Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
ba shi da L lambar Rukayyan ballantana ya kira sai ya yi tunanin ya je gida ya gani, nan ma ba ta nan kuma ya na cigaba da kiran wayarta amman ba'a ɗauka ba har bayan la'asar.
Ba tunanin da sheɗan bai sakaa masa ba Har hassowa ya yi wai Mimi ta bi wani namijim Ransa in ya yi dubu ya ɓaci, kirjinsa na sama da kasa idanuwansa sun yi jajirce, Zagaye kawai ya ke yi a falo ko zama ya kasa yi ya kira wayar Mimi bai san iyaka ba amman ba ta iya ɗauka ba.
Su kuma suna asibitin har la'asar sai da a ka cire ma Mimi ƙarin ruwa sannan eesult ya fito, Mimi ciki gare ta na tsawon sati shidda da kwanaki, ita kanta ba ta san da shi ba amman dai ta san watan da ya gabata ta yi ɓatan wata, Ita likitar ma ya ba ma tarkadan sakamakon Rukayya da Jaheed suna waje kuma ko da ta fito ba ta faɗa musu ba sai kawai ta ce maleria ce, da tare da Rukky za'a kaita gida amman sai mamansu ta kira waya hankali ta she ta ce Rukayya ta zo mijin Bibi ya kirata ya ce tana asibiti za ta haihu., Don ma ta yi ɓarin cikin ta na farko da ta jima da haihuwa. Dalilin da ya sa suka rabu a nan kenan ta hau abin hawa zuwa asibitin da a kace Bibi na can ta na naguda shi kuma Jaheed ya ɗauko Mimi zuwa gidanta.
Aji na jin ƙaran bude get ya yi zaraf ya fito haraban gidan a kan idanuwanshi Jaheed ya shigo da motarsa ya yi parkimg sannan ya fito ya zagaya ya buɗe ma Mimi ta fito. Jikinta ba karfi yasa ta yi kamar za ta faɗi sai ya riketa sannan ya karbi jakar hannunta, takardan Result ɗin cikin kuma na cikin aljihun rigan jikinta ta saka.
Aji na ƙofar falon gidan yana kare musu kallo a ƙankance, Ba abin da sheɗan ke gaya masa sai Mimi ta bi tsohon saurayinta sun je sun gama yawon iskancin su shi ne ya kawota gida saboda dukkansu ba su da kunya.
Saboda kishi da ɓacin rai har wani huci mai zafi yake fitarwa ta baki Mimi ta na tafe a hankali jaheed na riƙe da hannunta tana dagowa suka haɗa ido da Aji sai da ta ji ta warke gabaɗaya da sauri ta kwace hannunta a na Jaheed ta na jin gabanta na faɗuwa. Aji a fusace ya juya ya koma cikin falon yana tsaye ya na zagayen falon yana huci hannayensa goye a bayansa.
Suna shigowa Mimi ce a kan gaba sai Jaheed ya na tafe da jakar Mimi da ledan mganganinta na karin jini da na saka cin abinci, tunda an rubuta magani suka tsaya phamarcy suka siya.
Mimi ce ta yi sallama amman ko ƙarisa sallaman ba ta yi ba Aji ya daka mata wata razananiyar tsawar da sai da ta yi baya kaman za ta faɗi, Jaheed dake bayanta ya tare ta yana faɗin" Subhanallah ki yi a hankali kin san jikin ki ba karfi."
Aji ya kallesu tuni sheɗan ya haska masa zargi a cikin zuciyarsa idanuwansa ya rufe bai yi tunanin da ya ciza ya hura ba.
Cikin nuna su da yatsa ya ce"Me kuma ya kawo ku gidana? Wato saboda ba ku da kunya kun gama watsewar ta ku a waje shi ne sai kun zo har gabana kun nuna min ku ƴan ta zubar ne?
