Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
tsaya ta hau zai kai ta in da ta ke koyon Computer bai fito da ko wallet ɗinsa ba sannan ba kuɗi a hannunsa amman ya ce zai shiga gidan anjuma.
Yana komawa ɗakinsa na cikin Camp ɗin ana Sake kiran shi yana dubawa sai ya ga Baba, sai bai ɗauka ba sai da ta katse sannan ya bi bayan kiran bayan sun gaisa, daya ke sun kwana biyu ba su haɗu ba shi fa tun barowar Inna wannan gidan anguwam bai ƙara komawa ba, ko kan maganar Mariya a camp Auwalu ya zo ya same shi suka yi mganar, kiran Baban ma saboda haka ne yana gaya masa waliyyan yaron sun zo suna bukatar a saka musu Shekara mansoor ya ce a saka a hakan ai kamar gobe ne, kuma tunda an yi bincike yaron da sana'arsa ɗinkin maza da mata yake yi kuma ba shi da wata matsala.
Sun tattauna kan maganar sannan suka yi sallama ya zauna ya ci wainar da Inna ta aiko masa sannan ya sha tea ya haɗa da soyayyen buredi da ƙwai.
Yana gama ci ya natsa kawai sai ya koma ya kwanta ya yi ta barci tun yau ba su da Traning sai gobe yana ta jin hayaniyarsu sun fita can haraba amman bai iya ta shi ba, wayarsa ma kashe ta ya yi sai gabda azahar ya ta shi ya yi wanka lokacin har sun yi sallah tunda suna da masallaci a cikin Camp ɗin sai ya yi na shi a cikin ɗaki sannan ya kunna wayarsa.
Ya duba sakonni masu muhimmaci, har da sakon Mu'azzam daman ya faɗa masa zai je wajen Mimi a jiyan, sai a lokacin ya tuna da takardanta da sauri ya miƙe ya isa ga ma sagalan kayansa ya zura hannu a aljihun wandon da ya sa jiya ya ɗauko takardan ya zo ya zauna a saman ƙaramin gadon dake ɗakin ya warware ya fara karantawa..
*SHARUƊƊAN KOMAWA TA GIDAN AJI.*
1. BA ZAN KOMA BA SAI NA SAKE YIN WANI TARON BIKIN.
2. SAI KA HAƊAMIN LEFE, DOMIN BAN ƊAUKE MAKA BA.
3.SANNAN ZA KA RIƘA ZUWA TAƊI, DUK BAYAN BAYAN KWANA UKU, DA KUMA YAWAN TURAMIN SAƘONNIN SOYAYYA..
4. NA ƘARSHE SHI NE SAI KA GYARA MU'AMALANKA DA KOWA CIKI HAR DA SASANTAWA DA ABOKAN KA, DA MAI DA DANGINKA DANGINA DA MAIDA DANGINA DANGINKA."
"Amincewar ka ga sharuɗdana sune tikitin komawata gidan ka."
A ƙasa sai ta rubuta sunanta Fatima Kabir Dabo, shima daga gefe sai ta rubuta sunan shi Manaoor Ibrahim aji, sannan daga kasa ga wajen saka hannu da kawanan wata.
Ya maimaita takardan ya fi sau goma amman ya rasa wani yarinta ne ke damun Mimi? Wai sai ta sake sabon taro ? Shi na lefen ma bai dame shi ba, sannan wai ya riƙa zuwa taɗi sai kace mara aikin yi? Ga tura saƙonin soyayya wannan ai ga na masa azaba kawai za ta yi ina ga ya ga lokacin wannan shirmen tab, ko taɓa takardan bai yi ba ya ninke ta ya ijiye. Sauran wainarsa na safe ya ci ya sha ruwa sannan ya fita da kwando waje, Su Zinder ya gani ya ba su ya ce su cinye su wanke kwanon, suka karɓa suna mai faɗin" Thank you Captain."
