Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
su gaisa, a karon farko Madiha da Mansoor Aji suka gaisa cikin girmama juna sannan suka yi sallamam
Da dai Madiha ta rasa abun cewa sai ta bige da faɗin" Ina fatan dai kuna nan zaune lafiya ko?
Mimi ta ce mata suna nan lafiya kalau. Sai Madiha ta gyara zama lokaci ɗaya tana faɗin" To gwara dai haka, kar dai ki zauna soyayya ɗa namiji ta rufe miki ido, duk da kina aiki ya kamata ki fara tunanin fara wani kasuwancin da kuɗin ki."
Kai tsaye Mimi ta ce"To zan yi magana da mijina in sha Allahu."
A karkace Madiha tace"Mijin ki? Au daman kuɗin shi ne?
Mimi ta ce"Kuɗina ai kuɗin shi ne tunda ina ƙarkashinsa, ko Mommy ma ta ce duk abin da na gada nawa ne, kada na kuma zartan da wani abu ba tare da na shawarci mijina ba ko a addinmun hakan ba laifi ba ne, kada kuma ki manta ko yau na faɗi na mutu abin da na tara rabi na shi ne."
Sai Madiha ta kasa mgana saboda ta ga kamar Mimin ta fi ta gaskiya.
Da yake ba wata sakewa tsakanin su ya sa ba su jima suna hira ba suka kwanta sai da eafe Khadi ta kira Mimin ita ke gaya mata Madiha a gidanta ta kwana kai tsaye Khadi ta ce"Mimi na ji kun fara yawon honneymoom ke da mijin ki, Kaduna ba ta zo muku a layi ba ne?
Mimi na dariya ta ce"Ta kusa zuwa layi in sha Allahu."
Khadi na dariya ta ce" Yauwa, don Allah ku zo mun nima muna da wajen kwana ko wata ne ma za ku iya yi."
Da haka suka rabu bayan ta ce ta miƙa ma Madiha wayar nan ta bar su suna waya ita kuma ta fita zuwa kitchen.
Tare suka fita Mimin ta sauke Madiha a gidan Daddy za ta gaishe shi itama ba ta tsaya ba ta wuce wajen aiki, tana zuwa bayan ta gama karanta labaran safe ta karisa bangaren su Rukky ta same ta ta zo aiki amman duk ta faɗa ta yi wani iri kamar Rukky ba, Mimi ta damu ta kalli Rukayya lokaci ɗaya tana faɗin"Me ke faruwa ne? Kin ga yadda kika wani lalace? Kuma kin ce za ki zo gida ki same ni kuma ban gan ki ba."
Sai Rukky ta furzar da numfashi kafin ta ce" Ki bari in muka tashi mu je gidanki mu yi magana, nan ba wajen mganar nan ba ne."
Da haka Rukky ta samu kan Mimi ta yarda sai sun ta shi aiki za su tafi gidanta su yi zauna su yi mgana.
Da wuri suka baro ma'aikatan na su ita da Rukky suna tafe ne amman ba wani mganar da ke shiga tsakanin su, Rukky ta yi tagumi daga ganinta tana cikin dqmuwa Mimi dai ba ta ce mata komai ba amman tana tuki tana kallon Rukky cikin tausaya ba ƙaramin abu ne zai saka Rukky ta zama haka ba, ta ma fita surutu fa amman ji ta ko mgana mai karfi ba ta son yi.
Sun isa gidan amman ko ruwan da ta kawo ma Rukky ba ta sha ba zaune kawai ta yi , kamar mara lafiya, Mimi ta kariso ta zauna kusa da Rukky lokaci ɗaya tana dafa Kafaɗanta cikin wani yanayi ta ce"Me ke damun ki ne Rukayya? Na damu da ganin ki cikin wannan halin don Allah ki gaya min abin da ke damun ki.?
Rukky ta furzan da numfashi kawai sai ta sakar ma Mimi kuka kamar wata ƙaramar yarinya. Ta ɗora kanta a saman kafaɗan Mimi tana shesshekan kuka daga gani kukan na fitowa daga ƙasan ranta ne wanda ya daɗe yana cin ta a cikin zuciya ta kasa furtama kowa.