Mamaki ya hana daga Mimi har Jaheed magana, kawai sai Aji ya cigaba da faɗin"Ashe kina can tare da tsohon saurayin ki shi ya sa nake ta kiran wayarki ba ki ɗauka ba ko? To me ya dawo da ke gidana,? Me ya sa ba ki bi shi can gidan na su ku cigaba da barbaɗan naku ba."
"MANSOOR...!"
Mimi ta ƙwala sunan shi cikin karfi da karkarwa ba in da jikinta ba ya rawa, Idanuwanta har sun fara zubar kwallah ta nuna kanta Lokaci ɗaya tana faɗin"Me ka ke nufi? Kana nufin kana zargina ne da Jaheed?
Kai tsaye ya ce"Ba zargi ba ne tabbaci ne, saboda ga shi nan tare kuka dawo kuma Saboda ba ku da kunya a gaban idanuwana yake taɓaki ai dai kwaji kunyar aikata son ranku a gaban idanuwana amman da yake damman an ce mara kunya ya aikata duk abin da ya ke so. Ya yi miki kyau."
Ya karishe faɗa cikin fusata Jaheed ya buɗe baki zai yi mgana Mimi ta hana shi. Kukan bakinciki take yi da har gobe Aji bai yarda da ita ba, da zai yi tunanin za ta iya cin amnarsa da wani namijin?
Ko ya yi nadaman kalamansa saboda Idanuwansa ya rufe yasa ya ce ta juya su koma in da suka fito, ba musu ta juya za ta fita Jaheed ya ce"A'a Mimi ki tsaya na yi masa bayani."
A Fusace ta ce" Sai ka tsaya ko ba ka ji abin da yace ba ne? Tunda ya na zargina babu amfani zama da wanda ba zai iya shedar ka ko a bayan idonka ba."
Daga haka ta fice Jaheed da Aji suka kalli juna kafin Jaheed kaɗa kai yana faɗin" Ina jin tsoron wannan kishin naka kada ya lalata muku aure, ya kamata in rai ya ɓaci hankali ya nemosa, sannan ka sani in an ciza a hura saboda kada rashin hurawar ya taho da nadama."
Ya na gama faɗin haka ya juya ya bi bayan Mimi da sassarfa, Aji sai ya tsaya yana kallon in da suka bi a cikin zuciyarsa yana faɗin"Sai kuma ta bi shii ɗin suka fita?
Bai ƙara dawowa hayyacinsa ba sai da ya ji ƙaran buɗw get yana leƙawa ta window ya ga motar Jaheed ta fice daga gidan.
*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3016*
*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*
https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC
No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.
Sheɗan ya shiga hasko masa su cikin yanayin da bai kamata ba, kenan ta zaɓe shi a kan shi,?
Sun koma su cigaba da abin da suke yi kenan? Wani irin tururi ya ji yana fitowa daga cikin zuciyarsa har ya na jin hucin zafin a cikin fatar jikinsa, bakinsa ya saki iskar na fita yana ta kuma sakin hucin da sauri sauri ga sanyin A.C ga na fanka amman gumi na ke tsattsatso masa kamar wanda a ka watsa ma ruwa. Bai san lokacin da ya dungule hannanunsa guda ɗaya ya daki bangon ɗakin da shi ba.
Ya ji radaɗin har a tsakar kansa daga. Har sai da ya yarfe hannu nasa saboda azaba. Cije baki ya yi kafin ya kalli hannun nasa ganin ya sale har ya fara jini kan kujera ya koma ya zauna ya na ƙokarin daidaita numfashinsa da ke fita da zafi sannan a kai a kai kamar wanda ya yi gudun tsere, yana nan a zaune nan ba abin da sheɗen bai saka masa ba har tunani ya yi daman raba musu jiki Mimi take yi shi da wannan tsohon saurayin nata? Ya kasa tuna waye Fatima a wajensa? Ya kasa tuna matsayinta a ransa ya kasa tuna shi ya karɓi ƴan matancinta, ya kasa yi mata kyakyawan sheda saboda kishinsa na banza da wofi ya saka zargi a cikin auransa.
