Author : NONE Category : African Stories & Novels
sauri ta wuce sama ranta a mugun bace
bappa zaidu yabita da kallo..cikin lumshe ido da budewa yace Allah ya kyauta. the tablw was quite for a moment sai can snn yy karamin nasiha ma yayansa akan karda su biye ma uwarsu suki zumunci, saida duk suka nuna sun fahimceshi snn ya sallamesu suka wuce makaranta..
wani irin makokon baqin ciki da haushi mai tsanani ne ya turnuke ammi babba kasama zama tay a dakin sai safa da marwa take tsakanin corridor da corridor tanaji tsanar ibaad din na kara ninkuwa aranta bana kadan babu kalar abunda bata raya aranta ba, can sai ta wuce daki da sauri ta dau wayarta kusan bugu ma uku sai aka dauka
atake take ta sauya murya izuwa na makirce tana maganan tana dan jan girma "wa alaikis salam safeera, Allah sarki na katse miki baccin safenki ko?
dagata dayan bangaren anty safeera tace bakomi ammi babba ynxun nan na dawo daga raka mijina zaije aiki
"Allah sarki..toh ya gidan naku..ya mijinki ya yaranku.. anty safeera tace duk lafya muke dama ammi karamace kawai bataji dadin jikinta ba..
yi tay kmr bataji hakan ba cikin sharewa tace "uhum kinajin labarin antynki kuwa? ina nufin hajy hamida shettima ..anty safeera tace a'a, amma dai naji ance yarta zainab arifah bataji dadin jikinta ba so bana tsammanin ma zatazo wnn wkends anjima dai nake so na kirata inji ya jikin.
tace ohhh ayyah hala ko shine dalilin dayasa kawu babba yace suna neman ibaad agidan, did she say sumtin abt him to them? ko har sun amince zasu bari ta kulla soyayyan ne dashi, hmm amma da abun baiyi ba..
adan mamakance anty safeera tace ahh toh gaskiya nide bansani ba amma kinsan abu me wuya ne dama su hanata abunda takeso..
wani irin zafin tsana da kishi me tsanani ammi babba taji na tsagawa aranta, tay shiruuu, san can sann taja nunfashi adan dakile tace hmm toh Allah ya kyauta..nidai nake xaune da yaron nan nine kuma nasan halinsa, inda ace zaku nemeni shawara ta danace muku karda a sake abar zainab arifah tay wannan mummunn zabin makanta..wallah yaron nan baida mutunci kigadai mugun bugun daya ma zainaba ranar gashi da girman kai sam baida kunya ko kadan
anty safeerah tay shiruu batace komi ba sai can tace yanxu dai bani da tacewa ammi babba kisan dai kawu babba ne keda ikon yanke duk wani hukuci akan yarsa amma in har anty hamuda ta neme shawarata i will try nd talk to them
cikin washe baki ammi babba tace toh ai shikenan bakomi, pls inkin kira kinji jikinta saiki gaya min snn ki gaida min hajy kice ina mata fatan alheri.
anty safeerah tace toh ammi mungode da gaisuwa duk dai abunda ake ciki zan taɓaki
...murmushi tay tace toh kardai ki manta nagode safeerah agaida yara insun dawo.
daga haka suka katse wayar..anty safeera bata kawo komi aranta ba duk dama tasan da cewa abun ammi babban harda zafim kishi da tsanar datakewa ammi karama aciki, deep in her heart tasan a nitsuwa da hankali da kyau da komi ibaad yafi karfin ya aure zainab arifah nesa ba kusa ba. infact banda gata da arzikin da ubanta yake dashi da ko kusa da ibaad akace tazo bazatazo ba. saidai bataga lefin ammi babba datake zafin kishi da ammi karama ba, ammi karama is almost perfect ga kyau, ga kamala, nitsuwa, ga kuma ilimi, itama kanta safeeran bata kaunar kalmar kishiya bare ƴayanta. kai kaf duniyan nan ma babu wani abunda ta tsanaji kamar batun kishiya. ji take ranar da uncle moh ya ce zai mata kishiya toh ranar zata iya kashe kanta kota kona gidan gabaki daya.
