Idan An Ciza Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   40 / 49

117K to 120K   out of 146.6K words

da me zai taya ta sai ta ce bakomai, har girkin ya ce ta daina yi tunda ta na da  juna biyu, itama fa haushi yake ba ta tunda har bai yarda da ita to ba ta ga amfamin soyayyar dake tsakanin su ba.

  Sannan duk shi ya haɗa mganar cikinta har Mommy sai da ta ji,Hajiya da Baaba uwani sun zo dubata, ta ji sauki sai dai kasala da jiri take fama da shi da tsinkewar miyau sai zazzabin dare, ba ta koma aiki ba amman Rukayya ta zo dubata, kuma daga can ma'aikatansu ana ta kiranta ana gaisheta. Jaheed ya kira ta sau biyu shima bai samu natsuwa ba sai da ta ce masa ta koma gidanta sannan ya samu salama har ya na cewa"Kina ganin kiran ma da nake yi miki ba matsala? Kai tsaye ta ce"Kada ka damu ba zai kara kuskuran da ya aikata ba, ko ba soyayya kai shakikina ne saboda haka bai isa ya hanani mu'amala da kai ba."
To ai bai ma ga fuska ba,Mimi ko da yaushe fuskarta a kirne kuma ba ta son ma kallon shi in zai fita ta ce masa a dawo lafiya in ya dawo sannu da zuwa ta yi masa duk abin da yake bukata ta shige ɗaki ta kwanta.

  Ko zai yi ta mgana ba ta amsa masa, Saboda dai ya saka su fita ya ce ta shirya su je barkan matar makama. Jin gidan Bibi ne ya sa ta shirya suka je da daddare suka yi mata barka an dawo da ita gidan su wajen mamanta tun bayan sallamota daga asibiti ba ma za'a yi taron suna ba saboda yanayin rayuwar da ake ciki, bayan sun baro gidan suna hanya ya yi mata surutun ba ta ga yadda jaririyar ta mata kyau ba kamar ce ta ta ce, sannan ya koma mata magiyan me ta ke so ya biya ya siya mata.
Sai a lokacin ta kalle shi kafin ta ce" Abu ɗaya nake so shi ne ka ƙyaleni."
Daga haka ta kauda kanta muryanta kamar za ta yi kuka dole ya kyaleta amman tsakani ga Allah ya gaji da wannan horon bayan fagen.

  Fiye da sati biyu suna cikin wannan rayuwar, ya gaji ya fara bin ta da ban hakurin ta yafe masa ,ita kuma ta ce ta yafe kawai dai ta kasa sakin jiki ne tunda har shi bai yarda da ita ba, in ta tuna haka har kuka ta ke yi saboda bakin ciki. Tana mamakin yanayin cikinta baya sakata amai sai dai tashin zuciya wani lokacin, ita dai sai dai kasala da jiri sai zazzabin dare ba ta kuma zaban abinci amman dai ta na cin goro, saboda sauƙin tashin zuciya ta na iya kula da kanta da gidan aikin ma za ta koma ranar Monday tun da ta samu sauƙi.
Ranar da Allah ya nufi su shirya. Ranar asabar ne Walida da Mariya a gidan suka yini suka girka shinkafa da miyar kifi. Kifin ma tun Tsaraban Inna ne na Argungu, ba ta ma sani ba suka saka shi a miyar sai kuma ta yi mata daɗi taci sosai a daran ma ta ƙara ci ta dora da maltina ta kwanta ai misalin sha biyun dare cikinta ya hana ta barci sai tashin zuciya, haka ta rarrafa ta shiga Tiolet ta rika kwara amai kamar za ta amayar da hanjin cikinta.

