Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
kuma da ta nuna sun fi kowa ga shi nan su ne rayuwarsu ke wulaƙanta gwara gwara ma Auwalu da shi yanzu ya zama Enginer ba ya gini sai dai karɓan kwangilan gini kuma ba laifi yana samu sannan ya na yi mata tunda ba halinsu ɗaya da Saddiqu ba, Jummai sai dai ta zo ta ƙarbe na ta, har gwara ma Zuwaira to yanzu haka shi kan shi Saddiqun kusan ci da shi na wajen su ne tunda ba shi da komai yanzu sai bakin rai.
Mariya kuma ba domin su ba da tuni itama rayuwarta ba ta inganta ba, tana da tabbacin da bikin ta in ya zo su ne za su yi komai da abunda uwa za ta yi da abin da ubq zai yi ta na da tabbacin suna yi domin Allah ne ba domin komai ba in da ace suna yi domin ganin ido ne da tuni sun daina tun baya da take nuna hassadatan a fili, yanzu kan ta saduda tunda ta ga jama'a ma suna gudunta har su Gaje yanzu sai su yi wata ba su leƙo ta ba, ko wani abu ya faru a anguwa sai dai in ta biya musu su ce sun shiga jaje ko Allah ya kyauta, amman ba sa nemanta Ta dai fahimci duniyar ce gabaɗaya ta sauya gwara ka aikata alheri yanzu in da mutuwa ta yi fa? Haka mutanen da ta zauna da su za su yi mata? ta kuma fahimci lalle ka zauna da mutane lafiya shima wani abu ne, Sannan ka aikata alheri tun kana duniya za ka ga amfanin haka, ga shi Meri ta bar mata gidan amman kamar ta tafi da duk wani albarkan gidan gabaɗaya.
******
Tunda Inna Meri ta ga Baba Ɗanjuma da Mansoor ta san ƙaranta ya kai. Shi ya sa tunda suka shigo ta haɗe rai, ta ga fa zuwan su suna zaune a falo suna jiranta Baba Ɗanjuma ke saman kujera Mansoor kuma yana zaune a ƙasa. Walida ce ta kawo musu ruwa Aji sai faman waige waige yake yi ko zai ga Mimi amman ba ta fito ba.
Inna Meri ko kamar da gayya ta shiga aikace aikacenta wai wanke wanke da daddare saboda dai kada ta sauraresu.
Mansoor yunwa ya ke ji bai ci wani abun kirki ba, sai ya tambayi Walida abin da suka dafa kai tsaye ta ce"Tuwo Inna ta yi da rana na zubo maka ne?
Sai ta amsa mata da eh, ai kam tana zuwa Kitchen ɗin Inna ta ga za ta zuba abinci ta tambayeta wa zai ci? Ta ce yayanmu ne.
Kai tsaye Inna Meri ta ce"ba zai ci tuwon ba, rufemin kular nan"
Cikin mamaki Walida ta ce"Saboda mene Inna? Inna ta mata wani kallo kafin ta ce"Sai na ji shaƙa sannan."
Walida na jin haka ta yi sum sum ta fita daga Kitchen ta koma ta gaya ma Mansoor abin da Inna ta ce sai ya yi mirmishi kawai ba tare da ya yi mgana ba Baba Ɗanjuma ya ce" Me ya sa Meri take hakane? Ban san ta da wannan fushin ba."
Kawai sai ya miƙe yana faɗin bari ya je ya sameta a cikin madafin.
Yana ta shi, Mansoor ya kalli Walida yana faɗin" Ina Antyn ki?
Sai da ta kalli ɗakin sannan ta ce"Tana ciki, kila ta kwanta ne"
Kai ya jinjina mata sai kawai ta wuce ta shiga ɗakin nata, ta iske Mimi kwance amman ba barci take yi ba, ta na shiga ta yi saurin miƙewa zaune lokaci ɗaya tana faɗin" Aji ne ya zo?
Sai Walida ta ce"Eh shi da Baba, wai me ya yi ma Inna ne? Abinci ma fa hana shi ta yi.".
