Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
zai zama sai bayan wasu wattani za ta ganshi kamar Mu'azzan kenan. Shi kuma baya son haka ba ta da kowa sai su ba zai yuyu in har Mu'azzam na kano shi kuma ya bar Gombe ba, saboda Iyalansa ya san a kai a kai zai riƙa zuwa Gombe ba kuma ita saboda aikinta ba sai saboda wannan dalilin na shi, da kuma dalilin ba ya son barin garin Gombe saboda yana son garin kamar yadda itama Gombe ta zame mata wani jigo a rayuwarta ba tun yanzu ba tun tana ƙarama take ƙaunar garin.
Bta dawo gida cikin tashin hankali, ko wasan su Aji da aka haska a tashar Rt Tv ta dai kallah ne amman hankalinta baya wajen sai daga baya ta fahimci Nageria ita taci ghana da ci biyu da ɗaya. A Daran Khadi ta kira ta tana mata murna ta ce suna ma kallo ne sannan Rukky ma sun yi mgana ta ce sun kallah jar da Daddy shima da Mommy sun kalli wasan na shi,a gida kuma Inna ma ta kalla tunda Walida na gari ta zo gida hutu, ita duk ba wannan ne damuwanta ba ya za ta yi da cikin jikinta? Sun kuma kasa samun lokacin su yi mgana ta waya sai dole ta yi hakuri suka dawo daga Ghana ya zo Gombe sannan ta gaya masa ga halin da take ciki ya fara murna kamar zai goyata cikin taruwan hawaye ta ce" Ummi fa ko shekara ba ta yi ba Baban Maryam? Sai ya kalleta kafin ya ce"Shi ne me? Ummi ai ta girma ta na tafiyanta ko'ina ina waɗanda ke samun ciki bayan sun yi arba'in ma? Amman ke nan da kafin ki sauka Ummi ta kusa shekara biyu ba na son wannan koke koken naki, daga Allah ya baki kyauta sai kuma ki fara min kuka?
Cikin hawaye ta ce"Ni ina tsoron haihuwan ne kai da kai ne sai ka ga ba lokacin ma da za ka iya ma yaranka tarbiya."
Kai tsaye yvace"Ba ruwanki da wannan tarbiya ta Allah ce duk da ke ma da naki kokarin amman ni nasan tarbiyan ƴayan da zamu haifa ba za su gagaremu ba, Sannan in mganar halin rayuwa ce daman ita kan saka a guji haihuwa ma gabaɗaya Fatima Allah ya rufamin asiri ba ma ke da yayan da Allah zai bani ba, ina ɗaukan nauyin mahaifiyata da ƴan'uwana saboda haka duk abin da kike tunanin ma ba zai faru ba ba zai faru ba, in sha Allahu. Abun damuwar kawai lafiyan ki da ta Ummi za mu je asibiti mu yi mgana da likita sai ya bamu shawara ko? Mimi dai ta kasa mgana sai kuka, shi ya share mata hawaye ya rumgumeta yana lallashinta ga shi ta na so ta ce so take ta koma makaranta amman ba ta samu wannan damar ba.
Washegari tun safe suka tafi asibitin da ta ke zuwa, suka samu likitan da mganar Ummi da lafiyan Mimi nan da nan ya ba su shawara ya ce bakomai. Za ta cigaba da shayar da Ummi har sai cikinta ya kai wattani biyar sai ta yaye ta tunda dai akwai rufin asiri Ummi ba za ta wani samu matsala in dai za ta samu abinci mai rai da lafiya da zai gina mata jiki ita da Mimin gabaɗaya, nan ta ke Aji ya ce ya yi alƙawarin sai in da karfin sa ya kare sun baro asibitin bayan ya rubuta ma Mimi maganganun karin jini saboda cikin jikinta tare dan ƴan dokokin daza ta kiyaye kaɗan ba ma su yawa ba, suna hanyar komawa gida Mimi ta roƙi Aji da Allah da Annabi kada ya yi tallar ta na da ciki kamar yadda ya yi da ita a cikin Ummi ganin ta damu ya sa ya ce ba zai gaya ba amman in har aka tambaye shi zai faɗi gaskiyansa ta ce ta ji kuma ta amince.