Mimi ta riƙa lallashinta ta hanyar ɗan bubhuga bayanta da sigar lallashi. Har sai da Rukky ta daina kuka sannan Mimi ta ɗago kanta ta saka hannu tana share mata hawaye lokaci ɗaya tana faɗin" Ki daina kuka ki natsu ki gaya min abin da ke faruwa."
Rukky ta ja numnfashi kafin ta ce"Nasir ne."
Mimi daman ta tsammaci haka amman kuma sai da ta nuna mamakinta kafin ta ce"Me ya faru da Nasir ɗin? Ko kun yi faɗa ne?
Rukky ta girgiza kanta kafin ta ce" Ba faɗa muka yi ba matsala ce daga wajen mahaifiyarsa ta ce ba ta amince Nasir ya aureni ba."
Cike da wani karin mamaki Mimi ta ce"To Saboda mene kuma? Ba an gama mganar cewa tura magabatansa kawai zai yi gidan ku ba.?
Rukky na sharan ƙwallah ta ce" Eh mana, mun gama mgana da shi kawai daga baya yake gaya min maman shi ba ta amince ba."
"To saboda mene?
Mimi ta je fa mata tambaya, Rukky ta gyara zama lokaci ɗaya ta na faɗin" Saboda hujjarta na fi karfin Nasir idanuwana sun buɗe na yi karatu mai zurfi sannan ina aiki zan zo na fi karfin shi, zan raina shi zan kuma raina yan'uwansa da matansa Shi ya sa ta ce ya bar mganata ba ta amince ba."
Sai kawai Rukky ta kara fashewa da kuka ta na cigaba da fqɗin" Ina son Nasir Mimi shi ya sa na shiga tashin hankali, yana ta ce min zai samu mafita amman har yanzu ba mafita ko mgana ta waya ma mun rage baya zuwa wajena saboda maman shi ta hana shi, ya a ke so na yi? wlh ina son shi ina jin wani zafi a cikin zuciyata Mimi"
Haka ta ke faɗa tana kuka kamar wata ƙaramar yarinya, Mimi ma ta shiga tashin hankali cikin damuwa ta ce"Subhanallah to shi daman ya san ba ta amince ba ya tusa kansa? wallahi ban sani ba kuma ina jin ko Aji bai san abin da ke faruwa ba."
"Ba wanda ya sani, ba na tunanin ya faɗa ma wani"
Sai Mimi ta kaɗa kai kafin ta ce"Abin bai yi daɗi ba, ki yi hakuri ki daina kuka bari na kira Aji na gaya masa kila akwai abin da zai iya yi a kai."
Da haka Mimi ta ɗauki waya ta kira shi, amman bai ɗauka ba daman sun fi mgana da daddare ko da asuba sai Mimi ta cigaba da lallashin Rukkaya da kalaman kwantar da hankali.Har ta samu ta daina kuka ita dai Mimi ta ce ta yi ta addu'a abin da ya ke alheri ne Allah ya zaɓa mata amman kuka da damuwa ba nata ba ne, Rukky na gidan har mangariba tare suka yi girki da Mimi ta na shirin tafiya sai ga wayar Aji nan fa Mimi ke gaya masa abin da ke faruwa kai tsaye ya ce"Topha, Shi kuma Nasir ya zai yi haka? Ya san ba amincewar iyayensa kuma ya zo ya bata ma ƴar mutane lokaci?
Mimi ta ce"Ka ji fa, ita ta damu ne na ce ko za ka shiga mganar ne?
Da sauri Aji ya ce"A'a ni bai gaya min ba kin ga kenan bai so na sani ba. Kawai ta koma gida ta cigaba da addu'a, mgana in ta haɗa da iyaye tana da karfi in mijinte ne kaddara za ta sake haɗa su."
