Idan An Ciza Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   3 / 49

6K to 9K   out of 146.6K words

na lokacin da ka kirana ko wanka ban yi ba."
Hararansa Aji ya yi kafin kai tsaye ya ce" Nasir ina fatan ba gorin Iyalai kake yi min ba ko? Nasir ya yi wata yar dariya kafin ya ce" Nayi maka gori mana. Domin har yanzu ba mu ji Mimi ta fara tafiyar nauyi ba, in kana so ka fara amsa sunan mai iyali sai ka fara yara Ƴaƴa daga ɗaya zuwa biyu amman yanzu dai kana matsayin magidanci Mata kawai."
Aji ya yi shuru ya na kallon Nasir na yi masa dariya numfaahi ya shaƙa sannan ya fesar.

"Nasir tambayan ka na zo na yi! In fatan za ka faɗa min gaskiya"

Yadda ya faɗi mganar ne ya sa Nasir ya san ba wasa a maganarsa, tun ballantana ma shi Aji ba mai yawan wasa ba ne duk maganar da ya faɗa ya na kan gaskiyarsa ne. Sai shima ya gyara zama lokaci ɗaya yana faɗin" In sha Allahu zan faɗa maka iya gaskyan abin da na sani"
"Game da kaina ne Nasir, ina son na san wani abu a game da abin da nake yi ne."
Nasir ya kalle shi cikin mamaki kafin ya ce"Topha! Kamar na me kenan?
Aji na shirin mgana wayarsa ta fara kiɗan alamun ana kiransa ya na ɗaukowa ya fuba sai yaga Mu'azzam ne, Sai bai ɗauka ba sannan bai katse kiran ba sai da ta katse ta katse kenan ya na shirin kashe wayar gabaɗaya Saboda ba ya so wani abu ya katse shi in ya fara sauraran Nasir. Sai dai bai kai ga kashe wayar ba sai ga wani kiran amman wannan karon daga Baba Ɗanjuma ne.

  Shima bai ɗauka ba, sai da ta katse sannan ya yi saurin kashe wayar ya buɗe cikin ɗan bankin motar ya jefeta, Nasir na kallonsa ya ce" Ka ɗaga kiran mana, in ya zo mai muhimmanci ne fa?
Aji ya ce"Kada ka damu, yanzu dai mu yi mganar da ta kawo ni."
"Ina jin ka"
Nasir ya faɗa ya kosa ya ji abinda Aji ke son sani kuma game da kansa shine har sai da ya zo wajensa.

"Ina so ka faɗamin shin ina aikata wasu abubuwa ba dai dai ba ne? As in ina da wasu mugayen hallayan da ba'a jin daɗin zama da ni?  Sannan ina da hali mai kyau ko ba ni da shi? Kana ɗaya  daga cikin waɗanda suka sanni tun ba yau ina da tabbacin za ka iya sanin wasu abubuwan a kaina."

  Ya faɗa ya na huro iskar bakin shi, Nasir ya yi kasaƙe kawai yana kallon Aji har sai da yaji shuru shima ya Juya ya na kallonsa kafin ya haɗe rai yana faɗin" Ba kallo na na ce ka yi ba  amsa za ka bani."
Nasir ya sauke numfashi kafin ya gyara zama yana faɗin" Na ɗauka duk waɗanan tambayoyin naka za ka fini sanin amsar su."
"Inda na sani zan zo har nan in tambaye
ka? Aji ya faɗa cikin jin haushi.
Nasir na danne dariyan shi ya ɗaga hannu yana faɗin" Shike nan mai da euƙar  kai ka girma ammman ba ka daina gitina ba."

"Da gaske kenan ni fitinanne?

  Ya faɗa ya na kallon Nasir wanda ya yi jim kafin ya ce" E,wannan ai jalittarka ce tun a baya, ka manta in dai mu ka zauna waje ɗaya kafin mu rabu sai mun yi faɗa kamar Sau uku ko sau huɗu, Ko da yaushe Makama da Ahmad na cikin raba tsakanin mu, kai fitina ni kuma rashin jaƙuri."
Ya karishe faɗa yana yar dariya Aji kuma kansa ya kauda bai ce komai ba sai Nasir ya Cigaba da faɗin.

