Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
Allah kuma ya kaɗe fitina a tsakanin ku."
Aji ya amsa da Amin Amin kafin ya zura hannu a cikin aljihun rigarsa ya zaro kuɗi bai san ko nawa ba ne ya ijiye a gaban Daddy sannan ya miƙe yana yi masa sallama Daddy duk da yana da rufin asirin sa amman ya girmama wannan alherin ya miƙe Lokaci ɗaya y na ɗaukan kuɗin kafin ya ce"Har da ɗawainiya? To yau dai zan ce na ci kuɗin ƙwallo kenan."
Mirmishi kawai mansoor ya yi ba tare da ya yi mgana ba Har haraban gidan Daddy ya rako shi, suka kara yin sallama shi ya koma cikin gidan shi kuma sai ya hau mashin ɗinsa ya bar gidan, yana tafe iska na kaɗa shi yana jinsa kamar ya na shawagi a sararin samaniya, sannan nauyin da ke zuciyarsa ya ji ya yaye, wani irin nishaɗi da farinciki ke shigar sa bai sani ba, Yana tafe yana Faman mirmishi shi kaɗai.
Daddy kuma yana komawa cikin gida Mama daman na falo tana jiran shi ya na shigowa ta miƙe tana faɗin" Har ya tafi? Shi kuma bai ba ma tambayarta wani muhimmamci ba ya ce" E."
Ya faɗa lokaci ɗaya ya na zama kan ɗaya daga cikin kujerun falon gefensa ta koma ta zauna tana faɗin" Allah sa dai ba ka ba shi fuska ba"
Kai tsaye ya kalleta kafin ya ce" wani fuskan kuma ? Na saurari bayaninsa na nuna masa Kuskuransa kuma ya karɓa ya ce zai gyara na kuma bashi izinin in Mimi ta dawo ya je su zauna su daidai ta."
Mama ta yi wani iri wanda har sai da rashin jin daɗin ya bayyana saman fuskarta.
Cikin mamakinta Alhaji Hamza ya kalleta kafin ya ce"Sai na ga kamar ba ki ji daɗin jin hakan ba ko?
Da sauri ta ce"Ba wai ban ji daɗi ba gani na yi yarinyar nan ita ta ce ta na so daga farko amman yanzu kuma ta ce ba ta so, kana ganin a tsaya sauraran shi ba ɓata lokaci ba ne? Sannan sam ba su dace da juna ba ji irin gidan da ya kai Mimi domin Allah fa."
Mirmishi ya yi domin shi ya gama gano in da ta dosa amman gudun ka ɗora ma mutun zargi ya sa yac e" To ba ki san tsakanin mata da miji sai Allah ba kenan? Itama a lokacin ɓacin rai ne amman tana son mijinta kuma ba za ta so rabuwarsu ba, mganar gida kuma ai ta san ra'ayin sa tun farko kuma ta ce ta ji ta gani, ba hurumun ba ne yanzu mu san abin da suka yanke ni dai na ce ya same ta su yi mgana abin d suka tattauna namu na saka albarka ne."
"Amman ba dai wanman gidan na su za ta koma ba ko?
Mama ta faɗa cikin yanayin damuwa a muryanta kai tsaye ya ce"Ban sani ba,ko ma can ne ko wani gidan ne can tsakanin su dai."
Sai Mama ta sauke ajiyar zuciya ba tare da ta yi mgana ba sai Daddy ne ya kalleta na wani ookaci kafin ya ce"Na san damuwarki kan Jaheed ne."
Da Sauri ta juya gare shi tana faɗin"Yallabai Yaron mu na son Mimi har yau ya kasa ba ma wata mace dama, bayan dawowan nan nata baka gq murnan da ya yi ba."
