Idan An Ciza Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   38 / 49

111K to 114K   out of 146.6K words

ce" Ina kuma za ka je?
Haka ta faɗa tana hararanshi kansa a ƙasa ya ce" Zan zan je wajen Mimi ne Inna."
Wani sakaran kallo Inna ta yi masa kafin ta ce"To mara kunya, sai yanzu ka san da ita ? Ba cewa ka yi ta bar maka gidanka tun da tana cin amanar ka ba  miye za ka zo kana wani sanyin jiki? Fita ka ba ni waje kafin na tashi na yi maka dukan mahaukaciya wlh."
Ido ya zaro ya na kallon Inna, wai ta yi masa dukan nahaukaciya. Ganin yadda ranta ya baci yasa jiki ba kwari ya yi kamar zai bar falon sai kuma ya dawo ya duka a gabanta muryansa na rawa ya ce"Don Allah Inma ki yi hakuri wlh sharrin sheɗan ne."
Banza Inna ta yi masa har tana ƙara volume ɗin radion ta, tana jin sa yana ta ban hakuri yana ta kuma faɗin sharrin sheɗan ne.

  Haushi ya kamata kamar ta watsa masa mari, ba ta san lokacin da ta kashe radion hannunta ba a fusace ta ce"Rufe min baki, in ƙara jin kace sharrin sheɗan ne ka ga ni in ban watsa maka marin ɓarin makauniya ba." Haka ta faɗa ta na hararanshi. Kallon Inna ya yi cikin mamaki kafin ya ce"Inna kin ce za ki dakeni yanzu kuma kin ce za ki mareni? Baban inna ne fa?
Inna ta ce"Eh  Mansoor ba ɗan ibrahim na gane ka, ka wuce dukan ne? Ka ƙara cewa sharrin sheɗan ne ka gani in ba wanke fuskar ka da mari ba."
Sai Aji ya yi gum kansa na ƙasa. Domin ya san in kuma ya sske ya sake mgama tabbas Inna za ta iya wanke sa da mari.

"Ki yi hakuri inna, na tuba.."

  Haka ya ke ta faɗa, Inna sai da ta ga dama  sannan ta kalleshi kafin ta ce"Sheɗan din ne ya sake ka da sauri haka? Ƙaryan banza Ka raina ma kanka wayau, waye sheɗan din in ba kai ba, in ba sheɗan ba waye zai aikata abin da ka aikata, kana zargin matar auran ka Mansoor? Kai kam wani irin jaki ne?
Baki ya buɗe yana maimaita kalmar jaki a ransa a she a fili ne a fusace Inna Meri ta ce"Eh mana jaki mana, wani mutum ne mai tunani zai aikata abin da ka aikata? Ka kore ta ba ka tsaya ka ji bayanin ta ba. Yanzu da ta je wajen iyayenta ta sanar da su fa? Wallahi da sun daina ganin ka da daraja, sai ta yi wayon zuwa wajena ni kuma wlh zan bi mata kadin abib da ka yi mata ne. Tun da har kana zarginta ya tabbata auran ku ba zai zauna lafiya ba gwara ka sake ta na maida ta hannun Iyayenta ka fin ka aikata abin da za ka hanani shiga mutane."

  Haka ta faɗa tana kallonsa cikin ɓacin rai. Cikin zaro ido ya ce"Saki kuma Inna?
"Eh haka na ce"
Ta faɗa tana haɗe rai. Sai kawai ya yi zaman dirshan gaban Inna lokaci ɗaya yana faɗIn" Ki yi min rai Inna don girman Allah ki yi hakuri."
"Rai ai na Ubangiji ne, ba ka yi tunanin haka za ta faru ba ka aikata abin da ka aikata?
Da sauri ya ce"Inna kishi ne, kinsan ina da kishi, kuma ina takiran wayarta ba ta ɗauka ba sannan na ga sun dawo tare ya na riƙe da ita, kuma Inna tsohon saurayinta ne fa me kike tunani?
Inna tac e"Ba komai sai alheri, zuciyarka ce ba ta da kyau kishi halas ne ga matar ka amman naka ya yi yawa ya zama na jahilci da daƙikanci tunda kake zargin matarka da cin Amanarka? Kai ba ka da lura ne? Ina tunaninka yake? Na sha gaya maka in ka ciza ka hura Mansoor, in rai ya ɓaci hankali ke nemosa. Hadisi ne fa Annabi(SAW) yace ma wani sahabinsa Kada ya yi fushi har sau uku sannan a matsayin ka na musulmi mumini in ranka ya baci sai ka lallashi zuciyarka ka yi hakuri ka jira in ka huce sai ka yanke hukunci amman yanke hukunci cikin fushin shi ke haifar da dana sani Mansoor."

