Chapter 82 Reading ABUNDA KE BOYE HN Novels

ABUNDA KE BOYE

Author :  NONE Category :  African Stories & Novels

Chapter   82 / 88

243K to 246K   out of 262.2K words

bari za'a miki kwanan nan? wallh safeera kin ban mamaki da kyanki da iliminki zaki zauna namiji har ya miki kishiya kuma it seems like ure even happy abt it..ni banga alaman kinma damu ba ,ke ko irin kishin matan nan baki dashi

kirjin anty safeera ma bugawa tara tara tace tsaya anty hamida bangane za'a min kishiya ba..ni din?? anya kinji da kyau kuwa..ni wallh mijina bai taba mafarkin zaimin kishiya ba i use to go tru his phone sumtimes baida wata budurwa ma

hajy hamida tace hmm safeera kenan, it seem like ure abt to be shocked!! nide ba abaki na zakiji gulma ba amma wallh uwar mijinki ne jiya ta gaya ma alhaj cewa aure biyu za'a daura dana zainab dana kaninsa muhammadu

wani kalar dariyar mahaukata mai karfi anty safeera tay kafin nan ta fashe da kuka abazata batace komi ba ta katse wayar cikin sauri

hajiya hamida tay kwafa tace hmm yanxu sai ace na hada waje kenan ko???hehehe toh Allah ya raba lafiya


****
wani irin haukataccen kuka anty safeera tay for a moment in shock, dan tasan dai hajya hamida bazata taɓa mata wasa ko karya ba...saida tay kukan sosai dan shock din ya fice ajikinta snn ta share hawayenta ta fita tana jan zuciya luckly enuf tana sharoro kwana kuwa taji muryansa a daki yana kan maganan auren da wani abokinsa ta labe a bakin kofa taji yana kyakyatwa da dariya harma maganan ma anko sukeyi na abokai..

lokcin wani hajijiya ne ya fara juyi da ita dan batamasan awani duniya take yawo ba dan tay kamar bata sama bata kasa bata tsakiyar kamr a iska kawai take yawo kirjinta yay nauyi kamar an daure dutsi a haukace ta shigo dakin tana huci suna hade ido yay maza ya katse wayar ya mike tsaye yace "lafya kuwa Safeera what is dis zaki shigomin babu sallama u cud run into my private conversations

ɓari gabaki daya jikinta ya farayi maqudaan hawayen datake kkrin dannewa suka watso mata a lokaci daya akan fuskarta suka sauko baja baja tana kallonsa kamar zata kasheshi the call has already confirmed everything to her

muryanta har yana amo tace "i cud run into ur private stupid cnvrsation ko kuma wani munafurcin kake kullawa abayan ido na bansani ba

adan rude yace meye hakane kam safeerah pls what is wrong with you ne

wani dan uban mari ta daka tsalle ta watsa masa da ihuu tace "you are what is wrong with me muhammad...how dare u..how dare u ...how dare u plan ur weding behind my back, dama sau yaushe ne zaka gaya min? bai gama farfadowa daga marin ba tay wuff ta cakumo wuyarsa a borance tace sai ranar auren ne zaka tozarni a bainar jama'a sann ka gayamim cewa zaka min kishiyya. what wrong ive i ever done to you da zaka saka min da irin wann walakancin

dakyar ya fincike hannunta da karfi ya riketa muryansa na rawa rawa guilt ya gama rufeshi dan yama rasa me zaice yafara bare bare yana cewa "safeera is not what u think...i was going to tell u bansan ya zan gaya miki bane
..you knw i love u..i care about how you will feel shiyasa ban gayamiki

kara fashewa da kula tay a mugun haukace tafara cewa "so, now you care abt how i will feel..amma da banji awani waje ba wallah da bazaki gaya min ba...kai durun uwarka, inka sake cewa you care about wallah saina kasheka, banza
..munafiki kawai,, wallh i dont deseve this frm you.., ranta a mugun bace ta fara kai masa duka tana cewa wallah baka isa kayi auren nan tunda ata hanyar munafrci zaka yi..u want to embrass me...inkaga kayi auren nan it will only mean i am dead. wallah wallh ka gwada kagani..