  Da jan jiki ta dawo gefen gado ta ɗauki waya ta kira Aji, daman bai yi barci ba yana duba wani tsare tsaren wassanin su na gaba me ya ga kiranta, kuma sai da gabansa ya faɗi ya san ba lafiya.
Sanda ya zo har ta fara galabaita tana son yin aman amman ba komai a cikinta, ganin yanayinta ya sa kawai ya saka mata hijabi ya taimakamata suka fita falo,da gudu ya ɗauko key ɗin mota jallabiyansa a juye ya saka ya rike Mimi zuwa wajen mota megadi ya taso  ga gudu ya na jera mata sannu, kawai sai Mansoor yace a buɗe masa get.

  Wani asibitin kuɗi ya kaita mafi kusa,  suna zuwa a ka karɓe ta saboda emergency ne  Mimi ta sha wahala duka sai da ta amayar da abin da ke cikinta sannan a ka mata allurai bayan an saka mata drip anan asibitin suka kwama ita an ba ta gado shi kuma ya na zaune da ita,.Sai bayan ya je sallar asuba ne ya dawo ya kira Inna ya faɗa mata hankali tashe ta ce gata nan zuwa, likitan da ya karɓe su ya kira shi ya yi masa bayani Mimi ta daina cin kifi domin cikin ta ba ya son shi, ta na daina cin wani abun da cikinta ba ya so. Allah ya sa abun ya zo da sauƙi Inna Meri ta zo ta yini da ita a ranar sai Hajiya da Mansoor ɗin ya je ya gaya mata, kwananta viyu a ka sallameta ta koma gida duka yan'uwanta sun kirata a waya kuma kowa ya san ta na da ciki Khadi har da mata tsiyan cewa Oho su Mimi da ciki an kusa zama uwa.

  Mommy ba ta zo ba amman suna mgana ta waya, Mama da Anty har Daddy ya zo gida dubata shi ya ce a bar mata Baaba Uwani ta zauna da ita Hajiya ta ce itama me ta ke yi a gidan? Mansoor kuma ya ce har Hajiyan don Allah su zauna tunda Walida ba ta da lokaci yanzu. Yadikko ma ta zo ita da iyalanta su Anty Amina da su Bintu ma duk sun zo. Su jummai da su Zuwaira har Maeesha da matar Auwalu.
Magajiya da su gaje sun zo duba ta, kuma taji daɗi kwarai yadda suka nuna mata kulawa shima kanshi gogan rawan jiki kawai yake yi, Nasir da su Makama duk sun zo dubata Rukayyan kusan kullum tana gidan. Zaman Hajiya da Baaba Uwani ya daidai ta Mimi da Aji, tunda dole ta bar musu ɗakin ta koma ɗakin Aji tana kwana kuma suna gidan ai ba za ta masa horon da ta saba a gabansu sai ta ke nuna komai lafiya sai sun shiga ɗakin ta yi masa gum  Ranar dai ya gaji cikin dare ya miƙe ya kunna hasken ɗakin ya ta da Mimi, ta tashi tana sosa idanuwanta cikin sanyin ta ta ce"Me ya faru?
Gurfana ya yi daga saman gadon a gabanta ya ba ta kanshi lokaci ɗaya yana daɗin"Gani ki yi min duk abin da kike ganin za ki wuce, na gaji Fatima kina horani wlh na tuba ba zan ƙara ba."
Ya faɗa kamar zai yi kuka idanuwansa sun kala yana bukatar matarsa amman sama da wata ɗaya Mimi na masa kisan munmuƙe.
Kallonsa ta yi kafin ta kauda kai tana kokarin komawa ta kwanta da sauri ya rikota ya jawota jikinsa ya kamkameta ya na Faɗin"Kin ce kin yafe min amman ki duba abin da kike yi min? Ba ki yi min mgana ba na ganin dariyan ki.  Ni fa bayan ganin ki a tare da ni ina bukatar ganin ki cikin farincikin ba na jin daɗin ganin ki haka don Allahi ki yi hakuri mu koma kamar baya."
Mimi kwallah suka cika mata ido cikin rawan murya ta ce"Me zan maka? Na kasa manta maganganunka ne Aji, da bakin ka kace tabbaci gare ka  a kaina ba zargi ba ne. Ni wai na ke cin amanarka? Ni wai haba don Allah ban yi lalacewa tun ban da aure ba sai da na yi aure zan lalace? Me ya sa ba ka za kamin uziri ba? Ni ba ka yarda da ni ba? Kai ne fa ka taɓa sanina  a ƴa mace amma har kake so ka saka zargi a zaman aure  mu  Saboda ina sonka ina kiyayema duka dokokinka komai ka ce in yi shi nake yi saboda mu zauna lafiya amman duk ban tsira ba, ka ce wai kana da tabbacin ina cin amanarka.. Aji ni ce fa Mimin ka ni? Abunda ya fi min baƙin ciki shi ne yadda ba ka yarda da ni ba, sannan kana mijina wanda ya fi kowa sanina ka kasa iya shaidata to waye zai yi shaida ta?.

