Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👠Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*
Sallah da kwana uku mai gyaran jiki ta fara zuwa gida yi ma Mimi, kuma gashi in an fara ba'a san ana yawaita zirga zirga in da ma Allah ya taimake ta a satin sau uku take da karanta labarai, sai ta samu natsuwa amman duk ranar da za ta fita dogon hijabi da safa fuskarta ne kaɗai a waje kuma kowa ya ganta sai ya yi maganar ta ƙara kyau da fari har da su Aisha Farida iyayen gulma waɗanda Rukky daman ta gaya musu mijin Mimi yana nan yana danƙara mata wani katon gida, sai bakin su ya mutu daman can suna ta faman yawo da mganar ita ko Mimi har yanzu tana nan a wannan gida kamar a kurki?
  Tun da ba wanda ya san abin da ya faru ya sa daga Rukky sai na jiki jiki. Ba wanda Mimi ta yi maganar da shi, sai dai ma na faɗan cewa za ta koma sabon gida. An shirya daman za'a yi waliman sauka a gidan Aji kuma daman ya ce za'a yi Saukan Qur'ani a gidan kafin ta tare, daga shi har ita ba su da sukuni ita tana ta fama da shirye shirye. Shi ma kanshi baya samun zama tun salla ba su ƙara haɗuwa ba sai dai su yi mgana ta waya. Tuni har ta karɓo ɗinkunan da ta ba da ɗinki. Maganar kayan gida kuma daga waje Mommy wannan karon ta yi mata Oder bayan sun yi mgana da Daddy, Cikin Satin nan ma kayan za su iso. Sai turarukan wuta na jiki da na ɗaki, duk da ta lna da su amman ta siya wasu ta ƙara domin wannan karon ba auran wasa za ta je yi ba, auran ne da gaske take kuma fatan har Abada ya zama mutuwa ce za ta raɓa.
 Gyaran jikin sati ɗaya a ka yi mata. An yi mata dilka da halawa, masha Allah Mimi ta yi wani irin kyau, fatar ta ta yi wani irin silɓi da tsantsi. Ta ɗan dakata da zuwa wajen aiki tunda ta samu izinin Manaja da cewa za su tare a sabon gida akwai shirye shiryen da za su yi. Sai ya ba ta sati ɗaya shi ya sa suka samu lokacin zuwa kunshi da gyaran kai ita da Rukky. Wacce ba ta da zence sai na Nasir, Mimi ta gaji ta ce"Wai kuma kike ta yaɓon Nasir. Bayan kin gama zaginsa da cewa ɗan renin wayau ne." Sai Rukky ta harare ta kafin ta ce"Ba na son sharri, lokacin kafin mu fara mu'amala ne na san shi sosai."
Mimi ta kalleta a karkace kafin ta ce" Ikon Allah! To Allah ya tabbatar mana da alheri."
Rukky ta amsa da Amin tana murgaÉ—a baki, Tunda Nasir dai ya yaÉ—a manufarsa kuma ta amsa masa.
 Gyaran kai Mimi ta fara yi sannan sai washegari tun safe suka tafi kunshi, ba da motar ta ta je ba ga shi kuma sun yi dare dole Aji ta kira ya zo ya ɗauke su. Tare da Nasir suka zo ita dai Rukky a hannanye a ka yi mata. Ba su bi su Mimi a daidaita Nasir ya tara zai raka Rukky gida, sai da suka hau kan titi ne Mimi ta kalli Aji lokaci ɗaya tana faɗin" Abun mamaki, Nasir wai aure zai ƙara?
Hankalinsa na wajen tuƙi ya ce"Ikon Allah me? Ai ba abun kunya ba ne, ko kawar ta ki ta fi karfinsa ne.?
Mimi ta kama baki kafin ta ce"Ni ban ce ba, kawai dai ina mamaki ne.Duka duka fa na ga Yayansa biyu ne, kuma zai ƙara aure sai na ga kamar ya yi sauri da ya ƙara aure."