fannin su inayah kuwa yauma suna idar da Alwala a bore-hole din makaranta tadan miƙo tattausan hannunta tariko kyakkwan fuskar ayanah tanamai sakin sassanya kuma nakasshiyar mrmushi mecike da tsumayi wanda yake saurin fallasa wann dumbin kaunar datake yima yar uwantan aranta.
ahnkli tahau gyara mata zaman dark green hijabinta dakema ayanahn tana da yololon ɓakin suman gaban goshin mai hade irin wani kwantaccen shatin saje mai daukar hankali wanda yake yawan nunawa a fili sosai, idanuwanta masu cike da nuna kaunar da take mata ahnkli take fmr cusa suman ciki tana cewa "Ayaana am, Idan wata rana kikaji sanyin ruwa ko iska me sanyi tana busawa, har kuma tashafi gashin kanki, ki sani ina nan kusa da ke."koda ace ranar bana numfashi soyayyata zataci gaba da zagaye ki, "koda ace bani da murya,
addu’ata zata rika zuwa gareki tamkr yadda iska yake riskan ramin hancinki ayanzu, inaso koda bana nan a duniya kicigaba da kulamin dakanki, ina sonki sosai anayo am kinji ko??.
..ayaanah data zuba mata ido ta dan kyalyale da dariyar yaranta "addana ina sonki nima sosai ai bazamu taɓa rabuwa ba har abadan abada ko mutuwa zamuyi tare zamu mutu..bakiga duk kika tashi a bacci cikin dare kina ciwo nima sai natashi sai naji zuciya na yanamin ciwo ba?yo duk inaa kikaje aduniyan nan saina biki shiyasa ma Allah yayimu mu biyunmu awajen ummanko ko??
ahnkli inayah tay mata dariya me sanyi ta gyada kai sai batace komi ba..
..kusan duk rana sukan yi ire iren wnn maganan shirmen atsakaninsu amma dukansu basu taɓa daukarsa akomi ba inayah ne kawai takeji ajikinta da xuciyarta kamar dai wani abu nadaban xai faru da ita.
washe gari shine ranar da zasuyi papernsu na karshe sassafe tun kan akira sallahn fajr inayah tafarka jin jikinta ya dau zafi sai kuma taji cikinta na kugi kusan aguje tawuce bayi tayi zawo sosai sai snn taji dan dama dama
saidai tunda ta fito wani dan uban kasala ya sake rufeta, ko yar dauriyan nan yau takasa yi sabida tunda tay zawon kasalan yabi ya dameta ta zama bata jin karfi ajikinta ko kadan. yau ko abincin safen ma bata ji sha'awar ci ba, haka hanklin taawure yatashi sai kawai ta ɗeba mata fura da nono a gora akan idan tay jarabawar sai ta zauna tasha tunda jarabawar karshe ne anatashinsu da wuri..
tace daga antashesu yau suje kasuwa su zauna a shagon hajy mairo har saita dawo daga saida nono ne zasuje chemist abawa inayan maganin zawon daya jawo mata wann kasalan yau da safe
ahaka suka rabu kowa ya fita sana'arsa amma hanklinsu nakan inayar, dake gabaki daya yau ciwon yaki sam ya ɓoye kansa, kusan a daddafe ma tay jarabawa dama kuma shine mata na karshe, tagama firamare kenan, ba a wani bada wani kyauta a schl din amma ita sosai ta samu kyautar jinjina daga wasu malamai musmmn ma na lissafi, wasu suka bata kudi naira dubu biyar, wasu suka bata littafai da jakan baya, wani dan nysc har na tunanin biya mata kudin zuwa private scndry schl a cikin garin kano sabida aganinsa bai dace dumbin ilimin inayahn ya tafi a banza acikin kauye ba.
duk da ciwo na cinta aciki haka ta matse tay musu godiya, ta kuma nemi yafiyar kowa aka rabu cikin lumana da ita, ayanah na rike da ita duk inda zataje sabida wnn dan uban kasala da zafin datakeji ajikinta har yanxu.
ahnkli ahnkli suke tafiya manne da juna, but is like every few mins jikin inayahn ke dada sacewa karshe ayaanah ta nema musu wani gindin bishiya ahanya suka zauna dan ta samu hutu tay catching breath inta, suna zama ayaanah ta ciro goran nonon ta girgiza ta bude mata hankli a matukar tashe tace "tashi kisha wann adda koda zakiji karfi..tana faɗa tana kai mata baki.. idanunta duk yay jazir da damuwa aciki.
