Idan An Ciza Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   42 / 49

123K to 126K   out of 146.6K words

ma Aji mgana shi kuma wannan tuni ya manta ma.

  Direban ya ji mganar Oga Aji bai yi gudu ba amman sun isa wajajen uku ne na rana. Shi kan shi Aji ya yi mamakin saurin su haka yace ma Mimi da suka yi waya. Murna wajen Hibba da Mu'azzam ba'a mgana, suka rasa ina za su saka su saboda murna sun iske wasu daga cikin ƙanen Hibba da yayenta sun riga su zuwa tun jiya suke. A ka rasa ina za'a saka su kawo wannan miko wannan Sun rasa bakin godiya ga zuwa ga abun alheri Mu'azzam sai da ya yi ƙwallah domin Yayan nasa ya gana mishi komai bayan kudin da ya tura masa ya biya kuɗin mota sannan ga ɗawaniyar kayan suna da kuɗi, ya kira shi zai masa godiya ya kashe wayarsa. Ba su zauna ba da yamma a ka fara aikin suna raguna biyu a ka yanka ma Maryama da safiyar suna. Sannan sun dafa shinkafa sun yi alale da Zoɓo an kuma soya kayan ciki bayan haka kuma ga nama ya siya ɗanyen an yi girki da shi, a ranar Mimi ba ta samu fita ba sai washegari ranar lahadi Bintu da Walida tare da mariya suka rakata gidan Dr ta fara zuwa baya nan ma yana asibiti sai dai Jawahir nan suka yi sallar la'asar sannan suka wuce soron ɗinki, Inna Zainaba sai da ta mata tsiyan ta ɗauka za ta kwana ne amman sai ta ce washegari za su koma gabaɗaya, suna can har dare sannan a ka saka direba ya dawo da su gida.

  A ranar daman su Yaya Amina suka soya Nama a ka diɓar musu na su a daran. Na Inna daban haka na Baba sai sauran kuma a ka haɗa su gabaɗaya. Amman na Baban inna roba guda cike da nama in ji ɗan'uwansa, misalin sha biyun rana direban yazo amman sai da suka yi azahar suka ci abinci shima yaci sannan suka ɗauki hanya nan suka bar ƴan'uwan Hibba su sai jibi za su koma anman ƙanwar mamanta na nan sai ta yi arba'in.
Sai mangariba suka iso gida, gidan Inna su ka yada zango, nan suka raba naman kowa ya ɗauka na shi, sannan Mu'azzam ya ba su kwalin omo da sabulu yace su raba gabaɗaya.

  An raba amman Mimi ba ta amsa ba, Naman ma cewa ta yi su haɗa ma Inna sabulun kuma ta ba ma Jummai omon kuma ta ba ma Yaya Zuwaira su sun fita bukata.
Yaji jegon ma an ba su wanda ƴan'uwanta su ka mata sun raba gabaɗaya. Zuwa bayan isha'i kowa ya yi gidanshi inna ta diɓar ma Magajiya naman da Yaji ta ba Mariya ta kai mata, Gaje ma har na Harira an ɗiba mata ita daman Inna an san rabar da shi za ta yi kila ma ko a bakinta sai an yi da gaske za ta ɗanɗana.

  Mimi dai nan ta jira Aji ya zo ya ɗaukota da daddare suka tafi gidansu, daman a daddafe ya yi kwana biyun nan. Washegari ma ba ta samu zuwa wajen aiki ba sai ranar laraba ta koma.Miyan ma da ta yi masa ko sau ɗaya bai yi amfani da ita ba. Ya dai ci cake da samosa, itama ya ce domin ya na so ne yasa ya soya ya ci, da tace ina ya ke cin abinci ya ce gidan Inna da ta gama za ta kira shi ya je ya cika cikinsa, ina zai iya wani Dafa shinkafa bayan ta gama sangarta shi..
In da Allah ya so ta da rahama ba ta yi mugun laulayin da zai hana ta aikace aikacen da kuma biya ma mijinta bukata ba ko amai ba sosai take yi ba bar ta dai da cin goro sai kayan kwalama suma ba kasafai ba. Cikin fari ne amman Alhandulillah ta same shi da sauki fiye da tunaninta, fatan ta Allah yasa yadda ta samu laulayi da sauki ta samu haihuwan ma cikin sauƙi.

******

*BAYAN WATTANI BIYU..*

Har Hibba ta yi arba'in ta zo gombe ta yi sati ta kawo ma Inna takwaranta wacce suke kira Ammi. Mu'azzam ya zo ya ɗauke ta suka koma gida, cikin Mimi kuma watannin shi shida ne, har ta fara zuwa awo a wani asibitin kuɗi a cikin gari tana kuma cigaba da zuwa aikinta.
Cikin ya bi jikinta tunda tana da tsawo sai da ya saka ta buɗe daga kasanta saman ta kuma mamanta sun yi manya kumatunta ya kumbura sannan hancinta ya ƙara girma tuni dai halittar ya sauya. Hajiya ce ta gaya mata cikin jikinta ya bi shi ya sa ba'a ganin girmansa, shi kuma Aji ya ce ta zauna a haka ta fi masa kyau a koda yaushe ya kalleta ya na jin farincikin yau ita ce ke ɗauke da cikinsa wannan ma abun alfahari ne.

