Author : NONE Category : African Stories & Novels
yadan samu nitsuwa taciki. shirun dayay yasa atake jikinta ya bata, waje ta nema ta zauna kusa dashi akasan da sanyin murya tace rayyan pls talk to mummy, kunyi magana da bappanka ne ko?
yana dago kansa taga idanunsa yay jaaa zai magana cikin katsesa tace "honey, Its for the best" Dan Allah kayi haquri none of us wanted this for u. musmn ma kawunka wallh jiya ya bani tausayi dan inda anbita nashi da ya gwammaci hajiya mairo ta tsine masa akan daya maka wann auren..pls look at it as ur destiny...kay hakuri...
cikin girgixa kai hawayensa tsilli daya ya sauko murynsa na rawa yace "Ammi wallah bana kaunarta, kuma bappa bai taɓa bani umarni akan wani abunda banaso ba sai wann karon, iyakan zamana da shi a gidansa he always defended me har sama da farin cikin matarsa, ni ynxu bansan me zance masa dan banason saɓawa umarninsa kuma harga Allah banason na aure zainab sabida bana kaunarta kwata kwata banajin zan iya kallonta a amatsyin matata..
da tausayinsa a idonta tace "nasani..dama kuma ba auren soyayya muke nema agareka ba rayyan...inada yaqinin cewa zainab wata bangare na jarabawa da kuma qaddarar kace, hala wani gwaji ne da Allah ya aiko maka dan ya jarabce rayuwarka snn karkamanta tun tana karama sosai ta fara wann abun. gashi har yanxu ta girma dashi yaxo yanaso yay sanadiyar rayuwarta, toh da ace ka bijire ka wargaza zumunci akan rashin haquri kuma zaonab tazo ta rasa ranta sanadiyarka gara ace kay musu biyayya kay hakuri ya zamo kaine aka zalunta bakaine ka zalunce kowa ba..if ure patient Nothing evil will ever happen to u addua ta kullum yana tare da kai, nide hakuri nake dada baka dan Allah ka rufa mana asiri yazamo nan gaba baza'a a kalleka ace kaine kayi sanadiyar tarwatswer zumunci da kimar gidan al-mansur gabaki daya ba. pls dont think as her a matsayin zainab da baka kauna, just look at her as a fragile life dat needs ur company to be able to dream nd breath again, nd i know my son wudnt be the reason for sumones grieve, or life lost..u wont be the reason to tear this family apart, kaduba girman abunda zakayi a idon Allah, this is a huge secrifice for the entire family nasan mahaifinka zai yi alfahari dakai..pls keep ur desires aside rayyan, nd do this for sake of Allah... besides babu wanda zai hanaka auren wacce kakeso anan gaba
...kawai kay hkuri ka ansa wa kawunka, shima ya samu nitsuwa kaima ka samu nitsuwa gidan nan duka a samu kwanciyar hankali...inda mahaifinka na raye you know he will prefer to keep the peace too, kuma shima da abun da zai roka awajenka kenan.. duk wani walwala da farinciki da zumuncin gidan nan yanxu haka yana wuyanka ne, be the bigger person pls nd think abt it..amma koma miyene nidai dan Allah karkace ma kawunka a'a zaka kunyatar dashi, just let it go..nd let god see u throu. inma taruwa akayi agidan nan duka aka cutar da kai kabari kawai Allah zai saka maka. kuma in sha Allah zaka cinye wann jarabawar
hawayen dayake zuba a idonsa yasaka hannunsa yashare ahnkli muryansa a sanyaye yace toh shikenan ammi tunda kema hakan kike gani bakomi zanje na sameshi in sanar dashi na amince zan aure zainab din..
kusan dede nan kalmomin nasa suka dira acikin kunnen ayaanah datazo kofar dakin da sauri da niyyar zata gaisher da ammi dan yau exams na IRS zasuyi karfe 9am dai dai tanaso ne taje tafara shiri dan tuni tagama duk wani bitan karatu da zatayi.
