ABUNDA KE BOYE

Author :  NONE Category :  African Stories & Novels

Chapter   86 / 88

255K to 258K   out of 262.2K words

awajen tailor

to dake garin tattara wasu kayan Ayaanan jiya ammi taga red weding dress din da ibaad ya bata kawai sai ta umarceta aka tasaka shi da bori da kuka ayaana ta karba har ammi ta fita a dakin bata dena kuka ba gashi cikin su sultana babu wanda ya leko ita dayane, safiya kuma tsabar zumudin bikin yayanta already taje beauty shop agari za'a cancada mata kwalliya


gidan yay shiru koda ammi tazo falon hajiya sosai tasha mmkin ganin bappa suna gaisawa har dacan zai fara tuhumarta da fushi sai tay saurin nuna masa wayarta da yadda ta dinga nemansa sosai tun ranar da abun ya fara faruwa..

batai kasa agwiwa itama tahau gaggaya masa ababen da ya faru baya rage masa komi ba ranta a dagule hartana hawaye, wanda hakan ya bala'in shan bambam da karyan da hajya mairo ta gaya masa in favour of her son muhammad,sosai ran bappa zaidu ya hargitsa ya baci har jikinsa yana ɓari ɓari yanajin wani irin balain mamakin son zuciya da rashin hankali irinna dan uwansa muhmmad da kuma rashin girma da hajya ta nuna acan case din gabaki daya

ammi karama tagama share hawayenta kenan saiga su hajyan sun dawo, ammi babba ne agaba da katon hijabi dan kwata kwata 20 min past 10 ne kuma 11:30am sharp zaa je masallaci a dora aure wanda anriga ance tun sassafe ma manyan bakin prof suka fara hallara anata shirin daurin aure.


ganinsu datay cirko cirko ganan fatima na goge hawaye yasa taja tsaki ahnkli tabar musu falon tawuce sama domin duba uwargida safeera

tun data barsu a falon case kawai akeyi tsakanin bappa zaidu da hajya akan batun auren ayaana, wanda sai yau ammi karama ta fitar da abunda yake ranta ta gaya ma hajiya cewa tana nuna ma ayaana warayya da rashin yarda da kuma zargi snn bata tantance magana inda akan ayaanah ne kawai daukawa takeyi.. suka fara jayayya kowa na hawaye bappa zaidu har yagaji da tsoma musu baki ya zuba musu ido kawai yay shiru ya kyalesu dan sugama fitar da abunda ke ransu kafin ya fadi abunda ke tafe dashi



fannin ammi babba kuwa tunda ta shiga ta samu anty safeera babu abinda take sai cika baki da jiji da kai da gatse take cewa anty safeeran da ta nemi taimakonta da wallah yanzu takai ta wajen malami an tarwatsa auren nan,tayita cika baki tana buga kirji ma anty safeera akan cewa tsabr wayonta da kkarinta ne yasaka duk da hjya mairo tana raye haryau fatima bata isa ta shigo gidanta ba...tsabar kuri har tay sabutan baki tahau gaya ma anty safeera duk wani sirrikanta na cewa boka da ya mata aiki akansu tace har ta mutu agidan bappa zaidu baza a mata kishiya ba....

wani baqar maganan yakan cima anty safeera rai, musmn yadda ammi babba take mata kallon yar yarinya da bata san me takeyi ba tukuna, tana mata magana kmr ta maidata abun tausayi har wani shawara take bata akan taje tay gyaran Hq sabida yanxu ne uncle moh zai fara nuna mata asalin halinsa musmn idan ya latsa na budurwa..ta dinga kushe lamarin anty safeera acikin habaici tana gaggaya mata magana kamr irin ita tagama rufe kofa tafi karfin mijinta shiyas aka kasa mata kishiya

anty safeera ta share fake hawayenta daya zuba ita dai batace komi ba tay shru tanajin ammi babba wai hartana mata tallan maganin mata na wajen zinariya



daga can kuma anata hayya hayya a falon hajiya can dataga fatima tafita gaskiya sai tafara musu rantsuwar cewa babu wanda ya isa ya hana yuwar auren nan. ita final decison dinta kenan. tafara ihu tana cewa wai duk an rainata inba haka ba ai rayyanu da safeera bazasu samu livern daga hannu su mata wani abu agidan nan ba.

