Author : NONE Category : African Stories & Novels
kuma ahnkli tace "yaa zaidu, Mujaheed ne yakira yace in sanar dakai cewa yaga sakonka kuma yana daf da isowa gidan nan shima yanzu".
babu yabo babu fallasa cikin sassauto da bacin ran dake fuskansa ya kalleta cikin sauke karamin ajiyan zuciya snn ya amsata da "toh fatima Allah ya kawoshi lafiya, komi yar hakuri ce dan haka ki kwantar da hankalinki evrything will be fine.
kanta akasa tana share kwallanta Tace mishi toh Ameen. dan kadan ya mayar mata da sanyin murmushi ita kuma tay maza ta sauke kanta kasa adan kunyace.
kallonsu ammi babban takeyi kamar zata tashi tsaye ta haɗiyesu su da mugun bugu, dan ɗan wnn calm gestures da yake yawan wakana tsakaninsu bakaramin kona mata rai yakey ba, wato itace datake matarsa na sunna ma bazai amsata ya bata hakuri ba caraf yahau amsa wannan makirar matan. satar kallonsu kawai take tana raya abubuwa masu tsauri aranta ayayinda babu abunda idonta yakey face hararar fatimar tareda jan musu kananan tsaki
share hawaye hajiya tay adede lokacin da wani gulluton baqin ciki ya kara rufe mata kirji inta tuna hotonan nan
ganin datayi kmar Ammi babba zata kara yin wani magana, nan tay marmaza cikin katseta a masife tace "haba, haba..ya isa haka mana ke kuwa Raihanatu, kinyi ta maganan nan duk anji ra'ayinki akan ayanah amma kisani nide ban aminta da gurguwar shawarar kin nan ba, yoo sai kuma aje har babban masallacin jumua ayi shela ace ma jama'ar Annabi S.A.W. cewa yarinyar nan tagudu ranar daurin aurenta sai kace muna kwapcen wasan kwaikwayo?,..
adan masifa ammi babban tace amma hajya kema kinsan halin kawu babba wallh bazai lamunci azo da batu daga gidanan a tozarta shi a bainar muhimman mutane ba aranar daurin aurensa yarsa zainab arifah ba.
fuskar tsohuwar ba asake ba takalle bappa tace "zaidu maganan nan fa ya kare bama sai anje ga tozarta zayyanu agaban mutanensa ba tunda abunda kuke gudu kenan, dolene kawai ayi auren Ayanaah ayau din nan, babu wata zancen guduwa ko fasa shi, tunda shi wanda ya sakar mata fuska ya mata alherin shi ta cutar ta tozarta, yau koma uban waye mukaga dama dashi za'a a daureta yau, inyaso taje can can gidansa ta karashe rayuwarta dashi inma kashe kanta zatayi a dakin miji gara tay da akanda tazauna min agabana ta cigaba da tonamin asiri tay karuwanci a birni ubanta juma nacan kauye yayimin dariya, aure kam kamar an daurashi ayau ko tanaso ko bataso
wani irin shiru wajen yakara daukawa a falon ayayinda fuskar sauran matayen looks soo soo confuse da furucin tsohuwar duk da alama basu wani gama fahimtar inda maganan tsohuwar ya dosa ba, to da waye kenan za'ayi ma ayana auren dolen? da mujaheed ne ko wani ne nadaban daga waje? saidai tun kafin dayansu ta budi baki tay tambaya bappa zaidu yakalle su duka biyun fuskarsa ba a sake ba still cikin gyaran murya yace ya kamata kubami wuri zanyi wata magana da hajiya"..
babu tantama kowaccensu suka mike tsaye cikin hadiye tambayar dake ransu snn suka fice waje.