  Duk abin sa Inna ta faɗa gaskiya ne, Kai tsaye ya ce"Inna sheɗan ne, amman wallahi gar ga Allah ba na zargin Mimi ki yi hakuri."
A kufule Inna ta ce"In sheɗan ne me ya sa ba za ka nemi tsari da shi ba? In ka ji zuciyarka na zafi ka kira sunan Allah mana  ka nemi tsari daga sharrin sheɗan din mana ka gani in abubuwa ba su yi maka sauki ba."
Shi dai sai hakuri ya ke ba ta amman Inna ta fusata ta ce tunda yana zarginta shike nan ya ba ta takardan sakin Binta ta fahimci bai san darajan mace ba.
Daga karshe ma banza da shi ta yi yana mgana shi kaɗai, ta shi ma ta yi ta shigewarta ɗaki, sai kuma ta dawo falon kada barinta falon ya sa ya shiga wajen Binta so take yi sai ya gane kuranshi wanda nan gaba ba zai ƙara gigin aikata haka ba..
Yana zaune in da ta barshi sai ta shige Kitchen ta barsa gajiya ya yi da zaman ya ɗauko wayarsa ya kira Mu'azzam kamar an saka masa batir ya shiga gaya masa duk abin da ya faru.
Mu'azzam ya saka salati ya saukewa kafin ya ce"Haba Yaya Mansoor me ya sa ka yi haka?  Gaskiya ba ka kyauta ba."
Shi dai Mansoor faɗi ya ke yi Mu'azzam ya taimaka masa ya kira Inna ya ba ta hakuri sai ya ce bari ya kirata.

  Inna na kitchen Mu'azzam nata kiran wayan ta anan falo Manaoor ne ya ɗauka ya kai mata tunda ta ga Mansoor ta san kan zencen, bayan ta ɗaga kiran sun gaisa tunda ya fara rage murya ta sakatar da shi da cewa"Ka fita daga mganar nan Mu'azzamu ai tunda shi Yayan naka Babban kwabo ne ka fi shi sanin darajan mace shike nan ya sake ta sai ya zauna shi kaɗai tunda yana da kishi baya son a ga matarsa amman shi zai fita ya na kallon  matan wasu, in dai saboda shi ka kirani ni ina aiki ne."
Daga haka ta kashe wayar, Mansoor tsaye a Kitchen kamar ya kurma ihu, Inna Meri tuwo ta ɗora abunta ga shi yunwa yake ji anman ya kasa mgana jiki ba kwari ya fita falo ya sake kiran Mu'azzam kawai sai ya ce masa"kawai ka zauna kada ka tafi sai ta baka matarka."
Shawaran Mu'azzam ya bi ya yi zamansa a falo ga shi ba halin ya shiga ɗakin Mimi Inna Meri na kai da kawo, yana zaune ya fara barci sai da Inna ta zo ta tashe shi ta ce bai ji ana sallah ba ne sannan yafita masallaci ya yi sallah ya sake dawowa.
Allah ya bashi sa'a Inna na ɗakinta sai ya yi wuf ya shige ɗakin Walida har da rufo kofa Mimi na kan darduma ta idar da sallah itama duk ta faɗa ga laulayi.
Ba ta san ma ya shigo ba ta na can tana tunanisa. Sama sama ta ji faɗan Inna ta ɗauka ma ya tafi ne. Sai ji ta yi kawai ya duka ya rumgumeta ta baya ƙamƙam cikin wani yanayi kamar zai yi kuka.