Mimi ta zaro ido kafin ta ce"Kai.!
Walida ta zauna gefenta tana faɗin" Wlh Allah, kuma fa ta ga har da Baba amman ta na kitchen tana wanke wanke."
Sai Mimi ta yi shuru ba ta yi mgana ba, to ita me za ta ce? duk da ya yi mata ba dai dai ba amman bai kamata Inna ta hora sa da rashin abinci ba, gabaɗaya tausayin shi ta ke ji, Kamar ta ta shi ta je ta roki Inna kuma tana da tabbacin bai ci wani abinci ba tun jiya nan, amman ba za ta iya ba sai Inna ta ga kamar ta yi rashin kunya kuma duk abin da take yi ta na yi ne saboda ta ƙwatan mata ƴancinta. Suna ciki suna jin tashin maganar Baba da Innar a talon, kenan Baba ya samu nasaran Fito da Inna Meri daga cikin kitchen.
Inna Meri na saman kujera Baba Ɗanjuma na gefenta Mansoor na gefen Baban kansa a ƙasa. Shi kuma Baba Ɗanjuma sai faman kallashi inna yaoe yi da kalaman ban hakuri faɗi yake yi" Haba maryamu ban san ki da dogon fushi ba, ina miki shedar ke macece mai afuwa, tunda har ya san ya yi laifin kuma ya ce ya yi nadama ya ba da hakuri to me zai hana ba za ki yi hakuri ki ba shi matarsa su koma gida su daidaita ba?.
Inna Meri ta yi shuru kafin ta muskuta lokaci ɗaya tana faɗin" Ya gaya maka zargin matarsa yake yi? Ya sanar da kai shi da kansa ya ce ta fitar masa a gida, shi isheshe mai gida ba."
Ta faɗa tana hararanshi lokaci ɗaya tana cigaba da faɗin" Ya yi sum sum da kai kamar mutumin ƙwarai. Ahalin ya iya aikata tsiya kala kala, ace a shekaran Baban Inna talatin da ɗoriya bai san ciwon kansa ba? Ƙanin sa Mu'azzamu wlh ban taɓa jin kansu shi da matarsa ba. Amman shi kamar wani ƙaramin yaro daga wannan sai wannan., ni kuma na gaji da wata rana ya yi abin da za mu kasa shiga mutane gwara ya sauwaƙe mata cikin girma da arziƙi na maida ma Hajiyar jikarta na ba ta hakuri."
Inna Meri ta gama faɗa tana ƙara haɗe rai shi dai Mansoor sai faman ba da hakuri ya ke yi, Baba Ɗanjuma ma haka.
"Duk ya faɗa min wlh, na kuma yi masa faɗa tunda dai ya yi nadama ki duba girman Allah ki yi hakuri Maryama.."
Baba ya kirata da mafi soyuwan sunan da ya ke kiranta da shi wani lokacin, ta ɗago ta kalle shi daga shi har ɗan na shi sun maraiiraice sai ta ji wani abu a ƙasan ranta, Da sauri ta kauda kai tana faɗin"Shi mai uba ko? Ya je ya ɗauko ka, kun yi min taron dangi saboda ni kunga nawa uban ya mutu ko? Da Sauri Baba ya ce"Ko ɗaya, ke yanzu kin fi wata mai uban, Allah ya ba ki ƴaya sanyin Idanuwanki waɗanda suka lulluɓeki da alheri sannan kina da ni, ina da tabbacin kin gama samun komai a nan duniya sai fatan cikawa da Imani kawai Maryama
Inna Meri kauda kanta ta yi tana share ƙwallah kafin ta ce"Shike nan amman ya sani wannan ne na farko kuma na ƙarshe wallah tallahi in ya sake aikata wani kuskuren sai ya rasa Binta."
Da sauri Mansoor ya ce"Ba zan ƙara ba Inna, ki yarda da ni."
Kallonsa ta yi kafin ta ce"In ka ji irin haka ya shige ka, ka kira sunan Allah domin ka samu natsuwa ina ƙara yi maka nasihan cewa ka koyi sarrafa wannan zuciyar taka saboda watan wata rana za ta kai ka ga aikata abin da ko kaso ka gyara ba zai taɓa gyarun maka ba."