Duk da haka ya kasa samun natsuwa. Har waya ya ɗauka zai sake kiranta amman ya fasa ya kuma kasa fita ko'ina ya na gida ya kasa zaune ya kasa tsaye, tunaninsa bai hasaso masa me zai faru ba, a tunanin shi duk in da ta je za ta dawo, in tana kunya ba za ta bari wani ya san abin da ta aikata ba.
Yana gidan a zaune a saman kujera a cikin falon yana kallon ƙofar falon, motsi kaɗan zai ji zai ta shi ya leƙa ta window amman Har mangariba ba Mimi ba dalilinta sai ya fara tunanin ina ta bi shi suka tafi? Gidan Hajiya? An ya za ta je can kuwa?
A lokacin idanuwansa sun rufe ya kasa sarrafa zuciyarsa har sai da ya ga an yi isha'i tara ta kusa na dare sannan nadama ya fara shigarsa ya fara tambayar kansa da me na aikata kenan?
Cikin Rawam jiki ya ɗauki waya ya kirata amman sai ya samu wayarta ta na kashe, kansa ya dafe da ke sara masa a karon farko ya furta" Hasbunallahi wa'imal wakel."
Ya aikata kuskure babba. Zafin zuciya da kishi sun saka Mimi ta zaɓi wani namiji sama da shi, hankalinsa ya dawo jikinsa ya na tuna kalaman da ya je fa mata, Ya san Mimi mai tarbiyace duk abin da ya ke tuhumanta a kasan ranshi yasan ba za ta aikata ba amman sheɗan ne da bakar zuciyarsa suka kaisa suka baro sa.
Tunanin kiran Hajiya ya yi, amman kuma sai ya fasa saboda kunya me zai gaya mata in Har Mimi ta je ta faɗa mata mganganun da ya yi a kanta? Kansa ya dafe ya na faɗin"Aji me ya sa ka yi haka? Sai yau ya fara jin haushin kansa da haushin wannan zuciyar tasa, sannan ya fara tunanin kishinsa zai saka wata rana ya aikata wani abun da zai dawo yana kuka da idanuwanshi saboda nadama. Ko abinci ya kasa ci, ruwa ma bai iya saka ma cikinsa ba, barci kuma sai dai ɓarawo amman kusan raba dare ya yi a falo idonsa biyu wayar Mimi kuma ya kira bai san adadi ba har ya gaji ya tura mata saƙo.
_Don Allah Mimi ki yi hakuri ki faɗa min in da kike sai na zo mu yi mgana. Ki tausayamin sharrin sheɗan ne_
Tunaninsa Allah ya sa ba gidan Hajiya ta je ba. Sannan Fatansa ya sa ko kila gidan kawarta Rukayya ta je, amman in har ta je gidan Daddy ta faɗa masa, to shi fa ba shi da bakin kuma da zai iya kare kansa wannan karon.
*****
MIMI.
Bangaren Mimi kuwa tana zaune a bangaren mai zaman banza a motar Jaheed amman ban da kuka babu abin da take yi, kuka sosai mai Sauti fuskarta ta yi chaɓa chaɓa da hawaye har da majina Jaheed na bata hakuri amman kamar yana ma ƙara zuga ta ne.
"Mimi don Allah ki daina kuka, kin ga fa halin da kike ciki, ba ki da lafiya na ce miki mu koma ki ba shi hakuri mu yi masa bayanin abin da ya faru."
Mimi ta dago fuskarta duk hawaye cikin Kuka ta ce"Ba ya bukatar wani bayani Jaheed da kunnen ka ka ji ya ce ba zargi ya ke yi ba, tabbaci gare shi a kan ina cin mmanarsa tare da kai, abin da ya fi min baƙin ciki ace yau mijin da kake so kuma ka ke aure shi ne ba zai iya shedar ka ba. Yau ni Aji ke kira da lalattaciya ina lalacewa da wani namijin Alhalin nasan ina da aure wannan abun ya fi komai baƙan tamin rai."