A kaikace Aji ya kalli Mimi kamar zai yi mgana sai kuma ya fasa. Sai ya kauda mganar da cewa" Yau masu aiki fenti suka yi , zuwa gobe za su ƙarisa."
Mimi ta jinjina kai kafin ta ce" Aikin ya yi sauri gaskiya. Daman Gobe za'a kawo kaya, Mommy ta min mganar in da za'a ijiye kayan, na ce daman zan maka mgana in an gama gidan sai a je a gyara a sauke kayan a can kada ya zama wahala biyu."
 Aji ya yi shuru kafin ya ce" A'a sai an gama daman na saka Baba ya samo waɗanda za su yi sauka ina so kafin a fara komai sai an gama saukan Qur'anin da na ce miki." Cikin gamsuwa Mimi ta ce"To ba matsala, Allah ya nuna mana."
Sun ƙarisa gida kenan Aji ya kalli Mimi kafin ya ce" Ina Atm ɗina? gabana na ta faɗuwa na san gabaɗaya kin gama kwashe min tattalin arziƙina."
Mimi na dariya ta buɗe karamar jakarta ta ɗauko ta mika masa ya karɓa lokaci ɗaya ita kuma tana faɗin" Na gode Mijina, Allah ya ƙara arziki da wadata."
Ya amsa da Amin yana yi mata wani kallon ƙasa ƙasa kafin ya ce"Dole ki yi min addu'a mana tunda kin gama ƙwaçe min ƴan kudaɗe na."
 Yana dariya tana taya shi, sun ɗan jima a Motar suna Hira kafin ya rakata har kofar falon Hajiya sai da ta shiga gida sannan ya koma ya shiga motarsa ya bar gidan ita kam Mimi wani abu ne ke ba ta mamaki duk irin rawan kafa nan na matasan zamanin nan Aj ba shi da shi, ko dai ba shi da lafiya ne? In ya zo fa daga rike mata hannu in ya yi abu mai nisa ne ya rumgumeta, ita ce ma take sumbatarsa wani lokacin, ba ya wuce gona da iri sannan yana da kiyayewa har tunanin Ko dai ba shi da lafiya ne duk ta yi shi, bayan ya koma gida ya kirata sai da ta yi masa mganar da cewa.
 "Wai ba ka ga lalli na ba ne, ko ka ce ya yi kyau? Sannan na yi gyaran jiki kowa ya ganni sai ya yaba amman ban da kai."
Kai tsaye ya ce"Kin nuna min ne?
Baki ta buÉ—e kamar ya na kallonta kafin tace"Au ba ka gani ba,?
Kai tsayen ya sake cewa" Ni ban gani ba."
Sai Mimi ta kasa mgana ganin zai yi wasa da hankalinta cikin raÉ—a ta ce" In dai ko ba ka gani ba, ko dai ko dai.?
"Ko dai mene ne?
Sai ta kasa mgana ta koma tana dariya ya fahimci maganarta bai san lokacin da ya yi sariya mai sauti ba, kafin ya ce "Yaro yaro ne. Yaro man kaza, Uhmm"
Haka kawai yace bai ƙara yi mata wani mgana ba suka cigaba da hiransu ita ba ta san yadda yake iya surving ɗin rayuwarsa in har ya zo su ka haɗu ba, ko muryanta wanka ta ke saka shi in ko ya je ya ganta in ya dawo sai y yi wanka dauriya yake yi ba ya so ya wuce gona da iri, kuma shi yana da kiyayewa ba ya son ya watsar da darajan auransa a kan titi shi ya sa ba ya rawan kafa wajen taɓa jikinta shi ya sa take tunanin ko ba shi da lafiya ne? Lalle ko zai nuna mata kwanjinsa da lafiyansa ƙila har sai ta fara cewa ita ta gaji.
