Idan An Ciza Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   1 / 49

1 to 3K   out of 146.6K words



*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*

MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT

SHIN KINA DA LABARIN MACCE MAI GYARA DABAN TAKE GA ZUCIYA MIJIN TA, MUNA DA KAYAN MATA MASU ZAFI NA BUGAWA GA JARIDA

HAJIYA TA KUDI DA KUDI AKE NEMAN SU

INA MASU FAMA DA MATSALA RAMA BA GABA BA BAYA KINA ZAUNE ANA KWATANCI DAKE KINA CI BAKI KOSHI MUNA DA MAGUNGUNA DA ZUMA 3 IN 1 KIBA BRST HIPS TA CIKO MIKI KU INA KIYI FRESH MUNA DA KWAYOYI MUNA DA GARI DUK MASU CIKO JIKI NE KIYI DUM

INA MASU FAMA DA MATSALA BRST KU TSUHU YAFI SON YAGA NONO A TSAYE DUK MAI MAGANIN DA TACCE MIKI ZATA BAKI MAGANIN NONO KAI TSAYE YAYI MIKI KARYA CE MAGANIN BRST SAI KIN SHA ADADIN WANDA ZAI MIKI SBD DUK CIKIN GYARAN JIKI NA BRST YAFI WAHALA YI

INA MASU FAMA DA MATSALA SANYI MUNA DA MAGANIN SANYI ORIGINAL

INA MASU ZAMAN BANZA BABU SANA'A KINA KONE DATA KI GA BANZA WURIN TSEGUMIN KALLON STATUS DIN WASU GA DAMA TAZU MUNA HAR GIDA GA WAYAR HANNUN KI KI MALLAKE MOTA MILLION 8 HAR FIYE GA ALBASHI GA RIBA GA KYAUTA KAYAYA KI
08066726866

Mai mashin ɗin da ya ɗauki Mimi bai direta Ko ina ba sai ƙofar gidan marigayi Sulaiman Dabo da taimakon kwatancen da ta yi masa. Ta sauka ta ciro kuɗin sa a cikin jakar dake hannunsa ta bashi ya karɓa yana ta mata godiya ganin ta ba shi har dubu ɗaya sannan ba ta tsaya yin mganar karɓan chanjin ba har ta kai jikin get ɗin gidan ta fara bugawa.

  Megadi na zaune ya ji ana ta buga gida sai ya taso zai buɗe amman yana tambayan waye?. Cikin Shaƙewar murya Mimi ta amsa masa da ita ce Binta ce, da sauri ya buɗe karamar Kofar sakamakon akwai hasken ƙwai wuta a wajen sai ya samu sararin ganin fuskarta tar da ta yi wani ja ja alamun ta sha kuka sannan Idanuwanta sun yi jajir sun kuma tasa.

"Binta? Ke ce tafe da daddaaren nan?

  Ya faɗa cikin mamakin ganinta. Domin har bayan ya leƙa bai ga motar ta ba sannan bai ganta tare da kowa ba, halin da take ciki ne ya sa ba ta tsaya ma sauraran megadin ba ta wuce shi da Sauri zuwa Kofar da za ta sadata da falon Hajiya, shi kuma sai ya bi ta da kallo domin wannan zuwan dai daga yanayin Bintar ma za ka fahimci ba Lafiya lau sai ya fara tunanin ko dai wani abu ne ya samu Hajiya? Gabansa ya faɗi a sarari ya furta" In sha Allahu khairan."

  Kofar falon a rufe ta ke sai da ta buga, Baaba Uwani ɗakin na falo ne amman ba ta ji bugun kofa ba, ta yi aikace aikace ta gaji daman tana da nauyin barci, Mimi har ta ga ji da buga Kofa ta dakata tana ƙokarin lalubo wayarta ta kira lambar Hajiya. Sai ta ji kamar ta shin magana daga cikin falon, Ashe Hajiya ce ba ta yi barci ba ta ji bugun Kofa Daga ɗakin ta  shi ne ta fito ta leƙa ta na kiran Sunan Baaba Uwani sai da ta tashi Sannan ta ce ta ta je ta buɗe Kofa ta ji kamar ana bugawa.

"Buga ƙofa kuma Hajiya?

