Author : NONE Category : African Stories & Novels
safiyan ta dawo da jakarta na makaranta tun daga kofar falon ta doka musu fulll sallama jikinta sai rawa yake hawaye na zuba mata tana kan tarewa da oversized veil din data rufe kanta dashi ,wani irin mugun kallo ibaad ya mata snn ya bata izinin shigowa ciki, still ta gefen maheer din taja ta tsaya, yaja tsaki yana juyowa zai kwace jakar suka hade ido da maheer girarsa sama a dage ahnkli yace hey mr temper, please kabarni da ita i will take it frm here..ibaad baice masa komi ba ya kalli safiyan yace ke zo nan..da dan uban sauri ta karaso ta tsuguna agabansa, yar nasiha maheer din ya mata akan tana nitsuwa, snn ta rage kallon series at dis young age ta fuskance karatunta kawai, ya mammata nasiha cikin lumana, ibaad na shiru bai kara cewa komi ba, dede ta bude assignmet dinta na farko da batay ba kenn sai ga ammi karama ta dawo da katon tray a hannunta mai dauke da manya manyan matured colour cooler dan kusan duk kayan kitchen inta daga wjen uwargida collection kawai take odersu.. cikin nitsuwa ta shigo tana cewa i am sorry i kept u waiting ko wsu ababen packagin nake nema bansamu da wuri ba.. tun bata gama surutun nata ba cikin sauri ibaad ya miqe yaje ya amshi tray din a hannunta suka karaso cikin falon tare, murmushi me sanyi tay ganin maheer na kan nuna ma safiya yadda zatay asigment dinta ayayinda safiyar ta bashi hanklinta sosai ta nitsu..
"babban mutum ka kyaleta kazo kaci abinci safiya kam ma ai na gaya mata aure zan mata kwanan nan dan naga gabaki daya wasa ne aranta bata kaunar karatu sai ta ganku, gidan nan dai duk wayake suwa 3rd position a schl in ba ita ba, ko kunya fa bataji
maheer na murmushi me sanyi yace aa Ammi haba aibaza ai mata haka ba she will grow up nd bcm a very succesful Data anlyst dan naga tafi iya lissafin computer ko ba haka bane safiya?
hawayenta ta share snn ta dago kai zatay magana wani mugun harara ibaad ya kara balla mata da sauri ta maida kanta kan littafin bata kara dagowaba.
suna kammala zama akan dinning ahnkli ibaad yakasa haquri with serious tone a muryansa yace ammi dan Allah kidena saurin gayamata cewa aure zaki mata da wuri karma ta sa shirmen soyayya aranta taki yin karatu, cikin katsesa da mamaki maheer yace dude relax, this is all fluff.. tsorata ta kawai ammi takeyi dan ta nitsu, cikin kyabe baki ibaad yace "auren ne zai sakata nitsuwa? in ana gaya mata haka babu wani tsoratar da zatay saidai ma ta kara saka abun aranta if not at dis age menene take kalla a indian series inba shirmen soyayyar karya ba, dahaka ne da suke saka abun aransu kaga yarinya karama wai tafara bin namiji... ammi dake kan jinsu batace komi ba tanakan bude warmers inta ahnkli wani irin qamshi ya katsesu maheer zaiy magana cikin katsetsa tace ya isa haka nifa bance kuzo kuyita musu agabana ba abinci kawai zakuci maheer please grab ur plate for me..da zumudi maheer ya bar maganan ya tura mata plate dinsa dake ta gabansa
wani dan ubansun Dambun Shinkafa da Nama tay irin nasu na mutenen maiduguri she steamed it with beef, onions, garlic, and butter, but she infuses it with Arab baharat spices dan ya kara masa dandano na musamman.
