Author : NONE Category : African Stories & Novels
fargaba aranta dantun bayan maganan aurenta basuyi waya ba kuma itama sultanan jiya da dare akace sun dawo daga field trip sai taga bata nemeta ba..
har takai bakin kofar sai kuma tsoron kalar fassarar da sultanan zata mata yasa tay reverse tay sauri tabar sashen ta nufi dakinsa datasan baya kullewa ta bude ahankli tashiga ciki
kimonon tafara cirewa ta aje akan gyararren gadonsa tashiga bayi da sauri ta kara kunna haske ta dudduba jikinta sosai taga ashe she is absolutely fine din snn ta kara sauke ajiyan zuciya...
ruwa ta watsa a kanta da fuskarta sosai har saida taji sanyi kafin tay tsarki ta doro alwala tazo tafara sallahn magrib tana idarwa ta dau wayarta ta kara gwada lambar ammi karama a ringing na biyu ammi ta dauka ta rasa me zata fara gaya ma ammi at first, anan ne ammin take gaya mata ai ibaad ma ya riga ya kirata tun yana hanyar shigowa gari kuma yace mata suna tare shi zai kawota gida anjima itama wani kauye suka shiga dazu da kawar hajya mairo shiyasa bata dawo gida da wuri ba., ayaanah was abit relieve tunda taji cewa ammi tasan inda take ynxu..hanklinta a dan kwance tay su ishai wanda batajima da idarwa ba saiganan ibaad din ya shigo suna hade ido da mmki yace mata meyasa bataje wajen sultanan ba...
tasowa tay daga kan sallahyan tazo inda yake jikinta a sanyaye
yanayinta yagani yace "what is wrong? bata amsa ba yace "zauna to mana muyi magana
meyasa zaki rubuta min texts cewa inbandawo ba zaki koma wajen ummanki what is wrong with you???da dan wasa a muryansa yace anmiki wani abu a gidan da bana nan?
yana gama furta hakan
taji zafin abun na dawo mata kai ita kanta bata san sanda ta fashe masa da kuka ba...
atake ya hade ransa tare da jawota suka zauna abakim gado sai yaga jikinta na rawa rawa ta sunkuyar dakanta can can kasa sosai ta lumshe ido tana kukan sosai.
hanklinsa atake ya fara tashi yace "kee wai meye hakane zaki sani agaba kinamin kuka did anyone hurt you..da sauri ta gyada masa kai yace and who is that? dede nan ta bude idonta ta kallesa muryanta na rawa tace "yaa, kana tafiya ranar haka kawai hajiya tazo tace wai aure zatamin kuma
..kuma..dede nan ta kara fashewa da matsanancin kuka saida ya riketa, da tsananin rudano d fushi a muryanta tace "waifa aure zatamin da uncle muhammad.. bai jira next word inta ba yace "whaaaaat?...ke karkiy wasa dani kinaji ko..kara sautin kukan tay tace "wallah bawasa nake maka ba yaa. nan ta fara bashi labarin duk abunda ya faru bata rage masa komi ba tun yana zaune har ya miƙe tsaye atake take taga idanunsa sunyi jaaa sosai....gashi kuka take masa sosai tana cewa yaa Wallah bazan iya aurensa ba,dan Allah karki bari hakan ya faru inkuma bari zakayi ni gara na tafi wajen ummana nasan bazata tabamin auren dole ba, kuma na gaya ma hajiya banaso banasonshi but she refuse to listen to me..if not becos banason kaji haushina da na gudu tuntuni nide wallah bazan aureshi ba..
jin yadda take maganan da tashin hankli da kuka mai zafi yasa yay sauri ya dawo gefenta ya jawota jikinsa da sigar lallashi, idonsa ya mugun tara ruwa ahnkli yana shafa bayanta muryansa harna cracking like he is utterly disgusted nd angry cikin dauriya yake cewa its okay babyna ya isa haka kidena kuka 'i won't let that happen okay? kanta kamar zai fashe ta shige jikinsa tareda lara kankamesa kamr wacce zaa kwace matashi, kusan ba acikin hayyacinta ba take cewa" i can't take it. ni bazan dauki wnn qaddarar ba..i dont want to...baisan sanda zzfr hawayensa ya gangaro kasa yana sauka a fuskarsa ba maganganun ta gabaki daya suke dawo masa kai yanajin wani irin zafi kamr ana tafasa masa tsokar zuciyarsa da ruwan dalma, dakyar yay contolling angernsa can har saida ya shanye hawayen ya share snn ya tallabo fuskarta suna kallon juna ahankli yace "hey..trust me no one will take you away frm me, i promise i wll fight, if not for myself but for you kinji???