tana dada jin muryansa aciki ta tsaya cakkkk dan har wani yaam yaam taji kunnuwanta na neman toshewa tafara jin jiri jiri ne ko faduwar gaba ne duk ta rasa me takeji, she instantly frozed har ta gama jin conversation dinsun na karshen yadda yake tabbatar ma mum dinsa zai hakura kawai ayi aure. ita iyaka nan kawai taji..yau yaa ibaad din nata ne dakansa yake cewa zai aure anty zainab arifah??
batasan how many minutes tay a daskare ba ita bata bude kofar ta shigo ba ita bata iya jan jikinta daga shock in datake ciki ta koma room inta ba, jim kadan sai taji inuwar mutum agabanta,
kirjinta na bugawa da balain karfi ta daga idanunta sama taga shine har ya fito, suna hade ido dashi hawayen da batasan daga ina suka taho ba suka fara sauka a idon ta jikin ta na rawa rawa ta juya da uban gudu zata koma daki yay saurin biyota yana furta "ayaanah, ayaanah..
...amma inaa bata tsaya ba tana shigewa dakin idonta a rufe kamar mai aljanu tanufi bayan gidan tay sauri ta kulle kanta aciki tareda rusunawa akasa da wani irin mtsanancin kuka me daga hankali sosai, hanklinsa a mugun tashe ya shigo dakin yana kirar sunanta safiya tay marmaza ta sauka akan gado ta fice basu waje.
kirjinsa kamar zai amon wuta ya tarwatse ya tsaya daga bakin bayin yana jin sautin kukanta yana cewa "ayanaah pls come out..is not what u think..dan Allah ki fito..kinji?? kukan kawai takeyi jikinta na rawa rawa dan ita kanta bata sanma me takeji a dukkan ilahirin jikinta ba, ji take kamar she just cant take it..gashi Allah yadora mata wani irin matsanancin kishinsa musmn ma akan zainab arifahn...
rokon duniyan nan yay mata ta fito amma taki fitowa har kukan ya lafa, muryanta na fita ahankli cikin sheshhka tace masa kawai ya tafi ita bata so tay magana dashi ne yanxu sabida batajin dadi. tun 7.30am yana tsaye har saida 8am ya wuce ayaana bata fito ba, dakyar ya hakura ya fita agidan dan kawai ta samu ta fito ta shirya taje exams dinta.
fadin tashin hanklin daya shiga wann rana bazai kiyastu ba musm da yasan ayaanah taji komi daga bakinsa nd he knows bazai taba samun nitsuwa aransa ba kuma yanxu..
tsabar kansa ya dau zafi yana komawa gida saida ya fada wanka da ruwan sanyi mai sanyi sosai, haka ya bar ruwan showern ya zuba akansa sosai, so that his muscles will calm down and relax, wnn ne karo na farko da yarasa yadda zaiyi da rayuwarsa everthing bcome so intense musmn da yaga reaction din ayaanah dan yasan yarinya kuma zaisha wahala kafin ta fahimce shi.
cikin danne abun aransa ya shirya ya wuce harkokin gabansa he tot abt it all day, yana yi yana gwada lambar ayanah amma har yanxu ji yake akashe, da yamma liss daya dawo bayan sallahn isha'i nan ya gaya ma bappa zaidu cewa "ya amince zai masa biyayya kawai dan haka yabar masa komi ahannunsa...bappa zaidu was very proud of him daya cika dan halak ya masa wann halaccin, nd for the immense secrifice nd respect for the family, duk dama baiji wani dadi ba dan haka nasiha yakara masa, yace masa wann abun jarabawar rayuwarsa ce, Hala haka Allah ya qaddara zai hadashi da wani abunda baya kauna dan yaga iya level din imaninsa da hakurinsa da juriyarsa da kuma biyayynsa ga dokokin Allah,...yace masa bama su kawai yay biyayya ba ya dinga tuna Allahn daya jarabce shi shima zaiy alfahari dashi in yay hakuri, snn zai samu ladan hada kan ahalin sa, da ladan yin hakuri da wnn mummunan qaddara, snn kar dan baya son zainab aransa yay amfani da wnn daman ko ikonsa na mijinta ya cutar da ita, dan a sanadiyar haka sai Allah ya shigar da ita aljanna shikuma rashin hakuri da rashin sauke haqqin aure akanta sai ya kaisa wuta. haquri ya bashi sosai yace masa duk yadda ake ciki shizai kasance tare dashi bazai taɓa kyalewa a cutar dashi ba, snn kowa cece yazo yace yanaso nan gaba zasuy kkri su aura masa, dan haka yay hakuri karyace komi ynxu har sai anyi aurensan zainab ta samu lafiya zasu san yadda zasuyi.