wani irin lumshe ido ibaad yay cos dambun shinkafar mamansa is his long time favourite maheer yafara lashe baki tun bata gama zuba masa ba ya dau cokali ya rike suna kallon juna da ibaad da tunanin irin dukan da zasuy ma abincin
ganin yanayin reaction dinsu yasa ammi ta zuba wata sasasnyr murmushi, tana gama zuba ma maheer nashi ta zuba ma ibaad shima snn ta bude wani cooler ta debo surprise din data ce zata masa yasha mamaki kuwa da yaga Fattah Lahm, special shuwa danderu ne da bata fiye yi ba dake da flat bread ake cinsa kamr shawarma. yana da mugun dadi dan is A whole hearty dish of slow-cooked lamb in spiced butter, layered with irin torn flatbread din nan, and the whole combo is soaked into a rich romon nama dayake tashen kayan yaji dana qamshi.
maheer nakaiwa baki yace wayyo Allah na ammi kin kasheni this is the besttttt food ever, dariya ammi ta farayi ganin banda bismillah ibaad bai ce komi ba kawai cin abincin yake kmr wanda yay shekara baici abinci ba, duk hirar da suke sai dai kaji ana uhmm uhm
safiya ta kafe kanta a asgment qamshin abincin yacikata amma sabida ibaad yasa batakoy gigin dago kanta ba.
bayan sun gama ci to the fullest ammi ta basu herbal tea inta me lemon tsami aciki suka sha, suna kan sha ana hirar karatu sama sama wayar maheer din ya fara kara ganin lambar mamansa ne yasa yayi excusing dinsu yabar sashen cikin gaggawa dan ya san halinta sarai ta tsani taji zancen yabiyo ibaad sunzo wajen ammi karama.
fitar maheer bada jimawa ta kalle ibaad din dake famar gode mata da abincin ahnkli tace its okay, dama haka kawai yau naji in maka abincin daka fi so yau and since u liked it ai shikenan
..ynx tayani tattarawa muje kitchen i want to have few some words with you alone.
..baice komi ba ya miƙe dan shikansa badon wnn yummy food treat din nata daya samu ba hala da tsananin bacin rai daya kwaso agidan kawu babba dazu zaiyi bacci..
cikin tsaftaccen kitchen inta dayaji jeren yan gayu suka shiga dede wajen sink ta juyo ta amshi tray in a hannunsa snn ta bude fridge ta fito masa da ruwa me sanyi wajen miƙa masa suka hade ido
daya kalleta saikuma yaji mugun tausayinta da kuma haushin shirun dayayi dazu ana zagar masa ita
suna daga tsayen taga mood dinsa ya fara canzawa cikin nitsuwa ta juyo dakyau tanata kallonsa ahnkli tace 'yadai rayyan, nikam ko baka jin dadi ne nide tun jiya kaketa faɗo min araina..ina fatan..
cikin katseta yace "Ammi, i am fine. kidena daga hanklinki pls
cike da yar maraicewa tace hmmm, badon kar yaa zaidu yay fushi ba yau danace ka kwana min anan but i get it, akwai schl kuma dama shi zaifi saka maka ido acan kayi karatun saidai bansan matarsa ba..did she still treat u diffrntly.,
ahnkli ya girgiza kai yace aa, cikin kauda hirar yace ammi, bappa bai gaya miki cewa kawu babba ya kirani gidansa bane???
waje ta kwalo idonta tace wani kawu babban? kana nufin bappanka prof zayyanu ya nemeka gidansa dabai barin uban kowa yaje?
tun be amsa ba adan tsorace tace 'why? wani abu marar kyau yakara shiga tsakanin ka da yarsu ko rayyan? dan Allah ka rufa min asiri mana ka fita aharkan yarinyar nan..ransa a hade cikn katseta yace haba ammi in fita aharknta kode sufita aharkata? tace ban gane su fita aharkan ka ba bayan kaine ka dakar musu yarsu yar kwai, wai kuma kana tunanin zasu yafe maka ne cikin sauki?
yace but dats like many months ago ammi. karamin scoff tay tace" okay, just tell me what was the meeting all about. kar ka boyemin komi..bana son wani fitina ya shiga tsakaninka da su musmn ma akan yarsu kana gani dai har hajy mairo prof bai kyaleta akan yarsa ba bare kai da baka da ubanka araye.