Kansa na ƙasa ya ce"In sha Allahu."
Baba Ɗanjuma na Mirmishi ya ce"Mun gode, Sai ki yi mata mgana ta fito su tafi, In sha Allahu hakan ba zai kara faruwa ba."
Inna Meri ta gyara zama kafin ta ce"A'a.."
A tare suka kalleta cikin mamaki kafin ta cigaba da faɗin" Itama macece mai ƴanci ita kuma ya yi ma wannan laifin zan kirata a gabanka a gaban shi, in ta amince ta masa afuwa ba zan hana ta bin sa ba amman in har ta ce ba ta hakura ba, ba zan iya hana kaina goyon bayanta ba."
Baba Ɗanjuma ya ce"Ba ma za'a yi haka ba, Kirata ta zo nima na ba ta hakuri."
Inna Ta mike lokaci ɗaya tana faɗin"Ba ma ta da lafiya, gwara ta zauna waje na har sai ta warware wannan mara tunanin magana kawai zai iya gasa mata da zai ɗaga mata hankali wani abu mara kyau ma ya faru.
"Me ke damun ta?
Baba Ɗanjuma ya tambaya kafin Inna ta yi mgana da sauri Mansoor ya ce"Baba Inna ce ta ce Mimi na da ciki, tsakani ga Allah kula da mai ciki ai sai uban cikin ko?
Inna ta ji kunyar duniya ya kamata Baba ma kai ya kauda kafin ya ce"Wannan gaskiya ne. To to Allah ya raba lafiya."
Inna meri kuma daƙuwa ta maka ma Mansoor kafin ta ce" Ba ka da kunya ko?
Sai a lokacin ya tuna tabargazan da ya yi da sauri ya maida kai ƙasa yana sosa keyarsa ya na yar dariya.
Walida Inna ta kwalama kira bayan ta fito sai ta ce ta kira mata Binta.
Mimi daman tana zaune nem Jin Inna na kirata ya sa ta mike ta zura hijabin Walida zuwa Falo tun da kuma ta fito gogan ya kafe ta da ido kuma maganar gaskiya ta rame ta yi wano fayau to wai daman haka alamun cikin yake? Me yas a shi bai gane ba?
Kusa da Inna ta zauna kanta na ƙasa ta gaida Baba ya amsa cikin sakewa lokaci ɗaya yana faɗin"Ya jikin Fatima? Kanta na ƙasa ta amsa da sauki ya ce Allah ya ƙara lafiya Mansoor a ka bari da amsawa Inna ta wurgeshi da maficin Hhnunta sai da ya same shi shi ya sa ya kama bakin shi.
Bayan tattaro duka bayanan Baba Ɗanjuma ya sake ba ta hakuri da cewa"Ki yi hakuri kin ji ko Fatima? Itama uwar taki mun ba ta hakuri kuma ta ce ta hakura amman mu tambayi izinin ki, ina so ki cire komai a ranki ko domin lafiyan abib da ke cikin ki, ki tashi ki bi mijin ki kin ji ko? Bai kyauta ba mun masa faɗa ya kuma ya ce ba zai ƙara ba, mu abin da kika yi mana na ɗauƙan mu iyayen ki ya fi komai yi mana aɗi Allah ya yi muku albarka Allah ya zaunar daku lafiya tare da zuru'a mai albarka."
Wannan karon gogan a cikin ransa ya amsa sai Inna ce ta amsa a fili. Mimin kanta na ƙasa ta kasa mgana.
"Kin yi shuru Fatima? Ki ce wani abu mana."
Baba Ɗanjuma ya tambayeta. Sai ta ƙara sadda kanta ƙasa kafin ta ce" Na hakura Baba, ni daman saboda zargin yake yi min ne ya sa na kawo muku wannan mganar."
Da sauri Baba ya ce"Eh wlh, kuma kin kyauta mganar zargi ai babban mgana ce, an yi masa mgana ba zai ƙara ba."