  "Mansoor mutum ne mai kirki da sanin ya kamata, sannan kana da kyakyawan mu'amala da mutane a baya. Sai dai tun bayan abin da ya fru tsakanin ka da mahaifin Mimi ka sauya Aji. Rayuwarka ta yi Juyin waina daga sama zuwa ƙasa."

  Aji ya juyo ya na kallonsa kafin ya ce" Daga sama zuwa ƙasa? Kamar ya? Ban gane ba."
Ya faɗa cikim sigar tambaya sai kawai Nasir ya dafa kafaɗansa lokaci ɗaya yana faɗin" Yes ka sauya tun faruwar abin da ya faru a Lokacin, ka guji kowa naka ciki har da mu, ka yanke alaqa da kowa ka koma kana wata irin rayuwar kaɗaici wanda ya ba ma sheɗan Ddman kara hura wutar gushi da zafn zuciya a cikin ranka. Ka koma mai wata irin zuciya mara yafiya da afuwa,  ka koma abu kaɗan in aka yi maka sai ranka ya ɓaci, Sannan sai ka riƙa gayyato mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ka riƙa saka su cikin Fushin ka, mu ina Laifin mu a cikin abin da ya faru? Ko laifin waɗanda ka haɗa kana Jin haushi? Ita kanta Mimi ba ta da laifi har ga Allah Mahaifinta ne kuma ya rasu  Aji me ya sa ba za ka bar zuciyarka ta huta ba? Sai ka riƙa fushi da wanda ta shi rayuwar ma ta ƙare tuntuni, Allah ma fa muna yi masa Laifi ya yafe mana duk girmansa. To kai me ya sa ba za ka kasance mai afuwa da yafiya ba? Duk abubuwan nan da suka faru rashin Afuwarka ne da maida komai ba komai ba ne da a ce ka kasance mai barin abin da ya faru a matsayin kaddara da ka kasance mai sanyin zuciya da kyakyawan daɓia a cikin mu."

  Ya karishe faɗa yana mai kallon Aji ido a cikin Ido kuma ya ga maganganunsa sun shige sa sosai, domin shuru ya yi na wani lokaci kafin ya fesar da numfashi ya ce" Yanzu kana ganin ni da a ka saɓawa in na nuna an ɓatamin sai ya zama Laifi?
Nasir ya girgiza kai kafin ya ce"In ka nuna an yi maka ba dai dai ba, ba ka yi laifi ba amman riƙon nan ba shi da wani amfani Aji, mutumin nan daga baya ya yi nadama ya aiko har gida a ka zo a ka baka hakuri Saboda su wanke laifin su, suka ɗauki Mimi suka aura ma a bisa tsarin ka shin ko zaman da yarinyar ta yi da kai duk da ka yake mata wasu haƙoƙinta ba ta chanchanci saboda ita ka manta abin da ya faru ka Fuskanci gaba ba?
Aji ya yi shuru domin ya san gaskiya Nasir yake faɗa masa sai ya kasa mgana domin nadaman abin da ya aikane ya zo ya ƙara lulluɓe sa.

  Nasir na ganin haka ya cigaba da faɗin" Don Allah ka manta baya mansoor ka bar zuciyarka ta samu salama, ka ɗauka a ranka da duk abin da ya faru Ubangiji ne ya shirya sannan ka rika tuna lokaci, a can baya Allah ya rubuta a wancan lokaci ba za ka auri Mimi ba shi ya sa abin da ya faru ya faru a baya, sannan a lokacin da ka aureta a lokacin ne Ubangiji ya ce Kum fa yakun Mansoor shi ya sa kagl ga alokacin ka aureta, abin da kake nunawa dai dai yake da ka na ja da ƙaddaran Ubangiji akan rayuwarka Mansoor."