Shi kuma sai ya koma ɗaki yana duba takardun da Coach ya ba shi jiya sai wajen uku da Rabi ya ta shi ya yi wanka ya sauya kaya lokacin har sun wanko kwanukan sun dawo da shi, azumi ke gabatowa akwai tunanin ba su hutu zuwa bayan sallah.
A masallacin cikin Camp ɗin ya yi sallar la'asar sannan ya kwashi kwandon da aka kawo masa abinci sai gidan Inna, nan kuma ya iske ba ta nan Bintu ce kawai da Walida a gidan wei ta je can anguwam Arawa matar Saddiqu ta haihu. Bai yi mamaki ba ya san halin Inna daman ba za ta zauna ba, bai tsaya ba ya ijiye kwadon abincin ya ce bari ya je ya dawo ya na fita suka fara gulmansa domin Hibba ta kyankyansa musu Su Yaya Mansoor ana ta zuwa biko. Har zuwan Mimi gidanta na kano sai da ta gaya musu.
Yana fita daga gidan Inna sai gidan Hajiya yana Hanya ya Kira Mimi ya ce ga shi nan zuwa, kafin ya kariso ta ci kwalliyarta cikin dogowar rigar atamfa ta kuma kashe ɗauri tana tashin kamshi yau kam ko mayafin ba ta saka ba. Sannan ta kawo masa abinci Jallop din shinkafa da nama ya ce ita ta dafa tace a'a sai ya ce sai ranar da ta yi masa girki sai ya ci kai tsaye ta ce"To in ka fara zuwa taɗi zam riƙa yi maka girki "
Bai yi mgana ba yana kallonta kenan da gaske take yi, shima ya sha kwalliyarsa yau har da hula tunda manya kaya ya saka ta kalleshi tana dage masa gira lokaci ɗaya tana faɗin"Ehye, an sha kyau za'a zo taɗi wajen ƴar budurwa."
Ta faɗa tana masa wani irin mirmishi, Kallonta yake yi ko kiftawa ba ya yi, da gaske take yi kenan?
Sai kawai ya saka hannu a aljihu ya fito da takardan harda ma bironsa ya zo, a kasan Cafet ya sauko sannan ya kalli Mimi lokaci ɗaya yana faɗin" Matso ki gani."
Ba nusu ta matso har kansu na haɗuwa waje ɗaya.
Lambar farko ta ga ya tsaya sannan ya kalleta kafin ya ce"Ke yanzu ban da rigima ina ke ina ƙara yin wani biki? Kiran bidi'a ko ɓata lokaci? Ko sake ɗaura mana aure za'ayi ba bikin da za mu yi ballantana haka kawai daga kin yi yaji kuma sai ki ce sai an yi biki. Gaskiya a'a ban yarda da wannan ba."
Kawai sai ya saka biro ya soke ta kallesa cikin mamaki ba ta samu zarafin mgana ba ya je ga na biyu ya na faɗin" Nawa kike bukata? Ya faɗa sannan ya yi ticking lokaci ɗaya ya zura hannu a gaban aljihun rigarsa ya ɗauko Atm ɗinsa na bankin albashinsa, ya sauke a gabanta lokaci ɗaya yana faɗin" Daga naira ɗaya har milyan ɗari za ki iya amfani da shi wajen haɗa abin da kike so."
Sai kawai ya gangara na uku ko ba ta damar magana bai yi ba.
Ya nuna rubutun ta kafin ya ɗago yana kallonta lokaci ɗaya yana faɗin"Haba Mimi yanzu da girman ki kike wani zencen taɗi? Haba ko yara kanana yanzu sun daina wannan ɓata lokacin mq? Me ye taɗi in ba a zo a samu fahintar juna ba? Ni kuma d ke tun muna yara zukatan mu suka samu. daidaito ba amfanin da aueren mu, mu zo muna wani abun ɓata lokaci. Sannan mganar wai saƙƙonin soyayya haba Fatima ni ina na ga wannan lokacin? Kin san fa yanayin aikina ni fa mutun ne kamar kowa ba zan miki karyan abin da ba zan iya ba, Mijin Novel ne ke tsara mace da kalaman Soyayya, ni kuma mijin zahiri ne, in Soyayya kike so tsantsan na gaskiya zan nuna miki ita a kan gadon mu na Sunna in sha Allahu"
Ya faɗa ya na kallonta ƙasa ƙasa, nakwa nakwa ta yi da fuska kamar za ta yi kuka sai ya saka biron hannunsa ya lakace mata hanci kafin yana faɗin" Rigimammiya."