dan lumshe idon sa yay kadan kafin nan ya bude ya kalleta da sanyin jiki snn ya fara gaggaya mata duk abubuwnda suka faru muryansa kamar na wanda zai mata kuka, yace ammi, bayan cin fuskar da sukamin wai they still want me ina zuwa gidansun akai akai dan kawai hankalin yarsu yana kwanciya, nide ammi dan Allah u have to talk to bappa zaidu abt this, inajin nauyin inje ingaya masa kai tsaye cewa bazan kara zuwa ba batare da na bashi kwakkarn dalili ba,amma wallh bazan iya kula musu da yarsu ba,akan me? ni kaina abubuwa sun fara min yawa na karatuna i need to focus..nd for god sakes bazan je inda za'a na zaginki da sauran yan uwana a gaban idona ba..
wani irin shiruuuu ammi karama tay batace masa uffan ba for almost five mins tana jinjina maganan sai can taja ajiyan zuciya tace hmmm toh Allah ya kyauta,
cikin kwayar idanunsa ta juyo takalla ahnkli tace "rayyan, toh duniyar ma nawa take bare abun cikinta.. jarabawa ne kawai ..kaima kasan kafi karfin amaka gori da maraicinka tunda ban mutu ba ina raye kawai hakuri duk zamuyi dasu. bt in sha Allah zan yi magana da bappan naka kai kuma sai ka cigaba da masa biyayya dan Allah kar kadinga saba masa, know dat i am alwys here for you..Allah zai kawo mana sauki, kaji ko? ajiyar zuciya me nauyi ne ya kusan kufce masa ahnkli yace toh Ameen ammi and thank you alot for spoiling us i wish i can eat dis all day long.
..kyakkwn fuskarsa ta shafa kadan tana yar murmushi tace karka damu i hve packed some acikin take aways wanda zakuje gida dashi sai kuci dede nan aka kwankwasa kofar kitchen din maheer ne ya shigo looking so awkward, ya samu dede ammi tana kkrin ciro take away rubbrs din madaidata har guda uku babu jira ya shiga tayata har suka gama tasa musu a ledoji, wani sabon shafin hirar sukayi cikin wasa da dariya wajajen 9:40 suka ce mata zasu koma gida lokcin safiya ta gama duka asigment dinta still ibaad ya mata fada akan kallon series snn yace mata bazata kara cin abinci ba kawai ta wuce taje ta kwanta haka kuwa tawuce daki taje bacci har suka bar sashen sukaje suka gaida uncle moh da anty safeerah a shashensu snn suka bar gidan mai gabaki daya
cikinsu a matukar koshe suka kamo hanyar GRA maheer yana ta tsokanan ibaad wai kodan abincin da sukaci ne yasa yadan saki ransa, shide bai wani bashi amsa me kama hankli ba har suka isa gida me gadi yana bude musu gate sukay parking suka sauko da ledan abincin riki riki ahannun maheer suna isowa sama ibaad ya mika masa key din mota yay sauri ya haura gaba, da wani abu aran maheer yace hey Dan Allah kazo muje wajen baba atare mana waime haka inbazaka je bama ka amshi ledar abincin toh ka rike, ibaad yana ci gaba da tafiya akan stairs yace aa bazanje wajensa yau ba kaidai kayi sauri kafin afara wasar psg da chelsea bakazo ba, kai tsaye dakin maheer din ibaad ya nufa tun be amsashi ba, dake shi maheer har tv yana dashi adakinsa.