Har ya koma Abuja yana lallaɓa Mimi ganin duk ta damu,amman har ya koma sai a hankali ba ta wani saki ba fahimtar haka yasa ya ce in ta samu sarari ta ziyarci Hajiya da gidan yaddiko da duk in da take son zuwa kila ko shiga mutane zai rage mata damuwa kamar ko ya sani fita mutanen da ta yi yasa sai damuwanta ta ragu sannan iya bakin ƙokarinta Mimi ta ɓoye cikin jikinta. Ita ce har gidan Nasir da Makama su rana ɗaya ta je musu ranar lahadi tunda ba ta da shiga wajen aiki ranar, kuma in ta dawo daga wajen aiki ta kan sauka gidan Hajiya ko Inna, ko sun gane tana da ciki ko ba su gane ba Oho ba dai wanda ya yi mata wata mgana, amman abin da ba ta sani ba daga Hajiya har Inna Meri sun fahimci Bintar ciki gare ta. Sannan yaddiko ma ta gane lokacin da ta je gaisheta sai da ta ce"Ai yanzu kya yaye wannan katuwar yarinya ko kina so ko bakya so."
Ita ba ta gane ba, saboda Yaddiko ta sha mata tsiyan girman jikin Ummi ya yi yawa ya kamata ta yayeta in ta shekara ko da wattani ne ita kuma ta ce sai ta kai wa'adi, ko da ta yi mata mganar har a cikin ranta ba ta kawo ta fahimci wani abu ba ne.
Ita a tunaninta ba wanda ya sani sai dai in ya fito a ganshi.
Cikin ta na shiga wata biyar ta cire Ummi a Nono, saboda ma kada kowa ya fahimci wani abu ta kasa kaita gidan kowa da sunan ya ye,sai babanta ne da ya dawo ya kwashi kayanta ya kai ma Inna da ya dawo ta tambayesa me Inna ta ce? Kai tsaye ya ce"Ta tambayeni dalilin yaye Ummi ni kuma nace ciki gare ki."
Ai sai Mimi ta saka masa kuka kamar ya daketa ya fara fahimtar wannan cikin mai son rigima ne mgana kaɗan ko a waya ne sai ta fashe masa da kuka, tunda ya fahimci yanayinta sai ya koma lallashinta har suka rabu lafiya.
Cikin uan'uwa Mimi ba wanda ya san tana da ciki sai yan Gombe ne da ya fito suka gani, Ita Mommy ta zo garin ta ga Mimi da ciki a gaba ta kama baki, suma yan'uwan Aji haka suka ganta da shi abun Allah kuma lokaci ɗaya ita da Bintu suna da tsohon ciki sannan itama Mariya na da ciki irin wanda ana zuwa a ke tutuɓe da shi a kofar ɗaki, kuma shima wannan cikin tun da wuri suka gama siyan komai Bintu ta rigata haihuwa An yi suna da kwana uku Mimi ta haihu, ta na fara jin naguda ta haɗa kayan haihuwa zuwa asibitin da take awon ta sannan ta kira inna ta faɗa mata sannan ta kira Hajiya kafin ma su zo ta na ɗakin haihuwa , wannan haihuwar dai ta ɗan sha wahala sai la'asar ta sauka wannan karon Namiji ta haifa baki mai kama da uban sak.