Sai Mimi ta jinjina kai kafin tac ce"Shike nan zan bi sa mu koma."
Baba ya ce Alhandulillah Allah ya yi miki albarka Mansoor kuma har da sauke Ajiyar zuciya.
"Amman kuma ina da sharaɗi. Sharaɗin nawa kuma ina so ku zama shaida Baba da Inna.."
Haka ta faɗa kai tsaye tana kallon Aji da ke kallonta, Inna ta yi mirmishi kafin ta ce" Faɗi sharadin ki, muna goyon bayan duka hukuncin ki Binta."
Sai ta kauda kanta kafin ta ce"Na yi hakurin zargin da ya jefeni da shi, amman ku zama shaidata wlh tallahi in har ya ƙara maimaita wani abu makamcin haka zan tafi, kuma in na tafi bazan dawo ba, domin ba zan iya zama da wanda bai yarda da ni ba sannan ba zai iya shaida na ko da a bayan idanuwana ba ne."
Baba ya jinjina kai kafin ya ce"Gaskiya ne, In sha Allahu ma haka ba zai ƙara faruwa ba." Inna Meri kuma ta ce"Kin yi min dai dai, ni da kaina wlh in ka ƙara sai na tursasa maka ka saketa, in dai kai ba ka san baiwar da Allah ya yi maka ba to ka in ka yi sakaci Binta ta bar ka sai dai ka mutu ba ka yi aure domin ban ga macen da za ta yi hakuri ta zauna da kai da mummunan hallayarka na rashin lissafi ba. kishi ai ba hauka ba ne sai ka hana yarinya walwala kawai saboda kishin ka na banza? To wlh ka shiga hankalin ka tun kafin wata rana ka yi ta kuka ba mai share maka hawaye."
Baba Ɗanjuma ya ce"Gaskiya ne, amman duk hakan ba zai kai ga faruwa ba in sha Allahu"
inna Meri ta harari bangaren Mansoor kafin ta ce"Shi dai ya sani,damar ta karshe gare shi, ki je ciki ki shirya sai ku tafi."
Mimi ta miƙe a sanyaye ta wuce Mansoor ya bi ta da kallo, shi yanzu ai yana cikin TSAKA MAI WUYA. Ya san yana da kishi amman kuma dole ya koyi sarrafa kishin sa matukar yana son zaman lafiya.
Bayan tashin Mimi nasiha faɗa haka Inna da Baba suka tasa shi suna yi har sai da Mimi ta fito Walida ta rakota da jakarta da kayanta da Walidan ta wanke mata.
Inna ta kalli Mimi lokaci ɗaya tana fadin"In kina bukatar wani abu ki gaya min sai na saka Walida ta kawo miki kin ji ko?.
Sau ta gyaɗa kanta, so take yi ta ce a zuba mata tuwo amman ta kasa mgana sai Walida ta yi ma raɗa ita kuma ta gaya ma Inna. Mirmishin su na manya ta yi domin ta na da tabbacin domin Mansoor za ta ɗauki tuwon nan sai ta ce Walida ta zuba musu a kula su ta fi da shi.
Mansoor ya ce Baba ya zo su fara sauke shi a gida yace a'a zai samu mai mashin su dai su tafi. Har bakin mota Walida ta rakata ta saka musu tuwon a bayan mota da jakar Mimi da kayanta tare da magungunta. Har su ka bar anguwan nan kallo Aji bai ishi Mimi ba shi kuma sai ya rasa abun cewa, ya kalleta sai ya ga ta na kallon gefe ne ba ta ma son kallon shi, sai ya rasa abun cewa sai da ya ji ta na tari sannan ya ce"Sannu, ko a rage A.c ne? Ta yi masa banza da kansa ya rage iskar motar sannan ya koma yana faɗin" Har da mura ke damun ki ko?