  Kansa ya jinjina kafin ya ce" Haka ma Mimi ta ce min jiya, wai ina ja da kaddaran Allah a kan rayuwata."
Nasir yace"Yes! Is Truth, duk abin da ta faɗa maka gaskiya ne, gwara ka buɗe zuciyarka."
Aji ya yi shuru kafin ya sauke numfaahi lokaci ɗaya yana faɗin" Na ji, to yanzu in ina so na manta abin da ya faru ya zan yi? Ko ina so na manta sai na kasa saboda zuciyata ce ta kasa manta abin da ya faru a baya."
"Sheɗan ne ke rinjayar ka, amman ka fara Koyon yaƙi da abin da ke cikin zuciyarka ka yi yakinin cewa na yafe ma duk wanda ya taɓa cutata, sannan sai ka fara kokarin manta baya ko da zuciyar taka tana dawo da kai acan baya sai ka yi saurin neman tsarin Ubangiji ina mai tabbatar maka cikin lokaci za ka manta komai sannan zuciyarka za ta samu salama da amincin da ta jima ba ta samu ba."
Nasir ya gama faɗa hannunsa saman Kafaɗan Aji, wanda ya runtse ido lokaci ɗaya sannan ya buɗe yana faɗin" Shike nan zan yi kokarin na gwada haka."
Nasir ya gyaɗa kai kafin ya ce"Allah ya sa, sannan don Allah ka rage kafiya da zafin zuciya, kuma ka daina jin cewa a cikin ranka sai abin da ka ga dama za ka yi, ka yi tunani da kanka ka gani ka girma yanzu  kana bukatar natauwa waje ɗaya da kyakyawan zamantakewa a wajen matarka."
Kansa na ƙasa ya fitar da Iska ta bakinshi kafin ya ce" Na ɓata komai Nasir, jiya nan na gaggaya Mimi mganganu ni har Babanta ina ji na kira da azzalumi."

  Nasir ya zaro ido lokaci ɗaya yana faɗin" Innalillahi, Aji garin ya ya ka yi wannan ɗanyen aikin?.
Mansoor ya saka hannu ya shafo kansa sannan ya fara faɗa ma Nasir abin da ya Ffru tun na kan tafiyarta Abuja zuwa jiya daga karshe yac e" Inna ma ta ji komai Nasir kuma kasan halinta, Ni banjin Mimi saboda nasan ta na sona za ta gama fushinta ta hakura, kuma ni tun jiya na yi nadaman maganganun da na faɗamata,  Inna nake ji za ta ɗauki fushi da ni, ka gani ma Mu'azzam na ta kirana shi da Baba kuma nasan kan mganar ne."
Nasir ya kalli Aji cikin matsanancin takaici kafin yac e" To da gaske ashe baka son Mimi? Ka daina sonta ne daga baya ko daman can tun farko ba  son ta kake yi ba?
Wani sakaran kallo Aji ya yi masa kafin ya ce" Wannan wani irin tambaya ne Nasir? Kasam Mimi ita ce rayuwata."

  "Ba ita ba ce rayuwarka, domin da ita ce rayuwarka da ba ka ci zarafinta tare da na iyayenta ba sannan da ba ka baro ta tana kuka ka yi tafiyarka ko a jikin ka ba Aji."

  Nasir ya faɗa cikin ɓacin rai, Aji ya dafe kansa kafin ya ce"Oh! Na ce maka na yi nadama, kuma kar ka damu da ita tana sona ba za ta iya dogon Fushi da ni ba?
"Haka kake gani ko?  yanzu kana da tabbacin ba ta tafin kamar yadda ta bukata ka amsa mata ba?
Cikin ƙwarin gwiwa ya ce"Yes! Ina za ta je? Na faɗa maka ba za ta iya tafiya ba, ni ne rayuwarta kamar yadda nima take matsayin rayuwata" Sai da Nasir ya yi yar dariya a cikin ransa ya na fatan Mimi ta yi tafiyar ta domin har yanzu Aji bai yi laushi ba akwai jin kai a tare da shi.

  Aji roƙansa ya yi akan ya zo ya raka shi gida ya t ba ma Inna hakuri, karo na farko da Mansoor yake jin tsoron haɗuwa da Inna, Sai Nasir ya ce bari ya shiga ya yi wanka wani harara Aji ya sakar masa kafin ya ce"Dilla mallam mu tafi, nima ai ba wanka na tsaya na yi ba."
Nasir yace"Shike nan ba zan shiga na sallami Iyalai na ba?
Kafin Nasir ya rufe baki sai gani ya yi kawai Aji ya ja mota sun bar ƙofar gidan sai Nasir kawai ya saki baki yana kallonsa shi kuma sai kawai ya ɗauke kansa har ya na wani ɗaga wuya lokaci ɗaya da tattare naman goshin sa.