tana gama furta haka a zuciye ta juya zata fita wanda yasan bazai wuce gidansu zata tafi yay sauri ya biyota yaga ta kama hanyar waje kusan a guje yana kkrin jawota kukan ta saida ya ratse koina kowa ya fito a rikice ana lafya lafya...

atake jikin ammi karama yabata abunda yake faruwa tay sauri ta rikotata snn a sann ta zube ajikin ammin kusanma ba acikin hayyacinta ba sai kuka kawai take kamr zata cire ranta.

duk su ayaana suka fito saboda kuka ne me kara anty safeera takey bana kadan ba

hajy mairo tace ke kuma safeera meye haka mutuwa akayi miki ne, muhammdu waye ya mutu..badai jikana mujaheed bako? dan jiya munyi waya dashi yace zaixo bikin nan sati na gaba

da sauri kuma a rude uncle moh yace yawwa hajiya dama akan batun aurena ne taji shine take fushi batama tsaya munyi magana ba

da muryan tausayi tace ayyoh Allah sarki yo ke safira kiyi hakuri mana karki cutar da kanki da irin wann kukan
...karka kanki yazo yana miki ciwo auren nan ai na rufin asirin mu ne baki daya nida nace ma bazaki ce komi ba saidai kisaka albarka...yarinya ne kin riga kinsanta tun tana karama kusan ma agabanki ta girmaa yanzu fisabillah da aka kawo miki wata shegiya awaje ba gara da za'a hadaki da ayanahn ba kinga saiki riketa kmr yar cikinki...

wani irin kukan kura anty safeera tay tace ""waaaa?? ayaanahhh fa kikace hajiya..

in shock ta kalle unlce moh jikinta na kar kar tana vibrting da tsawa da ihu tace 'dama ayaanah zaka aura??...

yace safira calm down i was abt to...wani irin mari ta kai masa saida ya kusa kifewa,

kafin ammi karama ta rikota tay kan hajiya mairo da naushi tana ihu tana cewa" munafukar tsohuwa, azzaluma wallah sai namiki dan bura uban duka dan ni ba kalar wacce zaku walaknta bane...

adaskare ayaanah ta tsaya cak tana kallonsu ana tirka tirka sd anty safeera ta riga ta kai mata naushi tsohuwa saida ta fado akasa tana ihu uncle moh yaje da gudu yana kkrin dagata

jikin ayaana yafara rawa rawa ita da safiya suka kalle juna in shock

anty safeera tana ihu tana zage zage tana kawo naushi dakyar ammi karama ka janta sai cewa take wallah wallah inhar ayaana zaka aura saina kashe ka..baka isaka ka dawo dakin nan ba har lahira zan kai ka yau, dacan gidan ubana zanje amma tunda abun naku walakanci ne da cin fuska wallah ina nan daram sai na kashe ka, mugu kawai, munafuki daga kai har tsohuwar taka saina numa muku cewa haukata yafi taku.

ana tsaka da wannn rikicin bazata sukaji ayaanah tafadi kasa sumammiya..

da sauri ammi ta sake anty safeera tazo kan ayaanah tana girgizata ayaana ayaanah sai shiru aka fara salati

anty safeera taja wata arniyar tsaki ta haura sama ammi ta dauki ayanaa ahannu tace safiya yi sauri ko kawomin key muje asibiti .

uncle moh yay sauri yakai hajya dakin tana ta rabza kuka kmr dukantan akayi

yana fitowa yazo ya samu dede safiya ta kawo key kenan yafara kkrin kwacewa yana cewa bani keys din ni zan kaisu...

ammi karama batasan sanda ta mike jikinta na rawa ta daka masa wani irin hatsalallen tsawa ba...

ranta a mugun bace tace muhammad are u out of ur mind? wai baka ganin abunda ka jawo ne..kaje ka kashe wutar dake gabanka mana and for ur informatiom dont u ever come near this girl ya isheka haka.

