tafiyanta da kafarta ko'ina amman ita ba ta shirya kara haihuwa ba shirye shiryen komawa makaranta ma take domin yin Phd ɗinta tunda yanzu alhandulillah komai na duniyan ta samu, miji nagari sannan ta samu kuɗi tunda Allah ya saka ma kasuwancinta albarka Odar kusan na goma kenan kuma tana samun ciniki da sun iso da sun ƙare. Sannan Hibba na sara acan kano kuma ta na aikawa da shi Abuja Asma'u na tallata mata ta Online anan ma Gombe sai gqmdala tunda gidan Talabijin ɗinsu ta ba ta dama ta tallata kayanta Shike nan da ta kawo oder suke ƙarewa musamman ma abayoyin. Sannan Rukkya ma ta na saran Abayoyin ta na siyarwa tunda zaman ko me ka taka ba zai yuyu ba ita mace da sana'a a ka santa domin cigabanta. Duk da ta koma can lagos ɗin tana aikinta a wani gidan Talabijin amman duk da haka ta ce itama za ta fara kasuwancinta amman sai ta samu jari mai ƙarfi.
Duk da ba ta yi mgana da gogan nata kan maganar cigaban karatun nata ba amman ta saka a ranta za ta matsa masa sai ya barta tunda dai ba mazauni ba ne,sai ya yi wata biyu ba shi a Gombe ballantana yanzu da aka fara haskashi a duniya ba ma ƙasa ba, shiyasa ta yi tunanin ijiye aiki ta koma makaranta duk da tana da tabbacin mijinta ba shi da ra'ayin ya maida ta Abuja da zama a kusa da shi ya sha faɗa mata a Gombe za ta cigaba da zama ba wai don baya bukatar ta acan ba a'a sai saboda Inna in ya koma Abuja da zama