  Lokacin da suka isa gidan a kofar gida su ka haɗu da Baba Sani da Baba Ɗanlami suna ta kuskus sun haɗa kai, suna ganin Mansoor jikinsu na rawa suka tare shi,Irin gaisuwarshi ya yi musu, Nasir ne ya yi musu irin gaisuwar da suke so. Yana ƙokarin ya wuce cikin gidan amman Baba Sani ya tare shi da faɗin" A she kuma abin da ya faru kenan, To Allah ya kyauta na gaba kune yaran zamani in an gaya muku gaskiya sai kuka ga kamar ana muku bakin ciki ne, yanzu ina amfanin abin da ya faru?
Baba Ɗanlami ya karɓe da faɗin" Ba amfani fa, shi ya sa a kace kowa ya tsaya matsayinsa, ina kai ina auran ƴar masu kuɗi? Da cikin yaranmu ka nema ai da ba'a ji kan ku ba, ina riba ace aure ko shekara bai yi ba ya ƙare, abun dai ba daɗi."
Mansoor ya yi kasaƙe kawai yana kallonsu Nasir ma su yake kallo sannan ya koma ya na kallon Aji cikin mamaki.
Domin shima yana so ya fahinmci mganarsu ne.

  "Na ce ba, saki nawa ne ka yi mata? In ba uku ba ne sai a shiga a gyara lamarin saboda ko bakomai mu cece darajan wannan gidan kar a fara kirga ma ƴaƴan mu auri saki."

  Hankalin Aji sai ya fara tashi da sauri ya ce"Saki?  wa aka saka kuma?
Ya faɗa yana kallon fuskokinsu, Baba Ɗanlami da Baba Sani suka kalli juna kafin Su haɗa baki wajen faɗin" Toh ba ka son a sani ne? To ai Meri ce da safenan ta ce ka rabu da matarka tana ma gidansu tun jiya."
Aji ya zaro ido lokaci ɗaya yana jin wani abu kamar zafi zafi na ratsa sassan jikinsa cikin mamaki ya ce"Mun rabu? tana gidansu?
Sai kawai ya juya ya shiga gidan da sauri kamar zai kifa Nasir ya bi bayan shi. Domin in ya fahimta Mimi dai tun a jiya nan ta koma gidansu.

  A tsakar gida suka ci karo da Magajiya tana Aikinta tana wake waƙenta cikin gara'a, abin da ya ba ta mamaki ganin yadda Mansoor ya wuce kamar zai ta shi sama, Duk da ba kasafai take amsa irin gaisuwar sa ba, ta san bai taɓa shigowa gidan nan ya ganta zaune bai mata irin ta shi gaisuwan ba ko da ba za ta amsa ba, amman sai ta ga yau ya wuce fuu kamar Iska sai Nasir ne ya bari da gaisheta ta amsa a ranta tana tunanin me ke faruwa?
Wata zuciyar ta ce"Me ko ya faru, abin da ya faru da safe ne uwar ta kira duka ƴaƴanta ta sanar da su, sun zo sun cika gida, yau ko sai dai a yi fito na fito."
Tuna haka yasa ta ja tsaki kawai ta cigaba da aikinta.

  Ɗakin Inna cike da ƴayanta da jikokinta suna ta faman maida yadda aka yi tun bayan zuwan su Yaya Amiman, Inna Meri alwala ta yi ta koma cikin ɗakinta kawai ta zauna ta rasa mafita. Domin ta gama yarda Baban Inna baya son  farincikinta sannan Babban Burinsa ya ga ya ɓata mata rai ya saka ta a cikin wani hali, ina amfani wannan jin kunyar da ya jawo mata, kamar daga sama ta ji muryaansa a cikin falonta cikin kaushi yana faɗin" Ina Mimin take?
Sai falon ya yi tsit, kowa na kallon kowa ciki  mamakin ganinsa ba su Bintu ba hatta su Yaya Amina sun kasa mgana domin suna ganin yanayinsa a fusace yake.

