Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
da Mimin Aji ta dace dashi, sannan mijin ki ya zamo sahu maza masu rabo irin Mansoor Aji.
Maeesha ma ta kawo mata gumba mai kyau ta na sha da madara. Mariya na ta nurna ganin Walida duk da tana da ƙawaye amman ai Walida ta dabam ce kuma ƴar'uwanta ce.
An je jere ana saura biyu daurin aure angon Mariya ya yi gidansa ɗan daidai an danka mata shi da kaya ko wata yar gatan sai haka gado biyu ga tibinta ga firiza ga gas ga Tv stand ga center table ga cafet ga labulayan masu kyau da zannuwan gado kitchen ma koma ya ji ga kayan garanta an yi daidai gwargwardo har dake dake ma yan'uwan Magajiya sun yo sannan su Gaje ma sun ƙara mata. Inna ce uwar Amarya da su Gaje da su ake shawara.
Aji sai ana gobe ɗaurin aure ya dawo daga Abuja ya yi kiba ya ƙara haske. Murnansa ya ga Inna da matarsa da Ummi ai ko shima ya yi mamakin girman Ummi yana dariya ya ce yar lukuta.
Ranar a gida Mimi ta kwana ana sabunta amarci sai can rana ya kawota gidan wanzamai inda ake sha'anin bikin,Inna ta bashi tsarabanta ya karɓa da godiya a ranar ma da yamma jallabiyan ya saka haka kuma ya ga Mu'azzam ma ya saka naahi, sai suka kalli juna suna mirmishi suma suna ta shiryen shiryen wajen daurin aure a masallacim kusa da su ne amman sun saka an share kofar gida an gyara shi saboda mutane. Har saddiqu da shi ake komai ya ga ba sarki sai Allah ya saduda. Yaya Mansoor sama Yaya Mu'azzam domin ya fahinci in ya yi tawaye ba riba hakama Magajiya ta faɗa masa.
Gida cike da baki ana ta hada hada
Matan sun yi ankon Atamfa na biki,sannan ko walima ba'a yi ba sai ranar lahadi a gidan Amarya.
Mariya a gidan Bintu za su yi zaman su tunda kusa ne sai ya kasance su Mimi duk suna can har da su Nafisa da Bibi matar Ahmad dai sun koma kaduna.
Har da Yan'uwansu Hibba duka da su ake sha'anin ƙannen mahaifansu Yaya Amina kuwa, daman duk wani sha'ani da su keyin shi kuma duk saboda Inna Meri ne a ka zo a ka yi ma Magajiya karan.
Ana jibi bikin nan suka kawo lefe akwati shidda kuma da kayansu ma sha Allah daidai karfin talaka mai nema.
Ranar asabar aka tashi da shagalin biki sha daya na safe aka ɗaura auren Mariya da angon ta Aminu, Baba Ɗanlami me waliyin Amarya anan wajen ya ce ya wakilta Aji ya yi ma Mariya wallici shi ya ba da auranta ga waliyan Aliyu sannan bayan ɗaurin auran ana rawan jikin gaisawa da shi wanda bai ma san shi ba an gaya masa sunan shi.
Ango da tawagansa sun sha fararen kaya suma su Mu'azzan kowa da kalan kayanshi amman sun saka babban riga har da Saddiqu da ya saka ta bikin shi, Baba ma sabuwa Mu'azzam ya ɗinka masa da Sabon takalmi a cikin gida kuwa ana ta hada hada an dafa ahinkafa da alala sannan an yi waina Amarya da ƙaawayenta sun yi firaidi rice din shinkafa da Alala sai nama da Mimi ta bada kuɗi aka siya kilo uku saboda baki Walida yan jami'an an sha kwallya tunda sun yi makeup, nan aka bar wasu ƙawayen su Mimi suka tafi da Amarya can gidan ana ta hotuna duk rashin son hoton Aji su Yaya Amina suka rike shi sai da ya shiga amman ya na rike da Ummi a kafaɗansa ɗayan hannun kuma ya na rike da Junior da damam ɗan gidanshi ne.