Dariyansu na manya ya yi kafin ya ce"Shi ma dai sakarai ne, mace da mijinta bai sake ta ba ne yake murna a kanta? Ke ce kuma ba ki ga ya masa gaskiya ba gwara tun da wuri ya hakura da Mimi in da ace tana son shi da ta zaɓe shi amman tunda ba ta iya zaɓarsa a baya ba yanzu ma ba za ta zaɓe shi ba, ki zauna ki gaya masa gaskiya Mimi ta haramta gare shi gwara tun lokaci bai ƙure masa ba ya nemi wata domin ba zan barshi ya tsallake shekaran nan bai yi aure ba."
Yana gama faɗin haka ya mike ya shige ciki ya barta zaune da tagumi, har Allah ta na jin haushin Hajiya domin ita taƙi ba ma Jaheed goyon baya in da tana so da Mimin ba ta isa ta yi gaddama ba, amman an na ce an ce sai abin da take so ga ta nan ga abin da ta ke so ɗin nan ya na wahalar da ita. Ranta ba daɗi itama ta bar falon zuwa ɗaakinta tana tunanin kiran ƙanwarta Hajiya Turai su tattauna mganar.
*******
*MIMI*
Lokacin da Daddy ya samu wayar Madiha wajen kwana uku da zuwan Aji wajensa ya na ta kiran wayar Mimi ba ya samu sai ya kira ta Madihan tunda suna tare, bayan sun gaisa ya ce ta haɗa shi da Mimi sai ta ce tana na ɗakinta in sun fito zuwa masallaci da yammah zata sanar da ita akan ta kira shi.
Wannan saƙon Madiha ta gaya ma Mimi sai ita kuma ta kunna wayarta ta nemi Daddy a waya suka yi mgana ba tare da wani dogon mgana ba ya ce" An gaya miki mijin ki nata zuwa neman ki baya samun ki?
Sai ta amsa masa bai ba ta samar mgana ba ya cigaba da faɗin" To daga ƙarshe dai ya zo ya same ni mun tattauna ya karɓi laifukansa ya ce zai gyara na ba shi damar ya same ki ku yi mgana kin ji ko?
Gaddama ba halinta ba ne ya sa ta ce masa in sha Allahu sannan ya ƙara da cewa"Yaushe za ku dawo?
Kai tsaye tace" Bansa ni ba amman ina tunanin cikin satin nan." Sai ya ba ta umarnin in ta dawo ta nemi mijinta su yi mgana har ya kara da cewa" kada ki damu na yi mgana da shi na fahimci fushin zuciya ne amman shima ya na sonki kuma ya faɗamin ma da bakin shi, kawai dai ki yi amfani da wannan damar ki sauyashi zuwa yadda kike son ya dawo kin ji ko?
Cikin girmamawa ta amsa masa sannan su ka yi sallama sai ga ta rumgume da waya a kirjinta tana hamdala karfinta zuwanta umra akan Aji ne ta roƙi rabil samawati ya sausauta zuciyar bawansa Mansoor ya sanya masa salama da Aminci da natsuwa ya daidai ta masa rayuwarsa sannan ya Haɗe kansu shi da ita su zauna Lafiya su gina rayuwa mai kyau tare da zuru'a ɗayyiba, in da alheri a komawarta in kuma babu alheri ya cire mata son shi salin alim a cikin zuciyarta.
Itama dai tuni duk wani fushi da take yi ta ji komai ya yaye mata ta ji ta yafe masa duk da cin zarafin iyayenta da ya yi in ta tuna ranta na ɓaci, sannan kuma sintirin da ya riƙa yi a kanta ya tabbatar mata da cewa tana da wata ƴar daraja a wajensa
Sai yanzu ta ke ganin amfanin shawaran Rukky kuma a yanzu take da damar sauya rayuwarsa kamar yadda Daddy ya yi mata gugar zana. Daman tun da suka zo garin Ma'aiki ta kashe wayarta tana Ibadunta, wayar da suka yi da Daddy ya sa ta fara yi ma Madiha zencen komawa, ita kuma daman ta na siyayya shi ya sa a satin ba su samu dawowa ba sai da wani satin ya shiga sannan suka dawo lokacin suna da sati huɗu kenan a can. Sun dawo suka iske Jawahir ta sauka amman sai da aka yi mata C.S. Shi ya sa kwana uku kawai mimi ta yi ta huta sai ta bi jirgi daga lagos Jirgi zuwa Kano Ta kunna wayarta ta yi mgana da Hajiya da Rukky tana gaya mata halin da a ke ciki Rukky ta buga shewa kafin tac e"Dakyau. Lokacin mu yanzu ya fara, ki kira shi ki sanar da shi kin dawo amman za ki tsaya a kano saboda haihuwar Matar Dr"
Haka ko ta yi amman ta kira shi har sau bai ɗauka ba sai ta tura masa saƙo.