Kwana ɗaya ta yi a asibitin suka maida ta gida, Aji sai dai ya ga hoton Baby boy da Mimi ta ɗauki hoto ta tura masa, Ya yi farinciki sannan ya yi godiya ga Allah jin Mimin tana lafiya tun da aka faɗa masa namiji a ka haifa Ya raɗa masa suna IBRAHIM, ita kuma Mimi ta na murnan a saka mata sunan Abi sai da ya dawo ta ji yana faɗin ya yi ma Jariri huɗuba da Ibrahiim,abun na ranta ya sa sai da ta furta masa shi kuma ya ce ai haihuwa yanzu suka fara ta yi kokari nan da wattani kaɗan ta kara samun ciki sai ta haifi Baban nata, Murgaɗa masa baki ta yi ba tare da ta yi masa mgana ba ganin kamar da gayya yake mata mganar, su khadi sai dai suka zo suna suna mai cike da mamakin daman Mimi ciki ne da ita? Shi ne ba su taɓa sani ba Mommy ce kuma da Hajiya su kuma ba su yi mganar da kowa ba, ko Rukky a bakin Aisha Ta Karamchi ta ji Mimi na da ciki ta kirata tana mata tsiya ta samu zuwa suna tunda daman wannan shi ne karon farkonta na zuwa ganin gida.
Shima a sunan Ibrahim wanda za'a riƙa ma alkunya da Babangida, an yi abubuwa sosai kamar na sunan Ummi ma sha Allah, a haihuwan Babangida Aji ya siyama Mimi danƙareriyar sarka gold mai tsada a matsayin tukwaicinta. Sannan ya ce itama mota za ta biyo baya da yardan Allah. Mimi ta ji daɗin wannan kyautar sosai haka ta riƙa nuna ma mutane cikin jin daɗi. Haka dai mimi ta cigaba da jegonta wannan karon Baba uwani ne ta zauna da ita na sati biyu sai ta koma gidan Hajiya ita kuma daman ta iya ta cigaba da Kula da kanta da ƴayanta. Miji kuma sai dai su yi mgana ta waya Aji na neman ya ɓace ma ganinta saboda yanzu duniya ce ta san shi ba jiha ko ƙasa ba.
Mimi na kula da yayanta gefe ɗaya kuma ta na kula da kasuwancin ta da yanzu sai habaka yake yi, Aji kuma na can Abuja sai ya samu lokaci zai zo ya ganta amman fa komai na bukatar rayuwa ya tanadar musu ba abunda take nema ta rasa kuɗin ta kuma suna account ɗin ta. Ba abunda ta ke siya in ba kyauta za ta yi ba,ko ta ga wani abun ta ke so za ta siya ko za ta siya ma yayanta.
Rayuwrta take yi cikin kwanciyar hankali tun tana damuwa na rashin Aji a kusa da su ne har ta fara sabawa tunda ga ƴanuwa lulluɓe da su, ta gama arba'in ɗin Babangida Mariya ta haihu suka sha suna, Ta samu namiji an saka sunan baban mijinta Ahmad, Walida kuma tana kano sai sun samu hutu ta kan zo gida, Inna kuma daman ta saba zama ita kaɗai in kuma tafiya ta kamata ta rufe gida ta je ta yi zumuncinta, ko kuma wani lokacin yaran su Bintu na gidan suna ɗeɓeta mata kewa. Amman Ummi kan sai dai in tare da Mimin suka je gidan Aji ba mutum ba ne da kan bar yaransa su je wani waje hutu ba, ko da gidan Inna kwana in ya wuce ɗaya zuwa biyu sanda ta fi sati ma lokacin da ta yaye sati biyu ta yi da kansa bayan ya dawo ya je ya ɗaukota zuwa gida. Shi ba shi da ra'ayin irin haka ba wai domin yana da wani dalili ba ne.