Tana gama faɗin haka sai ta ƙara rushewa da kuka Jaheed ya girgiza kansa cikin damuwa kafin ya ce" Gaskiya bai kyauta ba, bai kamata ya yi haka ba."
Daga haka sai ya yi shuru saboda shi ya ma rasa abun faɗamSuna tafe Mimi na cigaba da kuka Rukayya ta kira wayar Jaheed bai ɗauka ba saboda kukan Mimi sai ya maida wayar a silent.
Kuka take yi ta manta ma da in da take sai dai kawai ta ga Jaheed na hon a bakin get ɗin gidan Hajiya sannan ta dawo cikin hayyacinta. Da sauri ta kalli Jaheed hankalinta a tashe lokaci ɗaya tana faɗin" A'a mu juya Jaheed ba zan je ma Hajiya cikin wannan yanayin ba."
"To ina za ki je?
Ta yi shuru kafin ta ce" Mu je gidan su, wajen mahaifiyarsa."
Jaheed ya kalli Mimi kafin ya ce"Me ya sa sai can? Kai tsaye Mimi ta ce"Ba na so wani acikin dangina ya san abin da ya faru, kowani aure ya na da nashi ƙalubalen Jaheed. Gwara na je wajen mahaifiyarsa a kan na je ma Hajiya ina koke koke."
Sai ya jinjina kai alamun gamsuwa har Megadi ya leko ganin motar Jaheed ya buɗe get amman sai ya ga ya juya kawai ya mike bai shiga gidan ba cikin mamaki ya bi motar da kallo kafin ya koma ya rufe get ɗin bai lura ma da Mimi da ke gaban mota ba a tunaninsa ƙila wani uzirin ne ya sa bai shiga gidan ba.
Suna ta fe Mimi na masa ƙwatance har ƙofar gidan Inna Meri, Jaheed ya bi gidan da kallo kafin ya ce"Nan ne gidan?
Sai ta kaɗa masa kai ta na share hawayen fuskarta da mayafinta lokaci ɗaya tana faɗin" Eh nan ne Mahaifiyarsa ke zaune."
Sai suka yi shuru gabaɗaya. Jaheed ya mika mata jakarta da ledar mganinta kafin ya ce"Ki kula da kanki, kinsan dai ba ki da lafiya."
Ta buɗe baki za ta yi mgana da sauri ya tare ta da faɗin" Na sani ba zan gaya ma kowa ba. Ciki ko har da Rukayya, ba na fatan na zama silar samun matsala ga auran ki, ki yi masa bayani in ma bai yarda ba akwai Rukayya ita za ta zama shedarmu."
Wani mirmishin takaici Mimi ta yi kafin ta ce"Kada ka damu ba abin da zai faru. Na gode kwarai ka gaida su Daddy."
Da ga haka ta buɗe mota ta fita. Ta ɗaga masa hannu shima ya ɗaga mata sannan ta juya tana tafe a hankali jiri ma take gani, mamakin ta wai tana ciki? Bayan ɓatan watan nan ba ta fahimci wani alamun tana da shigar ciki ba sai yau da zazzaɓi ya rufe ta.
Gidan ya na buɗe sakayawa kawai a hankali ta tura kanta ta shiga yamma ta yi tunda shidda saura ne, Inna Meri na tsakar gida tana kwashe shanyar zogalan da ta zo da ita daga can gida ɗanya shi ne take shanyawa tare yakuwa, ganin mangariba ta kusa yasa ta fito tana kwashewa. Tana duke ta na tsince na kasan da ya zube lokaci ɗaya tana sakawa cikin farantin gabanta, ba ta ji sallamar Mimi na farko ba sai da ta ƙara yi sannan ta ji ta, da sauri kuma ta ɗago kanta tana kallon Mimi take tafiya dakyar kamar za ta faɗi, Cikin mamaki Inna Meri ta miƙe lokaci ɗaya tana faɗin" Binta? ke ce da yamman nan?