Ammi dai tana wajen uwarta Mu'azzam dai daman ba shi da wani nane ma yara.
Gabaɗaya ahalin gidan Wanzamai a ka haɗu a ka yi family picture su Gaje da Harira da yayansu maza da mata da su Baba Ɗanlami Inna meri da Magajiya da Baba Danjuma da su Aji da yayansu da matansu gabaɗaya a ka dauki joton kowa ya gansu sai ya ji sun ba shi sha'awa babu abunda yafi haɗin kai daɗi.
Bayan La'asar Mansoor da Auwalu suka dauki amarya zuwa ɗakinta daga umarmin Baba Ɗanjuma, tare da Inna su ka je da wata ƙanwar Magajiya sauran daga baya su ka zo bayan ango ya kawo motoci, Mariya na ta kuka domin yayyenta sun mata faɗa ta zauna lafiya kowaani aure da ta gani yanzu na da shi kalubalen gwara ma ta zauna lafiya, Walida ne da sauran ƙawaye suka kwana a gidan sauran kuma suka koma gidajemsu suka kwana su Hibba dai a gidan Inna daman suke kwana Mimi kuma Aji ba barinta daman zai yi ba.
Sai washegari suka koma kai kayan da ake ba ma dangin ango bayan sun ɗauki Mariya zuwa gidan iyayen mijin, su Mimi da su Yaya Amina sai Inna da su Gaje,an gama komai cikin girma da arziki sun mika amanarta ga dangin mijinta suka baro ta acan tana kuka.
Wasu suka sauka gidan Magajiya wasu kuma gidan Inna irin su Mimi da sai dare Mansoor ya zo suka koma gida.
Wasahegari litini Mimi ta tafi aiki shi kuma sai ya leka Camp ɗin su na Gombe United su ka gaggaisa da su Kb suna ta cewa sun yi kewarsa ya ga pele sosai daman yake da kokari shima auransa ya kusa sun zauna da Caach suna ta hira kan sabon horon da yake samu anan Abuja sai can rana ya baro wajen ya isa ma'aikatansu Mimi ya ɗaukota suka dawo gida.
Ranar talata ya bi jirgi ya koma Abuja Mu'azzam kuma washegari shima suka koma kano, amman ba su tafi sai da suka sallami Safiya da kuɗin mota za ta koma
An yi cincin da dublan na Amarya an yi kuma na rabo an dibar ma su Mu'azzam sai Mansoor da Mimi ta haɗa masa cikin kayan snkas din ta yi masa , har da dambun kaza da miya ta yi masa saboda ya gaya mata wancan tafiyan ba karamin wahala ya yi ba, shiyasa wannan karon ta shirya ma tafiyar nashi sannan sun yi mgana da Mommy ta ce za tariƙa ba ma direba abinci da lambar wayarsa sai ya riƙa kai masa can Camp ɗin su.
Amman kuma ta san halin Aji ba lalle ya amince ba amman duk da haka sai ta ce za ta gaya masa, ta na ko yi masa mgana ya ce a'a ba ya son ya saka Mommy wahala da ɗawaniya.
*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3020*
Duk da yace ba ya son saka Mommy ɗawaniya amman duk weekend Asma'u kan yi abinci a saka direba ya kai masa har Camp ɗin su fitowa kawai ya ke yi ya karɓa. Daman abinci ya fi ba shi wahala saboda Camp ɗin Abuja ba ɗaya yake da Camp ɗinsu na Gombe karami ba wannan babban waje ne da ya tattara manyan yan wasan kwallo na ƙasa gabaɗaya duk wanda ka gani a cikin wannan kungiyar fitattace ne sannan ya kwarewarsa ce ta kaisa.
