Idan An Ciza Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   15 / 49

42K to 45K   out of 146.6K words

je ya yi yawo da shi cikin Camp ɗin su, Ko kuma ya yi yawo da shi acikin mota ya na siya masa kayan kwalama da kuma kayan wasa.

Ya so cikin satin da zai shiga ya je Kano duk da baya samun wayar Mimin amman hakan bai samu ba  baya samun shima lokacin kansa, wani girma ne Allah ya ba shi a sanadin wannan kwallon kafa. Matasa matasa dake Gombe da zagayenta suna yawan zuwa wajen sa neman karin bayani ko wani taimako,  duk da shima ya dan ƙwallo ba ra'ayinsa ba ne sannan ba burin shi ba ne, amman tunda abin da Allah ya zaɓa masa kenan sai ya rumgume shi hannun biyu, tunda shine komai na shi yanzu komai zai zama ko ya zama a wannan rayuwa sanadin wannan sana'ar ne a farko bai wani ɗaukesa da wani irin Muhimmanci ba amman daga baya sai ya rike abun ya san Allah ne ya yi masa kyakyawan zaɓi ta hanyar da bai za ta ko tsammani ba.

Har satin ya ƙare. Bai samu yanke shawara ba, a satin kuma da ya shiga suna da traninng saboda watan gaba suna da buga wasa, to duk ba ya samun zama sannan Baba ma ya kira shi kan maganar Walida da Mariya ya ce zai shigo gidan su yi mgana.
Abin da ya sa ma ya yi musu shuru ba su ci Jamb ba, ya na tunanin su jira wata shekara su sake rubutawa, sai su tafi jami'ar Gombe kamar yadda ya yi ra'ayi duk da ya san Baba aure yake so su yi saboda tsarin gidan wanzamai kenan ba'a dogon karatu a gida.
Suna mgana da Mu'azzam shi dai ya damu ya zo kanon nan ya yi bikon Mimin sai ya riƙa nuna masa zai yi tunanin har a lokacin bai gama gaya masa ga abunda ya yanke ma ransa ba., daga baya kuma sai ya ce ko ya na son zuwa ba shi da mafita tunda wayar Mimin tana kashe ne ta ina zai iya sanin adireshin gidan yayan nata.
Sai Mu'azzam ya ce ya na da lambar Dr. Sulaiman saboda tun a wajen ɗaurin auran shi suka karɓi lambar juna tun wata hira da ta shiga tsakaninsu ya gaya masa a kano ya ke aiki, to tun a lokacin ayyuka ya sa ba wanda ya neme wani a cikin su.

Mamaki ya kama Aji cikin ɗan shan kunu ya ce"Me kuka haɗa da su da kake ijiyar lambobin su?
Mu'azzam na dariya ya ce"Mun haɗa mana, tunda Yayana na auran ƙanwarsa ai an zama ɗaya in sha Allahu"
Uhm kawai yace domin ya ga Mu'azzam ne da Kalan dangi,  har ya na cewa kada ya damu zai raka shi gidan in ya zo kanon,  shi kuma ya ce bai saka shi ba, kuma ya ƙi gaya masa ga lokacin da zai zo ya ce kuma in ya dame shi zai fasa zuwa daga nan Mu'azzam ya kama bakin shi. Bangaren su Nasir da Makama sun yi fushi sun ce in dai Aji bai ba su haƙuri ba to ba za su haƙura ba.
Mu'azzam ya ba su haƙuri a madadin sa amman Nasir ya ce ya fita a wannan faɗan ba ruwan shi, shi ko gogan ya manta da abin da ya faru suna can sun ɗaukan ma kansu da Mu'azzam ya kara mgana sai cewa ya yi wani abu daman ya faru ne? Ya fahimci Nasir ya koya ma Makama banzan halinshi, shi yana da abubuwan da suka sha masa kai ba shi da Lokacin tunawa da abin da ya faru in kuma suna jiran ne shi ya Kira su ya ba su haƙuri alhalin shi dai bai san ya yi musu laifi gaskiya su yi ta jira. Suma ɗin fa su san halin shi kawai saka ma rai wahala ne amman Nasir na kira Mu'azzam ya ji ina aka kwana, saboda ya damu ko ya ya zai yi fushi da Aji abokatansu ba karya ba ne.