godiya ibaad yay masa suka bar maganan anan, sai ya shiga motarsa adaren yazo gida..kai tsaye ya wuce sashen amminsa zuwa yay yasamu wai ayaana tana bacci, ammi tace masa ai yau batay ma exams dintan ba a hall din taje ta fadi ta suma aka dawo da ita da zazzafan zazzabi tasha maganin kenan tay bacci..
lahawla wala kuwwata ya rika nanatawa acikin zuciyarsa hanklinsa gabaki daya baya jikinsa he stayed beside her for a while ko zata farka suyi magana ya lallabeta amma bata tashi ba, har sai wajajen 11.30 na dare kafin nan ya hakura ya koma gida.
washe gari ma sassafe haka ya dawo gidan, still ayaanah ta kulle kanta a daki taki sam ta kulashi, she missed 2 of her exams ma wann kwanakin, both IRS nd geogrphy dan wani irin kishi mai balain rufe ido yahanata numfashi ta kasa jin sauki aranta kona minti daya, duk sukabi suka dagula ma ammi karama tunani har tasoma gane cewa dole ne kawai da akwai wani abu special atsakaninsu...
ita bata san cewa ayaana taji cewa zai aure zainab arifah ba, so she cant really conclude cewa rikicin kishi da soyayya ne, shikadai yasan da hakan, arana sai yazo gidan sau hudu sau biyar duba jikin ayaana saitaga ita kuma ayaanan batason tana kulashi, sam taki su kebe suyi magana, taki sam yazo kusa da ita.
wann yanayin suke ciki har na tsawon kwana biyu lamarin auren bai hanashi bacci kamar tsnanin fushin da ayaanah takeyi dashi ba.
daga dayan bangaren kuwa aranar da aka kan shirin sallame zainab arifah da safe around 8:30am bappa zaidu yasha manyan kaya yay kyau ya shigo asibitin kai tsaye dan dama shi bai taɓa zuwa ba. koda security suka ga spitting kamannin da sukey da prof da kuma irin kwarjininsa na babban mutum mai ji da naira wata mayyar sky blue shadda ya saka garensan nan taji aiki me aji, sai maza maza suka bashi hanya, infact har ciki securiry suka rakosa ana masa fadanci har private room din da ake monitoring zainab din aciki...
her life line has increase with 50% chance of recovery saidai haryau bata magana kullum idonta a lumshe da hawaye aciki, prof yadan fita yana waya da lawyer dinsa kenan hajy hamida taji sallama a kofa...
dake ma har muryansu yana dibi sai tay zaton mijinta ne da mamaki ta amsa dan tasan mijinta baya yin sallama in zai shigo waje...
wani irin sanyin qamshin
turare taji me tsada da kuma dadi dayasa ta juyo da sauri suna hade ido da bappa zaidun atake fuskarta ya wani sauya tamiƙe tsaye da raini tana yatsinawa...
muryanta kasa kasa tace 'ohh ashe kai ne..
sama da kasa ya kalleta a dakile bai tsaya sun gaisa ba yace hamida ya mai jiki??
kafin ta amsa taga ya dauke kai ya wuceta wani irin zafi taji akan kirjinta dan tarasa wani irin jiji dakai wann mutumin yake ji dashi mutum ne da bata isa ta zageshi ko ta rainashi ba sbd kwarjininsa kuma da alama taga kamar rashin mutuncinsa da walakncinsa yafi wanda ka kanta yawa.
kai tsaye ya karasa gadon da zainab take ya zuba mata idanunshi for a while kafin yace.."Doter Zainab arifah are u awake? ya jikin naki.