Kalamanta sun tsaya sanda ta ga Mimi ta dafe kanta. Jakar hannunta ta sulale tare da ledan mganinta wani irin juwa ce ta kwashe ta za ta kai ƙasa cikin zafin nama Inna Meri ta tare ta lokaci ɗaya tana faɗin" Subhanallah Binta ba ki da lafiya ne?
Ba mgana sai kawai Mimi ta saka mata kuka, Inna ta ruɗe ga shi ita kaɗai ce a gidan Walida ba ta dawo daga wajen koyon ɗinki ba. Sai ta rike Mimi ta taimaka mata zuwa cikin falo ta zaunar da ita a kan Kujera, amman sai ta koma ta kwanta Inna Meri ta yi mata zuru tana kallonta lokaci ɗaya da nazarinta ba ta raba ɗayan biyu Fitinannen yaron nan ne ya yi wata tsiyar, Sake fita ta yi ta je ta kwaso jakan da ledan mganin ta duba daman ai daga ganin Binta ba ta da lafiya duk ta wani ɗashe, Inna ba maganin ta gani ta fahimta ba ita fa uwace tun lokacin da ta dawo Mimin ta zo mata sannu da zuwa ta ga yadda ta yi wani fari ta ga alamun Bintar na da shigar ciki, kuma a tunaninta daman dukkansu da ga ita har Baban Inna ba su san dashi ba.
Falon ta koma ta iske Mimi na rawan sanyi sai ta shiga ɗakin walida ta ijiye mata jakar da kedan ta ɗauko mata blanket bargo ta rufa mata sai faman jera mata sannu take yi, ta koma ta kashe fanka falon sannan tunda mangriba ta kusa. Sai ta saki labulayen falon ta kuma rufe ƙofar falon da Window saboda ɗakin dai ya yi ɗumi, kitchen ta shiga ta kunna gas tunda ta iya sai ta ɗora ma Mimi ruwan zafi ta samu ta yi wanka ta gasa jikinta sai taci wani abu ta sha mgani ruwan na tafasa ta fito falon sai ta isken Mimin na barci sai ta kyaleta.
Har a ka kira mangariba tana barci Inna Meri kuma ba ta tashe ta ba. Ta shiga ciki ta ɗauro alwala ta zo nan falo ta shimfiɗa sallaya tana cikin sallar ne Walida ta shigo gidan Inna ma jin ta tana faɗin"Laa Anty Mimi' Sai kuma ta leƙa ta kafin ta ɗago tana kallon Inna, goshinta ta taɓa ta ji da zafi kaɗan sannan ta ga tana zufa.
"Inna Anty Mimi ba ta da lafiya ne?
Innar na sallah ya sa ta san ba za ta samu amsarta ba. Sai ta kwashi hijabinta da jakarta zuwa cikin ɗakinta ta na shiga ta ji ana ta kiran waya a jakar Mimi ta gani yasan ta san wayarta ce ta buɗe kenan ta ɗauko wayar ta ga an saka Baby kafin ma ta yi wani abu wayar ta ɗauke da alamu ƙila ba chaji ne, ba ta yi tunanin saka mata chajin ba sai dai ta maida mata wayarta cikin jaka, ledan maganin ta ɗauka ta duba abun ya ba ta mamaki Yaya Mansoor ya yi tafiya ne? In ba haka ba me Anty mimi ke yi a gidan nan a dai dai wannan lokacin?
Ba ta da mai ba ta amsa ba ya sa ita ma ta sauke kayan hannunta ta faɗa tiolet ta yi alwala ta zo ta yi sallah tana cikin tahiyar karshe ta ji Inna na ƙwalamata kira shi ya sa tana sallamewa ta fice zuwa falo tana ce ma Inna ta na sallah ne lokacin da