Kimanin shuɗewar sati biyu Sannan ya samu natsuwar kansa. Ranar Asabar da Yamma ya shiga anguwan Arawa saboda maganar da za su yi da Baba, anan ya yi sallar Mangariba da Isha'i tare da su Baba A masallaci. Su Baba Sani har suna tara shi gefe suna mai faɗan zama haka ba amfani ya kamata ya ƙara aure, Baba Sani ya ce akwai yar abokinsa mallam mati in yana so yarinyar uwarta Jajir tunda Bafullatanace, kuma ta dauko kyan uwar ne, Baba Ɗanlami yace gwara dai ya zo ya duba a cikin anguwa in da ake ganin mutumcin ba inda ba'a ganin shi a wata tsiya ba.
Duk bai katse su ba sai da su ka gama koro jawabinsu sannnan ya gyara tsayuwa yana faɗin" Na gode Baba da kulawa. Amman ni ban saki matata ba, ta je gida ta huta ne amman za ta dawo soon in sha Allahu."
Yasan harda kuɗi suke bukata a hannun shi haka ya ba su 20k kowanne suka karɓa suna washe baki, duk da yana da abin da ya fi haka amman ba ya sakar musu kuɗi tunda yasan halinsu ba zuwa gidan suke yi su ba ma matansu a ji daɗi ba Sharholiyansu kawai su ke yi acikin gari shi ya sa ko kayan abinci ya gwammace ya ba ma Auwalu ya siya musu ya kai musu.

A kofar gida suka samu keɓewa da Baba Ɗanjuma ya yi masa mganar Walida da Mariya ya ce zaman su ne ya ishe sa ba sun gama karatu ba?
Mansoor ya ce" Eh sun gama matakin sakandiri ba, Ina so su cigaba har matakin jami'a in sha Allahu."
Baba ya yi shuru kafin ya ce"A'a ni na fi son kowacce ta kama ɗakin ta kamar sauran ƴayana."
Mansoor ya ce"To Baba, sun samu maneman ne?
Baba Ɗanjuma ya gyara zama kafin ya ce" To ban sani ba, amman abin da ya sa na kira ka kenan, ka kira su dukkansu ka zauna da su ka ji in akwai waɗanda ke nenan su, in ka ji akwai sai a bincika in an aminta da nagartansu shikenan."
Mansoor ya yi shuru kafin ya ce"In kuma babu fa? Baba Ɗanjuma ya ce shikenan sai ka ba su daman fara yin zence har Allah yasa a dace.
Bai yi gaddama ba ya ce zai yi mgana da su in ya shiga cikin gida anan waje ya bar Baban wajen abokinsa Mallam Hashimu ya na ko shiga da Mariya ya fara cin karo tana wankin kayan da za ta saka gobe a dara nan shi bai ma ganeta ba sai da ya ji tana gaishe shi sannan ya tsaya ya na kallonta shi ya daɗe ma bai ganta ba.

"Ke ina kike zuwa, ba na ganin ki a cikin gidan nan?

Haka ya faɗa lokaci ɗaya yana kallonta da sauri ta ce" E. mm ina gidan Yaya Zuwaira ne."
Kai tsaye ya ce"Me ya sa kika je can?
Sai ta kasa mgana kanta na kasa dai dai lokacin da magajiya, ta ɗago labule ta Fito ta na kallon su, shi kuma ko kallo bata ishe sa ba kawai sai ya juya ya na faɗin" Barka da dare, ke Mariya ki same ni a ɗakin Inna zan yi mgana da ku."
Yana gama faɗin haka ya yi wucewarsa Magajiya ta bi shi da harara. Bai ma san tana na yi ba tsaki ta yi lokaci ɗaya tana Kallon Mariya" Ko zai ce ki daina zuwa gidan Zuwairan ne tunda shi ne uban Ɗanjuma?
Mariya ta kalleta kafin ta ce"Kai  Magajiya."
hararanta ta yi kafin tac e" Dilla ta fi can sakara, kuma kije ki dawo ki gayamin abin da ya ce."
Mariya ba ta kara mgana ba ta dai shanya kayanta daman ɗauraya take yi, ta wuce Bangaren Inna Meri ta samu ɗakin Maeesha a sakaye tunda Yaya Saddiqun na gari tun shekaranjiya ya shigo garin sai firita take yi tana shwagaɓa ita mai ciki, a falon Innar Daga Walida sai shi Junior ma ya yi barci Inna Meri kuma barci take ji bayan sun gaisa ta ce za ta shiga ta kwanta ta huta amman ba ta fara barcin ba ta ji yana tambayansu ko suna da ma su son su?