cikin girgiza kai maheer ya rabi hanya yawuce sashen bappa zaidu har ya kai kofa da sanyin sallama a bakinsa samunsa yay a zaune akan arms chair shi daya yanata kallon tashar larabai wanda tunkan ya amsa sallamar daddn qamshin abincin ya fara bugosa nd its sound really familiar dan yasan irin wnn qamshin inba girkin fatima ba toh saidai in mamansa hajy mairo mai tuwo ce ta dawo
cikin ladabi maheer ya rusuna yace ina wuni baà, idon bappa nakan ledan abincin yace lafya har kun dawo? ya mutane gidan kuma.. yace lafyarsu kalau dama uncle moh yace in gaya maka wai zaizo ya sameka da safe a office akan batun dawowar hajiya..
bappa zaidu yace "toh Allah ya kawosa sunyi waya da hajyar ne? inaga karshe ibaad kawai zamu tura ya dawo da ita tunda abokin fadanta ne amma kuma tafi saurararsa. gskiy she needs to come home yanxu kauyukan nan are not safe att all.
maheer yace hakane uncle moh yafara gaya mana wai jiya an mata satar generator a shagonta case kawai ta wuni tanay a police station da mutane acan..
bappa zaidu yace hmm mama kenan koda tana da kudin siyan dubunsa sai ta so akama barawon nan just to put him into justice nd dats way more scarier, ynxu fa duniyar ta zanca mai gaskiya bayayin farin jini. ina shi ibaad din inafatan dai baka barsa acan ba?
dan shiru maheer yay kafin ya dago a nitse yace aa tare muka dawo amma yana can daki na.'..
bappa yace ohh, to mesa bakuzo nan tare ba, lfya kuwa naga bai gaya min komi game da zuwansa gidan kawun nasa ba..
cikin gyaran murya maheer yace umm about that.....
bappa zaidu ya dada mikewa zaune yana kallonsa cikin nitsuwa yace "wani abu yafaru ko?
kansa akasa yace baa is not like he talked to me directly amma i overhead him yana gaya ma mum dinsa cewa wai so kawai suke yana zuwa gidan dan hanklin yarsu ya kwanta and.....sai yay shiru...
bappa ya masa wani irin kallo yace and what maheer karkay wasa dan hanklina anan mana..
yanadan sosa keyan kansa ahnkli yace 'baa, i dont think they treat him well..he mention sumtin abt zagin da sukama mahaifyarsa agaban idonsa akan zainab, baba cemishi fa sukay wai hala dad dinsa yana dukan mum dinsa ne yana gani shiyasa shima ya girma ba'a bashi tarbiya ba kuma wai duk yunwa ne ajikinsa, they even cooked him a separate meal hmm maganan dai da yawa..
komawa jikin chair bappa zaidu yay yana girgiza kai ahnkli ya furta hmm, snn yace "rubbish, sai kaga mutane kamar sun waye but they are so petty
..wann ai karanta ne. dama nasan za'ayi haka, idankaji kiransu badai don Allah bane saidai in suna buktar wani abu ajikin mutum suke kulasa, but i wont let them insult him again karya suke wallah, kai.. tashi kaje nasan me zanyi ai bakomi..
maheer baice komi ya aje keys din benz din akan table zaija ledarsa ya fice kenan bappa zaidu yy gyran murya yace "waimeye ne acikin ladan nan ka shigomun dashi me qamshi...
da zumudi maheer ya juyo yace ammi karama ce ta mana abinci me masifar dadi dama sauran ne tabamu wai mukawo gida mu karaci...
cikin mugun muradin son yaga yaci abinci me tattare da wata iriyar kamiya bappa zaidu yace ohhh toh dama wakanku kawai kuka kawo kenan..
maheer yace a'a ai tabamu hada extra nagawai baka cin abinci ne in dare yay sosai, but if u will like to eat saina serving maka, cikin jan aji bappa zaidu yay shiru sai can yace kawo dai in gani, what did she have here dan ban fiye son cin abinci late ba..
