ABUNDA KE BOYE

Author :  NONE Category :  African Stories & Novels

Chapter   74 / 88

219K to 222K   out of 262.2K words

abunda ya faru kenan da sauki
dan wallah hanklina ya bala'in tashi da irin magngnu da ake kanyi akansa acikin gida.

yace "karki damu in few hours zamuje gidan in sha Allah babu komi sai khairan..


daga haka suka zauna awajen har sai kusan 12:30am to 1pm ma rana kafin suka sake ibaad daga interogation room ya fito ya samesu

bappa zaidu da ammi karama suka hau tambayarsa me akace masa bai boye musu komi ba ya gaya musu

after a while bayan sunyi maganan sai hukuma sukazo sukace zasu rikeshi detention sai jikin zainab yay improving out of danger zuwa yamma azo a daukesa

...bappa zaidu ya karkada kai dan tuni ya gane cewa prof ne kawai yake bada oder a case din nan bawai zunzurutun aikin gaskiya akeso ayi ba

dake shima ya kira mutanensa hakanan yasaka adinga saka masa ido, wanda yasa baiwani damu ba yasako ammi karama agaba suka dawo gida

sun iso gidan arnd 3 na yamma tun a mota yake bawa fatima hakuri saidai tunda hajiya ta gansu bataga ibaad ba tafara sabon hauka tana tuhumar bappa zaidu me ake ciki ita kuma ammi karama batace komi ta wuce dakin ta tanata hawaye sosai.

tun a wann lokcin bappa zaidu yafara ma hajiya bayanin abunda ya faru jiyan amma ta nuna masa kamr bata ma gane meyake fada ba, kowani furuci dake fita a bakinsa abaibai take jinshi, gani take bin nayan rayyanu kawai yakey ,zaa kashe mata jikarta zainab arifah, za'a kuma saka danta zayyanu acikin baqin ciki da kunci...

abu kadan saita cemai aibkao zaidu dake kai kana da zuka zukan yaranka ai dolene abun bazai maka zafi ba, mutuwa fa ba wasa ba..inda kai adali ne da kamata yay ma kace ma hukuma akai rayyanu prisona
inyaso yaje can yay muguntr sa, acan yaro shaidani, wallah wallah ubansa baida wann baqin zuciya, mustapa ba haka yake ba dan yafi kankara ma sanyi gashi da hakuri amma kuma yaje yahaihu mugun yaro
aikodan tausayin rai ya kamata rayyanu ya amshe yarinyar nan amma dake kuna goya masa baya toh gashi nan abunda ya jawo..

bappa zaidu dayaga ba fahimtarsa zatay ba hudu na yi ya mike ya wuce masallaci daga nan ya fita ya koma station din dan yajira time na releasing ibaad yay ya dawo dashi gida.


iyaka su maheer ne kawai suke kiransa uncle moh ko sau daya bai kira ba duk dama yaga miss calls din bappa zaidun na tun safe.

shida da anty safeera dakyar aka barsu suka shiga wajen zainab arifah suka duba ta saidai haryanxu taki magana da kowa sai kuka da yamma liss iyayen suka matsa akan zasu wuce da yarsu gida dan abata cikakken kulawa acan

baisani ba already zainab ta riga ta hada plan dinta da nala kafin tay aika aika ta tura ma nala text cewa tazo duk asbitin daka kwantar da ita ta aiwatar mata wani plan....

a fuska zakaga kamr she is too traumarized to even speak, amma tuni nala tazo ta zaga tabiya likita makudan kudi akay abunda zaayi aka faking result dan ta saka iyayenta su rasa duk wani makama.

ana gama processing sallamarsu doctor ya kawo ma iyayen tarin bayani game da Somatic Complaints kamr body weakness + headaches + fainting yace musu yanxu fa inhar zainab bata samu cikar burinta nan kusa ba she wil be attacked by frequent body weakness, headaches har da kuma sumewa on a regular basis.. snn zai iya haduwa mata da Adjustment Disorder me tattare da intensed Emotional Collapse where she will become too sad too withdrawn, too fragile.