Mariya da Walida suka kalli juna cikin mamaki, ita dai Mariya tana da samari ita kuma Walida ba ta da wani takammame, Tunda ba tsayawa take yi da samarin ba, Samnan ba ta da waya Inna ko yar ganin dama ce, in ta ga dama ko wayar ma walida sai ta yini ba ta gani ba Innar ta yi boyon kayanta mariya ko tana da waya wani Saurayin ta dake sonta ya siya mata.
Ganin duk sun yi shuru ya sa ya yi gyaran murya yana faɗin" Baba na son ya aurar da ku, ni kuma ina son ku yi karatu wacce take ganin ta na da wanda ke sonta sai ta yi mgana."
Walida ta yi shuru, kafin ta ce"Ni dai ba kowa, zan fi son na cigaba da karatuna Yar jarida nake son zama kamar Anty Mimi"
Bai ce mata komai ba tunda hankalinsa na kan wayar hannunsa ne.

"Ke fa?

Ya faɗa ya na cigaba da duba wayarsa, murya can ƙasa mariya ta ce"Ni.. ni akwai wani."
"Ina yake?
Ya haka ya katseta da sauri ta ce" A tudum wada. Yaya Auwalu ma ya san ashi."
Kai ya girgiza kafin ya ce"Ok zan yi mgana da Auwalu ɗin, ke kuma tunda ba ki ci Jamb ba  ba za ki zauna hakanan ba zan nema miki ko yar diploma ki je ki yi a kan na'ura mai ƙwalƙwala, kafin wata shekara sai ki sake rubuta Jamb ɗin mu ga Abin d Allah zai yi."
Gabaɗayansu su ka yi masa godiya,  nan ya bar su ya fita bayan ya ce Walida ta gaya ma Inna ya tafi, ya so ya gaya mata gobe zai je kano amman kuma bai samu fuska ba, Ita ko Innar ta na jinsa mirmishi kawai ta yi, ko da ace shi ɗin yana da fitina amman kuma yana da kyakyawan hallayan da fole a ɗaga masa kafa. Tana jin su walida na kuskus a falo, Ko da ce ma Mariyan ba ta da saurayin Magajiya ba za ta bari ta cigaba da karatu ba, aure za ta ce ƴarta za ta yi, Walida kuma ta san ba ta da wani saurayi sai tarkace ita ba za ta saka baki ba tana da uba da Sauran yayyenta abin da su ka yanke a kanta ba za ta ja ba.

Yana fita su ka kusa cin karo da Saddiqu da ya fito daga cikin ɗakin sa daga shi sai gajeran ƙaramin wando, Kallo kallo suka yi ma juna shi da Aji, kwarjini ya yi masa yasa ya ba shi hannu su ka yi musabaha duk da ya sha alwashin ba zai ƙara gaishe shi ba, sannan ga gulmar da Aishar ta kai masa amman ga shi ga Mansoor ɗin ya kasa masa wata mgana.
Shi ko kallon kasa da sama ya yi masa kafin ya ce" ya kamata dai kasan a yanayin da za ka riƙa fitowa, nan gidan akwai iyayenmu akwai ƙannen mu bai kamata ka riƙa fitowa haka ba."