  Zaman su suke yi lafiya cike da kauna sai ɗan abun da ba'a rasa ba. Tun da daman shi zamantakewa zo mu zauna ne zo mu saɓa ne, sai dai suna ƙokarin Fahimtar juna domin samun daidaito. Shi yanzu babban Blburin shi shi ne ya samu ya biya ma Inna ta je makka ta sauke farali, ga shi Contart ɗin shi saura shekara biyu ya ƙare a Gombe United amman bai yi tunanin yi ma kansa wani tanadi anan gaba, ya samu kuɗi tunda a wata ɗaya sun je kano da kaduna sun buga wasa bayan albashinsa akwai allowense. Sannan kuma mganar Contrart din Captain din Team an saba daga waje akan ɗauko wani a ba shi horo amman wannan karon sai ya samu Coach ɗin su da maganar ga Musa pele a cikin su yake yana da ƙokari tunda shi ne kamar matsayin Assitancen ɗin Aji, yace me zai hana shi a ba shi horon.?

  A lokacin kallonsa Coach ɗin na su ya yi kafin ya ce"In contart din mu ya ƙare, ka shirya in da za ka koma ne?
Sai Aji ya ce"Tukunna dai Coach."
Sai kawai ya jinjina kai kafin ya ce"Ba na so ka bar mu, kuma ina son cigaban ka ina inan ina yi maka wani ƙokari in ya tabbata zan neme ka, in kuma bai tabbata ba sai dai mu ƙara singing ɗin contart ɗin da kai amman ba zan bari Gombe United ta yi rashin zaƙwaƙuru irin ka ba."
Ya daɗe daman ya na jin Coach na yawan faɗin ya na masa jokari bai taɓa maida kansa ba, ballantana ya yi tunanin makomarsa anan gaba, shi kam me ya ke nema? Komai ya samu sai dai godiyar Ubangiji kawai mutum ne shi da ba shi da hange hange, saukaƙƙiyar rayuwa ce a gabansa ya yi ma iyalansa sannan ya farantama Iyayensa..

  Shi kaɗai yake da burin biya ma Inna saudiya ko da Mu'azzam bai taɓa yin zencen da shi ba, Saboda baya son taimakon kowa  yanzu dai haihuwan Mimi ne a gabansa sai Jamb ɗin da Walida za ta sake yi, ga bikin Mariya na matsowa duk da shi sai bayan ƙaramar salla gabda nabban sallah sannan za'a yi bikin.
Ya dai fara ba ma Mimi kuɗi ta rike na siyan kayan haihuwa, itama a ɓoye tana siyan ma kanta saboda in megidan ya gani zai yi mata faɗan cewa shi ya gaza ne? Ko ya sakata ne? Shi ya sa ma ta ke ɓoyewa ba ta bari ya gani ba saboda dai a samu zaman lafiya, duk da tana da kuɗi amman bai yarda da ta kashe ma kanta naira biyar ba, sai dai komai take so ta yi masa mgana, in bai da shi a lokacin sai ya ce ta ba shi lokaci, in ya samu sai ya ba ta, ba ya taɓa duba aikinta ko gadon da ta tara shi dai ya sauke nauyin shi, sai kuma yake ganin kamar gazawa ce da ci baya ya zauna mace na masa hidima da kuɗinta amman za ta iya siyan kayan ado domin kanta ko ta yi wani sha'anin a bangarenta ko kyauta ga wanda ta ga dama ba zai hanata ba.

Ya sake biya ma Walida Jamb bayan ya gama ja mata kunnen saura ta je ta faɗi, sannan ya saka ta jamb class, sai faɗa yake yi in aure take so ta yi mgana kada ta saka shi kashe kudi, Mimi ke tausan shi da cewa Jamb fa sa'a ne da rabo shi kuma ya ce har dakewa kuma da gaskiyansa duk abin da aka yi ma dakiya za ka iya cin ma nasara, itama Walidan ai ta sani dole ta dake da ƙoƙari. Sannan BUK ya cike mata saboda Mu'azzam ya ce za ta zauna a gidansa ta yi karatun ta, bai yi mata katsalanta kan ra'ayinta ba ya ce ta zaɓi Course ɗin da take so sai ta saka Microbiology.