hawayenta ya fara zuba tace "Dama ai abunda kuke so kenan, inbanda son zuciya ina ayanaa da zamowa matarka kaje kawai ka juya ma hajiya tunani..wallah Allah ya isa ma yarinyar nan, inba dai so kake ka cusa ma rayuwarta baqin ciki ba meye naka da auren yar cikinka kuma wanda ta taso agaban matarka wann ai baqin jini da tsana ka siya mata nide wallh karka sake kace zakazo kusa da ayaanah enuf is enuf

...tana ga firta mai hakan ta dauki ayaanah cak ta fice da ita tana kuka ta sata mota bata kira kowa ba saida ta isa asibiti

ayaanah went into nervous breakdown aka lankaya mata engine taya numfashi bata ko motsi..

ta kira layin ibaad baya shiga, ta kira bappa zaidu duk shiru har saida ta kira maheer ya dauka sann taji sanyi ahaka ma tanakan gaya masa tana kuka, hanklin sa sosai ya tashi dajin wann maganan, ya rasa yadda zaiyi yay, haka yaki gaya ma kulthum yay shiru atake atake yace mata zaizo gida akwai wani abu urgent da zaiyi.

he left malaysia by 10am bai iso kano na sai tara na dare, yazo ya samu ammi karama ce kawai anan asibiti sai safiya har ayaanahn tafarfado ta sake komawa she is still on sedatives nd oxygen

babu alamar shigar numbar bappa zaidu bare na ibaad kuma sam sam taki ta gaya ma hajiya asibitin datake bare suzo, anan tawuni batasan me ya gudana agidan ba.

saida maheer yazo kafin taji safiya tana bada labari cewa data koma yi musu abinci taga anty safeera ta dauko wuka tabiyo uncle moh har waje kan titi tatara masa makwabata, waihar ma yace zai saketa hajia ne tace masa a'a zafin kishi ne zata sauko.

case a gidan bai kare bahar washe gari ayaanah tana farfadowa in btwn amma daga zarar taga ba mafarki takeyi ba she will faint back...

gurmi yasaka ammi babba ta dawo gidan wai tazo danna kirji ma anty safeera amma inbanda kata hura mata wutan abun babu abunda takeyi dan agidan ma takwana komi anayi a idonta

a idon hajy mairo saita nuna hakuri kawai take bayarwa amma tana komawa sashen anty safeera sai ta cigaba da xugata sosai..ranar da abun ya faru uncle moh bai iya kwana a gidansa ba sabida tsoron ransa, kusan a hotel ya kwana shima acan alhaj ameer yazo ya karasa cire masa sauran tausayi da kunya yace masa ya share safeerah borin hauka kawai takeyi zatama yi ta gaji ta bari karda ya sake ya fasa auren nan sabida haukar kishi da matarsa safeera takeyi

BOOK 1 ZAI KARE NE A PAGE 50. PLS WANDA BASA IYA KARANTA BOOK DAGA FARKO KU daure KUNEMI PAGE ONE KU AJESHI KURKUSA DAN IN AZO CIGABAN LAST PAGE KUGANE INDA ZAMU DOSA COS I WILL HATE TO BE ANSWERING SILLY SILLY QUESTIONS IN THE FUTURE..💋❤️❤️👍 MORE LOVE!!
[16/12, 00:53] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫
arewabooks@surayyahm.


⏯️4️⃣9️⃣
Tunda Alhaj Ameer ya gama zugashi ya dada cusa masa ra'ayin cewa kar yasake borin kishin da haukar da safeera take ya hanashi auren ayaanah sai kuma ya dawo gidan da sassafe da wani gigin rashin kawaici da kunya na daban, babu tausayi ko fargaban kashesa datace zatayin kuma a idonsa cos he want to stamped his leg as a man tunda yay shige da fice ya samu hajiya mairo suka kara tattaunawa shikn kuma gidan ba a gane komi ba.