 Kamar yadda ya faɗa washegari ma'aikata suka karisa fenti, sannan a daran masu sauka suka fara, wani malami ne mai almajirai shi ya wakilta babban Almajiransa da yara goma suka kwana a gidan suka kuma sauke Qur'ani zuwa wayewar gari tare da sauran addu'o'i, zuwa safe kuma a ka sallame su da abun sadaka.Mansoor ya yi mgana da Inna kan gyaran gidan tunda an gama aiki sai Inna Meri ta kira ƴan'uwansa mata su Yaya Amina daman Hibba tana nab ba su koma ba,Mu'azzam hutun sallarsa na Sati uuɗu ne sai bayan tarewar Mimi za su koma, su suka hadu har da Walida da Mariya da matar Auwalu da ya ce itama ta je ta kama musu suka je gidan suka share suka goge amman fa kowa ya san wannan gidan ya kai makura wajen haɗuwa, har yamma suna can sai gabda mangariba suka gama gyarawa suka koma gida suna zuzuta ma Inna kyan gidan da tsaruwarsa.
 Bayan kuma barowansu gidan ba daɗewa kayan Mimi suka iso, Khadi daman ta zo garin a ranar ita da Baaba Uwani da Anty Mama cewa ta yi ba ta jin daɗi, Mimi ta kira Aji ta gaya masa sai ya ce su haɗu a ƙofar gidan da kwatance da komai suka isa. Shi ya ba su key ɗin gidan suka kuma gaisa da shi cikin mutunci. Masu kayan daman tare da masu haɗa su suke tafe a daran aka gama haɗa komai sauran ɗakunan kuma sai gobe, Ita kanta Khadi sai da ta yi santin gidan nan haka ta koma tana ce ma Mimi" ke ashe dai mijin nan na ki kuɗi ne da shi, Hajiya kin ga gida? Ma sha Allah wlh gida ya yi kyau Allah ya sa a shiga a sa'a"
Hajiya ta amsa a fili Mimi kuma ta amsa mata a ciki,.Washegari Jawahir ta iso itama duk ba wani taro ba ne Yayan Yaddiko sun zo da su aka haÉ—u a ka koma gidan da sauran kayan Mimi na gidan Daddy aka gama gyaran gidan gabaÉ—aya.
 Hatta bangaren Aji an saka masa kujeru a falo bedroom kuma gado da wardrope, ɗayan ɗakin daman ya ce kada a taɓa shi akawai abib da zai yi da shi, babban falon Mimi kujerun ta kalan browna mai haske haka ma kalan fentin yake sannan cafet da komai kalan shi kenan da labule, kowani falo Bedroom guda biyu ne. To duka gadajen guda biyu masu ruwan browan ne mai haske sai ƙaramin falon aka maida mata Kujerunta na farko, da gadon ta ɗayan bedroom ɗin kuma aka siya masa wani gado shima amnan ƙarami ne.
Kitchen ɗin ta kuma ga fali da fili. Nan aka cika mata da kaya, firizanta guda biyu, bayan akwai wani a ɗayan bedroom ɗinta amman shi ƙarami ne ga kuma again fridge a wajen dinning, gaskiya gida ya yi kyau ma sha Allah suka turare shi da turaren kamshi sannan suka yi ta Video Khadi jiki na rawa ta turama Mommy da Madiha, ita kanta Madiha tasan gidan da take ciki a lagos bai fi wanda Mimi za ta shiga ba yanzu duk kushenta sai da ta ce"Woww gidan ya yi kyau Khadi. Ko dai haya ne ba na shi ba ne?
Khadi na dariya ta ce" Na shi ne to ko wata biyu ba'a yi da fara gina shi, Kuɗi ne da bakin mijin nan na Mimi wallahi"
 Madiha ta jinjina kai kafin ta ce"Na ga alama wato abun na shi ma mugunta ce."