in aka kira sunan ibaad zatana firgita, zataki cin abinci, zatana yawan kuka zatana tsaya cak tana kallon bango. nd with time zata samu full emotional damage wanda inbasu wasa ba sai ankaita therapy na watanni shida awani waje.

bakaramin tashi hanklin iyayen zainab arofah yay ba, dan karfin gwiwarsu na batun tsayawa kyam akan batun su na hana auren tun anan ya fara gushewa musmn ma hajiya hamida datake ganin rayuwar yarta ya kare kenan inhar suka kyaleta ta samu cikakken tabu hankli

zainab arifah is busy pretending nd watching them danma ta dada tsoratasu suna kaita gida ta dinga kuka tana kwalla kiran sunan ibaad tana jan zuciya tana suma kamr ba acikin hayyacinta sai can kuma kaga ta farfado gabaki daya sai taki musu magana taki kuma taci abinci..


komi a idonsa anty safeera akayi ga ammi babba na kiransu akai akai ana bata labari haka zata kara maggi da gishiri taje gaban hajiya mairo tazauna ta zazzageshi duk saida ta tayar ma tsohowa da ciwon hawan jininta, ranar karshenta itama ruwan drip aka saka mata sai Allah ya isa take jama rayyanu duk dama tasan abunda take furtawa yana ma ammi karama zafi sosai amma ji take kamar ai ɗa baifi ɗa ba

babban damuwarta shine rayyanu zai mata asarar jikarta snn zai jawo gaba ya tsananta atsakaninsu da danta zayyanu dan tasan bazai taba yafewa ba


wajajen 5:30 bappa zaidu ya gama processing release na ibaad, mutanen prof din har wani cewa suke in wani abu ya sake tashi zasu kara nemansa

bappa zaidu yaja tsaki ya sako ibaad agaba bai sake sunje family house tunda ya gama lura da take taken hajiya mairo ba gaskiya take da niyyar bi damuwarta na kasa ya dauki laifi dan kar na sama yay fushi

suna isa gida ibaad yay wankansa yazo masjid yajasu sallah banda da maheer daya kirasa bai sake wani magana da kowa ba after ishai bayan sunci abnci bappa zaidu baice masa komi ba yace masa kawai yaje yay bacci gobe da safen duk zasuje family house a zauna ayi magana

cikin wann daren fake draman da zainab arifah tama iyayenta bana kadan ba, suna bada baya zata sha drugs tay ta wasu abubuwa sukuma hanklinsu duk sai ya hargitsa ya tashi...

ranar haka aka zauna cirko cirko basuyi bacci ba washe gari sassafe prof yagama tunaninsa ya zaunar da matarsa yace mata bazai iya rasa rayuwar yarsa kwalli daya akan wann case din ba tunda haka arifah din ta zaba so be it...amma kuma saiyaje shi can wajen mahaifiyarsa sun tattaunawa ya dawo snn zaizo ya saka ma yuwar auren nasu tsauraran dokoki wanda dolene abi, itama zainab arifah din dole tabi. kusan babu yadda hajiya hamida ta iya itama haka ta goya masa baya dan kawai su ceto rayuwr yarsu....

da sassafen ya shirya cikin manyan kaya ya fito banda tea dayasa acikinsa baisha komi ba shidakansa yadauki babban motarsa as early as 7am da sassafen sai gashi nan a family house fuskarnn tashi a matukar daure kamar wani mala'ikal daukar rai.

yana kammala parking tun awaje yay gamo da uncle moh da jallabiya ajikinsa kowani gaisawar arziki basuyi ba suka karasa ciki, cikin sashen hajiya mairo direct yay dashi wanda tunda tagansa tafara koke koke tana maganganu akan abunda ya faru, mrzamaza tasaka a kira mata zaidu da ahalinsa duka suzo gida ayi magana anan atare...

maheer is already on his way dan da sassafen yabi jirgi zai taho, mujaheed ma tun jiyan yafara neman exit dan abarsa yaxo amma abun baiyu ba

mujaheed ya gama waya da bappa zaidun kenan an taru a dinning za'a breakfast saiga kirar ammi karama wanda da gangan hjya mairo tace lallai ita zata kira musu zaidu ai inyaga kirarta ne zai dauka da wuri kuma yazo akan lkci....