duk wani haukar da anty safeeran zatay basa amsawa ma bare su kulata saidai su hadu suyita nuna mata cewa itace taɓabbiya bata da hankali ne shiyasa bata fahimce cewa auren da zaiyi da ayaanan na rufin asirinsu duka bane, abu tun yana kamar wasa saida sukakusa saka anty safeera xarewa, gashi tay borin har dana fitan hankali duk saida makwabta sukaji ya xamo duk sanda hajiy mairo ta fito waje sai ka samu masu gulmanta kowa yana cewa basu kyautawa safeerah ba

kusan kwana biyu ayaana tay akwance agadon asibiti both friday nd sartuday anata jinyarta wanda tunda ta farka matsanancin kuka kawai takey tana cewa ita kawai zata tafi wajen ummanta bazata iya cigaba da zama ann dasu ba, dakyar Ammi karama da su maheer suka taru mata aka rarrasheta har tazo tasamu sauki da dare ranar asabar haka aka sallamosu suka dawo gida wanda suna dawowa hajiy mairo tabar sashenta tazo wai zata duba jikinta

suna hade ido ayaanah duk tabi ta birkice ma hjyan da ihu da kuka, tun tana gaya mata magana me zafi zafi tana cewa hjya damafa baki kaunata kin tsane ni, kin tsane farin cikina inbakiso na kawai ki maidani wajen ummana na mana ai ba'ace miki dole sai kin rikeni ba.

tay borin har ta gaji ta tsuguna da gwiwarta akasa jikinta na rawa rawa tana kuka tanata rokonta, har abun tausayi tana mata magiya akan karta mata auren dole batasonshi bazata iya aurensa ba

hajiy sai bata dau abun da wani zafi ba, ai dama tasan ayaana bazata so auren dole ba iskanci da kwadayin banza ta saka aranta she expected this xct reaction shiyasa ko ajikinta kukan ayaana da maganganunta bai dameta ba.. tace ai dama ba auren so zata mata ba, auren rufin asiri ne, inma karatun ne ai zata karasa agidan mijinta barema idan badan shi muhammadun ba waye ne zai aureta ya kula da ita sosai, ayaanah tana gabar hajiya mairo zatyi kudu

..kmr da wasa it becomes da begining of misery for them agidan, dan kuwa washe garin sunday ammi babba ta zuga anty safeera tammm tace mata ayaanan ma babban munafuka ce aisun dade suna soyyaya ne a boye shiyasa ya samu bakin cewa zai kara aure da ita, snn dan rainin wayo ma anayine agabanta all this gestures nd gift,sosai kuma anty safeera ta zugu data auna duk wasu prior bhvrs dinsa akan lamrin ayaanah, da safe anty safeera taxo sashen ammi karama tawuce dakinsu direct kawai akaga ta kama kkrin yin dambe da ayaanah zata bugeta, ihun da safiya tay ne yasa ammi taxo da gudu ta kwace ayaanan a hannun ta, anty safeera ta rufe ido ta borance ta zazzagesu tasss tace musu mugye makirai harsaida ammi kraman tamata karamar hauka tace mata karta sake zuwan sashen taje taji da wawan mijinta sann ta kyalesu.

tundaga ranar ciwon ayaana yake tashi akai akai is worst enuf da bata da number ko daya acikin abokan ibaad bare ta nemeshi anan, she called yasmin da sukay exchnging lay
tace mata ai dukansu me ma ba asamunsu a waya yanxu amma in no time zasu dawo hakan yasa ayaana ta cire kullum sai tay kuka.

yau kusan kwana uku babu kwanciyar hankli agidan gashi haryau babu duriyar ibaad din bare bappa zaidu gashi yazo maheer yay iya bakin kkrin sa amma inaa everyone is just selfish musmn hjy mairo farin cikin danta da kalamn rufin asirin kawai ta sako agaba

gani take wai gata take ma ayaanah daga baya kuma duk zasu gane

maheer yazo ma baya magana da hajiya mairon, duk shirinsa da uncle moh haka wann karon ko gaisuwa yazo baya hadasu, sumtims maheer din ne ma yake zama ya katse wasu makircin ammi babba

kansa sosai yay zafi yanata kkrin yaga ya dawo da anty safeeran cikin hayyacinta amma inaaa kusan zaman rikici da dar dar kawai akey agidan, uncle moh ya dena zuwa sashen ma kwata kwata saidai yaxo gidan da safe ya gaida uwarsa yasake fita kwata kwata yafara dauke kai memakon kaji yana fadin kalami masu dadi saidai ya fetsa maganan banza kuma sai cancikin dare yake dawowa yaxo yay bacci yama dena kula haukar safeera, ana shiga satin bikin on monday da safe maheer ya wuce malaysia....