kurɓi biyu zuwa uku inayah tay sai taji gabaki daya taste din nonon yana ɓata mata rai sosai dan haka kawai ciwon yake sawa taji ta washi cin abinci ko shan wani abu gashi kuma matsanancin yunwa takeji. magiya ayaanah ta dingayi mata amma taqi sam takara kurɓa, can sai ga wani dan yaro almajiri yayi futu futu rigarsa duk ta yi dukunkun baida takalmi ga mtsnancin yunwa ya galabaitasa tsabar layi agigice ya zauna akasa snn ya riƙe cikinsa yana nishi daga ganinsa kasan yunwa yakeji bana kadan ba. ganin wann almajirin ne yasaka inayah ta mance da nata yunwa ta kuma dawowa cikin hayyacinta babu shiri cikin dauriya ta miƙe tsaye ta isa gareshi da gorar furan ta miƙa masa tace mai yasha kusan a gigice yaron ya karba muryansa da jikinsa na rawa rawa yana mata godiya yakai baki ƙwad ƙwad yafara gwankwadar lafiyayyen nonon like his life depend on it har saida ya shanye tass, ya daga ido ya kalli inaya yace "Allah ya saka miki da gidan Aljannah
ayaanah na kkrin yin mgn ta tsareta da ido tana murmushi ahnkli tace ameen, yaron ya tafi,suna wuceshi tace ma ayanah suje can kasuwan kawai sujira taawure inyaso awajen hjy mairo zata nemi wani abunda zataci. hakan yasaka ayanah jin dama dama aranta sabida tasan yunwa na damun addanta sosai amma kuma sau taga bata iyacin abinci
suka rike juna suna tafiya ahnkli ahnkli har suka kai cikin kasuwa, as usual babban shagon hajy mairo me tuwon acike yake tammm da customers ana shige da fice ga qamshin abinci kala kala yana tashi takoina, ta kofar baya suka shiga suka sameta a inda take yawan zama, dake kamar kaka take awajensu suna gama gaisheta maza tasaka aka kawo musu lafiyayyen abinci shinkafa da miya da ganye akai wanda sun fara ci kenan still inayah ta dau rabin nata ta fita waje taje ta bawa wani mai daƙo da yunwa ya mugun galabaitashi ya daure cikinsa da tsumma ya jingina akan wheel barron sa awaje har ya kasa motsi.
anan ma koda ayanah tamata magana akan meyasa ita bataci abincin ba tabashi, saidai tay murmushi tace mata sudin sunfita bukata ne shiyasa take basu. bare ma awajenta ai ciyar da wanda bai dashi yana ɗaya daga cikin manyan ayyuka mafi soyuwa awajen Allah ta gwammaci hakan akan komi.
bayan sun tattauna kaɗan akan hadisai da kissoshi tareda ayanah wani irin bacci ne ya dauke inayan batare da taci wani abincin kirki acikinta ba duk da uban yunwa dake damunta aranta, ayaanah kuwa tuni tamiƙe tawuce wajen hjy mairo mai tuwo ta zauna tanata kallon yadda ake shige da fice tareda hada- hadan abinci dakema sunfi shaƙuwa sosai tafiyeson balbale hjya me tuwo da surutai na yaranta....
sallah ne kawai ya taɗa inayah wajen yin tsarki hakanan ta amayo da duk wani abu data saka acikinta batare da kowa yasani ba, gashi dakyar take tsugunawa kasa tsabar ciwo da zafin da cikinta yake mata, koda ta fito sallahn ma yau addafe tayishi can da yamma liss sai ga taawure ta dawo shagon hajya mairo ta debesu suka wuce chemist direct akay ma inaya gwaje gwaje akace musu wai typhoid ne, haka aka siya ma inayan wasu magani tana sha kuwa tadan samu relieve har kamar ta warware, a kwana na ukun da yamma suka shirya tsaf sukay sallama da hajiya mairo me tuwo da sauran mutanenta, taawure ta debi fiye da rabin tarun kudin cinikinta ta zuba a asusun hajya mai tuwo akan idan hutu yakare daga sun dawo za'a nemawa inayah makrntar sekandari tadan fara kafin mijin aure ya fito amata aure. bayan hakan ya kammalu wajajen 4:30pm na yamma suka kama hanyar komawa gidansu acan kauyen majiya da zimman sai hutu yakare snn zasu dawo.