Shi ya sa ko yanayin traning ɗin su ba ɗaya ba ne, duk da akwai manyan ƴan wasa da ƙasa ta jima da sheda fuskarsa dama duniya gabaɗaya wasu yanzu suke cin zarafin su wasu kuma suna cin zarafin nasu har kuma wa'adin da za su yi ritaya ya cimma musu shi ya sa a ka ɗauki ire iren su Aji masu ƙokari domin maye gurbin su. A baya ba shi da burin zama a wani gari face jiharsa saboda Inna da kuma yanzu ya zama uba kuma mai mata, ko a yanzu da ya samu sauyin wajen aiki bai ji ko a ranshi wata rana zamansu gabaɗaya zai dawo Abuja ba, ya saka a ranshi duk matakin da zai taka a rayuwa jihar Gomb uwace a gare shi ba da Mama.
Ya kan yi sama da wata a Abuja wani lokacin ma sai ya raba wani watan ya ke zuwa Gombe ya ga Mimi da Ummi da Inna tare da sauran ƴan'uwansa sannan in ya dawo in ya daɗe ne kwana huɗu zai koma Shi ya sa sai zaman kaɗaicin ya yi ma Mimi yawa sai ta ke roƙon shi bayan ta tashi daga wajen aiki ko ta biya gidan Hajiya ko wajen Inna to shima ɗin ba kullum ba ranar da bai ga dama ba sai ya ce ta koma gidanta ta zauna in ta ce ba kowa sai yace ga Ummi nan, kada ta damu ita uwace yanzu kuma yanzu suka fara gina rayuwarsu a kwai lukatan da za su yi nesa da juna ba domin suna so ba, sai domin neman halas da kuma inganta zamantakewarsu ta nan gaba, ta maaa uzuri sanin halin shi ya na da Kulafacin gida amman tunda ta ga Aji ya hakura da zaman Gombe ya koma Abuja ta san ya ƙarbi canji da Ubangiji ya yi masa da hannaye bibbiyu.
Wani lokacin sai su yini ba su yi mgana ba, ya fi kiranta da asuba ko can wajen sha biyun dare lukatan da ya ke samun sukuni kenan itama sanin ba shi da lokaci ba ta takura masa da kira sai in har tana da mgana da shi mai muhimmanci da ta shafeta ko ta shafi Ummi ko inna, sai ta kira shi in ya zo ya ga kiranta zai kirata daga baya. Hakan ce ta faru yau ma tunda tun kwanaki a wajen aiki sun yi mgana da Manaja kan wani sabon shiri da Ma'aikatansu za ta ƙirkira shirin kuma na mata ne, mai suna matsalolin mu Ayau shirin da zai riƙa gayyato mata dabam dabam domin jin irin matsaloli da challages ɗin da suka fuskanta a rayuwa kuma ana so ita ta kasance presenter ta shirin gabaɗaya ba, ba ta amsa ba sanin halin mijinta ta ce sai sun yi mgana da shi, to ba ta samu sun yi mgana ba saboda karancin lokaci, yau ɗin ma ba su yi mgana a daran ba ta kira shi wayarsa a kashe sai da Asuba ya kirata ya ce sun shiga Meeting ne shi ya sa ya kashe wayarsa sannan ba gama da wuri ba shiyasa bai kirata ba a tunaninshi ta yi barci kada ya tashe ta ita da Ummi.
Bayan gaisuwan da tambayar yadda take ita da Ummi su ka ɗan yi zantukan soyayyarsu na kewar da su ka yi da juna. Sannan Mimi ta shigar masa da maganar Manaja nan ta ke Aji ya fara faɗa ta in da ya ke shiga ba ta nan ya ke fita ba,Mimi ta jawo Ummi da ke barci ta rumgumeta a sanyaye ta ce" Kayi hakuri Baban Ummi."