ganin lokaci na tafy bappa zaisu yay gyaran murya
yace musu su nitsu su saurareshi shi ba wanm maganan bane ma ya kawosa.

bayan sun nitsun ne ya fito da hotonan ya rike a hannunsa, ya kalle hajiya anitse ya fara mata bayanin abunda uncle moh yace na cewa ya fasa auren

wanda tun bappa zaidu bai gama ba ta katsesa da ihu da bori tace sam sam laifin rayyanu ko kuma shine zaidun yaje yace ma muhmdu ya fasa shiru tay har saida tagama borinta snn ya dauki hoton yakai har gabanta yanuna musu da shi bai kalle video din ba ya bawa hajya suka kalla tare da ammi karama,duk jikinsu yahau rawa suka fara salati hajy ta rikito kasa ta kurma ihu tafara cewa ayaana ta tozarta....kusan wann ihun shi ya jawo hanklin ammi babba dan kuwa a falon anty safeera suka zauna suna kuma iyajin ihu akasa musmmn in yayi yawa.

a firgit ta mike da gurmi tace ke safeera bakiji hajya na ihu ba ne...cikin kyabe baki anty safeera tace "ihu kam ai dama ta saba sabida kuncacciya ce mahaukaciya in zakije kije nifa babu inda zanje ina nan, dama mujaheed kawai nake jira yazo in gansa tunda ban gayyace uban kowa awann taqadararen auren nasu ba

ammi babba tace hmm nikam dole najje toh sai na dawo...da sauri wauri ta fita ta nufi sashen hajy mairo har tana tuntuben dan kar ayi gurmi babu ita

tana fita anty safeera ta goge fake tears inta ta kwashe da dariya tace mahaukata...kadan kukaga gani..duk wanda yaci tuwo dani miya yasha..

tana daga zaune awajen jira take taji ance am fasa daurin auren kafin ta tura ma alhaji sauran balance her secret alhaj ba wani babba bane yaro ne dake mata aikin spy tun lkcin datake zargin mijinta ma shi take aikawa shago yana leka mata ayaanah yana kawo mata information...they change his name to alhaj sabida deals inta, bata so konan gaba asiri ya tonu kwata kwata a gane cewa itace ta siya deal da ruthy, tafiso a maida tunanin ga cewa wani namiji ne daban yake kkrin tona ma ayaana asiri dan ya tarwasa auren ta, alhajin ne ya kawo mata duk wani labarin rayuwar ruthy da case inta ma jim haushin ayaana da ruthyn takey abboye da tarihin gang dinsu har da bashin da ruthy take fama dasu, so she made him to do the deal on her behalf, yanxu haka ita kanta ruthy batasan cewa anty safeerah bane behind eveything duk ta dauka wani alhaj ne mai kudi.


daga falon hajya kuwa dakyar aka daga hajiy mairo akasa tana birgima tana ihu tana zagin ayaana, kowa jikinsa sai yay sanyi musn ma ammi karama da abun ya mugun daure mata kai cos ranar ayaana ai da ibaad ta dawo gida yaushe kenan har taje ta hadu da yan iskan gangs haka har tay a rayuwarta irin wnn illar?jin kamr bazata iya gane komi yasa tay shiru taja gefe tana tare hawaye...dakyar hajy mairo ta zauna akan kujera bappa zaidu ya kwace shaidun duka hannun ammi babba
snn aka zazzauna ana zama ya hade rai ya ja musu kunne baison yaji maganan awaje,

snn yace dole ne aji ta bakin ayaana dan haka ammi karama taje ta kirata amma kar wani acikinsu yace zai mata wani abu anan har sai angama mata tambayoyi.