  Baaba Uwani ta faɗa da sigan tambaya ta na kallon Hajiya. Lokaci ɗaya kuma tana duba agogon dake cikin ɗakin da ya zama nata tun farkon zuwanta gidan.
Karfe 11:04pm dai dai na dare a lokacin.
Hajiya na tsaye a kofar ɗakin ta ce" Fito ki Saurara ki ji, ni dai tabbas na ji ana buga Kofar falo."
A tare suka ɗumgumo zuwa falo dai dai lokacin Mimi ta ƙara buga ƙofar sai Baaba Uwani ta kalli Hajiya itama sai ta kalleta gabansu a tare ya faɗi, Hajiya ta yi Saurin cewa" Ko dai Hamza ne? Allah yasa lafiya hanzarta ki buɗe Uwani."

  Baaba Uwani jikinta na ɗan rawa ta ƙarisa wajen Kofar ba ta buɗe ba sai da ta fara da tambaya.

"Waye?.."

"Ni ce Baaba Uwani!"

"Ke ce wa?

"Bintu ce Baaba Uwani.."

  Mimi ta faɗa lokaci ɗaya tana ƙokarin maida kwallar da ta taso mata, Hajiya na bayanta ta ji muryan Mimi, Baaba Uwani ma sai daga baya ta gane muryanta jiki da zuciya na rawa ta buɗe kofar dai dai Hajiya ta kariso wajen tana faɗin'" Bintu kuma? da wannan daren?
Maganarta ta tsaya ne lokacin da Mimi ta shigo falon.Duk iya kokarinta na kar ta yi kuka ganin Hajiya sai da kuka ya kwace mata kawai sai ta tafi ga Hajiya ta faɗa Jikinta ta fashe da kukan da take ta riƙewa mai karfi yana kuma fitar da sauti, kukan zafin zuciya ne, kukan abin da kake tunanin kana so ashe shi tunanin shi ba shi a kan ka, kukan takaici da baƙin ciki wanda ka yi ma soyayya gaskiya shi kuma a na shi bangaren ba haka ba ne.

"Innalillahi wa'inna alaihirraju'un! Hajiya ƙarama lafiya kuwa?

  Baaba Uwani ta faɗa cikin tafa hannayenta, Hajiya kuwa daman tuni take ta salatin ta a cikin ranta,  ammam Mimi ba ta san suna yi ba ta kamkame Hajiya tana ta kuka nan tsayen ta saki jakar hannunta da mayafin jikinta kayan barcin dake jikinta suka bayyana Sai baaba Uwani ne ta duka ta ɗauke mata sai faman salallami take yi.
Ita kuma Hajiya sai ta riƙe Mimi cikin Kwantar da murya ta ce" Binta Allah ya sa lafiya? Ko wani abu ne ya samu mijin naki?
Sai ta girgiza mata kai alamun a'a Hajiya ta ƙara tambayanta ko wani abu ne ya samu Merin? Nan ma ta ce a a.
Gaban Hajiya na faɗuwa ta ce" To me ya faru kika biyo wannan daren ke kaɗai kina kuka? Ko wani abu ya faru tsakanin ki da mijin naki ne? Jin haka ya sa Mimi ta ƙara sakin kukanta lokaci ɗaya kuma ta rabu da jikin Hajiya ta kama hanyar ɗakinta tana Cigaba da kukanta kamar wacce a ka ce mata an yi mutuwa.

  Hajiya da Baaba Uwani suka bita da kallo, Baaba Uwani ta yi wani iri tana duban Hajiya kafin ta ce" Hajiya me ya ke faruwa?
Hajiya ta yi shuru kafin ta sauke numfashi Tana faɗin" Ban sani ba Uwani, amman mu ba ta lokaci ta samu natsuwa zuwa da safe mu ji, in taki mgana sai na nemi ita Merin naji abin da ya faru."
Baaba Uwani ta ce a sanyaye" Hakane Hajiya, To Allah ya ijeshemu alheri."
Hajiya ta amsa da Amin Amin amman Jikinta na ba ta wani abu ne gagarumi ya faru haka nan Binta ba za ta zauna tana wannan uban kukan ba.

  Karɓan kayan hannun Baaba Uwani ta yi ta bi bayan Mimi ta ɗauka tana ɗakin ta sai ta isketa nan saman gadon ta ta dunƙule tana faman kuka. Hajiya ta shigo ɗakin ta maida Kofa ta rufe sannan saman kujera ƙwara ɗayan da ke cikin bedroom ɗin ta ijiye mayafin Mimi tare da jakarta sannan ta karisa bakin gadon ta zauna tana faman kallonta amman kamar ba ta san tana ɗakin ba kuka kawai take yi mai karfi kamar ranta zai fita.