Tunda Mimi ta ji haka ta san cewa Aji ba zai yi wani abu ba Sai ta fara wani tunani acikin zuciyarta. Rukayya ƙawarta ce da kowa ya santa tare da ita abokiyar kuka abokiyar dariya ba za ta iya barinta cikin damuwa ba. Har ta Rukky ta tafi tana tunanin yuyuwar abin da take tunani. Ta so ta yi mgana da Aji ta neme shawaransa sai kuma ta fasa a tunaninta sai ya dawo sai ta nemi shawaransa.
Ba tare da wani tunani ba ta kira Jaheed a waya shima dai ya yi mamakin kiran nata tunda ba kiran shi take yi ba. Sai dai maganar da ta zo masa da shi ne ya ba shi mamaki, kai tsaye ta tambaye shi" Jaheed ka na da wata dudurwan da kake nema ne yanzu? Cikin mamaki ya ce"Eh a'a kinsan dai bazan rasa masu sona ba amman ni ba kowa a raina."
Da sauri ta ce" In ka yarda da ni zan haɗaka da ƙawata Rukayya na san ka santa kuma ina mai baka tabbacin za ka so ta."
Sai ta shiga ba shi labarin soyayyarta da Nasir da halin da a ke ciki. Amman ba ta gaya masa abokin mijinta ba ne ta roki Jaheed domin Allah ya fara mgana da Rukkaya domin ya yi mata gwaji ya tabbata dai, ba za ta kawo masa wani abu mara kyau ba.
Bai yi mata gaddama ya ce"Ki turomin da lambata da ni da ita za mu iya daidaita wa tunda duka zukatanmu suna fama da ciwo iri ɗaya."
Ko Rukkyn ba ta gayamawa ba ta turama Jaheed lambar Rukayya a daran, amman ta turama Rukkyn sakon cewa Jaheed zai kirata sauran mgana sai sun haɗu.
Sai washegari suka haɗu a wajen aiki Rukky ta tsareta da tambayan ba ta gane manufar ba ma Jaheed lambarta, Mimi kuma ta warware mata niyyarta na alheri Rukky ta ce"Ina son Nasir fa kin sani Mimi."
Mimi ta ce"Ki cire sa a ranki domin mganarsa sai dai in kaddara ki buɗe zuciyarki ku fahimci juna da ke da Jaheed kin san dai ba shi da wata matsala"
Ita dai Rukky kamar ba ta yarda ba amman ta kasa yi ma Mimin gardama bi sa ga abin alherin da ta yi masa.
Cikin ikon Allah kuma sai ga shi da Jaheed ɗin ya kirata ta saurare shi har ta ke jin za ta iya manejj da shi a yanzu ko hakan zai rage mata damuwa a kan Nasir da har yanzu ba wata mgana mai daɗi daga bangarensa.
Kwanansu Aji takwas suka dawo Mimi ta shirya masa tarba amman kuma sai ya Dawo a fusace kamar ya na jiranta.Faɗa kan faɗa ya na cewa shi ba zai iya ba ana kallonsa da mutumcinsa amman daga gefe ana masa kallon sakarai.
Abun ya ɗaurea Mimi kai ta ga dai ko da safen nan suna hanya sun yi mgana lafiya lau amman ya dawo kamar ya na jiranta ko an gaya masa wani abu ne a kanta mara daɗi ko an ce masa ta yin wanin abin ne?
Cikin mamaki Mimi ta ce" Me kuma na yi? Ko wani abu ne ya faru?
Kai tsaye ya ce"Komai ma ai ya faru, aikin nan na ki Allah za mu samu matsala da ke in har haka za'a cigaba da yin sa"
Kenan mganar aikinta ne sai ta kasa mgana amman tana mamakin abin kuma ya faru. Wayarsa ya danna ya nuna mata Sreenshoot ɗin da ya yi.
Ashe wai shirin labaran da sukan ɗora a shafin su ta facebook wani ya yi comment da cewa" Na ga Hajiya Mimi na ta kumatu ne ko dai an samu ƙaruwa ne?
Aji to ya shiga kuma ya ga wannan Comment ɗin a hanyarsa ta dawowa shi ne fa ya dawo a fusace.