"Na dawo, amman Ina kano Anty Jawahir ɗin Dr ta haihu, zan kai sati ina ga kafin na dawo Gombe."
Amman har dare ba ta ga kiran shi ba har ta fara jin haushi shi kuma suna Jos a lokacin sun je buga wasa sai dare ya ga kiranta da saƙon ta a lokacin ya ga ji sai kawai ya tura mata da cewa " Allah ya raya abunda aka samu, in kin dawon ki sanar da ni, nima ba na gari ina Jos"
Ta yi barci sai da safe ta ga saƙon sa. Sai ta yi masa uzuri tunda ta ji ya ce baya gari to sun je buga wasa ne tabbas.
Sai kawai ta share kafa a gidan Dr, Jawahir kuma samar matar likita ne tuni cikin kwana uku ta fara motsa jikinta Shi y asa ba'a ɗaga suna ba.Dangin Mommy da suka zo barka su ga Mimi ba su kawo wani abu ba har Inna Zainaba tunda Mommy ba ta sanar da su an samu wata matsala ba, Sai da suka zo suma mata tsiyan sai dai ta zo ta tsaya gidan Dr sh ine fa ta ji kunya ta bi inna Zainaba gidanta ta kwana ra ɗan zaga yan'uwa tare da dangi na kusa kwananta biyu a Soron ɗinki ta tuno da Hibba sai ko ta ɗaga waya ta kirata bayan ta cire ta daga Kullenta da ta yi, Hibba kamar amafarki ta ga kiran Mimi ta ɗauka cikin mamaki tare da neman yi mata tsiya Mimi na dariya ta ce tana kano ta tura mata adireshi gidanta za ta zo sai su yi mgana jiki na rawa Hibba ta tura mata, Mu'azzam na Office ta kira shi ta na gaya masa suna da babban bakuwa Mimi za ta zo, shima cikin murna ya ce zai baro Office ya zo su gaisa.
Tana tura mata ba daɗewa ta baro gidan Inna Zainaba, mai adaidaita ta nuna masa kwatance ya ce ya san Gidan ya na bakin hanya ne da ba ta gane ba ta kira Hibba Sai ta fito bakin gidan sannan ta hangeta, Bayan ta sallami mai adaidaita ta karisa suka rumgume juna da Hibba wacce ke yi mata tsiyan cewa" Anty Mimi idon ki kenan? Mu kan ba da laifi ba duk an haɗamu an hukunta."
Ta na dariya ta ce" Shi ya sa na zo ban hakuri."
Suna dariya suka karisa cikin gida Hibba ta rasa ina zata saka Mimi ta kawo mata Breakfast domin lokacin sha dayan safe ne Hibba ta ce ta karya sai dai na rana tunda nan za ta yi mata yini.
Nan fa suka zauna suna ta hira Hibba ta ce" Mu dai me muka yi ne gabaɗaya a ka kulle mu Hajiyar Allah? Mimi na dariya ta ce" Ba fa abib da kuka yi kawai dai lokacin sai a hankali na kuma san roƙo na za ku yi ni kuma ba zan iya muku abin da ku kuke so lokacin ba shi ya sa."
Hibba ta ce"Duk da haka dai, ni dai kinsan ba zan matsa miki kan abib da ba ki yi niyya ba, mu ka je har gida kika hanamu ganin ki sannan a wayar ma duk an rufe mu yanzu kin kyauta kenan? Laifin Babba Yaya sai ya shafe mu?