Haka kawai ta ke faɗa amman ya ma ƙi sauraranta sai faman faɗa yake yi yana faɗin" Ba fa mganar hakuri ba ne Fatima renin wayan ne na ga ya yi yawa. Me ya sa sai ke? Ke kaɗai ce ma'ikaciya mace a wannan wajen na ku? Haba sai ace ke dole fuskarki ce za ta riƙa yawo a akwatin Talabijin ɗin kowani gida? Haba ba ta yuyuwa kina matata ina son ki, in na kalle ki kina burgeki sha'awan ki na kamani, amman ace abun hauahi da baƙin ciki ni a matsayina na wanda Ubangiji ya yarje min ba ni da ikon kallon ki ni kaɗai na yaba, da wanda ya dace da wanda bai dace ba, kowa kallon fuskarki yake yi ya na yabawa. Wallahi Tallahi ko aikin nan da kika ga na barki kina yi ba a son raina ba ne Fatima , ina da kishi kishin da ni kaɗai na ke son na yi ta kallon ki ina yabawa. Amman ya zan yi? Yanzu ina hanaki wannan aiki sai ace ni mugu ne ba ni da adalci na ganki da aikin ki na aure ki kuma na rabaki da shi Ƴan'uwanki su zageni ke ma a ranki ko ba ki furta ba sai kin ce ni mugu ne ba ni da adalci."
Cikin Mamakin kalamansa Mimi ta ce"Ni? Me ya sa zan kira mijina da suna mugu? Ka isa ne shi ya sa ka hanani saboda kai ɗin mijina ne kuma shugabana, yan'uwana kuma ba su da abun cewa tunda ba suke aure na ba, na su sai dai shawara ne ko jin ta baki"
Aji ya ciji leben bakinsa na ƙasa kafin yacce"Ina son na hanaki, amman kuma gwara na yi miki adalci kema ki yi min,in na dawo za mu sake yin mgana"
Ta san cewa akwai mgana tunda ya ce sai ya dawo za su ƙarisa mgana, tun kafin ma ya ce bai amince ba mganganunsa sun nuna in da ya dosa yasa ta faɗa mana Manaja Megidanta bai amince ba sannan ta ba da Shawaran tun da a shekaran a ɗauki sabbin ma'aikata me zai hana su jaraba wata sabuwar fuska! Nan da nan ko a ka karɓi shawaranta a ka fara shirye shiryen kaddamar da shirn tare da zaɓo cikin sabbin ma'aikatan da a ka ɗauka domin cire wacce ta fi chanchanta a ciki.
Ko da suka yi waya da Rukky ta yi mata zencen itama sai da ta ce"Ke ma Mimi da son jan ma kanki faɗa kike yi, wannan mijin naki mai shigen kishi ne zai amince? Aikin ma ai ba ason ranshi kike yi ba, da kin sani tun da Manaja ya tuntuɓeki kin datse abun da ba ta kawo ku da gabar haka ba."
Mimi ta ce"Haka ne Rukky, ai na ce su nemi wata sabuwar fuskar mijina bai amince ba."
Ruƙayya tace shike nan kuwa sai ki zauna lafiya.
Saboda maganar na ranshi sati biyu tsakani ya dawo gida, amman sai da ya zaunar da ita yana gaya mata ba dole sai an riƙa ganin fuskarta ba akwai ma'aikata da dama da suke aiki ta bayan fage fa ba'a son su ba, me zai hana itama a maida ta wannan bangaren? Mimi ta ce"Ba ni da zaɓin bangaren da zan yi aiki, zaɓi na kenan bangaren da na fi ƙwarewa broadcating, Kuma ni ban isa in ce ga in da za su ijiyeni ba sai dai in zan ijiye aikin gabaɗaya na dawo gida na zauna tunda haka kake so."
Jin haka yasa bai ƙara mgana ba tunda ya ga idanuwanta sun ciko, ya san tana son aikinta kuma yanzu ya ce ta bari kamar bai yi mata adalci ba, ita ba wata sana'a take yi ba sannan shi kuma ba mazaunin gari ba sannan In har Inna ta ji labari sai ya raina kanshi shiyasa ya danne ma zuciyarsa bai ƙara mgana kan aikinta ba har ya gama kwanakin shi ya koma Abuja.