******
*BAYAN SHEKARU SHIDDA*
Bayan shuɗewar wasu shekaru kamar shidda. A ya yinda Mimi da Aji suke da shekaru goma da aure ƴaƴan su biyar Tunda Mimi haihuwan kusa kusa take yi bayan Babangida ta kara samun mace sai taci sunan Mommy, suna kiran ta da Batul,sannan ta kara yin mace mai sunanta sunan Hajiya kuma wato Fatima suna kiranta Fati ba sa mata alkunya, sai ƙaramin su mai sunan Mu'azzam shima ba sa masa alkunya, duka cikin shekaru goma Mimi ta haifi waɗanan Zzaratan ƴayan nata, tare da gwarzon mijinta Best Nigerian player Mansoor ibrahim Aji wanda ya shahara ya samu ɗaukaka ba iya kasar mu ta Nageria ba, ya kutsa kasaahen ketare sun buga wasa manyan kasaahen duniya ma sun kutsa sun buga cikin kwararun manyan yan wasan kwallon kafa, kama daga manyan manyan kungiyoyin kwallon kafa na kasashen ketare sun yi wasa da su. Sannan sun ta kawo masa hari domin hayarsa ya koma turai buga wasa ya ce har Abada shi sunan shi Aji Ajin kasar ne shi ba Ajin turawa ba, shiyasa an kasa siyan shi ballantana ya bar kasar sa ya koma wata ƙasa.
Sun buga easa tun daga Nation Cup da sauran manyan mamyan wasanin FIFA, a yanzu a kungiyar kwallon kafa ta ƙasa mai suna Super Ealges ba kamar ɗan wasa irin Mansoor Aji, tunda sannanun duk sun yi ritaya su Ahmad Musa, shi ne kuma ke rike da muƙamin Captain da ya samu wannan matsayin saboda shin ɗin Dodo ne a Filin wasa sannan ƙwararra ne wanda ya samu kyakyaawan ƙwarewa. A yanzu a Nageria Mansoor Ibrahim Aji ne fitattacen ɗan wasan kwallon kafa da ke kan gaba da kowa cikin shekaru kusan ashirin da ya kwashe ya na buga ƙwallo ya na da shekaru arba'in da huɗu a yanzu amman sai kace ɗan shekara talatin ne saboda hutu da jin daɗi da kuɗin da suka zauna masa, Mansoor Aji ya na da kuɗi da bai san iyaka ba, kwallo yake yi kuma ita ta raa masa. Duniya ce ta san shi ta dalilin kwallo ya taka kasaahen da bai taɓa tunani ba sannan ya buga wasanni da ƴan kwallon da a baya sai dai ya gansu a hoto.
Bya samu cigaba sosai acikin shekara shiddan nan da ta gabata ya kai Baba Makka har da Magajiya ta je ta sauke farali, Sannan gidan wanzamai a garin gombe da ke anguwan arawa in kasan gidan a baya a yanzu in ka so ba za ka gane gidan ba, an buge shi an gyara shi zuwa na zamani har da katon get. bangaren Magajiya an haɗe mata har da in da Maeesha ta tashi a ka mata flat mai girma sannan itama Maeeshan can bangaren an haɗe mata na in da Inna ta tashi ya zama Flat mai girma sannan kuna bangaren su Gaje man an maida shi na zamani sai wanda ya gani, gidan ya fita dabam a anguwa saboda kyan shi sannan ya gyara masallacin kusa da su an yi masa bene ya koma na zamani, sannan matasa anguwa da sauran jama'a ya na taimakon su daidai gwargwardo ba ma iya anguwansu ba kaf kafatin Gombe da kewayenta suna alfahari da samun zaƙwaƙuri daga jihar su. Har can gidansu na mallam Sidi ya gyara ya maida shi na zamani Yalwa dai an gama jinya an koma ga Allah ya ba ma Baba karimu jari mai kauri yana kasuwanci.