..jin ance doter zainab yasa tay firgit tabude ido da sauri hawayenta na zuba ahnkli tana ganinsa tace"uncle zaid??
dan karamin murmushi yay yace "how are u feeling? ya jikin naki..bata amsa shi ba ta langwane tareda fashe masa da kuka sosai ta motsa kadan ta matso jikinsa tarike masa hannu ta dora kanta akan hannun nasa tana kuka a agajiye...
da muryan kukan tace 'uncle zaid i am sorry dan Allah kar kace banyi hakuri ba...i jst cant take it anymore,.pls help me. amugun makirce take furta hakan da zimman takara cusa masa tausayi dan tasan shine bbn mtsalar yanxu dan taji sarai lkcin da akace shine yahana auren..
she was just crying nd begin him yayi shiru da tausayinta a idanunsa yana shafa mata kai yana sassaita ta
..aka bar hajy hamida tana kumbura fuska kamar zata tashi sama wato ma zainab tana da muryan yin magana shine su bata musu ba take ma wann mutumin
da tsananin bacin rai ta sabule ta fita a dakin ta samu prof a gefe yana waya tana isowa tana huci muryanta kamar zatayi kuka tace alhaj alhaji alhaji.. da sauri ya katse wayar yace "meyene? da bacin rai tace "wancan mugun dan uwankan ne yazo nd u cant believe it zainab is now talking to him...tsabar ta kufula hawayenta na zuba tace "for good 3 days muna nan muna wahala zainab bata mana magana ba sai shi? nikam wallah kazo karya kara juya ma yarinya kanta i am sure he is using magic nd charms on her..
tanakan maganan yaja tsaki da mamaki yace kina nufin zaidun ne yazo nan duba jikin zainab?? kafin ta amsa azafafe yafara kiran security babbansu na zuwa kawak ya daukes da mari yace how dare u let anyone come in here witou my permission? security ya fara bashi hakuri masifa ya ke ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, dakyar hajiya hamida ta janye shi suka koma daki suka samu bappa zaidu har yadaga zainab daga kwance ta zauna ya saka mata pillow ta jingina bayanta dashi
bai mata wani dogon nasiha ba,sama sama kawai ya gaggaya mata makomarta inta koma wajen Allah a matsayin wacce ta kashe kanta snn ya bata hakuri yace mata sunyi magana da ibaad karta damu. intay masa alkwarin zata cire komi aranta ta warke toh shida kansa zai tabbata anyi auren su da ibaad batare da anja lokaci ba, amma sai ta masa alkawari bazata sake yunkurin kashe kanta ba no matter what. .
tunda aka fara case dinnan zainab arifah bataji wani sanyi aranta ba face yau. da sauri ta amince masa, tare da masa alkwari cewa bazata sake yin haka ba.
yace mata shikenan shima zai cika mata alkwarinta zai ma babanta magana azo ayi maganan aure kawai
babu shiri yaji ta fado jikinsa ta rungumesa da karfi tana hawayen murna tace thank you sir thank u uncle zaid ure the best uncle in this world...