Cigaba da duba takardan ya yi zuwa lambar karshe sai ta ga ya yi ticking lokaci daya yana faɗin"Wannan ba matsala, Abokaina kada ki damu zan neme su mu sansanta duk da ni banga laifin da na yi musu ba, mganar dangina kuma daman ko Inna na ga alamun ta fi son ki a kaina. Sai mganar naki dangin ki suma in sha Allahu zan saki da su mu zama ɗaya saboda ina son ki, kuma abin d mata take so shi miji ya ke so? Ko ba haka ba Mimin Aji?.
Ya faɗa ya na kallonta, kawai sai ya ga ta koma ta zauna a gabansa ta harɗe hannayenta saman kirjinta tana wani ɓata rai sai shima ya miƙe ya zauna yana faɗin"To kuma yanzu menene laifina! Na yi miki fa duka bayani"
Kawai sai ta fara mgana cikin shagwaɓa"Ni dai wlh ko ɗaya ba zan soke ba, kuma ai ba gayyata zan yi ba kawai dai kawayena da Yan'uwana mganar taɗi kuma ni ko? Ba za ka rika zuwa kana ganina ba ko?
Yadda ta yi mganar ne ya sa bai san lokacin da ya ce"Na ji shike nan sai kuma me? Har ta na jan hanci kafin ta ce" Ni dai in ba ka amince ba, sai na ce na fasa komawa."
Har da kukanta fa, gefe kawai ya koma ya na kallonta kafin ya ce"Da girman ki, Mimi ki yi ta shagwaɓa?
Sai ta ƙara narkewa tana matsan hawaye, Har ta na cewa shike nan tunda baya sonta ba zai mata abin da take so ba.
Ya na jin haka ya ƙarisa gareta ya riƙo hannuwanta yana faɗin" Sorry, shike nan na ji ki daina kuka"
Da sauri ta ce"To ka amince? kai ya gyaɗa kafin ya ce"To ya zan yi? Tunda na auri yar gata shagwaɓɓiya."
Dariya ta yi masa sannan ta kwantar da kanta saman kirjinsa sannan ta jawo takardan ta saka hannu ta miƙa masa ya karɓa yana faɗin"Kamar auran coci, ni fa ba guduwa zan yi ba." Tana dariya ta ce"Eh na ji dai." Haka nan ta saka shi ya saka hannu sannan ta ɗauki takardan tana faɗin" In na fara zuwa aiki zan ba da a yi mana photocopy, na ba ka naka nima na ɗauki nawa." Sai ya yi fuska kafin ya ce"Ba na so, ki riƙe a hannun ki kawai"
Dariya ta fara ta na son kallon fuskarsa shi kuma ya haɗe rai ya kauda kai.Sai bin shi ta ke yi, daga karshe ma ture kanta ya yi daga kafaɗansa har ya na juya mata baya, ta shi ta yi ta koma gabansa ta na jan kumatunsa lokaci ɗaya tana faɗin"Ehem Ehem, kamo shi nan kamo shi nan."
Har matse masa fuska ta yi sai da ya yi dariya kawai sai ji ta yi ya riƙe mata hannuwana sannan ya rumgumeta yana sauke numfaahi, itama sai ta yi lakwas tana shakan ƙamshin turarensa.
"In na zo taɗin me za ki riƙa bani?
Haka ya faɗa cikin dishewar murya itama a hankali ta ce"Duk abin da kake so?