Ammi babba nan tay sashen abty safeera da uban sauri dan taje ta yafa mata gurmi
ammi karama nan tanufi dakin Ayaanah kai tsaye jikinta duk a sanyaye, ta iso kofar dakin Ayaanah bata sani ba, kife kai tay akan gadonta tana ta kuka me karsashi gashi ita kanta tarasa amsar da zata bawa kanta, kanta duk ya kulle, she was like is this actually happening to her abu ne da batay tsammani ba sai gaba daya sai taji ta fice hayyacinta, she wish zata bude idonta taga mmmunan mafarki kawai take,
kwankwasa kofar dakin da akay da dan karfi yasa tadaga idonta da sukayi jaaa suka kumbura tana kallon kofar amma bata da niyyar tashi tabude har akagaji da Knocking aka bar wajen.
Sai can wajen after good 40 mins data dan dawo hayyacinta tana xaune saman gadon kafin ta jawo wayarta da kyar da kamar zata bude sai taji xuciyarta ya kara rauni, MTN sim card dinta take son cirewa ta karyashi sai taga tarin missed calls din kawar aikinta Ruthy yafi guda talatin da wasu irin zafafan text messages da ya ninka calls din daga wajen ango to be din nata, ko wani message data bude zance daya yake yi, " i once trusted you, nina miki kaza nina miki kaza lokcin baki da kaza..kinci amanata ayanah, bazan yafe miki ba.." kowani kalma da ya rubuto mata suna daukene rashin mutunci da gori, tsana da zafin cin amana da butulci dayake famr tunanin tay masa.
wasu irin raunattun hawaye suka shiga bin kuncinta bawai dan zafin words dinsa ba sai gani datay wai har ya aminta da komi dayagani akanta kai tsaye, dan tay tunani in akwai wani wanda zai iya bada kwararren shaida mai kyau akan iliminta da tarbiyanta da shine mutum na farko da zai bayar, ita ko kadan batay tsmmanin cewa ya jima yana zargi da kallon ta a matsayin wance tasan maza ba ashe shaida kawai yake jira dama
fita tayi daga Inbox din hawaye me zafi na sauka a idonta, ta bude WhatsApp shi ma dai duk messages din ne har da gori masu zafi aciki, gashi shidin ba yaro bane bare tace ko yana furta kalaman nan ne da gigin yaranta wai yau namijin da ake ikirarin zai aureta ya rufa mata asirin kenan yake kirarta watsatsiya karuwa hmmm.
kirijnta taji kamar sai fashe badon fasawar auren na sao dan zafin kazafi da bata suna, Kashe wayar kawai tayi ta ciro sim card din ta karyashi into 2 pieces kamar yanda tayi niyya snn tajefar da wayar can can saman gado tana goge hawayen da ya ki tsaya mata, sam batay tsammanin haka kwakwalar maza ke aiki akan zargi ba dan wasu tsauraran maganganun nasa ya mugun tsaya mata a zuciya.
Knocking din kofa aka sake yi, ta kalli kofar sai kuma tamike a hankali ta nufi kofar ta budeshi ahankli, ammi karama ta gani tsaye suna hade ido nan da nan wasu sabbin hawayen suka ciko idonta tabi ta sunkuyar dakanta kasa cikin sanyin jiki
ammi ta shigo dakin ta kulle kofar ayaanah ta bi ta da kallo harta nemi waje ta xauna agefen gado snn ta karasa inda take ta durkusa kasa cikin sanyin murya me tafe da hawaye tace "Ammi don girman Allah kiyi hakuri, nasan kema zakice na tozarki wallah bansan komi akan wann abun ba.
ammi ta sauke wani ajiyar xuciya ahnkli cikin nitsuwa tace "Ayaanah i am not here to judge you, bare ma ai an riga anyanke miki hukunci auren nan naki bazai fasu ba, su hjiya sunce za'a daurasa a yau, kuma tun da har bappanku ya amince da wann hukuncin da hajiya ta yanke miki kema kinsan babu me ja da wannan hukunci nasu ke dai naki addu'a, nima ina nan ina taya ki da shi..