Ta ƙarishe faɗa ta na yar dariya Mimi na dariyan take yi tana ba ta hakuri.
Hibba ta ce"Ya muka iya? Dole mu hakura amman bayan an gama bamu wahala, Kawai sanadin ki sai ga Yaya Mansoor har gidan nan."
Mimi na mamaki ta ce"Kai don Allah."
Hibba ta ce" Wlh ai albarkacin kaza ma Kadangare kan sha ruwam kasko, kin ciru tuta tun dai ya na basarwa har dai ya fahimci ke ɗin ce, sai faman sintiri yake yi a saman hanya saboda ke fisabillahi mu dai a kyale mana Yaya haka anan ai dai ko a haka aka tsaya jikin ta ƙaura ya yi la'asar."
Mimi na dariya t ace"Tabbas haka ne." Nan ta shiga ba ma Hibba labarin wayarsu da Daddy da abin da ya ce. Duk da Mu'azzam ya gaya mata Yaya Mansoor ya je can gidan kuma an samu daidato sai Mimi ta dawo amman bai buɗe mata ba, Hibba ta ce"Ma sha Allah haka ake so, Wlh Yayammu ya sauya kamar ba shi ba. Gida kuma ai sai dai ya siya miki wani tunda har Inna ma yanzu ba ta a gidan."
Mimi ta zaro ido kafin ta ce" Innar? Me ya faru? Sai Hibba ta shiga warware mata abib da ya faru ta ƙare da cewa"To dai yanzu Inna ta samu cigaba tana gidan Yaya mansoor, ya kuma ce ya mallakaa mata har Abada."
Mimi na jinjina kai ta ce"Allah Sarki. Na yi ma Inna Murna, daman ni tuni nasan wannan Maeesha makira ne, kai Allah ya kyauta dai."
Hibba ta amsa da Amin lokaci ɗaya tana faɗin" Ke kam ai sai dai ki ba da izini kawai a fara ɗora miki gini."
Mimi na dariya ba ta yi mgana ba, Hibba kuma ta kara da cewa" A yi hakuri in sha ba za mu ƙara ba, kuma muna da kuɗi za mu gina miki duk irin gidan da kike so.".!
Nan ta bar Mimi da dariya. Haka suka cigaba da hiraran su, Mimi ba ta ɓoye ma Hibba komai ba kan shirin da suke yi ita da Rukky itama ta goyon baya da cewa"Dakyau, wlh ban ga laifin ki ba gwara ki gwara mana kansa irin su Yaya Mansoor sai da haka."
Sallah kaɗai ya tada su bayan sun Idar suka shiga kitchen Mimi na taya Hibba da yanke yanke suna yi suna hira tare suka yi girkin su ka gama sannan suka zauna suka ci. Ana ta kiran Mimi a waya Khadi ce ta ce ta iso amman ba ta ganta ba an ce ta na soron ɗinki ki sai ta ce ga ta nan zuwa Mu'azzam ma ta tsaya jira sai bayan pa'asar ya shigo gidan Mimi ta tambayi Junior Hibba ta ce mata ya na can Gombe wajen Inna.
Shima kamar Hibba Mu'azzam ciwon baki ya fara yi ma Mimi tana Mirmishi ta ce"Ku yi hakuri, a lokacin ba ni da abin da zan ce ne shi ya sa."
Mu'azzam ya ce" Duk da haka dai da an Saurare mu."
Mimi na yar dariya tac e"To shike nan ku yi hakuri yanzu za'a saurare ku."
Saboda ganin Mimi na sauri bai tsaya cin abinci ba ya ce Hibba ta saka mayafi su maida Mimi gidan Dr daga nan su yi barka.