hakan kuwa ya faru ammi karama taje dede ayaana ta gama bude windon ta jefar da kullin kayanta waje tana Allah Allah tajawo kujeran gaban mirror ta haura sama ta dira tafita ta backyard ta zille har ta fara jan kujerar taji ana mata kncking a mugun tsorace ta sake kujera sai taji muryan ammi karama daga kofa a raunace tace "ayaana kizo bappanku yana son ganinki nd pls be fast"..da fargaba ta amsa sabida jin kuka kuka muryan ammi datay she stood still for while, dan tasan is eida a mata adalci ko akara dulmuya ba but anyway ko an daura auren nan tariga ta gudura aranta cewa guduwa kawai zatay tunda yaa ibaad yace zaizo yanemota daga baya bata damu ba.

daukar red bridal veil din tay ta lulluba akanta tay wani irin kyau duk dama ba kwalliyar arziki ammi n ta mata ba but will the jan lalle da gyara da qamshin dake tashi ajikinta bakaramin haskawa tay acikin jan kayan ba.

cikin sanyin sallama ta shigo falon taga daga ammi babba sai ammi karama sai hajy mairo kusan bappa zaidun ne kawai ya amsa mata

mummunan fadi gabanta yay dataga irin walaknattcen kallon da ammi babba ta mata hajy mairo kuma ta wani dauke kai ta watsa gefe tana hawaye tana karkada kafa da tsananin fushi ayanayin jikinta

cikinsu ammi karama ne kawai bata dago kai ba amma hawayene ke zuba a idonta sosai na tausayin ayaana

kirjin ayaana na dukan tara tara ta tsuguna da ladabi ta gaishar da bappa zaidu ya amsa bayabo ba fallasa..

ganin basu da time ya fara mata bayani da tambayoyi tanajin shi tana amsawa ahnkli
she truly cant rembr anything bayan ganin ta datay ta farka a kasa ranar, tana maganan sai yay kamr raina musu hankli kawai takeyi hajya duk ta kara kufuluwa dataga ayaana bata amsa laifin ta ko daya ba.

kai tsaye bappa zaidu ya nuna mata shaidun jikinta da hannunta duka na rawa ta karba ta kalla tun alkcin taji kanta na juyawa bata dawo cikin hayyacinta ba har saida taji dirar kalaman bappansu na karshe...

(Recap page 1, wanda suka karanta page one basai kum nanata nan ba except akwai few abubuwan da zaku oya tsinta aciki wanda bansa acan ba) cigaban labarin nabayansa keep reading💋


Tun da ta ji kalaman Bappansu na karshe cikin lumshe ido da qarfi tasakar musu wani irin tsumammen kuka me daga hankali tareda kara cukuikuyo shararar doguwar red colour bridal veil dinta daya rufeta rass har izuwa kasa ,A hankli jikinta yake rawa rawa koinanta yadau kyarma tsaban takaici da wata iriyar matsanancin ruɗani dake famar cinta acikin ranta wanda bazata iya fasalta yawarsa ba, wasu maqudan hawaye ne kawai suka shiga gangaro mata akan fuskarta yuuu wanda daga ganinsu kasan bata shirya musu ba.

yanayinta mai cike da jin tsoro da kuma tsananin tashin hankali tadada sunkuyar dakai ayayinda take agurfane a tsakiyar babban falon

kuka kawai take rabzawa ahankali wanda zafinsa saida yy kama da kamarna wanda zata cire ranta ta fetar wajje, cike da dauriya tadago kai jin tsananin zafin maganganun bappan nasu nadawo mata kai, babu shiri kuma dakyar tadago kai takalli ammi karama dake kusa da ita tana goge hawayen dake sauka acikin kwayar idonta tadan sunkuyar dakai da wani irin sanyin jiki babu wata alamar dai yau zata budi baki ta kareta, zuciyarta a raunace ta kalli bappan nasu da yay maganan shima fuskarsa still na hade ne tamau tamkar bakin hadari jitay bata samu kwarin gwiwar cemasa komai ba shima dan gabaki daya batasan ya zata fara fidda kanta acikin wann cakwakiyar ba, Ammi babba dake falon itama duk tabi ta tsime sai tsaki take sakewa jifa jifa dan dama ta tsani auren, babu dai wanda yace uffan acikinsu, kara runtse ido ayaanah tay sosai tadinga rabza kuka me sanyi me kuma hade da zazzafar shesheka duk ta rasa ya zatayi, can dai hannunta dake rawa rawa ya fara motsi ba acikin hayyacinta ba ta capke bakin zanin hajya data rabza uban tagumi agefen bappan nasu ta mugun tsimewa da tsananin fushi ha idanunta sunyi jaaa zirr tanakan girgiza kafafunta a masife