  Rayuwar dai haka ta cigaba tafiya  a kwana a tashi ba wuya ga cikin Mimi na wattani takwas, Mommy ta yi mganar za ta koma gaban Hajiya ta haihu, Mimi na gaya ma Aji yace bai amince ba a tsarin shi ba tsarin matarsa ta je gida wanka a nan gidan za ta zauna ta yi wankanta da jegonta. Tunda kuma ya ce haka ta san yana kan matsayarsa sai ba ta matsa ba, ta ce ma Mommy za ta yi jegonta a gidanta ai suna kusa ba matsala,  A watan ta je kaduna Khadi ce ta samu ɓari ta yi ta zubar da jini kamar ba za ta rayu ba.

  Ba tafiyar mota suka yi ba Jirgi ne ita da Hajiya da Mama suka kwana biyu suka dawo. Amman ta je gidan Ahmad sun gaisa da Matarsa  ta na kuma dawowa Rukayya ta taso ta gaba kan shiryen shiryen biki tunda saura wata ɗaya da an yi ma sai dai an ƙara ma wata ɗaya ne a sama.
Ga cikinta ya tsufa ba ta iya wannan zaryan Aji ma ya ce Rukayya ta ɗaga mata kafa, ita kuma ta ce sai sun rama ma kura aniyarta itama haka ta wahala da na su bikin Aji ya ce dama ba don Allah ta yi ba kenan? Rukky ta na dariya tace eh sai an rama biki ba.

  Karamchi Tibi ta yi rashin ma'aikaciya Irin Rukayya domin tun saura wata ɗaya da wani ta ijye aiki, duka ma'aikatan sun yi kewarta musamman ma Na Misau,itama Mimin ta na so ta ɗauki hutu amman sai ta haihu saboda ta samu ishashen ookaci a gida tana kula kanta da abin da ta haifa tare da mijinta.Saboda shi ya na son kulawa ba zai mata uzirin domin ta haihu ta yi masa banza ba, nauyi ne zai haɗu mata dole sai ta samu lokaci da hutu.
Zuwa Lokacin sun gama siyan kayan haihuwa har na fitar suna, Itama ta ƙara ta siya ma kanta abin da take so da kuɗin ta.
Zirga zirgan bikin Rukayya ma ya sa ta sassaɓe. Ga shi biki gida biyu ga gidan su Rukayya ga gidan Daddy ana saura sati biyu biki a kai kai lefe akwati takwas kuma kaya sai wanda ya gani. Nan gidan za'a kawota ta yi sati ɗaya sannan mijinta ya ɗauketa zuwa lagos gidan da Jaheed ya siya fili ya na ginawa ba'a gama ba, sai an gama za'a yi ma amarya jere anan Gombe.

  An shiga satin biki zirga zirga da hidima ya ƙaru, Mimi da katon ciki a gaba ta ce ma ita ba wani kyau za ta yi ba tunda duk hallita ya sauya, sannan Gogan bai hana ta amman duk dare zai je ya ɗauko ta ta kwana a gida da safe ya maida ta, ba ta zama a gida ga zuwa aiki ga hidiman biki, shi yavsa ba ta san Mu'azzam da yayan na shi sun samu matsala har sai Baba ya yi musu sulhu ba, kan mganar biyama Inna aikin hajji ne, an ta biya sannan ga Walida ta samu Jamb har Buk sun ba ta admmission shi ne ya kira Mu'azzam kam hidimar makarantar anan ne ma ya ke faɗa masa kuɗinsa kaf zai haɗa ya biya ma Inna saudiya, shi kuma Mu'azzam ya na jin haka sai ya ji haushi ya ce ai tare suka ce za su haɗa kudi su kai Inna Saudiya me yavsa ya zare shi a ciki? wato ya nuna masa shi Inna ba ta haife shi ba kenan?, shi ta haifa Mansoor ya so ya fahimtar da Mu'azzam cewa ba haka ba ne. Amman ya yi fushi Ya riƙa kiran shi a waya bai ɗauka ba sai da Mansoor ya je ya gayama Baba  shi ya kira Mu'azzam ya yi musu sulhu, amman sai dai a ka yi yarjejeniyar Mansoor zai biya miliyan shida shi Mu'azzam ya cika sauran, dole a ka tsaya a haka sai dai Inna ta ji kawai ƴayanta za su biya mata ta je ta sauke farali ai sai ta saka kuka ta yi sujudaan godiya ga Allah ta na kuka ta na yi musu addu'an Allah yasa su gama da duniya lafiya.

  Ko kafin a gama bokin Rukayya har an kai Inna an mata pasport, an biya mata hajji ƙarkashin jihar Gombe.Kowa na ta zuwan ma inna murna baki ya ki rufuwa, ita kuma Walida sai bayan salla za ta wuce kano makaranta tunda azumi ya kusa. Gefe ɗaya kuma su Inna sun fara zuwa bita. Rukayya Amarya suna gama satin su suka yi sallama da ƴan'uwa suka ɗaga sai garin Ikko Mimi ta ba ta lambar Madiha tacce ga Yaya nan ta yi mata ba za ta yi kaɗaici ba.