ba su da isa garin su ba sai wajajen karfe 6:30pm dake akafa suka taƙa, kafin sukai gidan nasu gabaki daya inayah ta zama wani iri tafiyar da suka kwasa sosai ya motsa mata da ciwon cikinta,still maganin dasuka amsa a can chemist taawure ta kara bata hardai ta samu tay sallolinta yauma ko abincin arzkii bataci ba ta kama bacci, can cikin dare kwasam ta farka da amai, da zazzabi me tsanani kumburi da taurin cikin nata kuwa sai karuwa dayayi, duk sanda tay numfashi ko tari zafin datakeji acikinta ya tsananta sosai da sosai.
kafin kace wani abu inayah tafara ficewa ahayyacinta tun abu na wasa wasa har maganin chemist ya ƙare amma basuga alaman sauƙi ba gashi sunriga sunbar tudu bare ma su je asibiti.
ganin basuda mafita da safe taawure tafito tasame su awaje akan tabarma, ayaanah tana fifita ma inayah dake kwance riƙe da cikinta cikin azaban ciwo da murkususu wanda ruwama ynxu da kyar take iya shansa sai nishi kawai take da juye juye.
cikin ran taawure cike da fargaban yuwar dawowar mijinta any moment saidai duba da jikin inayah yasa kawai ta runtse ido ta saɓi mayafinta da karfin zuciya tana fitowa tadube yaranta dukansu abun tausayi muryanta kasa kasa ahnkli tace shannu innari dakyar inayan ta dan dago ta kalleta
..zuciyarta sosai yay rauni sosai dataga inaya bata ko iya amsa magana saidai ta dan dago idanu, cikin jan ajiyan zuciya tace "ayaana ki kula da yar uwarki ni zan gudu gudu inje tudu na sake karbo maganin ciwon innari wajen likitan nan na tudu tunda jikintan yaƙi yin sauki..
ayanah ta share guntun hawayenta ahnkli tace "toh saikin dawo ummah addana batako iya magana kiyi sauri jikin nata yana kara zafi.
ko gama amsata taawure batay ba sukaji kakkausar sallama akansu wanda saida yasaka zuciyar taàwure ya tsinke sabida jiyo muryan mijinta juma datayi, ayanaah kuwa tuni taji hanjin cikinta yana kaɗawa sabida balain tsoronsa data keji, inayahr ce kadai bata bude idanunta ba dan banda nishi bata iyayin komi..
fuskarsa ba a sake ba ya shigo cikin gidan ganinsu cirko cirko a tsakar gida ga innari akwance akasa akan tabarama kamar ruwa ya kwasota yasaka ya mugun hade ransa kamar ma ɓe taba murmushi a duniyar nan ba..
taàwure ta kalleshi da karyayyen zuciya ganin ya zuba musu idanu mecike da tuhuma sai tay sauri ta taho gabansa domin ta amshi jakar dake hannunsa wanda tunkan ta karaso ya tsime tare da daka mata tsawa yanamai cewa "Ke da Allah. Dakata min awajen. ya dada haɗerai yanamai kare musu kallo"wai meke faruwa ne na ganku haka a tsakar gida cirko cirko? kuma ina kike nufin zakije da mayafi ajikin ki batare da izini na ba. kafin ta bude baki cikin masifa yace "ikon Allah wato abunda ake yawan gayamin akanki gaskiyane, dake da yaranki duka baku da tarbiya daga nasaka kafa nabar garin nan dandalin bushasharku kawai kuke buɗewa kina yawo kamar wacce bata da aure su kuma kmr wanda basuda uba, duk kinbi kina zubar min da mutuncina a garin nan ana gulma na akanki keda ƴaƴanki, toh wallh taawure nafi karfinki, karyanku yakare tunda na dawo gidana kuma da cikinki na dawo, zan nuna muku cewa ni juma, tsayyayen namiji nake agidana kowa cikinku sai ya gane kurensa agidan nan.. mtss yaja tsaki daga fadin hakan ya kama hanya yawuce turakarsa fuuuu ransa a mugun zafafe.
