Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
gaske yake kyaleta, kwana huɗu suna gida ba su fita kuma ba wanda ya zo, domin shima sai a ranar ne da yamma ya je ya gaida su Inna sannan suka yi sallama da Mu'azzam za su tafi washegari da safe.
Itama a ranar Khadi ta zo gidan ta yi mata sallama ta ga Mimi duk ta faɗa ta fara mata dariya, ita da Jawahir Mimi ta marairace amman ba ta yi mgana Jahawahir ne ke bata shawaran ta riƙa cin abinci sosai tana kuma sakin jikinta, ta kuma kula da gyara kanta, sai a kwana na shidda ne Rukky ta zo gidan da yamma itama daman ranar litini za ta koma aiki. Har dare tana gidan Nasir ya zo tare da Aji Mimi ta ce daman ba don Allah yazo ba don Rukky ne ya ce to hakan ma da ta ɗauka dai dai ne.
Tare da suka fitan da Rukkyn zai kaita gida washegari asabar kuma tun safe suka tafi gidan Inna sai dai Inna ta gansu kwatsam tun da bai gaya mata nan ya barta ya je Camp ya dawo. Sannan ta taya shi ya tattara kayan shi tunda ya ce zuwa gobe zai saka a maida masa komai can har Injinan traning ɗinsa, bayan azahar suka bar gidan Inna zuwa gidan Hajiya suka gaisheta ba su daɗe ba suka tafi gidan Daddy sai su Mama shi baya gida nan ma ba su daɗe ba Daga nan suka biya kasuwa Mimi ta yi musu Cefane suka dawo tunda ta ce ta yi sati ɗaya ya kamata ta fara yin girki.
Washegar lahadi jigilan kayansa ne da Injinan training ɗin sa ya kwaso zuwa gida nan a ka saka mai cikin ɗakin da ya ce zai yi amfani da shi kafitar kuma can ya bar ta saboda baƙin kwana.Sai sauran tarkacen kayan kwallon sa da kyaututukar da ya samu a cikin kwalaye aka sako su. Kayan sawan shi na gidan ya kwaso gabaɗaya na Camp ma haka sai abin da ba'a rasa ba.
Ranar kuma Mimi ta fara girki, ta yi ma Inna kula ita da Hajiya, Aji ya ce har da Baba kuma da kansu suka kai musu da shi kaɗai zai je Mimi ta saka rigiman ba zai barta a gida ita kaɗai ba. Dole suka tafi tare gidan Wanzamai ne karshe suna can har goman dare abun mamaki Magajiya na maraba da su a ɗakinta ma suka zauna suka jira Baban kafin ya dawo, ba harara ba bakar mgana sai ma sakin fuska har ɗakin Meesha Mimi ta shiga sun gaisa da Baban ya dawo yana ta saka albarka wajen goma da rabi suka koma gida a gajiye suke wanka kawai suka yi suka kwanta amman da Asuba Aji bai barta ta huta ba, ga shi ranar za ta koma aiki tunda ta tashi ba ta koma ba tana kitchen ta na aiki shi kuma yana can yana motsa jiki,
Kafin bakwai ta gama komai dukkansu sun yi wanka. Tare suke karyawa cikin soyayya kamar yadda suka saba Mimi ta ci hijabinta jalbab har ƙasa Aji ya kaita tunda motarta na gidan Hajiya sai ta ta shi aiki za ta biya ta ɗauka bayan ya kaita ya dawo gida ya kwanta yana barcin gajiya, a can wajen aiki kuma ana ta ma Mimi murnan sabon waje Rukky kuma da suka haɗu tana mata tsiyan amarci ya karɓeta ta yi wani irin kyau na ban mamaki.
*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3013*
*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*
*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*
Haka suka sake cinye wannan satin cikin soyayya da ƙaunar junansu. A satin kaf saboda yana da free time shi ya kan kaita wajen aiki da safe sannan ya je ya ɗaukota in ta kira shi ta ce ta tashi aiki, duk da ta ɗauko motar ta amman ba ta fara fita da ita tukunna ba.
Zaman su suke yi lafiya cike da kauna da muradi. Ba mai zuwan musu gida an ba su ookaci su mori lokacin su, kuma sun mora gani suke yi a lokacin sun fi kowasu ma'aurata fahimtar juna da son juna.