cikin rawan murya da gunjin kuka takamo hannun hajy mairo ahnkli cikin raunateccen magiya muryanta bai fita sosai tace "Don girman Allah hajiya kicewa su bappa suy yi hakuri wallh wallah bansan komi ba banyi komi ba don Allah kice su dan saurareni ni ban san wanda yayi min haka ba..."

amugun fusace hajya mairo ta warce hannunta da wani irin fushi me tattare da buhun barkwanon masifa caraf ta mike tsaye tana cewa "Ni da Allah sakeni ki wallh haushi kike bani, wato ke har kinsan ki aje mu anan kiyita rabza mana uban rantsuwa akan karya alhalin ke din ashe babban munafukace ko Ayaanah?toh tirrr da halinki. makanki kikayi bawa mu ba dan ganan abu mun gani ido da ido me kq zakice mana kin cuce kanki, kin tozarni.. kin kuma kashe aurenki tun ba adaura shi ba. Allah ya isanmu ma irin tarbiyan da muka taru duka muka baki agidan nan nide Allah ya isa tsakanina dake muguwa kawai!wallah ko su zaidu zasu yafe miki nikam bazan taba yafe miki ba, baqar almuramura anjima ana kawomin kararki, Allah sai ya mana sharia, dan koda aka kawoki daga kauye ubanki saidai yaje har dakina yayimin zagin kaca kaca ya hadamin da mugun baki cewa zakizo gabana ki lalace a binni, wato shine kikeso ki dada tabbar masa ke asalin watsaiyace, kin zo gaban ƴayana kin zamo cikkyar marar mutunci marar kamun kai kika maida kanki yar kwaltaa abayan idanunmu yo shikenan ranar aurenki ne kika zabi ki toxartani kiji dadi ko? meye burge ki da wann rayuwan ynx uban wayema xai amince yakara aurenki a fadin duniyan nan wayyo na shiga uku ni me tuwo Wallah baki isa ki kasheni ba wani dan uban Dukan bazata takai mata ajiki abazata tana kuka cikin raki tana cewa...

..toh wallh ki sani uwata Azumi bata tsinemin ba, kafin ki dauko mana abun kunya gwara tun wuri mu mu kunyata ki yo meya burgeki da irin wannan rayuwar ta yan iska inba samun waje ba?

daga ita har ayanahn kuka sukeyii ganin ta kara tantameta duk dama dukanta take kanyi tanata kukan sosai kuma acikin ruɗani, bakinta har na rawa cikin kukq da magiya takecewa "Hajiya dan Allah ki saurare ni, nasan kinsan ban aikata komi ba, wallh zaki iya dubani kigani, wallah wallh wallh ban aikata abunda kuke tunanin na aikata ba.. sharri.. aka...bansan yaushe...bata karasa me zatace ba taji saukar wani dan uban saukar ginannen mari da hajya ta kai mata me mugun zafi a bqki sanda ta saketa tariqe bakin ma batasani ba.

"banace miki kiyi min shiru ba, makira kawai annamimiya duk za'a taru amiki karya ne bayan ga shaidu nan zaidu ya kawomin su kaca kaca?kece acikin bidion nan fa ayaana bayan kinsaka natara dangina da mutanen anguwa kafff, nayi shelar aurenki kina gani hakanan akayita zagina akanki, akace min naci amana, nayi son kai, har mayya sai da aka kira ni, kai meye ma ba acemin a anguwan nan ba? haka naruntse idona kyam sabida aurenki da yaron nan rufin asirine agaremu baki daya amma dan tsabr rashin sanin darajar kai saida kika kekeshe idonki kika tozarmu "Ayaanah.. ni menayi miki?...toh wallah wallah baki isa ki dora min hawan jini ba, muna da yadda zamuy dake inke ban isa dake ba ai akwai wanda na isa dasu agidan nan, ki tashi ki bace min ana kar na tattaki nakaiki har lahira.