kallon bayansa taawure ta dingayi cikin rasa nacewa
jikinta a matukar sanyaye ta dawo jikin yaranta da suke zaune akan tabarma itama tazauna tay wani irin tagumi shiru ne ya ratsa wajen banda nishi nishin inayah babu abunda ke wulgawa, can cikin tunani taawure ta miƙa hannu tajawo sauran ruwan maganin zazzabi data jikashi acikin kwarya ganyen rai ɗore ne aciki tana kokarin bawa inayar abaki sai kuma taji jikin inayar yay mugun zafi harma fiye da kima.
hankali atashe ta tallabota ayayinda taji jikin inayar yafara mild convulsing kusan koinanta yana rawan ɗari, zanin inayar atake yadan subuce gefen cikinta na dama inda ya kumburo sai yay kamr wani babban kurji ne acikin nata.
a mugun tsorace taawure ta kai hannu kan kumburi zata taɓa taji meyene tana tabawa kawai inayah tay wani irin gigitacen ihuuu saida dukan su suka rude sukaja baya suna salati me ƙarfi
rawanin juma a hannu ya fito daga turakarsa a mugun razane shima kusan arude yana cewa wacce yar kafurar ce take mana ihu acikin gidan nan waye..waye waye me ihun nan...yan iska kawai marasa tarbiya da imani mutum ya dawo gidansa bazai huta ba kenan wata shegiyar yarinyace tay ihun nan inci ubanta.
da gudu ayanaah taje ta kara rungumar inayah tareda fashewa da kuka me tsananin rauni wanda kukan ayaanahn ne ya dan katseshi,taawure tay sauri tarufe kumburin cikin inayan da zani dan karma juman ya gani yayi musu wani fassara na daban dan talura kamar ransa a mugun baçe ya dawo daga boda.
#surayyahms
idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata
*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*
*WATTAPAD @SURAYYAHMS*
*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*
#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025
[27/10, 19:43] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: _ABUNDA KE ƁOYE...._
_Love And scandal💕_
*_Arewabooks@surayyahms_*
⏯️8️⃣
juma yana gyara tsayuwarsa yace...
"Dabbobi ne agidan ina tambayarku kuna min shiru?
araunace taawure tace megida dama jikin innari ne babu dadi tunda muka dawo daga tudu yau kwanan mu uku kenan tana zazzabi..
wani irin yatsina fuska yayi cikin katseta da zafin kai yace "toh sai kuma me? akanta aka fara zazzabi ne?yo akan dan wnn ciwon zazzabin shine har zata daka min irin wann ihun jahilcin acikin gidana yo uban waye yasaka mata ciwon inba iskanci da sakacinku ba, nide wallah kar a sake min ihu agidana. ku karata tacan da abun kunyar ku ai da ɗa namiji kika haifa min da bazai zamo rago har haka ba. sai a zauna ana ihu akan zazzabi? _Ko waata nyiɗi, ɗum yoɓa wuro.”_
yana gama maganar sa still yaja musu tsaki a mugun zafafe ya kuma wucewa ciki lokcin kuka inayah da anayahn sukeyi rungume da junansu abun tausayi...
ayaanah bata taɓa ganin addanta cikin wann yanayin raunin ba sai gabaki daya zuciyanta itama ya fara mata ciwo amma take kkrin daurewa sosai danso take ta koya ma kanta jarumta..
tun bayan faruwar wnn hatsaniyar taawure ta kasa xama dan ko kaɗan bata iya ganin yaranta acikin rauni suna kuka gani take dolenta kawai ta neman musu mafita, acike da jarumta ta miƙe tabi bayan juma cikin turakarsa ta samu har ya gama warware jakansa yaciro kayansa mararsa nauyi daya saba sakawa inzai dan fita majilisansu na dattawa a kofar sarkin buzaye inda kowani gida ake kawo kwanon abinci aci atare. sanin cewa tunda aka haifo ayaanah aka dena cin abincinsa a majalisa ke dada bata mai rai, sabida al'adar kauyen ne inhar duk gidanka mata ne toh andena cin kwaryan gidanka kenan har sai ka haifi namiji ko da guda daya ne. ya dawo daga boda da tsananin fushin sanin kayan abincinsa bai