Ɗagota ya yi yana kallonta kafin ya ce"Komai fa kika ce?
Sai ta ɗaga masa kai, sai kawai ta ji ya Sumbaci bakinta kafin ya ce"Har wannan?
Sai ta fara waige waige tana zaro ido da sauri ta matsa daga jikinsa tana faɗin"No."
Mirmishi ya yi kafin ya ce"Ai ba ki isa ba kin yi alkwari yarinya."
Tana tura baki ta ce"Ni ban yi ba, ba wannan a sharuɗdan mu."
Kansa ya shafa kafin ya ce" Wa ya ga ya miki su Nasir na gaba da ni?
Dariya ma ya bata cikin mamakinsa ta ce"Au su ke ma gaba da kai?
Cikin basarwa yace"To ni me na yi musu? Suma dai da shisshigi ina ruwan su da shiga tsakanin mata da mijinta Ehe"
Mimi ta dage masa gira kafin ta ce"Kai dai."
Da sauri ya ce"Zan neme su amman ba hakuri zan ba su ba."
Sai ta kaɗa kai tana mirmishi shi kuma sai ya duba agogon hannunsa ya ga an kusa mangariba da sauri ya ce" Maganar gida matso mu yi mgana."
Ba musu ta matso kusa da shi, ya kalleta kafin ya ce"Ba ni da gida a ƙasa yanzu. Gini kike so a yi miki ko kuma a siya gidan kawai.?
Kai tsaye ta ce"Ina gidan ka?.
Sai ta nuna kamar ba ta sani ba hararanta ya yi kafin ya ce"Ban sani ba, shi wanda ya faɗa miki mun samu matsala da su Nasir bai faɗa miki Inna na ba ma gidan ba?
Dariya tayi har tana rufe bak. Mirmihi ya yi kafin yace" Kinga azumi na matsowa zuwa bayan sallah nake son ganin ki a gidana ya ya tsarin gidan ki, ya ki ke so ya kasance?
Sai kawai ta lamgwaɓar da kai ta ce" Ni ba ni da wani zaɓi tsarin da kake so shi nake so." Kai tsaye ya ce"Shike nan daman ina da wani fili sai kawai a gina tunda ina da kuɗi ginin zai kamallah nan da bayan sallah zan yi mgana da mai zane sannan zan nemi Auwalu."
Da haka suka tsaya kan mganar. Ana gab da kiran sallah ya tafi ta yi ta yi ya karɓi Atm ɗin sa, ya ce ta riƙe a hannunta ita kuma ta ce ko ta riƙe tare za su riƙa fita siyayya ya fahimci dai ya kawo kansa. Shi ya sa Mimi ta ke gungurashi duk yadda ta so.
*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3010*
*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*
https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC
No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.
*BAYAN KWANA BIYU.*
Tun bayan sharuɗɗan da Mimi ta saka tsakaninta da Aji ya zama duk ya takura, ya fahimci Mimi so take yi ta maida shi kamar wani sharukhan ɗin Kasar India, to da girmansa da komai ace sai ya koma yana soyayya kamar wani yaro? Ya tabbata yanzu matasa na sun daina wannan soyayyar domin duk yaudara ce, masu yin ta ma yanzu mayaudaran sun fi yawa.
Ko bai kirata ba sai ta kira shi ta ce bai turo mata kalaman soyayya ba. Sai ya ce zai tura mata ya rasa shi ina ma zai samu kalaman Soyayya ya manta da wannan tun a zamanin baya.
Dole dai ƙanwar naƙi ya shiga Playstore ya ɗauko Application na lalaman soyayya In hausa da turanci, bai ma tsayawa karantawa da safe sai ya yi mata copying da forwarding ya tura mata haka da rana in ya tuna haka da daddare ma, amman duk da haka sai da ta gane domin ce masa ta yi.
" Kalaman na ka ba emotion a ciki Aji, kamar dai wai da gasken ba ka sona."