Tana su bar shi amman ba su saurare ta ba, Suka ɗauketa tana musu kwatance har gidan Dr. Sulaiman sai dai a ka ga Mimi da baki tana dariya wajen cewa ƙanin mijinta ne da matarsa suka shiga har ciki suka yi ma Jawahir barka sannan ta raka su har haraban gidan suka tafi da alƙawarin Hibba na in sha Allahu za ta zo suna.
Bayan tafiyarsu Khadi ta kalli Mimi lokaci ɗaya tana faɗin"Ke da aka ce kin buga yaji da kukan sai kin kashe aure, sai kuma a ganki kina bin gidajen dangin Miji?
Mimi ta kalleta kawai amman ba ta yi mgana ba Sai Khadi ta fara dariya tana faɗin" Wai ni ki gaya min me ya yi miki ne da zafi haka? Aji ne fa Ajin nan da kike matukar so? Shege namiji ɗan Babansa ya kunsa miki kenan?
Tashi kawai Mimi ta yi ta ba ta waje saboda ta san tana dukan ruwan cikinta ne ta ji labari nan ta barta da Jawahir tana ta mganganu ita kuma sai dai ta yi mata mirmishi.
Har Dr. da ya dawo sai da Khadi ta ce masa" ƙanwarka an ce ta yi yaji amman kuma sai ga ta ta na bin gidan ƙanin mijinta.*
Dariya ya yi kafin ya ce"Bacin rai ne amman yanzu mun huce za mu koma."
Haka Khadi ta rika tsuntsura dariya tana Faɗin" To daman ita an gayamata soyayya ta na dauwamana, ku gaya mata kowa ma hakuri yake yi a gidan auran shi. Duk da ban so auran su ba amman daga baya na saki, duk lalacewar aure gwara auran da rabuwar wani lokacin, kawai ta cigaba da hakuri daman an ce baƙin mutum akwai faɗin rai sai kin ninka haƙurin ki."
Ƙala Mimi ba ta ce mata ba. Sai Dr ne ke kare ma Mimi yana faɗin har nan Aji ya zo biko kuma dai shi kam ya ba shi bikon Mimi.
Madiha ba ta zo ba sai ranar suna, Asma'u ma Mommy ta turo ta dag anan za ta tsaya gida ta yi hutu, Madiha ba ta san an daidaita har Mimi ta sauko ba sai da ta ga zuwan Hibba ana cewa matar ƙanin Mijin Mimi sai kuma da ta ganta sai ta tuna ta taɓa ganinta a wannan gidan da aka kai Mimi, Tun anan ta nuna ba ta ji daɗi ba Mimi ba ta ma san tana yi ba ta riƙa ina ta saka da bakuwarta Hibba ta na nan har dare har riga ta kawo ma Bby Girl da ta ci sunan Mahaifiyar Jawahir mai suna Hadiza, Sai bayan da Mu'azzam ya zo ya ɗauketa ne da daddare suna ɗakin Dr su huɗun gabaɗaya Madiha ta tada zencen da cewa"Ke Mimi me ya haɗa ki da dangi wancan matsiyacin?
Ba Mimi kaɗai ba harta Khadi sai ta ji wani iri, Dr ya kalleta cikin ɓacin rai kafin ya ce" Haba Madiha, ko an rabu ai bai kamata ki kira shi da wannan sunan ba, Ballantana har gobe a matsayin mijin Mimi yake."
Madiha cikin halin ko in kula, ta ce"To sai me? Ai sai ya sake ta wlh in ya yi taurin kai a maka shi a kotu,"
Khadi ta yi Saurin cewa"Ke, to tana son mijinta, yanzu hakama ya je ya samu Daddy kuma ya ce ya ba shi bikon ta, tana komawa Gombe sai shirin tarewa daman Yajin barazana ta yi ko Mimin Abi?
Mimi ta kasa mgana Idanuwanta har sun kawo kwallah, Dr ne ya tsawarta ma Madiha da cewa" Ki daina shiga hurumin da ba na ki ba don Allah, Mimi ba za ta ji daɗi ba."
Madiha ta kalle su cikin mamaki kafin ta