" kiyi hakuri Mimi don Allah, wlh na tuba ba zan ƙara ba."
Haka ya ke ta faɗa ya riketa gam. Ta fara kokarin kwace kanta amman kuma yaƙi ba ta damar haka,  wata zuciyar ta ce ya ce tabbaci gare shi Mimi kada soyayyarsa ta rufe miki ido, kawai sai ta saka ƙarfi ta tureshi da sauri ta mike tana kallonsa kafin ta ce"Ka manta ne, ni ce wacce kake zargin ina cin amanarka! Ko da yake kace tabbaci gare ka ba zargi ba ne."
Kawai sai ta saka masa kuka . Da sauri ya miƙe yana koƙarin nufarta da sauri ta ja baya tana faɗin"Wlh ka da ta ƙara taɓani, ai jikina najasa ne tunda ina tarayya da wani bayan kai."
Shi kokarinsa ya riketa kada Inna ta ji ta, ita kuma Kuka take yi yavsa ba ta san inda ta kai kanta ba sai ji ta yi ta buge kafarta da gefen gado azaba ya isheta sai da ta yi yar ƙara. Ta yi kasa tana rike kafarta shi kuma ya nufeta yana faɗin" Mu gani me ya same ki? Ƙwace kafarta ta yi, ta matsa baya tana kuka.

  Kofar ɗakin suka ji ana bugawa, da kuma Kiran sunan Mansoor da inna take yi lokaci ɗaya ta na Faɗin" Baban inna ka zo ka buɗe nin kofar nan ko na saɓa maka."
Ba shi da mafita illah zuwa ya buɗe kofar ya na buɗewa Inna Meri ta shigo da muciya a hannunta daman ta ɗauko ne za ta yi talge ta ji Kukan Binta, ba ta yi wata wata ba ta maka masa muciyan a gadon baya ya duke yana faɗin"Inna.."
Ƙoƙarin ƙara maka masa take yi sai Mimi ta riƙe muciyan lokaci ɗaya tana faɗin"Don Allah inna, kada ki yi masa lahani."
Sai Jikin Inna ya yi sanyi ta sauke muciyan tana hararan Mansoor da ya sadda kai kamar mutumin kwarai.

"Fita ka ba ni waje, kaji kunya ita tana tausayinka amman kai ba ka tausayin ta, Yaron ciki gareta ita da ke bukatar kulawa amman kai kake saka ta a damuwa."

  Sai ya kalli inna cikin mamaki sannan ya kalli Mimi da kanta ke kasa kunya ya kamata ya a ka yi Inna ta san tana da ciki?
"Inna yaron ciki? Wai mimi ke da ciki?
Muciyan ta ɗaga za ta kara buga masa ya sa ya fice da gudu da rakashi har falo tana faɗin" Zan maka rubiti da abin hannuna In baka fita daga idona ba. Takardanta za ka kawomin ka ji ma na gaya maka."
Kawai sai ta ga yana mirmishi kafin ya ce"Inna ba kyau sakin aure da ciki, ki yi hakuri kawai ki ba ni matata mu koma gida mu daidai ta."
Sai Inna Meri ta kasa mgana. Wani kallo ta yi masa sannan ta shige kitchen ta barsa nan farinciki ya cika sa, shima zai haihu Allah sarki rayuwa. Wata zuciyar ta ce da sanadinka cikin ya zube fa? A fili ya furta" da ba zan yafe ma kaina ba."