Yana gama faɗin, ya saki hannun shi ya yi wucewarsa ya bar Saddiqu na bin shi da harara sai da ya tabbatar da ya bar shashensa sannan ya saki tsaki yana faɗin" ƴan ƴan, sarkin iyayi ai sai ka hanani ni da gidan ubana."
Daga baya kenan.

********

*03rd Febuary 2023*

Ba a motarsa ya shirya tafiyan ba. Sai ya shirya tafiyar tasa a motar haya. Takwas na safe yana tasha kafin tara motar kano ta ɗaga da Aji aciki kuma har a lokacin yana kiran wayar mimi amman amsar ɗaya ne tana kashe ne, Daman tun kwanaki ya saka Mu'azzam ya tura masa lambar Dr. sulaiman ɗin bai kuma kira shi ba sai da ya sauka tashawajen sha biyun saura na rana sannan ya kira shi.

Wajen kira biyu ya yi masa ana uku ne ya ji an ɗaga kiran da sallama, shima sai ya amsa masa suka gaisa.

"Ba ka gane wa ke mgana ba ko?

Dagacan bangaren Dr. sulaiman dake haraban asibitin Aminu kano ya fito daga duba Patient ɗin da ya yi ma tiyata jiya ya samu Kiran Aji.

"E wlh ban gane ba. Lambar ba bu suna.".

"Sunana Mansoor Aji, mijin ƙanwar ka Fatima Mimi."

Mirmishi ya suɓuce ma Dr. Sulaiman yana gyara zaman gilashin da ke idonsa ya ce" Allah sarki, kasan da ya ke ba mu taɓa waya ba shi ya sa ban ɗauki muryan ba."
Aji ya jinjina kai kafin ya ce" Gani na sauka a tashar Kano. Adireshin gidanka nake so, na zo wajen matata ne."
Ciki mamakin da har ya bayyana saman fuskar Dr Sulaiman ya ce"Ikon Allah, ok to yanzu na shigo asibiti ne na duba patient ka gaya min tashar da ka sauka sai na ƙariso  na ɗauke ka ko?
Sai Aji ya waiwaya ya ga sunan Tashar ya faɗa masa sai Dr ya ce ga shi nan tafe in sha Allahu.
Sannan suka yi sallama ya ƙarisa wajen motarsa ya buɗe ya shiga. Sai da ya hana Mimi tafiya amman Daddy ya ce a kyaleta tunda dai har ya ji labarin ya bita wajen Hajiiya kuma ya taka har Abuja saboda ita amman kuma ba ta bari sun haɗu ba, Ya yi mata faɗan ta koma Gombe amman Mimi taki jin mganarsa yanzu kuma bai san da wani yare zai faɗa masa Mimi ta bi Madiha da mijinta zuwa Umra ba.

Yana wannan tunanin cikin lokaci ya isa ta shar Allah ya taimake shi bai haɗu da mugun Goslow ɗin kano ba, daga bakin tashar ya tsaya saboda in ya shiga wajen fitowa ne matsalan tunda tashar Kano Line ne sai ya kira layin da Aji ya kira shi da farko ya ce ya ɗan Fito daga tashar ya na nan a bakin tashar a wata mota mai ruwan toka.
Ba su sha wahalan gane juna ba, Dr Sulaiman ya fara gane Aji tunda ya san shi, shi kuma Aji fuskar Mimi ya gani a fuskar shi sannan ya ɗaga masa hannu kuma ga shi a jikin mota mai ruwan toka.
Aji ya na sanye da shadda mai ruwan toka ɗinki zamani ya dora bakar dara a kansa takalmin kafarsa sahu waje ne. Sai wayarsa kawai dake hannunsa.
Bayan ya ƙariso suka yi musabaha sannan Dr Sulaiman ya buɗe mai gaban mota ya shiga suka ɗauki hanyar cikin gari. Gidan Dr na anguwan sharaɗa ne.