Soyayyar su ta shekaru goma ta koma kamar sabuwa sun baje ta kawai suna jan harafin su. Kamar Yadda Aji ya faɗa haka ta ke gani domin ya ce daman in ta na son ganin soyayya sai a gidan auran su lalle ko tana ganin soyayya kala kala wajen Aji har mantar da ita kanta yake yi in suna tare, lalle ta yardan ma kanta shi dabam yake kamar yadda ya sha faɗa mata sunan mijinta Mansoor saboda haka ta bambamta da sauran wasu matan aure, ita dabam ce a wajen mijinta kamar yadda shima yake na dabam a wajenta.
Wakeend ya ƙara zagayowa haka suka ƙara yini a gida suna jin daɗin su, ta taya shi suka gyara ɗakin sa. Ta jera masa kayansa a wardrope da sauran dai tarkacen sa, ɗayan ɗakin da ya saka injina motsa jiki kuwa ya koma na so su biyu. Saboda itama matsewa take yi cikin ƙananun kaya ta ce itama ta zo motsa jiki ranar farko da ta shiryo ta zo ya kalleta daga sama har kasa kafin ya ce" To ke wani jiki za ki motsa? Ki na da kitse ne?
Mimi na lamgwaɓe kai lokaci ɗaya tana faɗin" Eh mana, ba na so na yi kiba ne kada na gagare ka ɗauka ka ƙaro min kishiya."
Saboda dariyan da ta kama shi sai da ya sauke karfen dake hannunsa ya miƙe zufa na tsiyaya daga jikinsa ƙaramin towel ɗin da ta kawo masa ya ɗauka yana goge jikinsa sai ta yi saurin karɓa tana goge masa lokaci ɗaya tana faɗin" Eh mana ai gaskiya ne saboda maza yanzu ba ku san mata masu kiba."
Ruwa ta ɗauko masa na gora ta buɗe masa ya karɓa ya kwankwaɗa kusan rabi sannan ya ba ta, ta karɓa lokaci ɗaya tana faɗin" Ba ka ce komai ba? Nuna min wanda ya dace da ni daga yau zan fara."
Dariya ya yi har sai da sautin ta ya fito. Da dariya na yi masa wahalan yi amman tunda suka tare ta na yawan ganin dariyansa a kai a kai, yau ma shagala ta yi da kallonsa sai ji ta yi ya riƙo kugunta da hannunsa guda ɗaya yana faɗin" Yaushe za ki daina haɗa kan ki da wasu matan ne Mimi? Sannan sai zuwa yaushe ne za ki daina haɗani da sauran maza? Na sha gaya miki ke mijin ki sunan shi Mansoor bai zama lalle rayuwar auran ki ta zama dai dai da na wata ko na wasu ba."
Sai ya ɗan dakata ya na kallonta kafin ya duka ya sumbaci bakinta lokaci ɗaya yana faɗin" Ni ba ruwana da kiɓar ki, ai ni ke na ke so ban damu da yanayin da za ki koma ba indai baki sauya da hallayan da na san ki da su tun farko ba. Sannan ba zan iya miki alƙwarin ba zan taɓa miki Kishiya ba, saboda in na yi hakan kamar na tsallake hurumina na faɗa bangaren Ubangiji, aure na Allah ne kamar yadda muka ga haka a zahirin auran mu, amman za ki iya yarda da ra'ayina? Wallahi tallahi ke kaɗai kin isheni rayuwar duniya Fatima amman in Allah ya nufeni da ƙara auran nan gaba to ki saka a ranki ba ki gaza ba, kuma ba ki kuskure ba sai domin sunnar ma'aiki da kuma abin da ya kaddaromin acikin kaddarata amman ke ce a jiya da yau da shekaranjiya har kuma gobe da jibin ma gabaɗaya."
Ya gama faɗa yana rumgumota zuwa jikinsa. Sai ta kwanta saman ƙirjinsa kalamansa na saka ta mirmishi. Tana son Aji saboda hallayarsa ma su kyau yana da gaskiya da sanin ya kamata yana mgana cikin natsuwa ba ya nufin kuma ya yi mgana domin wani ya ji daɗi, iya gaskiyan yake faɗa, kanta ya ke shafawa lokaci ɗaya yana faɗin" Amman tun da kina som rage kitse ba zan hana ki ba, amman kada ki yi min raki, domin na ga kin ɗauka ɗaga Karafunan abun wasa ne."
Dariya ta yi ya ja kunnenta yana faɗin" Bar dariya yarinya."