tana kuwa kira dake wayarna hannunsa ya dauka cikin nitsuwa da sanyin murya yace "fatima antashi lafia? da wani irin sauri ammi babba ta aje cupin shayi ta zuba masa wani dan uban ido mai tafe da mugun harara

after uttering few words yace toh bakomi muna zuwa snn ya katse wayarsa ya aje akan table yay banza da batun ya cigaba da breakfast dinsa hankli kwance dan baiga abunda zai sakashi yaqi cin abincinsa akan zuwan prof na

tajira tajira taji ya musu bayani sai shiru kai can dataji abun ya cicciyota sai tace 'yaa zaidu gidan lafya daiko ina dai ba jikin hajya bane ya kara tashi?? a dan dakile yace "a'a kudai kammala breakfast dinku ahankli sai muje muji..

suna gamawa kuwa kowa ya tashi sai ya kalle ibaad yace 'ibaad kai kazo kasameni a dakina yanxu zai aikeka office dina inyaso inka dawo saika wuce can ka samemu

cikin girmamawa ibaad ya amsashi, suna shiga dakin ya bashi aiki da akalla yasan zai dauke sa 2-3 hrs kafin yagama dan kwata kwata baijin yau zai iya zuba ido aje can gidan asako ibaad agaba a dora masa laifin komi snn agaya masa bakaken magana dan yana tabbacin cewa hajy mairo intana gaban danta zayyanu ba lallaine tabi bayan gaskiya ba....

he prefer to face them alone than ya barsu su taru suci ma ibaad mutunci da sassafen nan.


ibaad ne ya fara ficewa da aikan kafin nan suma suka shirya suka fito shida matarsa da yarsu sultana suka wuce family house....

coment nd share ur tots

#idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*

*WATTAPAD @SURAYYAHMS*


*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*


#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025
[13/12, 09:54] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫
arewabooks@surayyahm.


⏯️4️⃣5️⃣

Sai Wajajen karfe 8am saura kafin nan ahalin bappa zaidu suka samo isowa, wani irin shiru gidan ya dauka kamar babu mutane aciki in banda safiya da ayaanah da sultana banga wani mahalukin da baya falon hajiya mairo yau ba,
sanadiyar rashin isowar Bappa zaidu agaggauce, yasaka hjya ta umarce ammi karama akan tay musu breakfast while they wait, within few mins ammi karama ta gama aka kawo dadin qamshin wainar kwai, da su pancakes, kunun madara, da irish pritatas duk yabi yacika hancin prof yanata basarwa da kyar hajiya mairo talallabe sa yadauki abincin ya taɓa kadan dan da wani irin gingimammen rashin mutunci da girman kai tareda mnyance ya taho yana kallon kowa dan iska awajen.

banda ma Hajiya data masa tarban nuna masa tausayi da baiyi tsammani ba da hala ko xaman jiran zaidu bazai iyayi ba.

sun fara ci kenan bada jimawa ba saiganan sallamarsu bappa zaidu idon kowa na bakin kofa ana tsammanin ganin ibaad atare da su sai shiru har suka karasa shigowa aka fara gaishe gaishe nan tay general nasiha game da abunda ya faru da furuci masu cike da nuna son kai da kuma bangaranci tanakan bayyana musu prof a matsayin wanda aka zalunta aka tashi kashe masa yarsa kwalli daya

babu wanda ya tanka har tagama nasiharta snn takore duka matayen gidan aka barta daga ita sai yaranta su ukun a kewaye da ita

wajen atake ya dauka da shiru bada jimawa hajiya mairo tafara magana cikin mita

"kai kuma zaidu ya naga bakazo da uban gayyan rayyanu ba kodan tsabar raini yasa yaga bazai iya zuwa amsa kirana ba?

ba yabo ba fallasa bappa zaidu yace ibaad ai baida raini hajya, zaizo..nine na aikesa!

cikin karkada kai tace kullum acikin shan bakin sa kake toh wallah yau kwata kwata bana son raina ya baci da ku dan wann abu daya faru da yar jikata zainabu sam baiyi min dadin ji ba ace kuna yan uwan jini aima bai kamata azo ana samun hali irinna mugaye marasa tausayi acikinku ba.

kai kuma zayyanu nasan an riga an cuceka amma hakuri zakayi kasan ance zaka haifi da ne baka haifi halinsa ba, aikai kasan waye babban yayan naku marigayi mustapa, mutunin kirki ne sam baida hayaniya, yo aiko uwar rayyanun ma ba haka take ba ni sam bansan a ina yaje ya samu nashi halin ba.