Suna tafe Dr. Sulaiman na jan sa da hira shi kuma ya na amsa masa ɗaya da ɗaya, yawanci kan mganar wasa ne, Dr na zolayansa da cewa za su riƙe shi ya buga musu wasan kano Pillars da kuma Gombe United mirmishi kawai Aji ya yi amman bai yi mgana ba.
Su ɗan ja lokaci kafin su isa gidan, tunda da nisa, sun isa gidan ɗan madaidaci mai kyau da shi har sai da ya burge Aji.
A Haraban gidan ya faka motan suka firfito Aji bai yi niyyan shiga cikin gidan ba sai kawai ya ce"Ka yi mata mgana kawai."
Sai Dr ya ce" Haba dai ka shigo mana bakomai nan ma gida ne."
Sai Dr ya yi masa kwarjini ya sa ya bishi suka shiga ta falon ɓakin sa na kofar waje.
Sai ya ce Aji ya zauna bari ya shiga ya fito sai ya jinjina masa kai, ya samu ɗaya daga cikin Kujerun falon ya zauna yana ɗauko wayarsa yana dubawa.
Ya so ya kira Mu'azzam sai kuma ya fasa, yac e sai ya gama rigimarsa da Mimi sannan zai neme sa.

Dr. Sulaiman kuma na shiga cikin gidansa ya iske Jawahir a falo turus tana zaune da tsininin cikinta a gaba. Yara duk ba sa nan suna Mandawari sun je gidan kakanin su..ta na ganin shi ta sakar mai mirmishi lokaci ɗaya tana faɗin"Ka dawo da wuri yau."
Yana zama gefenta yac e"Kinsan ba aiki na je yi ba, duba Patient ne kawai."
Sai ta gyaɗa kai ta yinkura ta mike dai dai lokacin yake faɗin" Kun yi mgana da Mimi tun bayan tafiyar su Umra?
Jawahir ta ce"Sau ɗaya muka yi mgana lafiya dai ko?
Sai kawai ya miƙe yana faɗin"Bako gare ta. Mijinta ne ya zo."
Jawahir ta zaro ido kafin ta ce"Yana ina?
Sai ya nuna mata falon baƙi yana kora mata jawabin yadda aka yi ya ƙarishe da faɗin", na rasa me zan ce masa."
Jawahir ta ce"Gaskiya ba daɗi, tun zuwansa Abuja na yi ma Mimin faɗan ta yi hakuri ta koma gida ta saurare shi a kallah dai ai ya nemata, ina amfanin wannan abu kuma? Ai sai ya ɗauka kuma mutanen banza ne."

Dr ya mike lokaci ɗaya yana fadin"Daddy ne duk ya ke biye mata, amman yanzu dai haɗo min ruwa da lemu akwai abinci?
Sai ta ce sai da miya amman bari ta dafa ko shinkafa ne da Ssauri sai ya ce ta hanzarta, Ta wuce Kitchen duk da cikin ta ya girma amman matar likita ce motsa jiki a wajenta na da matukar amfani.
Shi kuma Dr. Sulaiman sai ya kira Daddy bai dauka sai da ya ƙara gwada kiran shi sai ga shi ya ɗauka sai daga baya ya tuna yau oahadi ne, bayan sun gaisa sai ya ke gayamasa zuwan Aji tare da cewa"Daddy ina jin kunya me zan gaya masa?
Kai ya ce"Ka gaya masa gaskiya mana, miye abun ɓoye ɓoye."
Dr Ya yi kasaƙe bai yi mgana ba jin haka ya sa Daddy ya ce"Ka ga kada ka damu, in har yana da hankali ya san in da zai zo komai ya warware."
Ya kashe wayarsa ya na yar dariya ɗan tselen uwa ashe dai ƴa na son fiyar ta shi har yanzu, in gaji da zagaye zagaye zai neme shi, a lokacin shi kuma zai gaya masa matsayarsa.

Jiki a sanyaye Dr. ya kwashi farantin ruwa da Lemu ya kai ma Aji dake zaune a falo har ya fara auna Mimi ta shigo falon nan ya fara balbaleta da faɗan sa amman maimakon ita sai Yayanta ya kara gani. Da ya ce ba zai sha ruwan ba sai ya nuna bai ji daɗi ba shi ya sa sai ya tsiyaya ya sha kaɗan shi da Babban shan ruwan shi ya

15 / 49