Ita dai Khadi na ta yi mata dariya, Mommy kuma da ta gani ta yi ta saka albarka da tarin addu'o'i, Rukky ta zo itama daga baya ta ga gida ya yi kyau ɗas da shi itama ta saka albarka washegari ya kama jumma'a a kuma ranar Mimi za ta tare. Daga nan bayan sun gama gyaran sun rufe gidan tunda akwai megadi suka koma gida suna ta ƙara Koɗa kyan gidan, Rukky kuma tana ciki tana na taya Mimi haɗa kayanta na gida a daran suka fito da akwatin da suka haɗa reras guda takwas cike da kaya, bayan waɗanda a ka dinka, kowa nata mamaki Hajiya ce kaɗai tasan da maganar kayan kefe. Sai Mommy amman ita ba ta gani ba Mimin dai ta sanar da ita.
 Khadi na ɗaga kaya tana santi ta gaji dai ta ce"Ke wai a ina aka haɗa kayan nan ba mu da labari ne? Rukky ce ta ba ta amsa da Cewa" Anan garin mana cikin azumi muka yi ta shiga kasuwa har da shi, ina gaya miki Anty Khadi Atm ɗinsa ya bamu muka siya komai da komar bai karɓa sai kwanan bayan mun gama duka shirin mu."
Khadi ta zaro ido kafin ta ce"Kai kaji rabo, kuma kuɗin ba su ƙare ba?
Rukky ta ce"Ko girgiza kuma mun kashe kudi ya yi miliyan huÉ—u wlh,"
Sai kowa ya fara hinjina kai, Æ´ayan Yaddiko na ma juna gulman daman mai kuÉ—i ne, Rukky ke ta kora jawabi da cewa" Daman fa da kuÉ—insa, kwai dai yana da dalilinsa ne tun fark. To É—an kwallo ne fa kuma Babba wallahi an ce suna samun mahaukatan kudaÉ—e."
 Khadi ta ce"Na ga alama. Muhammad ma ai ya faɗa min na ga kuma zahiri, ga gida ga lefe ina ga sama da miliyan talatin sai da ta yi kuka kai jama'a, amman ya shammace mu."
A na ta mata dariya ba ta gaji ta kara gyarawa tana ɗaukan Video ɗin kayan nan da nan ta tura ma Dr da Madiha da Mommy ta ce lefen Mimi ne,.Daman Mommy ta san da maganar ta na gani ta saka albarka amman ita kanta ta yi mamakin yawan kayan da darajarsu, Madiha kan sai ta kasa magana ta ce au har da lefe an yi ne? Khadi ta ce ga zahiri nan ta na gani lefe ne na gani na faɗa. Dag anan bakin Madiha ya mutu ta ji daman ta zo domin ta ba ma idanuwanta abinci amman dai za ta yi koƙari ta zo ko da baya ne domin ta ga komai da Idanuwanta.
 A daran suka gama haɗa komai, bangaren kayan gara ma Daddy ya aiko da shi komai buhu, itama Mimi ta kara siya ma kanta abin da take so, kamar irin su kayan kamshin girki da zannuwan gado na kamfanin FHB CLOTHING domin zamnuwan gadon su masu inganci ne, shi ya sa Mimi ke yaba kayan su, in kina so kema ki samu zannuwan gado masu kyau kamar irin na Mimin Aji nemi FHB CLOTHING Phone no 08034109622
Wtsapp no.08080266674
  Sun yi mgana da Aji da asuba a kan mganar Walima ita Mimi ta so a bari sai ranar asabar amman Gogan yace a ranar Za'ayi komai a gama shi.Saboda haka ta yi duk abin da ya kamata kafin biyu tana gidanta sai a yi waliman daga lokacin zuwa dare, Da ta gayama Hajiya da su Khadi su ka ce hakan ya yi zaman me za'a yi dama tunda ba wani gagarumin taro ba ne, Rukky ta faɗa ma su Aisha Farida da su Glorin na wajen aikinsu amman direct can gidan za su sauka tun da a matsayin walimar gidan a ka gayyace su.