Ya rasa da wani yare zai mata wannan bayanin da fahimta ba ruwan ina son ki da wasu kalamai, kawai dai ta ga soyayya aikace ina ruwanta da wani wai sai ya riƙa yi mata kalamai?. Da ya ga ba za ta gane ba sai ya ƙyaleta da ta matsa masa sai ya ce"Mimi ni fa ban iya duk wannan karyan ba, to ƙarya mana soyayya yanzu ai duk ta zama shirme ki buga ma misali da kan mu, ina son ki kina sona muka yi aure amman ki duba yadda matsaloli suka zagayen mu da ya saka sai da kika yi Yaji, to duk ina wannan son da muke ma juna? Zaman aure zaman haƙuri ne kawai da sadaukarwa, ina son ki zan iya zama dake har abada sauyin fuska ko wani nakasu ba za su shafi soyayyata ba ko da Sauyin hallaya ne sai dai zan yi koƙarin cewa ki gyara amman wani ina sonki na yi kewarki duk magana ce ta fatar baki ya kamata ki gane wanman Fatima."
A waya ne ya ke gaya mata haka sai da ta tura masa baki kamar ya na ganinta kafin ta ce" Wai na yi yaji? Haka fa ka ke cewa yaji"
Kai tsaye ya ce" To ba yajin kuke cewa ba? Ko barkonu zan ce."
Haushi ya sa ta kashe wayarta ta barshi ya na ta mirmishi, ya san ba za ta hakura ba da daddare da ya zo kwanciya ya kira ta nan ta ɗauka tana ta kumbure kumbure t sai ya nuna kamar bai gane ba sai ya ce"Gobe zan zo taɗi me za ki tanadar min?
Ita kuma sai tace"Gobe zan koma aiki."
Ɗan bata rai ya yi kafin ya ce"Tunda ba acan za ki kwana ba da sauƙi, zan zo bayan sallar Isha'i tunda sai na shiga na gaida inna."
Ganin kamar bai gane tana fushi da shi ba ne ya sa ta ce"Ina fushi da kai. Amman sai na ga kamar ka basar ba ka gane ba"
Ya na shafa kasan gemunsa ya ce" Au wai fushi kike yi? To wannan fushin na ki ba na komai ba ne sai na shagwaɓa kuma lallashin ki ai sai ina kusa, ki anada fushin har sai na zo kin ji ko matas?
Har gobe dai Aji ba zai sauya ba in an yi gabas shi sai ya yi yamma. Dole ta saki ranta suka cigaba da waya sai da ta fara hamma sai ya ce ta je ta kwanta saboda fita aiki gobe.
"Sai da safe Mijina, I love u."
Mirmishi ya yi mata kamar ta na ganin shi kafin ya ce"Sai da safe Matas, ki yi shigar nutumci gobe, kada ki manta ke matar aure ce matar auran ma matar Mansoor Aji."
Tana yar dariya ta ce"Yes Sir.."
"I love u."
Haka ya faɗa da sauri ta zaro ido kafin ta yi mgana ya yi saurin katse wayar ya barta da shauki. Ranar barcinta cikin natsuwa ta yi shi, har ta na makara sai shi ne ya ta she ta da asuba kamar ya sani ya ce ya ji a jikinsa barci ya kwasheta ta kasa tashi.
A gurguje ta yi sallar asuba da azakar sannan ta yi wanka ta shirya ta yi shigar lafaya ta yi kyau sosai tunda daman can ita mai kyau ce.
Motar ta tun shekaranjiya ta kira Bakanikenta ya zo ya tafi da ita da yake ta daɗe ba ta yi amfani da motar ta, ya yi ma ta juye da service sannan jiya ya dawo mata da shi tana so ma ta sauya mota da kuɗin gadon ta, amman kuma ba ta so Aji ya ga kamar ta na nuna masa kuɗi amman tuni Khadi ta sauya ta ta motar. Sannan an riga an gama ginin masallatan nan da bohol ɗin ruwa a wasu anguwannin dake cikin garin kano sai dai fatan Allah ya kai