"Fatima.."

  Hajiya ta kira sunanta cikin taushi. Amman Mimi ba ta amsa mata ba, kuka kawai take yi. Sai kawai Hajiya ta miƙe kan madubin da ke ɗakin ta isa ta ɗauko wayarta lokaci ɗaya tana faɗin" Tun da ƙin ƙi mgana ballantana nasan abin da ke faruwa bari na kira Meri, ƙila ita s ta faɗamin abin da ya fito dake daga gidan mijin ki, kika zo  nan kina ta min koke koke"
Ba ta san lokacin da Mimi ta sauko daga kan gadon ba sai ganinta ta yi a gabanta lokaci ɗaya ta warce wayar hannunta.
Cikin mamaki Hajiya ke kallonta kafin ta samu zarafin magana Mimi ta riƙo duka hannayenta ta jimƙe cikin nata pokaci ɗaya tana ƙokarin danne abin da ke ranta amman hawayenta ba su tsaya ba.

"Hajiya in roƙe ki wata alfarma? Na san tun tasowa ta a gabanki kike yi min duk wani abin da nake so, to ina so ki yi min na yau ko da zai zama shine wani abu na ƙarshe da za ki yi min"

  Mimi ta ƙarishe faɗa cikin kuka. Ganin haka yasa Hajiya ta jinjina kai sannan ta riƙo Mimin zuwa saman Kujera suka zauna sannan ta saka yatsun hannunta tana share mata hawaye lokaci ɗaya tana faɗin" To shike nan daina kukan hakanan kin ji ko?.
Sai Mimi ta gyaɗa mata kai, amman kukan na sake fito mata. Kanta na ƙasa ta ƙara rike hannayen Hajiya tana faɗin"Hajiya ki yi min alfarman ba za ki takuraman sai na faɗa abin da ya faru ba,  kuma ba za ki takuramin sai na koma gidan Mansoor ba."
Hajiya ta ƙura mata ido lokaci ɗaya kafin ta ce" Saboda mene?
Sai kawai Mimi ta kwanta a jikin Hajiya tana faɗin" Na hakura da AURAN nan Hajiya ba zan iya ba. Wallahi  ba zan iya ba."

   Take faɗa tana kuka, Hajiya ta yi shuru kafin tace" An taɓa cewa an haƙura da Bautar Ubangijine ba tare da wani dalili ba Binta ba? Ta faɗa lokaci ɗaya  tana dafa kafaɗan Mimin alamun lallashi,  Mimi kuma sai kawai ta kara saka ma Hajiya kuka cikin kukan tana faɗin" Hajiya ina da dalilaina amman ba zan iya faɗa miki ba, ki bar ni a baya ni dai na ce ina so  yanzu kuma na ce ba na so Hajiya domin Allah kar ki takuramin."

"Ya sake ki ne da kike faɗin haka?

  Mimi ta girgiza kanta kafin ta ce"Bai sakeni ba, amman zai sake ni dolen sa Hajiya."
Sai lamarin ya fara ba ma Hajiya tsoro amman ba ta sake mgana ba, ganin irin kukan da Mimi take yi yasa ba ta sake jan ta da wata mgana ba sai ta rumgumeta tana lallashinta cikin taushin murya take faɗin" Shike nan ya isa daina kuka ya isa Binta ya isa."
Take faɗa tana bubbuga bayan ta, Mimi tun tana kuka har ta koma sauke numfashi cikin dashewar murya, Hajiya ta lallaɓata ta koma kan gado ta kwanta ta rufa mata bargo kanta ta shafa kafin ta ce" Ki daina kuka. Da safe sai mu tatttauna kin ji ko?
Sai Mimi ta gyaɗa mata kai lokaci ɗaya tana jin yar salama tana da tabbacin cewa Hajiya za ta mara mata baya.