cikin haka sai ga su prof din sun bankado kofa sun shigo kamar wasu mayaka, he was dumpfounded dayazo yaga zainab ta rungume bappa zaidu tana kuka tana murna tana masa godiya
hajy hamida taji kamr zata fashe, fushi ya debe prof ya karaso tare da fincike yarsa
ajikin bappa zaidun yana cewa "how dare u show ur face here zaidu?uhhh kazo harnan zaka karasa min ita ko?to wallh ka fita kafin na maka abunda har ka mutu bazaka manta dani ba
wani irin kallo bappa zaidu yamasa yace" kai wai yaushe zaka girma ne kabar wann shirmen...as u can see ur doter is fine nd happy only bcos i came. i am not the monster u think i am zayyanu, kaine dai da kajima kana kokrin raba kanka damu kaine kake da matsala da kowa, zainab is like my doter too, i care abt her happiness.. anyways na gama duba jikintan ni zan wuce sauran bayani zakaji a bakinta
ya kalle zainab yace" doter Allah ya baki lafiya..
da wani irin murmushin jim dadi tace "thank you so much uncle zaid i love u soo much uncle..
bappa zaidu yana fita bakinsu a sake suka juyo kanta ganin tsananin farin ciki dake shimfide akan fusrkta kafin ya budi baki tace"Daddy, he said yes"
in unison suna kallonta kusan adaskare sukace "whaaaaaat?
share hawayenta tay da sauri ta sauko kamr ba itace tay kwana uku bata ko motsi ba.
tana kallonsu duka tace 'uncle zaid yace inhar na masa alkwari bazan kara memeta haka ba zai min auren,..nd i told him i promised..nd he said he will get us married..yace min he has told ibaad alredy nd kaima zakuyi magana kuje ayi maganan ranar auren.
wani irin tsaki hajiya hamida tay a mugun kufule tace nd "is that why ure fucking happy u bloody ingrate???
a daskare prof yake kallon zainab da mamaki yadda yaga tamike zaune garau
yace hamida is enuf karki sake mata tsawa, cant u see how this news has make her happy??yaushe rabonki da kikaga princess dina haka
...ohh my baby come here
..tana karasowa ya rungumeta yace i am so happy ure back okay? zo ko zauna ki gaya min duk abinda yace miki
tana murna tace thanks daddy..i know u love me nd i love u too...but, wil u go and meet him?
yay dariya yace 'sure princess, zanje mana. amma ai sai kin cika masa alkwarinsa
...since we have two more days in this hospital. prove it to me dat u want to get better. take all ur medications, deep sleep, don't cry..alwys talk to u daddy.
murmushi tay yana karasowa jikinta ta kara rungumesa tace 'i will do just that for u daddy.. da tsananin kaunarta aransa yay kissing inta slihgtly akan forehead inta yace dats my girl. snn ya jawota sula zauna tare akan gadon.
wani irin tsaki hajy hamida tajaaa tana masa kallon mahaukaci da sauri ta fita waje tana huci me zafi..
sam sam ranta baiyi dadi da aka gama case din nan da wuri har haka ba, dan koba komi taso ace an hada case dinnan yay zafi, dan prof yayi amfani da powernsa yaci mutuncin familynsa ya tagayyara zaidu da hajiya mairo ita babban burinta kenan taga yaci mutuncin ahalinsa musmn ma uwarsa snn yahada harda tsinannen yaron nan ibaad ya karar masa da rayuwarsa a lkci guda.
she stayed outside for a while, har saida abun ya wuce mata kafin tazo ta samu zainab arifah da babanta, this rush of emotions yasaka har line inta yatashi daga 50- yakai 68% kamar ba ita take kan langwabewa ba, tana ta hira da babanta, ya aji komi aransa yanakan lallabarta dan ta warke sosai..
fannin ayaana kuwa kwana biyun nan gabaki daya takita kula ibaad dan koyazo gidan bata sakewa ta fito inya kira kuma wayarta yawanci zaiji a kashe text message dinsa gabaki daya bata amsa ko guda daya ba. he explained most of the situation to her tru text amma haryau baiga ta sauko ta amsa shi ba, sai dai ta karanta tay ta kuka danji take kamar itama mutuwan kawai zatay in ya aure zainab arifah ba ita ba.
haka rayuwa ya kasance, 4 days later zainab arifah ta dawo cikin hayyacinta prof yana tsare da ita kome tace masa