nan da nan maheer ya bude ledar ya ciro roban take away din guda daya ancika shi dam ga dambun ga babban sokar nama ga kuma phatta lahm da romonsa agefe an shiryashi very neatly komi gwanin sha'awa, ana mika masa tunbai kai ga gama budewa ba qamshin yasakashi lumshe idon dole domin karyay zumudi agaban dansa ya dan hade rai maheer yana ta batun kawo masa spoon yaga gogan har ya buɗe abincin ya aje murfin akan table yana kkrin tashi yaje ya wanke hannu a hand washing sink dake falon aikuwa suna hada ido ya balla masa wata dakalken kallo yace" kai baynxu kace min kunci naku abincin acan gidan ba to uban me kake ta kallon nawa kuma??
maheer yay kamar zaiy dariya yabi ya gintse kayansa ya kama hanyar waje
bappa zaidu yana gama wanke hannu ya jawo abincin hannu abaka yay bisimillah yay wata makahuwar loma wa dambun ya kai bakinsa wanda tuni yaji wani nitsuwa dan baisan wani dunia dadin girkin yakai sa ba,.. ahankli lumshe idonsa ahnkli yana furta kai masha Allah, but fatima can cook oo, da ynxu ninace tamin irin haka bazata taɓayi ba saraunyar kunya...
kusan kasar wuyarsa ya furta hakan amma xurum kalaman nan suka fada acikin kunnen matarsa ammi babba da zuwanta kenan ko sallama batay masa ba tun ganin maheer da tay awaje da ledan abinci tasan za'a rina, ranta a dagule ta shigo tana kan huci ta bi ta tsaya masa akai a mugun tsime tace "yaa zaidu kenan ma aka samu haka aketa hanɗama kamar baka tabacin abinci aryuwarka ba"
..romo dumu dumu abakinsa ya dago kai ya kalleta yace" yaran nan ne suka dawo dashi daga can gidan shine nima suka sammin".
wani irin runste ido tay cikin daga murya tanamai cewa "aa malam dakata min, karka raina min hankali mana kawai ka fito fili kace dai kaine ka aikesu wajen tsohuwar farkanka da Allah baiyi zaka aurota ka tozartani akanta ba, sunje sun karbo maka abincinta kazonan kana ci ham ham sai kace bantaba maka girki agidan nan ba yaa zaidu gaskiya cin fuskr da kake min agidan nan fa ya fara isata..
cikin katseta da dakakken muryansa me razanarwa yace keeee, da Allah ya isheki haka baki gani inacin abincine kifita kawai kiban waje inci abinci na cikin kwancyar hankali dan duk wnn kananan maganan dakikey duk ke kika san su can miki.
wani kukan kura tay zata kwace kwanon ya wapce abunsa gefe suna hade ido yace raihanatu am warning you.. kinsan dai idon yaran nan biyu basuy bacci ba banason inci mutuncin ki anan wjn agabansu kiga lefina so just get out...inna gama ci kya dawo kiyi baccinki...
tsabar bacin rai kirjinta har na dokuwa take harararsa a zafafe tafara daga murya tana cewa ohh hakama zakace min?
toh wallh wallah ba a isa ba
ganin bakulata zaiyi ba kuma bai fasa cin abincin ba yasa ta fashe da kukan takaici ta fice waje a mugun zafafe..
dakin maheer din ta nufa kai tsaye tahau bubbuga kofaraa kamar an korota lokcin har sun kunna tashar ball sun fara kallon kwallo shida ibaad, it was hell of a ryd tsakanin chelsea da PSG...
buga kofar datay da karfi yasa suka razana maheer ya mike tsaye cikin sauri ya fito, da mugun sauri ibaad shima ya taso yana biye dashi abaya baya
..suna bude kofa suka gan ammi babba atsaye sai huci take kamar kububuwa hawaye taf fuskarta
kan maheer a daure yace mumy lafya kuwa? muryanta har na sarkfewa tace "Ina tsinannen abincin da ka kawo gidan nan
zai magana sai wani tasssss yaji diran yatsunta akan kuncinsa shikansa baisan sanda tasakar masa wata makuhar mari me kara ba..
ranta a mugun bace cikin dakamai tsawa tace Baqin munafuki kawai... Allah wadai naka ya lalace,.maheer wato ma dakai ake haɗamin