Sai ta daina dariya ta sha mur ta sake shi lokaci ɗaya tana ɗaga power hannunta tana faɗin"Nima ina da karfi fa."
Kallonta ya yi ta gefen ido kafin ya ce"To ai yanzu duk zamu ga ni."
Wani ƙaramin Karfe ya ba ta ya ce ta ɗaga amman abun mamaki yana sakar mata kawai sai karfen ya bi ta zai danne ta da sauri Aji ya riƙe karfin ya maida shi mazauninsa ita kuma Mimi ta kai ƙasa da sauri ya saka hannu ya ɗagota yana kallonta itama shi take kallo cikin haƙi tana faɗin" Na shige su, daman haka abun yake da nauyi?
Mirmishi ya yi lokaci ɗaya, yana faɗin" To daman mana? Kin ɗauka cin abinci ne ko aikin gidan tibin da kike zuwa ki zauna kawai ana ɗora miki camera?
Ya faɗa lokaci ɗaya yana laƙuce mata hanci, Mimi sai numfashi take saki ta tsorata. Da sauri ta ce"Ba wani mai ßaukin ɗauka?
Aji ya yi shuru kafin ya kai bakinsa saitin kunnenta yana faɗin" Akwai mana, gani ai ni ina da sauƙin ɗauka"
Kallonsa ta yi kafin ta balla masa harara lokaci ɗaya tana faɗin" Ba wani sauƙi, duk kanwar ja ce"
Ido ya zaro kafin ya ce"Au ni fa daman tausaya miki nake yi, amman tunda kika ce haka za ki gane baki da wayau yau. Sunan Hajiya da Mommy duk yau ba zai saka na ƙyale ki ba."
Tana jin haka ta yi saurin faɗin" Daga wasa? Ya fara bin ta in da ta matsa yana faɗin" Ni kuma ga shi ban san wasa ba."
Tana dariya ta ce"Haba Nawan. Haba mana ka ga fa ba mu ko ƙarya ba,"
Shi kuma ya ce za mu yi duk wannan daga baya. Ta kwasa da gudu za ta bar ɗakin ya tare ta cak ya ɗaga ta sama da nshi da komai ya ɗauketa yana faɗin" Duk anan karfina na yau zai ƙare."
Ta fara yawo da kafafunta tana faɗin"Wayyo Hajiya, Mommy Inna ku zo ku taimake ni."
Ya na tafiya da ita zuwa, ɗakinsu na barci yana fwaɗin" Su kaɗai? Ba ki kira Dr da Daddy ba, ki kuma ƙara Volume ba su ji ki ba."
Tana ganin sun shiga bedroom ɗin su shike nan ta saduda ta miƙa wuya kuma kamar mugunta, sai da ta fara masa kuka sannan ya ƙyaleta shima dai ya ce saboda yana da tausayi ne amman yadda ta haɗa sa da wancan karfen haka zai yi mata.
Sai bayan sun natsa sun yi wanka sannan suka yi zaman ƙaryawa. A lokacim Mimi ta yi masa mganar tana son zuwa ta ɗauko Hajiya ta zo ta ga gidansu, sai ya ce ta bari an juma sai su je su ɗaukota Inna ma yana son kawo ta itama ta ga gida ta saka albarka.
Bayan La'asar suka sake wanka suka fita gari. Gidan Inna suka fara zuwa suka gaishe ta, ita kaɗai a gida suna gidan Walida ta dawo. Sun ɗan jima kamar awa ɗaya sannan suka tafi gidan Hajiya, ba su daɗe ba suka ɗaukota Baaba Uwani daman ita ta je ta ga gidan lokacin tarewan. Sun kawo Hajiya ta ga gida ta yi ta saka albarka har tana faɗin" Kai Mansoor ya mganar mu ne! Na fa ga ya maka na ji na gani ka zo mu daidaita ba zan bar ma Binta wannan gidan ba ya yi mata girma."
Mimi na dariya ta ce"Hajiya na tare gaba na tare baya, ba ki da muhalli a wannan gidan"
Shi kuma Aji ya ce"Kada ki damu Hajiya ke ma ai sai na gina miki wani gidan wanda ya ninka wannan kyau da tsaruwa."
Hajiya ta ce"Shike nan kuwa an raba gardama."