Da wani irin izza prof yace "A ina kuwa zai samu bayan irin tarbiyan da ya taso dashi ajikinsa kenan mama, ni ba nazo nan bane dan in tsaya jin wani hakuri. ke kanki kinsan anjima anaso aga bayana da ba'a gani ba shine aka turo min wani shaidanin yaro yake son ya ruguza rayuwar yata toh wallah bazaiyu ba.

cikin katsesu bappa zaidu yace hajiya ban fahimceku ba wai maganan waye akeyi ne haka?

baki bude ta kallesa tace waye kuma inba rayyanu ba, yanxu kai zaidu abunda yayi jiya da rayuwar yarinyar nan yay mata adalci kenan? aikamata yay ace ka tasosa agaba yaxo ya tsuguna anan agabanmu ya bawa zayyanu hakuri akan tashi kashesa masa yarsa kwalli daya daya tashi yi, dan tsabar daurin gindi ai aikansa kayi kenan shi bazai nemi afuwar kawunsa ba ko??

bappa zaidu yace "aa hajya, yarsa ce dai ta tashi kashe kanta dakanta, ina kuma ruwan ibaad aciki?..snn Abunda ya faru jiya fa ya shafe kowa, bangane kina neman ki dora laifin a bangare daya ba in har abunda kika tara mu akai kenan banga amfanin zuwa na nan ba, dan inhar baza'a yi magana cikin gaskiya ba babu amfanin taro mu anan

da wani irin izza prof yace "wani gaskiya?? yanxu kai zaidu har zaka iya budan baki kay wani magana after all everything dat happened was ur fault, yes ..yaron nan a hannunka ya taso a lalace he is a liar and a manipulator bai ayyana komi ma rayuwarsa ba, kuma na jima da gane take takenka, kaine kake zugashi yana aikata min duk wani abunda yaga dama agidana toh wallah mama kigaya masa zan dauki mummunan mataki akansu dukansu.

kafin ya karasa rufe baki bappa zaidu yace ahhh ahh ahh mataki kam ai akan yarka zaka fara daukawa kafin kayi zciyat juyowa kan ɗan wani, kana magana ne kamar kai kaɗai abun ya shafa, snn Ka manta cewa muma muna da mutunci da xuciyar da kuma son yayan. Ba zaka zo ka yiwa kowa kallon me laifi ba saboda matsalarka da yarka daka kasa magance shi.


da bacin rai hajiya tace kaiii zaidu wallah banason shashanci wai meye haka kuke fada wa junanku kai da zayyanu???ashe bazaku tsaya ku fahimce junan a sulhunta maganan nan kamr na masu hankli ba


bappa yace In dai za a raba tsakanin tarbiya na gaskiya, to mu a nan muna da hujja, snn Kada kowa ya zo ya juyar da laifi ya ɗora shi kan bangare daya..

Da bacin rai prof yace mama ban yarda a yanke wa Zainab Arifah wani hukunci saboda kuskuren wani ba sabida ita akekan cutarwa, dagangan akayi ma yata haka dan anriga an tsaneni, kuma inda jiya ta mutu da kowa sai ya dandana kuɗansa agidan nan dan wallah bazan yafe muku ba

cikin jan tsaki bappa zaidu yace "inda ta mutu da babu abunda ka isa kayi saidai ace yarka ta kashe kanta abanza kuma kasan wuta zataje aiko..

da wani irin hargagi prof ya juyo zai amsa maganan

cikin katsesu uncle moh yace yaa zaidu, dan Allah kuyi hakuri wannan maganan fa mai sauki ce, wanda yay kuskurei a fito fili kawai abashi duka rashin gaskiyarsa, ita zainab macece mai rauni koda dan halacci ba ai akwai yan uwanta ka. we all know yaa zayyan dakyar ya samu haihuwar nan kuma yarsa kenan kwalli daya bazafa mu cigaba da rufa rufa muna kallo ana wasa da rayuwarta haba yaa zaidu ayi magana cikin adalci mana.