  Mansoor ya ki tafiya ko'ina Inna kawai ya ke ma magiya har ta gama tuwonta kuma ba ta saka masa ba, ya ce rabon sa da abinci tun jiya Inna Meri ta ce ina ruwanta ai tunda bai san baiwar da Allah ya yi masa yanzu ya fara zama da yunwa kiri kiri Inna Meri tahana shi, ruwa kawai ta bar shi ya sha sai faɗa take yi tana fadin ya fita ya bar mata gida in kuma yana takaman gidan shi ne sai su su fita su bar masa gidan.
Yana jin haka ya mike ya dau key ɗin motarsa ya fice yana faɗin" Inna gidan nan fa naki ne, me ya sa za ki ce haka?.
Inna ta ce"To ba zan ce ba, ka zo ka min zaune kamar wani ɗan kaciya"

  Ai da gudu ya bar gidan kafin Inna ta saka a yi masa a tare, gida ya koma ya yi wanka ya sauya kaya sai ya kira Mu'azzam yana faɗa masa yadda suka ƙare da Inna. Mu'azzam ya ce"Ga shawara ka je ka samu Baba na san shi ne kaɗai zai sauko da fushin Inna."
Sai a lokacin Aji ya tuna da Baba ai nan da nan ya kirasa a waya sai ya ce baya gida zuwa anjuma in ya dawo Mansoor ɗin ya zo ya same shi. Shi ya sa bai sake fita ba. Dakyar ya iya dafa ruwan zafi ya sha tea Rana ɗaya kawai ya fara raina kansa, amman da ya tuna Mimi na da ciki sai ya ji kamar an saka sa a cikin Aljannah.




*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3017*

*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*


https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC

No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.

Bai fita ba sai bayan mangariba bayan ya sake kiran Baba ya gaya masa ya dawo gida ya zo ya same shi. Shigar manyan kaya ya yi harda hula sannan ya hau motarsa ya nufi anguwan Arawa, yana hanya ya ji ana ta kiran sallar Isha'i ya iso kofar gidan na su ya iske Baba na alwala shi da amininsa Mallam Hashimu sai shima ya bi a yarin su ya ɗauro alwala suka karisa masallacin suka yi sallah. Bayan sun idar ma sun ɗan dade a waje matasan anguwan nan suna ganin Aji suka dafe masa sai da ya ji da su sannan ya samu ya sulale.

Ya samu Bab da su Baba Sani suna mgana.  Bayan sun gaisa sai suka yi musu sallama suka shiga gida, tunda yanzu sun gane karatun sun rage roƙo sun fahimci ko ba su roƙa ba Meri ta riga ta yi tarbiyan Ƴaƴan ta da alheri gabaɗayan su.
Baba Ɗanjuma ya so su shiga ciki amman Mansoor ya ce su dai tsaya daga wajen zai fi.

"Me ke faruwa ne Baban Inna? Na gan ka kamar a gaggauce ne?

  Mansoor ya yi shuru kansa a ƙasa. Da kunya ya fadi abin da ya aikata amman kuma ba shi da wata mafita  dole ya buɗe baki ya warware ma Baba Danjuma duk abin da ke faruwa har zuwan shi gidan Inna da matsayar ta ya ƙarishe faɗa cikin bayyana nadamarsa lokaci ɗaya yana faɗin" Wlh Baba sharrin sheɗan ne ban san abin da ya shiga kaina ba ne a lokacin, na tuba na kuma gane kuskurena in sha Allahu ba zan kara ba, ka shigemin gaba mu je ka ba ma Inna baki ta taimaka ta ba ni matata Baba."
Baba Ɗanjuma ya kalli Mansoor cikin wani yanayi kafin ya ce" Innalillahi wa'inna Ilaihirraju'un haba Mansoor haba. Sau nawa na sha faɗa maka ka riƙa tausasa zuciyarka sannan ka daina yanke hukunci cikin fushi, itama mahaifiyar taka ko da yaushe nasihan ta kenan ka rika haƙuri sannan ka san yadda za ka yi ka sarrafa fushinka saboda gudun faruwan abin da ke faruwa yanzu.
"Ka yi hakuri Baba, na yi nadama kuma in sha Allahu zan iya bakin ƙoƙarina wajen sarrafa fushina in sha Allahu."
Mansoor ya faɗa kamar zai yi kuka har ya na marairaicewa.