  Kawai sai ya fita har yana bangaje Nasir ɗakinta yana buɗe ne sai dai an sakaya ne shiga cikin ɗakin ya yi yana kiran sunanta amman shuru shi ne har bedroom ɗinta har toilet ya leƙa ba kowa ya duba kayanta na cikin wardrope ya ga ba'a taɓa komai ba.
Sai hankalinsa ya ɗan kwanta da sauri ya fito daga ɗakin ya sake dawowa ɗakin Inna sai ya iske Nasir na durkushe suna gaisawa da Inna.

"Inna me ya sa kika bari Mimi ta tafi?

  Ji wata tambayar renin wayau haka Hibba da Bintu suka ce acikin ransu, Inna kuma baƙin ciki ya sa ta kasa mgana kawai miƙewa ta yi ta shige ciki ta bar shi nan tsaye jiki a sanyaye, Yaya Amina ce ta yi gyaran murya kafin ta ce"Tun jiya Mimi ta tafi gida nima ina faɗan me ya sa suka barta ta tafi? Shi ne suka ce min Inna ta ce tafi,sannan sun yi sun yi su hana ta tafiya ta ce sai ta tafi."

"Is ok! duk in da ta je ma ai za ta dawo, Nasir ta shi mu je."

  Haka kawai ya faɗa cikin bacin rai sannan ya bar ɗakin sai ma ya fice daga gidan gabaɗaya. Nasir mamaki ya kama shi Aji yaushe zai yi laushi ne ya gane Annabi ya faƙu? A mota ya same shi yana cika yana batsewa sai da ya shiga motar ya rufe kawai sai ya ga Aji ya ja motarsa sun bar kofar gidan.
Cikin mamaki ya juya yana kallonsa kafin ya ce" Ya haka?  mu da muka zo ban haƙuri?
Kamar ba zai yi magana ba, hankalinsa na wajen tuki sai can ya ce"Inna ta yi fushi ba za ta sauraremu ba yanzu. Sai bayan kwana Biyu in ta huce."
"Ita Mimin fa? Ba za mu je can gidan Hajiyar mu ba ta hakuri ba?
Kallonsa Aji ya yi na wani lokaci kafin ya ce"Itama ka ƙyaleta, duk in da ta je ai za ta dawo tunda da aurena a kanta."
Nasir ya ce"Ina mganar da ka ce ta ce tana jiran takardanta in kaƙi, za ta kai ka Kotu.".
Cikin mirmishi Aji ya ce"Kai ka yarda za ta iya kai ni kotun? To ta kaini kotun sai a ga ni shege ka fasa."

  Nasir mamaki ne ma ya hana shi magana har Aji ya maida shi gida. Shi dai har cewa ya yi ya kira ta a waya.Aji ya ce ko ya kirata ta hau dokin zuciya ba za ta ɗauka ba shi kuma ba ya son ya kira ba'a ɗauka ba in ransa ya ɓaci abun ba zai yi mata daɗi ba.
Yana ijiye Nasir a gidansa ya juya kan mota ya koma gidansa. Sai da ya yi wanka ya sauya kaya sannan ya kunna wayarsa ya kira Mu'azzam. Shima dai duk mgana ɗaya ne bai kyauta ba Inna ta ce ta cire hannunta a kan shi, shi na Innar ya fi damun shi sai kawai ya ce"Mu'azzam kar ka damu kanka, ba sai ka taho ba komai zai dai dai ta in sha Allahu."
Mu'azzam ya ce"Ta ya ya? Inna ta rantse da Allah ta baza ta saka baki ba. Na yi ta kuma Kiran wayar Mimi ba ta ɗauka ba, mun yi mgana da Baba zan shigo jibi sai mu dumguma mu je mu same ta mu ba ta hakuri."

  Kai Tsaye ya ce"Ni ban aike ku ba, kowa ya cire bakinsa a mgana ta da Mimi, ba kuma wanda zai je ba ta haƙuri."
Daga can bangaren haka Mu'azzam ya

3 / 49