Ya koma ba Daɗewa Mimi ta samu wayar Mommy ta ce tana neman ta a Abuja, a she ba ita kaɗai ba gabaɗaya yayan nata har da Dr tunda shi ne babba, kiran ya ba su mamaki amman su a tunanun ko maganar gidane, kuma dukkansu ta ƙi ce musu komai a waya ta dai ce su nemi izini wajen mazajensu weekend ɗin da zai shiga tana son ganin su gabaɗaya, Aji ma da ta gaya masa sai da ya ce" Topha! Allah ya sa lafiya."
Mimi ta ce"Ina tunanin ba lafiya, dukkan mu fa ta kira har Dr, ni ba ka ce min ka je wancan satin ba? Ko ka fahinci wani abu ne? Aji ya ce"A'a lafiya lau take ba wata matsala, mun daɗe muna hira da ita, ba na jin ko akwai wani abu na damuwa sai dai in wata mganar ce ta dabam, ki kwantar da hankali hairan in sha Allahu."
Da haka ya samu ta natsu amman ita duk ta damu, Abun da ya ƙara ba ta mamaki da ta je gida gaida Hajiya nan ta ke gaya mata ta saka Daddy ya nema musu jirgi gaɓadayansu har da shi za su tafi Murja na neman su. Sai Mimi ta saka a ranta ƙila kan mganar gida ne tunda ba'a raba gidan ba har yansu su sun ce sun barshi Mommy ta zauna har karshen rayuwanrta ne.
Daga gidan Hajiya gidan Inna ta biya ta na gaya mata za su tafi Abuja tare da Hajiya da Daddy, Inna ma kanta sai da ta ce"Lafiya kuwa? Ko wani abun ne ya faru?
Mimi ta ce"Lafiya ƙalau Inna za mu je dai mu gaishe ta ne."
Haka ta faɗa ma Inna, saboda itama ba ta san dalilin kiran ba.
Nan ta kai har mangariba saboda Aji baya nan ya sa ta koma da wuri kuma a motar ta ta zo, washegari kafin ta je aiki sai da ta kai Ummi asibiti ta kwana kuka ashe kunnenta ke ciwo a ka bata mgani. Daga asibitin ne ta wuce wajen aiki amman ba ta daɗe ba ta koma gida saboda Ummi, amman Alhamdulillah mganin da a ka bata ta ɗiga mata sau uku shike nan ta samu sauƙi ta cigaba da walwalanta irin na su na yara.
Tun ranar Jumma'a Khadi da Madiha suna Abuja, su Mimi kuma jirgin safe suka bi, wajen sha ɗaya suna falon gidansu a Abuja, abun da ya ƙara ninka mamakinsu ganin har da Inna zainaba suka iske a gidan kenan mganar babba ce, a yinin dai ba'a yi wata nagana ba an haɗu ana ta hira kowa sai mamakin kiɓan Ummi yake yi khadi ta dauketa ta na nishi lokaci ɗaya tana faɗin"Ka ga min burtuka, ke ubanki ɗan firit uwar taki kuma ba kiɓa ba, to ina kika ɗauko wannan jikin?
Hajiya na dariya ta ce"Ƙibar yara ce, taba fara girma za ta ragu, sannan ita kanta Binta haka Murja ta yo goyonta sai da ta fara girma sannan ta fara raguwa."
Mommy na wajen ta ce kwarai haka ta yo goyon Mimi da wannan kibar kamar kazar turawa jiki suɓu suɓu kamar Ummi, Dr ya ce to ga in da ta yi gado nan wajen uwarta ana ta dariya har Madiha ta na saka baki ta ce Yarinyar na burgeta ta na son ganin yaro da kibarsa sannan da ƙarsashinsa har ɗaukanta ta yi, Allah ya haɗa jininta da na Ummi duk ba ta damu da ɗaukan yara ba, nata