  Dukkansu daga Mimi har Hajiya ba wanda ya samu cikakken barci, Mimi damuwa da bakinciki ne suka hana ta kwanciya, Ita kuma Hajiya tunani da kuma damuwa suka hana ta samun barci da wuri. Ta yanke shawaran da safe za ta kira Hamza domin ya zo ya ji abin da ke faruwa ita a tunanin ta matsala ce tsakanin Binta da mijinta kuma shi aure yana da tsari da doka domin ta ce ta hqƙura ba za a barta a zura mata ido ba ya zama dole a yi binciken abin da ke faruwa.

******

  Yadda Hajiya da Mimi suka yi kwanan damuwa da rashin barci. Haka Inna Meri ta kwana salla tana kai ma Allah kukanta Hibba da Walida ma sun kusa raba dare ba su yi barci ba, gwara ma Walida ta samu barci daga baya amman Hibba ta kasa saboda duk farkawan da ta yi sai ta leko Inna a falo sai ta ganta tana sallah tausayin Inna Meri ya gama cika mata zuciya.
Domin hannu ta ɗaga sama tana hawaye  lokaci ɗaya  take faɗin" Ya Allah ga bawan ka nan Mansoor ka fi ni sanin abin da ke cikin zuciyarsa Ubangiji ka saka mishi salama da yafiya a cikin ransa, ka saussauta masa wannan baƙar zuciya dake damunsa, ka ba shi zuciyar yafiya da afuwa, Ya Allah ni ba zan iya ba ka dafamin ka shiryamin rayuwar wannan yaron."

  Tana yi tana kuka, Hibba sai dai kawai ta koma ta kwanta har tana sharan kwalla, a daran ta kira wayar Mu'azzam ba ta samu ba. Sai da asuba sannan ya kira ta akan mganar tafiyar ta, sai kuma Hibba ta sanar da shi wani labari mara daɗin ji.
Cikin tashin hankali ya ce" Subhanallah! Yanzu ina ita Anty Mamin?
Hibba ta ce" Ta tafi gidan Hajiya tun a daran Jiyan." Da sauri ya ce" Me ya sa kuka barta ta tafi? Inna kuma ba ta hana ta tafiya ba?
Hibba cikin sanyin murya ta ce" Inna ba ta hana ta ba, ni ce na hanata tafiya amman ta rantse sai ta tafi." Mu'azzam ya dafe kansa daga can bangaren kafin ya ce" Yanzu ina shi Yaya Mansoor ɗin?
Hibba ta ce" Wlh ban sani ba, tun jiyan ya fita ya bar gidan."

  Mu'azzam ya saki huci kafin yac e" Kin gane bari na neme shi a waya, Ina Inna take ?
Hibba ta ce"Inna na tsakar gida,.Duk ta damu jiya kwana ta yi ba ta yi barci ba gaskiya abin da ɗan uwanka ya yi bai kyauta ba kuma ina tsoron haƙƙin Mimi da Inna ya kama shi."
Mu'azzam ya jinjina kai kafin ya ce"Bari na neme sa a waya." Daga haka ya katse wayar cikin tashin hankali ya fara neman lambar Mansoor din amman wayar ta na kashe ne.
Gabaɗaya sai ya rasa mafita. Sai ya sake kiran wayar Hibba ya ce ta ba ma Inna wayar, lokacin da aka kai mata ta karɓa suka gaisa sama sama.

"Inna na ji abin da ya faru yanzu Hibba ke faɗamin, Inna me ya sa ba ki hana ta tafiya ba? Da sai a zauna a sulhuta mganar a nan gida ba sai ta je da mganar gidan su ba."

  Inna Meri ta yi mirmishin taakaici kafin ta ce"A a Mu'azzamu in na yi haka kamar na danne ma yarinyar nan haƙƙinta ne, gwara da ta tafi gidansu danginta su nema mata haƙƙinta, in na ce ta zauna ai ba zan iya taƙwasa Mansoor ba,  ya fi karfina, tun da kuma har ya furta baya sonta to ko ƴata ce iyakar abin da zan yi mata kenan."
Duk yadda Mu'azzam ya so ya fahimtar da Inna amma ta dake kan magana ɗaya wallahi ba za ta saka baki ba, Mansoor sai ya saki Mimi ita kuma da ya saka ta jin kunya ba za ta yi masa baki ba, ta yafe masa amman wallahi tallahi ta cire hannun ta a kan rayuwarsa za ta kira can kwami ta sanar da su halin da ake ciki ta yi iya nata ba za ta iya ba su zo su saka hannu suma tunda ɗan sune.