da yamma ammi babba ta raka anty safeera sun dawo daga asibiti suka zo suka samu an jere mata akwatuna a dakin sunkai seti total of twelve boxes masu shegen tsada wai ankawo mata na fadan kishiya, haka tasaka aka kwaso kayan har waje tsakar gida ta debo kanazir ta cinna musu wuta gidan ya kara birkicewa koina ya cika da hayaki

dakyar aka kashe wutar duk anguwan saida hankli ya fara tashi, kafin ace uncle moh ya zo gidan anty safeera tama hajy mairo zagin tasss taci mata mutunci kmr bata santa ba har saida tasa hawan jininta ya kara tashi ruwa ruwa aka kaita dakinta can kafin aka samu sa'ida aka kashe wutar, da dare haka yazo yaga abunda safeera tay yayta bori har da rubuta mata saki su ammi babba da hajy mairon suka taro suka hanashi furta sakin da kyar mgnn nan yazo ya kare gida yay shiru..

cikin wnn daren ammi babba tazaunar da ita tafara analysing mata cewa mutanen nan bazasu rusuna ba snn kamar babu fa wani abunda zata musu su rusuna da batun auren nan saidai ma nata auren ya mutu a karshe

tunda ammi babba ta gaya mata wann mgn tay kukanta cikin dare taji sauki washe gari da safe tay wanka tabar gidan, har yamma bata dawo ba har sai can cikin dare, ta dawo kuma sai sukaga tay sanyi bata hauka bata bori she was soo sullen nd unpredictable snn koyaushe fuskarta a daure yakedan ko ammi babban ma bata gaya mata inda taje ba in zatay waya kumq bata sakewa wani yaji me take cewa..

a washe garin ranan tunda aka ga ta dawo daga inda taje ta dawo shiru shiru harma aka dauka tafara gajiya ne da haukar tafara rusuna zatay hakuri

tunda aka fara case din nan ranar friday ammi karama bata sake bari ayaanah ta fito koda kofar sashensu ba dan da kyar ta lallameta ta dawo hayyacinta suna zaunensu suna ibaada sallan dare da rokon Allah ya tarwatsa auren babu wanda yake sanin ya suke ciki dan ko wjen hajiya mairo bata zuwa ynx

maheer baida yadda ya iya tun kafin su fara shirin zuwa ya zaunar da kulthum ya gaya mata gaskiy cewa babanta fa yace zai aure ayaanah sai tay kmr ta fahimce auren dole ne, saidai daga baya tana kiran anty safeera sai kuma komi ya lalace, anty safiran tashiga gaya mata karya da gaskiya tace bawani auren dole makirci ne kawai kuma da sannin ayaana za'ayi auren nan. dat night kulthum send ayaanah a very very insultive text message har ta zagi iyayenta aciki

ayaana tay kuka bana kadan ba gashi sultana taje schll field trip kaduna batama san meke faruwa ba, duk sai ta kasa kirarta awayan itama danji take kmr zasu hade mata kai su tsaneta yanxu.

daga dakinsu sai dakin ammi bata iya zuwa koina kuma haryau bata sake ganin idon uncle moh daya riga ya lalata mata rayuwarta ba, safiya ne dai take fita taje jin gulma, ita kuwa ammi babba tunda taga anty safeera tafara dauke kai babu halin kara zugata tay hauka sai tafara bin makwabta tana barbaza maganan dan akwai taga ana zagin hajy mairo da ammi karama taji dadi, dan babu kalar sharrin da batayi musu a gari dan kawai ta bata musu suna..

daga ta gaya ma wnn sai ta gaya ma wancan,haka wasu dattijan mata kuwa

82 / 88