Haka suka zauna suna ta hira xuciyan hajiya kamar farar takarda saboda jin daɗin ganin Mimi na zaune lafiya da mijinta. Hana ta tafiya suka yi har dare sai da Mimi ta gama dinner suka ci sannan suka maida ta gida a tare Ranar litini Mimi ta fara fita aiki da motar ta in yana da morning traning wani lokacin ma ya na riganta fita, ko kuma su fita a tare, megadin su wani matashi ne daga can anguwan Arawa Auwalu ya samo shi, an san gidan su ba shi da matsala shi ya sa in Mimi ta yi abinci Aji ya ce ta riƙa zuba masa amman fa bai amince ta riƙa fita da kanta tana ba shi ba sai dai ta ijiye in ya dawo ya ɗauka ya kai masa.
Kashedi iri iri Mimi ta sha shi da za ta koma wajen aiki.Kada ta riƙa mgana da maza ba ya son ta je ana haskata a gidan Tibi tana dariya kada ta manta ita matar aure ce, matar ma matar Aji. Ta san halin shi da mugun kishinsa na bala'i aikin ma ba domin Inna ta yi mgana ba da tuni ya rabata da shi, ita kuma saboda tana son aikinta ya sa take tsaka tsantaan. Tuni faman ta daina saka mayafi in za ta je wajen aiki sai dai hijabi, in kuma za ta saka mayafi sai in suna tare irin za su fita gidan Hajiya ko gidan Inna, shima sai ta masa yar shagwaɓa ta ce daga mota fa sai gida wane ne zai ganta ballantana ya ce wani abu, to in ta ce haka sai ya barta amman bayan haka sun zame mata kaya na ajiya kawai.
Kimanin sati uku da tarewarsu. Ya ɗauko Inna ta zo itama ta ga gida ta yi ta saka albarka Baba Danjuma ya zo tare da su Baba Sani da suka ji zai zo su ka ce suma za su zo, Mimi kuma ta yi ta hidima da su sai da suka ci suka ƙoshi, sannan Aji ya ɗauke su a mota ya maida su gida iyakarsa kuma daga Kofar gida shi tunda Inna ta bar gidan bai ƙara taka kafa cikin gidan ba Magajiyar ne baya son gani daman Inna ke kaawo shi kuma yanzu ba ta a gidan ba shi da abun ɗauka a gidan kuma, ya ɗauka sai ya shekara bai taka kafarsa a cikin gidan ba amman dalilin Magajiya ba ta da lafiya zazzabi da ulcer suka kwantar da ita har a gadon asibiti Inna Meri ta kira shi ta faɗa masa ya bar Mimi su je dubiya tare da su Bintu ya ce a'a, ta bari in zai je sai su tafi tare daman kuma Bintu ba ta matsa ma kanta ba sau ɗaya ta je ta duba ta gwara ma su Yaya Amina sun je sau biyu Inna kuma kullum sai ta je kuma ta yi abincin ta tafi da shi wazai hana ta? Ko an hana ta ba za ta ji ba shi ya sa yayan nata suka saka mata na mujiya.
Kwanan ta uku a asibitin a ka sallamo ta, Kuma duk Aji ne ya yi hidima asibitin Ƴaƴanta nata da take ganin ba kamar su ba su da shi gwara ma kowa ma da Saddiqu duk ya wani susuce. Lagos ɗin ma tunda ya dawo bai koma ba, matan kuma daman duk a wahale suke Manssor din dai da Mu'azzam su ne nauyin gidan nan, Washegarin ranar da aka sallami Magajiya da daddare ya ɗauko Mimi suka zo gaisheta shima ko asibitin bai je ba amman dai ya tura ma Auwalu 20k, Sun iske har su Zuwaira a gidan da Saddiqu da matarsa, Mimi daman ta yo abincin ta zo da shi bai hana ta ba saboda ba zai iya hanata aikin alheri ba. Amman in da ba ta ce za ta zo da abincin ba, ba zai taɓa matsa mata ba, a hanya ta kuma saka shi ya siya kayan marmari ta ce ai ba za su je hannu rabbana ba.
Ai ko duk sai suka yi tsuru tsuru sai ga Magajiya na amsa gaisuwan Aji da Mimi cikin rawan baki. Baba baya nan lokacin shi ya sa ba su wani daɗe ba. Mimi ta tura kyakyawan kulan abincin da ta zo da shi tare da ledan kayan marmarin gaban Magajiya, Saddiqu daman