  Tana mgana ta na kuka saboda abun in ta tuna sukan ranta yake yi, Aji gabaɗaya jikinsa ya yi sanyi haka ya kara kamkame Mimi shima kamar zai yi kuka yana faɗin" Wlh sharrin sheɗan ne da kuma sonki, ina sonki Fatima shi ya sa nake kishin ki."
Cikin kuka ta ce"In kana kishi na sai ka bari ka kasa yarda da ni? Haba don Allah shekara nawa muna tare? Ka rika sarrafa zucyarka sannan  ka rage kishin ka, ka tuna sanda ka ɗauke ranga ranga zuwa asibiti ka manta likitan namiji ne ya dubani a lokacin ba ka damu ba saboda lafiyata kake nema, To haka za ka rika hakuri da rayuwa dole zan fita wasu za su ganni kai ma za ka fita za ka ga wasu abunda kawai za ka saka a ranka shine ka yarda da ni, ko bayan ba idanuwanka ni mai tsare maka amana ne amman wlh abunda ka yi min yasa min bakinciki a zuciyata sannan kuma yasa na rage ganin ka yadda nake ganin kaa cikin Idanuwana."

Haka ta faɗa tana kuka, Aji ya ruɗé yana faɗin"Don Allah kada ki daina sona Fatima, in kika gujeni wa zai so ni? Zan gyara halina zan riƙa sarrafa zuciyata da kishina amman kada abunda ya faru ya sa ki ji kin tsaneni."
Mimi ba mgana sai kuka shi kuma ya na ta ban hakuri kamar zai mata kuka. Tabbas ya yi nadama kuma ba zai yarda ya ƙara aikata abin da ya aikata ba.
Itama tana son mijinta duk da wasu hallayan na shi ba su da kyau.Sai dai ai daman ɗan adam tara yake bai cika goma ba, a komai ba za ka ce ka samu abu ɗari bisa ɗari ba. Ko 50% ka samu sai ka yi hakuri da shi, tunda har ya Ffhimci bai kyauta ba ta na da tabbacin gaba ba zai kara yarda ya aikata abin da ya aikata a baya ba.

  Sai ta rumgumeshi cikin shesshekan kuka ta ce" Shi mgana zarar bunu ce, kuma wata mganar ta fi kaifin takobo kaifi, in ka caka ma mutum zata huda cikinsa har ta fita ta waje, ka daina barin ranka na ɓaci kana faɗin mganganu mara kyau a kan abin da ka ke so, wata rana za ka cutar da ni cutar da bazan iya yafe maka ba."
"In sha Allahu ba zan kara ba."

Da haka ta yafe masa ta kuma yi alkwarin manta abin da ya faru amman ta ce ba yanzu ba sai a hankali za ta iya manta abin da ya faru.
Shike nan ma'auranta suka shirya, amman duk da haka Mimi ba ta sakin jiki da Aji, in ta tuna kalamansa a kanta sai gwiwanta ta yi sanyi shi dai ko da yaushe ban hakuri ne.
Satin Hajiya biyu suka koma gida tunda Jikin na Mimi ya yi kwari, ta na yin amai amman ba sosai ba.
Kasala ne dai da jiwa shima ba sosai ba. Sai zazzabin dare shima ya yi sauki sai dai ta yi fari fayau ta kuma rame.