  Dole ta saka Mu'azzam ya ce ma Hibba ta zauna zai shigo garin jibi jumma'a domin ya ga halin da ake ciki, amman zai dai cigaba da neman layin Mansoor ɗin ya ga ko zai same shi.
Jikinsa a sanyaye ya shirya ya tafi wajen aiki, amman yana tunanin me ya sa Yayan na shi ya aikata abin da ya aikata? Yana masa tsoron kar haƙƙin Mimi da  na Inna ya kama shi kamar yadda Hibba ta faɗa. Har ya je office ɗinsa wayar Mansoor tana kashe ne ya rasa kuma hanyar da zai same shi su yi mgana.

  Gama wayar Inna da Mu'azzam ba daɗewa, Inna na kofar ɗakin ta, ƙokarin dama kunu take yi. Ta ji tashin hayaniya daga Bangaren Magajiya ta ji muryan Baba Sani da na Baba Danlami, amman mganar da ta ja hankalinta har ta dakata  da abin da take yi ta saurara shivne muryan Baba Ɗanjuma da ta ji cikin fushi yana faɗin" Ba ruwan ku a wannan mganar. Ɗaki dai nawa ne, kuma ni ba ma Mansoor ɗakin nan da Kaina na ce ya zauna da matarsa har sai shi da kanshi  ne ya gaji ya ce zai tashi. Saboda haka kai Sani da Ɗanlami baku da iko kan abin da yake mallakina tunda ina raye ban mutu ba."
Tunda Inna  ta ji wannan kalaman jikinta ya fara rawa shike nan ta faru ta ƙare, abin da ta daɗe tana gudu sai da Baban Inna ya ja ai ya kyauta.

  Cikin wannan halin ta dama kunun saura kaɗan ma ta saki tukunyar ruwan zafin a kafarta saboda damuwa. Tunda sai tashin maganganu take ji daga bangaren Magajiya, Ta dama koko kenan ta ɗora ruwan zafi sai ga Magajiya ta faɗo shashen Inna Merin cikin hargowa tana faɗin" Malama ki faɗa ma ɗanki ya tashi ya bar ma masu gida waje, tunda dai ko bayan Ɗanjuma ya faɗi ya mutu ba shi da gadon ko filoti a cikin gidan nan."
Take faɗa tana kallon Inna Meri cikin reni, sannan ta rike kugunta alamun yau da bala'i ta shigo

  Kallonta kawai Inna Meri ta yi amman ba ta yi mgana ba, Baba Danjuma ne ya shigo ya na kwalama ta kira cikin tsawa" Magajiya ba na ce ki bar mganar nan ba ne?
Baba Sani da Baba Ɗanlami su ka shigo har suna haɗa baki wajen faɗin" Me ya sa za ta bar maganar? Ai gwara ta faɗa mata domin ta ji  yadda ta bar agolan ɗan ta ya kame a gidan nan gwara a sake fahimtar da ita ba shi da gadon ko taku a cikin gidan nan."
Abun mamaki har da Saddiqun shima yana bayansu amman bai yi mgana ba, Inna Meri ta kai kununta ɗaki. Sannan ta sake fitowa hayaniyar har ya fito da Walida da Hibba.
Baba Ɗanjuma ke nufar Inna Meri yana faɗin" Meri kar ki tankasu yi shigewarki ɗaki domin Allah."
Inna Meri ta yi mirmishin takaici kafin ta ce" A'a kyale su gaskiya su ke faɗa, nan ai ba gidan uban shi ba ne ni kaina ban ga dalilin zaman shi ba."

  Ta faɗa lokaci ɗaya tana haɗiye wani abu da ya taso mata daga ƙasan zuciyarta.
Baba Ɗanjuma ya kalleta cikin mamaki amman ya kasa mgana Baba Sani ya ce" Kwarai ashe kema kin san gaskiya. Na rasa me yaron nan yake so a duniyar nan, yana da gidan shi amman nan dai haƙƙin wasu marayun ne ya tsole masa ido."
Saddiqu na daga baya ya ce"To ni in baya son gidan ne ya ba ni na zauna, in kuma ba haka ba ya tashi ya ba ma magada wajen su." Baba Ɗanlami ya ce"Ahto in ya na son zama a gidan gado sai a koma ƙauye a zauna

1 / 49