  "Amman ka san wannan abin da  ka aikata ba mai kyau ba ne Ko? Sannan kana sane da cewa zargi na daga cikin abin da ke ɓata aure ko?
Baba Ɗanjuma ya faɗa yana kallon Mansoor ɗin wanda ya sadda kai ƙasa kamar bashi ya aikata ba, ya yi nadama shima ba laifin sa ba ne laifin soyayyar Mimi ne da ya yi masa yawa shi ya sa yake kishinta kishi mai zafi amman yanzu ya fahimci komai sai ka bi shi a sannu ya sani zai fara sarrafa fushinsa amman ba zai iya daina kishin matarsa ba har abada.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Na sani Baba, in sha Allahu hakan ba zai ƙara faruwa ba."

  Sai Baba ya kaɗa kai kafin ya ce"To bari na shiga ciki na sanar da Magajiya sai mu je tare na yi mata mgana."
Tare suka shiga cikin gida, Mansoor ya ce bari ya gaida magajiya, suna shiga suna ma tsakar gida ne ita da Mariya suka shigo ya rankwafa ya gaida Magajiya da irin salon gaisuwarsa ta amsa cikin sakewa kamar yadda ta saba yanzu ta daina ɗaure musu fuska, ko da ma da sauran wani abu a cikin ranta ta boye ma zuciyarta
Mariya na gefe ta gaishe shi ya amsa lokaci ɗaya ya na faɗin"Ke kina nan?  yaushe rabon da na ganki?
Kanta na ƙasa ta ce"Kwanaki mun je gidanka ba ka nan Anty Mimi kawai muka samu a gida."
Sai ya jinjina kai Magajiya ta ce" Ranar lahadi tunda tana gida sai ku je ke da Walida ku gaishe su."
Sai ta amsa dai dai lokacin da Saddiqu ya shigo gidan fakan fakan kamar mahaukaci, daman ya samu labarin yanzu sai yawon gari can lagos ɗin dama yar buga buga ce kuma jari ya suɓuce. Har da Auwalu sun yi mganar ya ce ya zo ya fara harkan gini ya ce ba zai iya ba ya koma sai zaman shagon wani abokinsa. Dole Maeeshan ta nemi aikin koyarwa tana zuwa domin ta rufa ma kanta asiri.

  Ko Magajiya bai gaisar ba. Sai ita ce ta ga zai wuce zuwa bangaren matarsa ya sa ta ce" Kai Saddiqu ba ka ga Yayan ka ba ne?
Sai ya juyo ya na kallonta ya na kuma kallon Mansoor tunda akwai wuta haske ya gauraye tsakar gidan. Sai ya kasa mgana Yana mamakin yadda Magajiya ta koma ruwan sanyi shi fa jin su kawai yake yi, ba bu wani abin da mutum zai yi maka wanda Allah bai maka ba. ƙaramin tsaki kawai ya ja ya yi wucewarsa mirmishin gefen baki Mansoor ya yi domin wanda bai daraja uwarsa ba har yaushe kake tunanin kai zai iya daraja ta ka mahaifiyar? Magajiya kunyar duniya ya kamata saboda abin da Saddiqu ya yi mata.

  Dai dai lokacin da Baba ya fito cikin shirinsa yau kwanan Magajiya ne sai gobe ne  yake gidan Inna shi ya sa yana fitowa ya kalli Magajiya lokaci ɗaya yana faɗin" Magajiya Mansor zai ɗauke ni zuwa gidan Meri zan dawo zuwa anjuma in sha Allahu.".
Sai Magajiya ta kallesa a sanyaye kafin ta ce"Ina fatan dai ba wata matsala?
Da Sauri yace"Lafiya lau, wata yar matsala ce amman kada ki damu."
Ganin bai faɗa mata ba ya sa ta kaɗa kai kafin tace to Allah ya sa a dawo lafiya.
Mansoor ya yi mata sallama suka fita tare da Baban ta bi su da kallo tana girgiza kanta, Ko ta ƙi ko ta so Ƴayan Meri da agolan da ta raina su ne su, yaran nata

38 / 49