Ayaanah ta mike jiki babu kwari duhu duhu take gani agabanta har ta fita a falon tana kuka sosai kamar ranta zai fita..

direct dakinta ta nufa don tasan komei xata ce anan babu wanda zai saurareta ders too much evidence dat are pointing againts her which she knew nothing about, bayan tashiga daki kan gadonta tanufa tana rabza kuka sosai ayayinda kanta da kirjinta ke bugawa dan harga Allah batasan wani irin hukunci kuma za'a yanke mata ba.

bayan wucewar ayaanah daki hajya mairo tana kan kuka ta kalle bappan zaidu tace "yau naga ikon Allah Zaidu. dan Allah ayaga hotonan nan bideon ma duk agoge kaji? sann ayi maza arabata da wayann mutanen banzan datake bibiya, banason wani a dangi ma yasake jin labari bare ganin shaidun nan.

tun be amsa ba ta dada rushewa da wani kukan kmr an bugeta, "Allah mun gode maka, wai sai ka haifi ɗa amma baka haifi halinsa ba wallah mahaifyar ayaanah mutuniyar kirki ce yanxu meye wannan take so maqiya na suce akaina kenan..

cikin sauke ajiyan zuciya bappan nasu yace Ahtoh nide nagaya muku hajiya Auren ayaanah dai ya fasu, sun kirani yace ya fasa bazai aureta ba, snn shine ma ya tura min wann shaidojin ga kuma jama'a sun taro dama sai an daura auren ayaanahn ne kafin agabatar da na su zainab Arifah, ni duk rasa mafita yanxu kam ai jin kunyan mutane ne kawai ya rage mana saidai in....

wani caraf Ammi babba ta capke maganan abakinsa tanamai cewa 'a'a, yaa Zaidu tsaya, ai magana kam ya riga ya kare tunda auren ayanah ya fasu me kuma zamuyi ai kawai afito fili kawai aje a bayyana masu kawu babba komi kar abata musu lokaci kasan yadda yaci buri akan auren yarsa zainab Arifah yatara manyn mutane kar abata musu lokci akan aikin banza. hhmm ayyuriri dama anbar yarinya tana abunda tagama dama kam ai babu wani abun da za'a samu a karshen rayuwrta face jin kunya, kuma ai wanda suka taru sua bude mata hanya ta lalata kantan sunsan kansu..

da gefen ido ta jefa baqar maganan ganin ammi karama bata ko dago kai ba taji wani irin dadi aranta dan dama wnn irin ranar kawai take jira na jin kunya danta gumsa musu bakin ciki.

fade fade take inda take shiga bata nan take fita ba, ganin dai babu wanda yace mata uffan haryanxu yasa tafara daga musu hankli burinta kawai aje filin taro a fallasa komi..

hidima biyu ne ga lokaci nata tafiya inma tsoron zubda ma kawu babba kimansa akeyi, toh mezai hana kawai a tura ayanahn takoma inda tafito ace kawai guduwa tayi takoma kauyensu if not wallah kaf zuria sai munji kunya bana kadan ba dan abundai akwai zubar da kima da mutuncin manya aciki.

tunda ta fara maganar kauda kai kawai bappa zaidu yay kamar wanda baijin surutan nata ahnkli yanamai lallatsa wayarsa da alama yana rubuta wani sakone, yana gama rubuta sakon ya tura ya tabbata ya isa snn yakashe wayarsan, sai a sann ya juyo ya kalleta adan taikace amma baice mata uffan ba kawai ya girgiza kansa..nan take falon ya kuma dauka da wani irin shiru bakaramin hade rai ammi babban tay ba sabida ta tsani tay magana duk taga an shareta..

within 5 scnds karar waya yakatse shirun nasu ammi karama dake zaune shiru tana hawaye ita ta dauki wayar after uttering few words ta katse wayr snn ta kalli bappa zaidu da sanyin jiki ayayinda muryanta ke fita a cikin nitsuwa

86 / 88