wani irin numfashi me karfi ayaanah taja abazata wasu sabbin hawayen da bata san dasu ba suka cigaba da sauka mata yuuu amma batace komi ba
cikin lallami ammi karama tace is okay kiy hakuri ayaanah snn kisani nobody is perfect but as long as we learn from our mistake ai shikenen, dan Allah ki kwantar da hankalinki kinji everything will be alright kuma koma waye ya aikata maki haka sai dai mu ce Allah ya isa miki da ya janyo miki wnn masifar harda kuma auren dole da wanda ba musani bama tukuna.
a mugun mugun rikice Ayaanah tadan mike tsaye is like sai yanxu kunnenta ya farajin batun wani auren dolen da ammi ta ambata..
atake jikinta sai ya fara rawa cikin dafe kirji tare da sakin birkitacen kuka me tafe da rudewa tace "ammi Auren dole da wani wanda baku sani ba kuma? auren dole fa kikace again Ammi? dama badashi za'a daura auren ba kuma.?
jiki a sanyaye ammi ta dan gyada mata kai tace shikam ai yace ya fasa saidai wani to wanin ne bansan ko waye ba.
a mugun ragwabe ayaanah ta fado kasa tare da durkusowa kasa cikin kuka mai kara, tarike hannun matar tana cewa dan Allah kar ayi min haka Ammi wllh xan iya mutuwa, ammi talk to him plss ai bappa yana jin maganarki sosai, dan Allah kiyi ma hajiya magana i can explain myself wallah wallah bansan komi ba, basai sun min auren dole ba nasan zata saurareki kodan karamin lokaci su karamin i will find a way out of this.
cikin runtse ido tare da jin tsananin tausayinta matar tace nima basu gaya min komi akai ba, amma dai mujaheed is on his way. kinga tunda angon shi yace ya fasa i have no idea what they are planning to do now, ga dai su can a falo inaga by now kuma inaji kmr ma har ma an daura. i am very sorry dear, kisani cewa I trust you. but i think wann ne kawai mafita agaremu duka gwara amiki auren kawai. snn koma waye suka miki auren dashi nasan dai bazai cutar dake ba Allah yasa shine miki mafi alheri.
Ayaanah ta dada rushewa da wani tsumammen kuka cikin mugun tashin hankali take cewa "Na shiga uku Ammi, yanxu baxa ki iyayin komai akai ba?auren dole fa zasu min da wanda kemafa kince baki san shi ba, ya xan yi da raina idan hakan yafaru, wallh ko ya mujaheed din ne bazan iya aurensa baa innalillahi wa inna ilaihi rajiun..."
Mikewa ammi tayi da hawaye taff idanunta da mugun tausayinta aranta tanufi kofa da sanyin jiki ta bude tana fita takulleta da keys ta waje........
*CIGABAN LABARI...*
fannin ammi babba kuwa tunda ta shiga ta samu anty safeera babu abinda take sai cika baki da jiji da kai da gatse take cewa anty safeeran da ta nemi taimakonta da wallah yanzu takai ta wajen malami an tarwatsa auren nan, tayita cika baki tana buga kirji ma anty safeera akan cewa wayonta da kkrinta ne yasaka duk da hjya mairo tana raye haryau fatima bata isa ta shigo gidanta ba...tsabar kuri har tay sabutan baki tahau gaya ma antu safeera sirrikanta na cewa bokab da ya mata aiki akansu yace har ta mutu agidan bappa zaidu baza mata kishiya ba....
wani baqar maganan yakan cima anty safeera rai, musmn yadda ammi babba take mata kallon yar yarinya da bata san me takeyi ba tukuna, tana mata magana kmr ta maidata abun tausayi har wani shawara take bata akan taje tay gyaran Hq sabida yanxu ne uncle moh zai fara nuna mata asalin halinsa musmn idan ya latsa na budurwa..ta dinga kushe lamarin anty safeera acikin habaici tana gaggaya mata magana kamr irin ita tagama rufe kofa tafi karfin mijinta shiyas aka kasa mata kishiya
anty safeera ta share hawayenta daya zuba ita dai batace komi ba tay shru tanajin ammi babba wai hartana mata tallan maganin mata na wajen zinariya
**********
kafin nan daga falon ba ajima da korar su ammi ba hajy mairo ta sako maganan wanda ya dace 'a maida auren ayaana akansa dan su ceto kansu daga tozarta
kai tsaye tace ai anjima dace mata ibaad yasan komi game da irin abunda ayanaa take aikatawa da rayuwrta dan haka shine ya dace ya riketa inba haka ba babu wani wanda zai aureta agidan nan asamu kwanciyar hankli da rufin asiri dalilai goma da ashirin duka ta jero masa, zaka sha baqar mamakin jin cewa ashe tuntuni taawure ta gaya ma hajy mairo cewa in ayaana ta girma ta hadasu aure da ibaad
tuntuni bata tashi tuna maganan nan ba saiyau datakeso tafito kiri kiri tay weaponising dan kawai asiri ya rufu kar yaranta su tozarta.