Sama da wata ɗaya sannan Mimi ta koma aiki. Gogan ya yi sanyi yanzu yana gani za ta saka mayafi ta fita sai dai ya kauda kai tunda ya yi alƙwarin yarda da matarsa kafin kishin sa a gaba, itama kuma tana yi domin ta ga ko da gasken ya daina abunda yake yi.
Da gangan take saka abaya ta sha rolling ta wuce, baya mgana amman dai ya kan ce" Abaya tana nuna sufar jiki ko za ki saka hijabi ne Mimi?
Sai ta kalle shi ta ce"Sai in saka ɗin in kana tunanin har yanzu ba ka yarda da ni ba."
Da ta ce haka sai ya ce Allah ya ba ta hakuri,  In sheɗan ya saka masa wani tunani sai ya yi saurin yin ta'awizi ya kuma tuna cewa ba yadda zai hana Mimu fita to saboda haka sai ya yi hakuri da wasu abubuwam

  Mimi kuma sai harabasa take yi ta ga ko zai kara yin wani abun amman sai ta ga da gasken ya gyara halinsa. Kuma har a lokacin ba ta gaya masa Alaqar Jaheed da Rukayya ba har manya sun shiga mgana abu ne daman me za'a jira? Har an saka rana wattani shida amman dole Rukky za ta bar aiki da karamci Jaheed ya ce a can zai nema mata aiki. Sai dai Mimi ta ba ma Aji mintin saka ranar Rukayya da Jaheed
Baki sake y ace"Mimi abokin nawa fa?.
Kai tsaye ta ce"Ya tsaya wasa. Ga ɗan gaske nan ya zo ya ɗauka."
Nasir kam da kanta Rukayya ta gaya masa, Ya damu tunda shi a tunaninsa ta na jiransa ya daidaita da iyayensa ne.
Jin ga wanda za ta aura ya sa Nasir ya ce"Ni miye laifina da zai huce a kaina ya kwace min dudurwa."
Aji ya yi masa rantsuwan Mimi ba  ta faɗa masa. Kuma saboda ta kure shi har gidan ta sake gayyato Jaheed, tare da Rukayya ba tare da ta gaya masa ba domin ta ƙara jaraba nadamarsa.

  Ko da ya dawo ya gansu bai nuna mata wani abu ko a fuska ba, sun yi masabaha da Jaheed har ya bashi hakuri kan abunda ya faru a baya shi kuma ya ce komai ya wuce shima ya na mai bashi hakuri.
Rukayya sai a lokacin ma ta san an samu rashin fahimta ba ta yi mamaki ba, ita kawar Mimi ce ta san kishin Aji a kanta.
Ita kam har ya na zolayanta da cewa ta yaudare su ta ce su ne suka yaudare ta.
Sai yamma suka tafi, Aji bai yi ma Mimi mgana sai da daddare bayan sun kwanta ya kalleta yana faɗin"Fatima, wai ke nan har gobe ba ki yarda da nadama ba! Ba ki amince da na ce bazan ƙara ba?
Sai ta yi shuru ba ta yi mgana Mirmishi ya yi ya na rumgumeta lokaci ɗaya yana Faɗin"Abin da nake so ki gane har abada ba zan daina kishin ki ba Fatima, ina sonki ba na so kuma ki kasance abun burgewa a idanuwan wasu mazan, gwajin ki a kaina ba shi zai saka ki gane nadamata ba, in na ce zan bar abu to kokari na ke yi na yi yaƙi da
zuciyata a kan haka, na fahimci yarda shi ne kan gaba akan kishi shi ya sa na aminta da ke, ina son ki kuma ba zan daina kishin ki ba kema ina rokon ki aminta da ni kin san ina sonki ina kishin ki. Don Allah ki kiyayewar motsawar zuciyata Mimi"
Ƙara shigewa jikinsa ta yi lokaci ɗaya tana faɗin" In sha Allahu Merapyaar.."
Ya na mirmishi ya ce"Sunan Indiya kuma a ka saka min?