Kamar ba ta motar haka ta yi masa, Ya yi ta taƙalan mgana amman Mimi ko uffan ba ta ce masa ba, har suka isa gida yana hon megadi ya buɗe musu get suka shiga gidan yana gyara parking ta yi saurin buɗe motar ta fito, baya ta buɗe baya ta ɗauko jakarta da ledan mganinta da sauri ya zagayo ya karɓa lokaci ɗaya yana faɗin"Ke da ba ki da lafiya ina ke ina ɗaukan kaya Mimi?
A sanyaye ya yi mganar, sai kawai ya ga ta ƙara kauda kai ta sakar masa kayan hannunta ta juya a hankali ta nufi cikin gida shi a ka bari da kwaso kayan har da kwandon da Walida ta zuba musu tuwon ko da ya shiga falon har ta shige ciki ya duba ba ta a bedroom ɗinsu a she ɗakinta ta shige a bin ta yana shiga kuma ya ganta ta tuɓe za ta shiga wanka, bai yi mgana ba ganin kallonsa ma ba ta san yi, dole ya koma falo ya zauna yana shafa kansa.
Mu'azzam ne ya kira shi suka yi mgana ya ce masa Inna ta hakura, shima sai da ya ƙara yi masa faɗa sannan suka yi sallama Hibba na gefensa da katon cikinta ta ce"Kai ni dai na kasa gane halin yaya Mansoor."
Mu'azzam ya ce"Ya dai kusa zama uba watarana sai labari."
Hibba ta zaro ido kafin ta ce"Mimi na da ciki?
Sai ya gyaɗa mata kai, sai kawai ta saka shewa har suna tafawa da Mu'azzam a fili ta ce wa ya ga Yaya Mansoor da ɗa akwai shan kallo, Aji baya jin kunyar faɗan Mimi da na ciki shi a ganinsa abun alheri ne miye kuma na ɓoye ɓoye.
Ya na nan zaune ya na ɗuba saƙonnin sa na kan WhatSApp da ya kwana biyu bai duba ba, har da na Makama ya tura masa hoton jaririyar, tun ranar da a ka yi haihuwar bai ma duba ba kuma ko barka ma bai kirasa ya yi masa shima yana cikin wani hali alokacin. Sai yanzu hankalinsa ya dawo jikinsa tunda Mimi ta dawo gare shi, a kasan hoton jaririyar da Makama ya turo masa ya yi tagging ya rubuta" Allah ya raya, nima nan da lokaci kaɗan za'a haifa min irin ta ko irin shi a gidana."
Ya gama rubutawa kenan ya ji buɗe kofa, Ya juyo sai ya ga Mimi ce ta yi wanka ta saka rigar barci riga da wando masu taushi, ba ta kalle shi ba ta nufi jakarta da ledan mganinta ta ɗauka ta juya kenan ta ji ya ce"Tuwon fa? Ko ba za ki ci ba ne?
Ba ta juyo ba a sanyaye ta ce" Na ƙoshi."
Daga haka ta yi shigewarta ɗaki, yana jinta tana saka key sai kawai ya yi zaune yana bin ɗakin da kallo, tun bayan auransu ba su taɓa raba ɗaki ba, ko da sun samu matsala ba ta kai su ga raba makwanci amman yanzu kan ya san bashi da gaskiya shi ya sa ya kasa wani motsi. Zai jure har sai ta sauko ya godema Allah tunda Inna ta ba shi matarsa.
Haka ya zauna ya ci tuwon nan sosai leda ɗaya ya rage kawai sannan ya tattara komai ya maida kitchen miyar ya saka ta acikin Fridge ya kashe komai na falon sannan ya shiga ɗakinsa ya yi wanka ya yi shirin kwanciya sai ranar ya samu yin barci sosai da safe shi ya tashi ya buga ma Mimi ƙofa sai ya ji ta na tashi tunda ta yi masa gyaran murya, Mimi gasan ƙuma ta ke yi ma Mansoor ba ta masa mgana ko zai yi mganan duniyan nan daga eh sai a a ne, Tunda ta dawo za ta yi masa abun karyawa da na rana da na dare, a baya in ta ce ya zo ya taya ta aiki sai ya ce shi ta na bashi wahala amman yanzu haka ya ke zagewa ya na shige mata da faman nacin