bappa zaidu yace shifa bazai tursasa ibaad auren kowa ba har sai inshi yace yana so suna cikin maganan kuwa sai ga su maheer da ibaad sun karaso
hajya bata bari sun zauna ba ta dau waya tace driver yaje maza maza ya karasa dauko mata alhaj hamza ace masa its very urgent.
driver na tafiya magana ta dawo sabuwa, haka hajy mairo taki firrrrr bappa zaidu ya fayyace ma su ibaad dalilin fasa auren ayanaa da uncle moh sai tay sauri sauri takwace maganan gabaki daya abakinsa tafara tuna ma ibaad alkwarinsu da taawuure
wasu maganganun da ta boye masan ba sai yau yakeji, ashe asali wa ibaad taawure ta roki alfarman hajiya cewa abashi ita ya aura inta girma
kuma hajya tana tune da wann maganan kawai dai ta kulle zuciyarta ne tay burus, dan taso ne tahanashi ayaanan kwata kwata saita aura ma wani ko muhammadu just so that she will impressed her son zayyanu akan batun zainab arifah dan su karfafa alaka dashi ,anata tunanin ai auren ibaad da arifah shime kadai zai hada kan yaranta..
she try to hide this informations in her words amma tuni maheer da ibaad din suka gane inda ta dosa
duk sungane cewa asali ta hanashi ayaana ne dan kawai ta turasa ya aure zainab ita kuma ayaanah tunda batada amfani a famlynsu sosai saita bada ita ma wani namijin ya aura koba dan gidan su ba,toh da muhammadu ma yazo yace yanaso ma sai ta haukai ta zauna kawai.
haka ta dinga rika rikita rikitan bayani, tace kawai rayyanu yayi musu biyayya ynxu ya aure ayaana a rufa asirin maganan nan tunda ma muhammdu ya fasa auren ayaanah ai dama tun dacan ma shi yarta taawure tay sha'awan auren ba muhammadu ba
first time da ibaad ya zama soo speechless kenan akabarta da maheer yana dada kwaco sauran bayanai abkinta data jima tana boyewa
jim kadan saiganan magabanta ayaanan suka iso da alhaj hanza da wasu dattijai su biyu su ukunsu suka shigo palon da tarkadan test na ayaana da hajyan ta aika masu jiya.
ana zama nan ma magana ya dada kwabewa musmm da alhaj hamza yace ai sun kira taawure tun ranar kuma tace musu ma wani mai suna ibaad hajiya tace zata aurawa ayaanah
ashe gabaki daya bata gaya musu gaskiya ba, tsoronta kar taawure taji gaskiya ta tabi bayan ibaad ahana muhamadu mata snn asa jikarta zainab a hanun rai ko mutuwa
she was just giving them countless reason na dalilin dayasa tay hakan.
don akashe maganar bappa zaidu ya girgiza kai da takaici kawai ya tambaye ibaad, snn yace masa yayi hakuri da yanayin hajiya mairo karkuma yace mata komi yanxu, nd if he can do this kawai ayi anan agama lokaci na tafiya 11am yawuce zasu wuce daurin aurensa sa zainab...