  A kunnensa ta msa raɗa da cewa"Eh My love(Merapayaar) da yaren hindi."
Sunan ya yi masa daɗi ya sa ya yi kyakyawan mirmishi kafin ya ce"Ke kuma kin koma My jan, domin ke ce rayuwata amman Ina son sunan ki, ina jin ɗaɗin kiran ki FATIMA.."
Suka kara ƙamkame juna cikin soyayya da muradi, shike nan zaman lafiya ya ɗore musu kamar yadda ya roketa ta manta baya sannan ta na kiyayewa motsawar zuciyarsa.
Tana masa abin a yake so, tana kiyaye abin da baya so,shima kuma ya daina takura mata amman fa mganar kishi, sai da ya rage shi duk da kuma hakan in ya ga abunda baya so zai yi mgana kuma za ta gyara,. Da gaske ne ya yarda da ita, itama ta aminta da shi sai suka samu kyakyawan fahimtar juna, Hankalin Inna ya kwanta tana fatan daga yanzu su rika fahimtar matsalan junansu suna magancewa da kansu.

  Cikin Mimi na da wata huɗu Hibba ta haihu, kuma lafiya lau a gida ta haihu a hannun mijinta.Sai washegari ne suka je asibiti a ka duba ta an samu mace tun a daran Mu'azzamu ya raɗa mata suna MARYAMA."




*Janafty*

[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3018*

*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*

Tunda Mimi ta ji labarin haihuwan Hibba shike nan ta fara murnan tafiya kano suna. Ba ma ita kaɗai ba hatta su Bintu kowa na ta shiri saboda haihuwanta na fari a gida nan Gombe ta zo ta haihu. Wannan karon ne za'a sha shagalin suna a gidansu da ke kano, Kuma uwa uba kuma Maryama sunan yarinya Inna Meri a ka yi ma takwara sai ya kasance sunan ma na musamman ne.

  Tun sanda labarin haihuwan ya zo Gombe Ƙanwar mamanta ta shirya ta tafi wajen Maijego su kuma nan duk suna shirin tafiya ana gobe suna ne gabaɗayan su. In da Allah ya taimaki Mimi haihuwan ranar Jumma'a ce kenan tana da lokaci a weekend sannan kuma daman tana so in ta je ta leƙa har kofar Soro ta gaida dangin Mommy sannan ta leƙa har gidan Dr ma so take yi Mera ya bar ta ta yi ko da sati ne sannan ta dawo.
Ita kaɗai take shirin yin sati ba tare da ta yi mgana da megidan ba. Bangaren Inna kuma tace an yi mata takwara ba za ta zauna ba ta saka a ka yi ma Hibba yajin Jego da kuma garin kuni mai yawa wanda zai taimaka wajen ciko mata da ruwan mamanta. Sannan kuma ta saka su Halima kowa ya kawo abin da yake da shi, a haɗa na kayan suna, su ma suka ce za su yi kan jiki kan karfin su in dai a kan Mu'azzam ne.

  Anty Halima turmi biyu ta kawo da kayan jaririya da sabulai, Yaya Amina ma haka Bintu kuma wani less ne mai tsada wanda ta siye shi da kuɗin adashen da ta yi, Inna Meri kuma da ƴan kudaɗen dake hannunta itama ta sa ka aka siya turmin Atamfa da kayan jaririya masu kyau guda biyu. Ba ta yi ma Mansoor mgana ba sanin ko ba ta yi masa ba zai iya bakin ƙokarinsa. Maganar kawai ma su zuwa suna suka yi tunda akwai masu zuwa da yawa sai yace gwara a ɗauki tashar mota kawai tunda da Magajiya ta zo mata barka ta ma ta mganar zuwa

40 / 49