Inna kuma ta je saudiya sau biyu sannan ta je Umra, Mu'azzam ya samu karin girma an sake cilla shi kaduna shima yayansa uku, su Bintu kuma dukkansu suna cikin rayuwa mai kyau, Aji ya ba ma kowacce jari suna kasuwanci, Auwalu kuma ya zama babban Enginer har gidan kansa ya yi shi kuma Saddiqu na zama a shagon da Mimi ta buɗe na Abaya da Takalma da Jaka mai suna MIAJ STORE shima yana saida jallabiyan maza da huluna ba ta masa mugunta yana samu sosai ya na rufa ma kansa asiri. Aji ya siya mata sabuwar motar ya yi mai kyau sannan ya siya ta yara wacce ake kai su makaranta har Inna ya siya mata mota ya kuma ɗaukan mata direban da zai riƙa zirga zirga da ita, tsohuwar motarsa kuma ya ba ma Baba ita, mashin ɗin kuma aka siyar sai a siya ma baba Danlami da Baba Sani sabbi suna hawan su, babu wanda Aji bai taimaka ba adanginsu ba, Mu'azzam ma yana iya bakin ƙokarin shi. Tunda bai kai Aji samu ba shi da a wata yana samun sama da Miliyan albashinsa( ba ƙarya ba yan kwallo suna samun mahaukata kuɗi balle shi Aji da kasa ke alfahari da shi).
Gidan gwammatin Gombe ba ya da shamakin shiga haka ma can Villa a garin Abuja, sannan ya zo ya na taimakon Gombe United camp din su, su zinder suma duk sun samu cigaba sai wasu ne eake cigaba da rain sannan har Coach ɗin su bai manta da shi ba alheri daidai gwardo yana yi masa. Shi dai burinsa matasa su cika burinsu, har Team na shi na musamman ya kirkira daga anguwan Arawa mai suna M.I AJI ARAWA TEAM, jaririya ce horar da matasa ake yi masu sha'awan ƙwallon kafa.
Kaf ƴayan nan huɗu a gombe Mimi ta haife su, sai karamin su ne Mu'azzam ta haife shi a garin Abuja ko da yaushe Aji na kan hanyar zuwa ya gansu ko kuma in sun samu hutu su je ita da yara, Inna ta gaji da zirga zirga ta zaunar da shi ta ce ta yafe masa ya ɗauki iyalansa zuwa in da ya e zaune domin Mu'azzam ne ya gaya mata abunda ya sa Ajin ya ƙi maida Mimin can Abuja gaɓadaya, lokacin daman an maida ta Editer a ma'aikatansu na karamchi ta daina karanta labarai Office gare ta duk ta dalilin Aji domin kishinsa bai ragu ba, sai ma abin da ya karu, dole ta ijiye aikinta ta tattara ita da yara suka koma Abuja gida kuma sai megadi tunda in suka zo garin nan suke sauka har Mu'azzam ma yanzu ya mallaki gida an garin Gombe. Su Nasir ma duk sun samu cigaban rayuwa, amman duk da haka Aji bai manta da su ba ana tare har yanzu kamar baya sun zama manyan mutane sun girma sun yi 6aƴa girma ya kama su shekaru sun ja, A shekaran da ta Mimi ta koma Abuja suka je suka yi aikin Hajji tare da Aji a kuma wannan lokacin tana karatunta na Phd ta online a wata jami'a a america sannan gefe ɗaya ga kasuwaancinta yanzu kai tsaye take oder kaya daga India ko Dubai.
Da kyakyawan takardunta da ƙwarewanta wajen aiki ta samu aiki a NTA Abuja matsayin News Editer again, burin Aji ya cika an daina nuno fuskarta ta daina karaɗe duniya ya zama shi kaɗai yake kallonta ya na jin daɗi, ya na nan faɗacin sa amman kuma rayuwa tasa ya rage wasu abubuwan sai mai hali baya fasa halinsa, kuma hausawa sun ce hali zanen dutse. sannan itama Mimi ta nan a yadda take yar gayu mai kyau domin ba ta amince ta bar jikinta ya lalace ko da yaushe cikin gyara take, tunda ta rike surayya dee mai gyaran amarya da uwargida ta zama tauraruwar mata a zuciyar Ajin ta.+234 803 277 3332
Nemi Surayya dee Bojuwa domin dacewa da sahihin kayan gyara.
Sannan bayan haihuwan Mu'azzam ta so yin tsarin Iyali Aji ya ce bai amince ba dole ta