"Ba ta yuyuwa kina matata amman daga gefe kina burge wasu banzayen ba,ki ji fa wannan wulaƙanci? Ina ruwan sa in kin yi kumatun? In ma kina da cikin ina ruwan sa? Matarsa ce? Ko ƙanwarsa ne ya dace ya Faɗi haka?
Mimi ta kasa mgana kanta na kasa ta ce"Ka yi hakuri zan musu magana su rufe comments section ɗin"
Tashi ya yi a fusace ya shige ciki ya bar Mimi da dafe kai, gabaɗaya tarban da ta shirya masa duk ya rushe saboda kishi baya ya juya mata duk son harka irin ta Aji bai laluɓeta ba, ga shi ta sha kayan gyara daga Kwararriyar mai gyaran amare da uwargidaye daga Surayya Dee Bojuwa da kanta. Kayan gyaranta suna da kyau da inganci tun da Mimi fa fahimci nagartansu shikenan ta riƙe su, kema in kina son zama tauraruwar mata a wajen mijinta irin Mimin Aji nemi Surayya dee Bojuwa domin ki zama kasaittaciyar mace a gidan auranki.+234 803 277 3332.
Tuni yanzu Mimi ke da lambarta suna waya duk abin da take so, in ta siya za'a saka a mota a kawo mata har gida, wani lokacin daga gidan yadikko ta kan saka makocinsu ɗin nan ya karɓo mata a tasha ya kawo mata har gida.
Sai da mganar nan ta fi sati sanman Aji ya bar ta ta wuce, shima bayan Mimi ta yi ma Manaja mganar a rufe comments section mutane ba sa sanin abin da suke faɗa. Kada mutane su kashe mata aure saboda mijinta na da kishi, maganganun na su ya na harzuƙa shi, kowa ya aminta da ita sai kawai a ka rufe comments section ɗin gabaɗaya.. Aji kuma ko yana zaune ne in ya tuna da abin sai ya yi ta tsaki shi kaɗai har ce ma Mimi Ya yi" Malama wai ba za ki iya komawa wani shashen da ba mai ganin fuskar ki ba ne? Kawarki ai tare kuke aiki amman ai ba'a ganinta ko?
Mimi shuru ta yi ba ta ce komai ba, saboda lamarin Aji ya daina bata mamaki neman fin karfinta ma yake yi. Kishin sa a kanta mai yawa ne, ba ƙaramin hakuri yake yi da aikin nan nata ba amman in abun ya kunna shi ya riƙa cewa"Kai da matarka amman ba kai kaɗai take Burgewa ba, har da kowani kare da doki."
Ita dai bakin Mimi daga ka yi hakuri sai kuma shuru kada ta furta wami abu na ta ya yi zafi.
Inna Meri daga Tureta. Argungun ta wuce ta na can ba ta ma saka ranar dawowa ba, ba ta nan a ka yaye su Walida, a ka ba su certificate Tana kuma wajen Mqgajiya har a lkacin kuma lafiya kalau ba nuna bambamci tsakaninta da Mariya. Sai dai ta leƙa gidan Bintu ita da Mariya, kwana biyu da yayesu suka fara zuwa gidan Bahijja ita da Mariya saboda darajan Inna yasa Bahijjan kyauta za ta koya musu, duk da tana karɓan 20k na mutum ɗaya a wata shidda shekara 40k kenan.
Sai da inna meri ta shafe sati shidda da kwanaki samman ta dawo gidanta, yaranta duk sun yi kewarta Mu'azzam ya zo mata sannu da zuwa tare da gaisuwa Hibba ba ta zo ba cikinta ya yi girma ba ta iya doguwar tafiya, Inna ta raba tsarabanta hida uku ne, ka shi ɗaya na ƴayanta ɗayan kuma ta aika ma Magajiya ta ce ta diɓar ma su gaje ɗayan kuma ta rabama makota da abokan arziki Har Hajiya ta zo ma Inna gaisuwa ta ɗiɓan mata tsaraban gujiya da gyaɗa da yawa da ta zo da shi.