da zafin nama hajiya tace yawwa muhammadu gaya masa gaskiya dai yaji dan naga alama babu Allah acikin zuciyar zaidu, inba haka ba kiri kiri kana kallo zaa cuce rayuwar dan uwanka zayyanu wanda kuka zauna acikin tare amma ka rufe idonka kace sam ba haka ba

bappa zaidu yace hajiya inada tambaya, shin yaron nan menene yayi muku guda daya? inhar zaku iya gayamin laifinsa da kuskurensa direct wallh zan amsa

kuka hajiya ta fashe dashi tace aww ynxu kai zaidu duk anan bakaga ga laifin rayyanun ba shifa ya jawo zainab ta tashi zata kashe kanta haba zaidu.

bappa zaidu ya kara hade rai yace "okay shi kenan yaje har gidansun yace mata ta kashe kanta ko?toh inba haka ba ya zaku taru kuna blaming dinsa shikadai akan abinda yarinya taga damar aikatawa kanta ai ita tafimu sanin ita daya ubanta ya haifa da batay la'akari da hakan ba duk bai muku ciwo ba???saishi ne da baida gata agidan nan ake so ace komi lefinsa ne bayan yariga ya gaya mata alaqa bazai yi tsakaninsu ba, mama shine me duka laifin da har za'a turo hukuma su kamashi a kulleshi??? nifa bawai inace miki ibaad baiya kuskure ba, ko ranar da abun ya faru ainay masa fada sosai sabida zainab ai ya mace ce tana da rauni, damuwata yadda kuke kkrin kuce lallai shine yasakata ta aikata wann abun wakanta gaskiya babu gaskiya ko adalci aciki, he is also a victim too, ai ɗa baifi ɗa ba..inkina jin zafi akan rayuwar zainab arifah shima ibaad din ai jikanki ne meyasa bazakiy la'akari da halin da hakan zai jefashi aciki ba wai shin ana soyayya dole ne..ynxu saiki gaya min menene wanda ya kamata yay mata tun dacan wanda baiyi b..soyayya ne yace bayayi
..kuma ya gaya mata toh menene..

da wani irin bacin rai prof ya miƙe har jikinsa na bari zai magana hajiya mairo ta daga musu hannu da muryan kuka da fushi tace "kai Ya isheku haka duk ku nitsu kafin naci muku mutunci karnasake jin bakin kowa anan dan naga alama maganan bazai kare ba, yanxu menene mafita guda daya? zayyanu kaji abunda xaidu ya fada kai meye ba'asinka...

komawa yay wajen zamansa ya zauna yana wani irin hura hanci da wani irin girman kai yafara gaya mata abunda likitansu ya fada akan lafyar kwalwlawar zainab wanda tun yana tsaka da bayanin hajiya ta rafka salati ta fashe da wani irin sabon kuka.

wayyoo Allah ni mairo, zainab yanxu haka rayuwarki ya dawo sai kace me taɓon hankli? innalillh wa inna ilaihi rajiun au dama abun har yakai haka ne zayyanu, Allah ya isa miki zainabu! toh wallah ko anaso ko ba aso dole ne mu dauki mataki, muhammadu kaine shaidata anan kace ma yayunka maza su sasanta kansu a tsaya a kan magana daya rayyanu ya sauke girman kai ayi auren nan kodan yarinyr nan ta samu lafiya bayan haka banason na karajin wani hayaniya..

bappa zaidu yay shiru ya zuba musu ido yana dai jiransu sugama

rimi rimi prof ya dinga kawo kananan magana yana hura hanci da izza yana cewa shima sharawar daya yanke da matarsa kenan duk dama yasan yafi karfin ya bada yarsa ahaka saidan samun lafyarta sabida yariga yasan cutarsa kawai xa'a yi, ana baqin ciki da daukakar da Allah ya masa anyi asiri an juya ma yarsa kwakwala da ciwon so dan kawai aga bayansa, kuma shi dukiyarsa ba'a isa aci abanza

74 / 88