Tun safe Mimi ta yi wamka mai kwalliya ta zo ta yi mata sannan sun kira mai hot. Wani leshi Mimi ta saka ɗinkin riga da sikat kayan sun karɓe ta matuka ta sha hotuna ma su kyau da yarari. Gidan ba kowa daga su Khadi sai Anty da ta zo da safe da Yaddiko da ƴayanta, Rukky ma tun safe ta zo ita da Bibi, suma sun sha kwalliyar su gwanin burgewa, Mama ma ta zo ita da ƙannen Jahedd wanda dole dai ya hakura da Mimi tun da Har Daddy sai da ya kira shi ya yi masa fata fqta, sannan tun bayan abin da ya faru tsakaninshi da Mimi ya fara kokarin cire ta a ranshi tun kuma bayan sallah da ya tafi bai dawo ba amman ya yi ma iyayensa alƙwarin cire soyayyar Mimi a ranshi domin ya gina sabuwar rayuwa.
 Rukky har video ta saka Mimi ta yi na waƙar kewa na mawaƙi, Auta waziri ta kuma tura ma Nasir. Shi kuma bayan ya gani sai ya tura cikin group ɗin su ya yi tagging ɗin Aji da cewa"To kai fa Aji ka ji, maganar gaskiya yau kada ka ɗaga kafa Amarya ta ce ta yi kewar ka."
Su Ahmad suka fito suna ta dariya shima yana gari bai koma ba shi da matarsa,Aji kuma bai ma ga sakon ba sai daga baya yana gani ya yi delete for everyone, Nasir na ganin haka ya ƙara turawa Aji ya sake gogewa tun da dukkansu kowa admin ne, Har wajen sau uku, Aji na ganin haka ya danna ma Nasir kira yana ɗagawa ya ce. "Nasir miye haka? Hoton matata ne zai sama abun wasan ka?
Nasir na dariya yana kwaikwayon waƙan" Kewa. Kewa. Nayi kewar masoyiya."
Aji ya ce"Mallam ka goge shi a wayarka tunda ko a shari'a ya haramta ka riƙa ganin hoton matata, to wai ma a ina ka samu wannan Vedio? Ni fa ban da shi"
Nasir na dariya ya ce" Baby Rukky ta tura min." Aji ya girgiza kai kafin ya ce"Lalle ne ma,." Daga haka ya katse wayar ya kira Mimi, an ci ko sa'a Rukky ta É—auki wayar Mimi na É—akin Hajiya kai tsaye ko ya ce mata me ya sa ta tura ma Nasir video É—in Mimi? Sai tacl ce saboda ba ta da lambarsa ne. A dakune ya ce" Ki goge shi haka kurum ni ban ga adon matata ba wani gardi na can na gane min hakan adalci ne?
 Rukky na danne dariyanta ta ce ya yi hakuri za ta goge, sannan ya ce yauwa ya kashe wayar ya bar Rukky na dariya. Kamar haɗin baki sai ga Nasir ya kirata nan fa ta sabar da shi abij da Aji ya ce ya na dariyan mugunta ya ce"Kyale shi, nima ai ya kirani ya na min surutu."
Rukky ke gaya ma Mimi abin da ya faru, Mimi ta harareta kafin ta ce" Ke ma da gulman tsiya, Mijina bai ga kwalliya ta ba sai saurayin ki.?
Rukky ta ce"Na bani, ni da masu miji miji ko?
Mimi ta yi mata fari kafin ta ce"Kwarai, masu miji ehe."
Nan Jawahir ta zo ta same su Mimi ta gaya mata abin da ya faru tana dariya ta ce"Maganar gaskiya ba'a kyauta ma Ango ba dole ranshi ya ɓaci, ke kuma Rukky baki kyauta ba."
Mimi ta fahimci suna mata shakiyanci ne sai ta bar musu wajen kawai.
 A can gidan Inna Meri ma kamar tana sake sabon biki, makota sai zuwa suke