Daman washegarin ranar da ta dawo Mimi Daga wajen aiki nan ta yini sai dare Aji ya zo ya ɗauketa suka koma gida suma ta tarin tsaraban su, Walida tana murna Inna ta dawo gida daman ta yi kewar Inna. Abin mamaki kaf yaran Magajiya sun zo ma Inna gaisuwa. Sannan kwananta huɗu da dawowa a daran Magajiya ta zo ita da Gaje Maeesha tare da Matar Auwlu suka zo.
Karon farko da Magajiya ta tako kafarta gidan inna, ta kuma ta karbesu hannu biyu, sun jima sai wajem goma na dare suka tafi, Magajiya dai ta kasa sakin jiki kunya da Nauyin sun isheta ta gama ganin ishara, Innar dai da take yi ma hassada da kyashi ta ga in da Ubangiji ya yi da rayuwarta ita kuma hassadarta da kyashinta ya cinyeta, Ƴaƴan inma Merin sune gatan su ita da na ta iyalan gaba da naya, ita Inna Meri ko a fuska ba ta nuna wai daman ba su shiri da Magajiya ba suna ta hira da Gaje tana kuma sako magajiya a cikin zencen na su.
Daman haka rayuwa ta gada, hassada mugun ciwo ne mai hassada sai ta ci sa, in ka zauna da kowa lafiya da zuciya ɗaya sai Ubangiji ya turama masu hassada da kyashi a aniyarsu.
Bangaren Rukky da Jaheed kuma soyayya ta mika har Jaheed ya zo garin saboda Rukayya. Maganar Nasir kuma ta sha ruwa tun da mahaifiyarsa ba ta amince ba. Nasir ya yi ma Aji mgana shi dai ya ba shi shawaran ya fara daidaitawa da iyayensa tukunna, haka su Ahmad suka ce da ya fito group ya yi mganar, ita kuma Rukky Jaheed ya fara ɗauke mata hankali ya zo gida sun yi magana da alamu za su daidaita nan da lokaci kaɗan Mimi ta fi kowa murna. Tana so ta yi mganar da Aji sai kuma ta sha'afa yasa har lokacin bai san abin da ke faruwa ba.
******
_Monday_
Tun da ta tashi take jin jikinta ba daɗi amman ba ta nuna ba, Aji da wuri ya fita suna da morning traning tare suka fita ya sauke ta wajen aiki da cewa za ta kira shi in ta tashi domin ya je ya ɗauko ta.
Kanta ke sara mata da safen kuma ta sha paracetamol, amman kamar ya sauka ashe bai sauka ba dakyar ta gama karanta L
Labaran safe ta koma Setting Room ta kwanta.
Cikin lokaci kaɗan sai zazzabi ya rufeta ta fara rawan sanyin Aisha Farida ce ta je ta kira mata Rukky ta ga halin da take ciki. Sai ta yi amfani da wayar Mimi ta kira Aji amman har kira uku bai ɗauka ba, itama kuma tunanin abun na gaggawa ne ya sa ta kira Jaheed ta ce ya zo ma'aikata ya same su Mimi ba ta da lafiya jin haka ya sa a ruɗe ya taho daman bai koma ba a ranar yake tunanin bin jirgi zuwa Lagos.
Ba jimawa sai ga shi ya zo, zafin zazzabi yasa Mimi ta kasa ma mgana Rukky ta riketa suka fita ana bin su da Allah ya sauwake ganin ko iya buɗe ido ba ta yi ya sa Jaheed yace su tafi asibitin da suke zuwa itama a can Mimi ke da katin ta.
Wani asibitin kuɗi ne suna zuwa a ka karɓi Mimi aka dibi jininta, sai a ka saka mata drip da allurai.
Jaheed da Rukky suna tare da ita, Ita Rukky ta manta da wayar Mimi a cikin jakarta kuma sun barota a motar Jaheed, Aji na ta kira ba'a ɗauka ba daga Camp ma'aikatansu ya biya Na misau ke gaya masa Mimi ba ta da lafiya Rukayya da wani namiji sun zo sun ɗauketa.
Da farko ya ɗauka Nasir ne sai da ya kira shi sai yace masa yana wajen aiki. Sai ya fara tunanin to waye? Shi kuma