duk da cewa ibaad ya kara shan mamakin halim hajy mairo amma bai wani ɓata lokaci ba hade da ganin darajan dattijan nan da sukazo da tunanin cewa shine mijin yarsu, sai kawai amince atake bappa zaidu ya kara sadaki akan wanda za'a bayar na zainab 5million da suka riko, aka biya na ayaana double of it das 10 million naira snn aka yi all the nesscry ladabun aure aka daura musu auren awajen sharply
maheer da sauran dattijan suka zamo cikakun shaidu bayan an daura auren Dr Ibaad al-mansur da ayaana jumah, maheer kuma ya dauki su alhaj hanza ya wuce dasu can masauki
bappa zaidu ya kalli ibaad dayayi shiruuu cikin rasa abunda zai yi tunani aransa, cikin jin tausayinsa yace ya tashi su tafi wajen daurin aure inyaso su mujaheed su samesu awajen tunda har yanzu bai iso ba.
sun tashi zasu wuce kenan hajiya ta wani hade rai tace zaidu ina son nayi magana dakai, kai kuma rayyanu kabamu waje.
ibaad baiko kalleta ba ya fita baisan kuma me suka tattauna aciki da bappa zaidu, kawai yana fitowa suka shiga mota basu biya masallacin kai tsaye ba saida sukaje suka dauko wasu yan uwan babansu snn suka wuce wajen daurin auren..
waje ya cika makilll da manyan motoci da manyan masu gida yan siyasa da daidaikun sarakuna kowa ya dau wankan kece raini babu kuma kalar mota me tsada da bazaka gani awajen
kafin su shiga msallaci wajen daurin auren ne mujaheed ya iso, bappa zaidu ya tarasu agefe dukan su ukun ya gaya musu cewa hajiya ta riga ta umarceshi da ya cike wajen muhammadu shi a daura aurensa da ammi karama...
he was straight foward to them bawai neman shawara ko yarda ba he just dont want them to freak out..maheer me ya fara supporting dinsa kafn mujaheed nd ibaad was just neutral sabida kansa gabaki daya a lulle yake, he need alot of answers to the main reason da uncle moh ya fasa auren ayaana a dying minute.
bayan they are all cool with the information ma auren bappa zaidu aka shiga masallaci aka fara dana su ibaada da zainab arifah with alot of formalities na rainin hankali da kaskamci
tunda da suka kufular da ibaad sosai dacan da 5million dim sukazo dashi zasu bayar ibaad dayaga yadda prof yake kkrin tozarta bappa zaodu akan kudi sai ransa ya baci, danma yadada nuna masa yarsan ba komi bane sai yace shi 500k kawai zai iya bayarwa yanxu..
bakaramin rikici akay da prof akan haka ba, ibaad yaki jin maganan kowa yace wallah shi abunda zai bayar kenan, at end prof ended up paying his doter'sa dowry in dollars just to show off da sunan cewa ai shima kawun ibaad ne da rashin mutunci ibaad kuwa ya soke kudinsa a aljihu waje ya dauka da tsegumi
prof na zaune dake yan uwan nasa ba damuwarsa bane he dint even care to notice cewa muhammadu baya nan, next akazo daura auren bappa zaidu da fatima, maheer yace sam sam zai biya hka ya biya babansa yasha mamakinsa sosai. bayan angama aure it took them along time kafin aka gama gaishe gaishe, ibaad ne kawai hanklinsa baya jikinsa
gashi prof ya takura masa yanata nunasa ma abokansa...
Daga fannin ammi karama kuwa saida tay jimm ajikin kofar tana jin kukan ayanah snn itama tashare kwallarta daya zubo mata juyawarta keda wuya suka hade ido da hajiya mairo da alama ta fito daga falon kenan ta tsaya cak tana dan share sauran kwallanta da bakin mayafi itama
muryan ammin a sanyaye tace ahmm hajiya kardai har an daura?..
hjy me tuwo batace komi ba tagyada mata kai cike da had'iyar wani gulluton baqin ciki aranta tace eh an daura. "Fatima, dama ke nake nema, amma kafin muje can sama dakina inaso kiyi min