  Bikin Mariya zai kama gabda babban sallah ne, Magajiya ta ce a ɗaga shi sai bayan babbar sallah Uwar amarya ba ta nan lokacin ta dawo Inna kenan, tunda yanzu Magajiya ta saduda ta nemi gafaran Inna suna zaune lafiya sannan ƴa'yan gabaɗaya sun haɗe kansu, Maeesha da Mimi ma sun haɗe kansu waje ɗaya kamar wani abu bai faru ba Saddiqun ma harkan gini Auwali ya saka shi tunda shi yanzu sai godiyar Allah ya samu ɗaukaka.

  Ana azumi saura sati ɗaya Mimi ta sauka, cikin dare gab da asuba Naguda ya kamata Aji ya ɗauke ta zuwa asibiti daman tuni ta shirya akwatin kayan hqihiwanta cikin ikon Allah ko awa ba ta kai tana nqguda ba, ta haifi ƴarta mace jajir da ita idanuwan da bakin da hancin na Aji ne fatar da suman kan  kuma duk na Mimi ne. Turbarakallah mssha Allah sanda ta haihu Inna na asibitin da Yaya Amina sai Baaba Uwani da Mama tunda ya kira su a waya ya sanar da su.
Kafin gari ya waye labarin haihuwan Mimi ya karaɗe Gombe da kewayenta.
Kuma kai tsaye uban ƙarnin ke fadin an samu wata MARYAMA ta biyu.



*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3019*

*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*

https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC

No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.


Mimi ba ta kwana a asibiti ba, ta dai yini zuwa dare bayan an tabbatar da lafiyanta da na abin da ta haifa a ka rubuta musu takardan sallama amman fa asibitin nan ta ga gayya kashi kashi kama daga ƴan'uwanta zuwa ƴan'uwan Abu Maryam ɗin. Gidanta a ka maidata, saboda daman Aji ya ce ba ya son wankan gida matarsa a gidanta za ta zauna ta yi jegonta sai dai a samu mai zama da ita, Mommy tuni daman ta yi ma Inna Zainaba mgana ta na jin an haihu a ranar ta iso, amman a gida ta same su tunda ba ta taso a kan lokaci ba.

Hajiya bakinta yaƙi rufuwa har da ita a asibiti har kuma suka dawo gida, ta ɗauki Jaririyan ta saka albarka sannan ta kalli Mimi dake zaune gefen gado a cikin bedroom ɗin ta, wani katon Jug ne a hannunta Inna Zainaba ta haɗa mata tea bayan sun yi wanka ita da jaririyar. Sai ta ji kwallah ta tarun mata a cikin ƙwayar ido, Allahu akbar yau ga shi Binta ta yi aure har ta kai ga ganin ƴarta a duniya. Sai dai Kabiru baya raye. Burin shi kenan ya ga Binta ta samu kyakyawan rayuwa irin na kowa ta mace. Hawayen nata sai da suka zubo ta share lokaci ɗaya tana faɗin"Allah ya jiƙan kabiru. Allah ya cika maka burin ka Binta ta samu kyakyawan rayuwa mai cike da farinciki da kake yi mata fata."
Mimi ba sai hawaye ta tuna da Abin ta amman a cikin ranta ta na yi masa addu'an rahama da dacewa.

Su Mama da Anty duk suna gidan har da Mamansu Rukky da Bibi da Nafisan Nasir, Sai su Bintu da Walida da Mariya su Yaya Amina sun tafi kafin mangariba, Inna kuma daman tun a asibiti bayan an haihu lafiya isowar su Mama ta koma gida. Sai can bayan isha'i gidan ya watse a ka bar Inna Zainaba kaɗai sai mai Jego ta kasa zama sai kai da kawo take yi domin kula da Mimin wacce ta samu ƙari sai da a ka yi mata ɗinki tana bukatar shiga ruwan ɗumi lokaci bayan lokaci, Aji bai shigo gidan ba sai wajen goma suna tare da Nasir da makama yau kam bakinsa ya ƙi rufuwa bai taɓa tunanin haka a ke jin farinciki in a ka zama uba ba sai yau wayar da ya amsa na barka bai san adadi ba, Mu'azzam daman shi ya fara kiran shi ya sanar da shi Fatima ta sauka an samu wata maryama Mu'azzam ɗin ne ya rika gayama sauran mutane, har su Baba Ɗanjuma da rana sun je asibiti sun Duba Mimi da abin da ta haifa.

Itama ta bangarenta har sai da ta gaji ta amsa wayoyin mutane, bayan ta dawo hayyacinta na natsu daga gumurzun

42 / 49