gyada masa kai tay ya jawota jikinsa ya rungumeta kadan har saida ta nitsu snn yace "can u give me a minute?? ganin yayanayin da jikinsa yake rawa rawa ahnkli yasa tace okay snn ta mike tsaye ta dauki veil din kimononta ta wuce dakin sultanan dataki
zuwan dazu.
tsabar kukan datay gabaki daya idanunta ya kumbura tay kncking ahankli after like 3 min
sultana ta bude suna hade ido ta sauke waya a kunnenta da mamaki tace "ayaanah? da sanyin murya da fargaba ayaana tace can i come in?? tace sure sure nan ta jawota ciki tana dada kare mata kallo hankli tashe tace what is wrong with u ya naga idonki yay jaa haka are u okay sis??
hawaye masu sanyi suka fara sauka a idon ayaanah suna zama abakin gadon tace how can i ever be okay sultana
...havent u heard..cikin katseta sultana tace "i did...and i wont judge you ayaanah, sabida iyakan zamana dake i know u cant do this..da muryan kuka tace"thank you sultana..wallah ina cikin tashin hanklin da ku kanku bakusan yawanshi ba..i feel like everyone hates me
ta dauki wayar tace"kiga text din da kulthum ta tura min fa..bamtaba tsammanin zatay tunanin wai inaso na aure babanta ba..kuma har tana zagin tarbiyan da iyayena sukamin?
hawaye ya ciko idon sultana tace 'kinga ayaanah tun ina camp muke magana da ita nina katse maganan nace saina dawo yanxu haka ma da ita muke waya kuma niyyata muna gamawa zan kiraki kema. u guys shud schill, we are sisterrs fa. we shudnt betray or mistrust each oda haka...ayaanah tace amma fa na dole aka lakamin maganan nan sultana, so how is this even a betrayal? i am feeling like i cant breath anymore i am all tied up...da tausayi sultana ta rike mata hannu tace ayana kulthum ko anty safera duk bazasu fahimceki yanxu ba, akwai zafi akwai kishi akwai zargi but despite all this akwai qaddara..in Allah yace uncle moh shine mijinki duk ya zamuyi
ayaana tana kuka ta kwace hannunta ta miƙe tsaye tace sultana this has nothing to do with qaddara..ba a forcing in qaddare akan mutum, wllh dashi da hajiya dukansu they are forcing this marriage on me bawani qaddara..kuma ina da wanda nakeso sultana, is bad enuf that i cant have him now, amma harga Allah bazan iya auren uncle moh ba, dan dana auresa gara kawai na mutu ko wani abu ya sameni
...jikin sultana a sanyaye ta biyo ta tsaye itama tana hawaye tace"haba ayaanah haba ayaanah pls stop saying things kamr bakida ilimin addini pls dont even think of doing to urself what anty zainab did akan yaa ibaad to trap him into marriage dan kece zakiy asarar rayuwarki duniya da lahira so pls stop it
tace sultana is not abt what choose is abt how i feel i am truly nd deeply in love with sumone else kuma narasa yadda zanyi..sultana tace nd did he know zakiy auren? a sanyaye ayaana ta gyada mata kai, suna tsaka da hakan ibaad yabude kofar yanayin yadda ya kalle ayaanah yasaka sultana tuni tagane inda ayanah ta dosa..
sounding confuse tace yaa.. ibaad..good evening ya ibaad
...adan tsime yace 'how are u doing? ahnkli tace fine yaa. ya kalle ayaanah yace "are u done?
tana share hawaye tace uhmm i will be with u in a minute
..yana sake kofar yace be fast..
...da sauri tashiga bayi ta wanke fuskarta tafito sultana ta rakota bakin kofa tariko hannunta tace ayanaa i think i might knw who ure in love with
..ayana tace ohh pls forget it kawai innaje gida zamuyi video call...
daga haka suka rabu ta tabishi a mota dats filled with hrt breaking silent..time to time yana murza hannumta cikin nashi in a comforting way ita kuma ta sunkuyar dakanta kasa sosai tama hawaye mai sanyi tana imagining ya rayuwarta zai kasance idan babushi aciki
suna kaiwa gidan saikuwa ga uncle moh a kofa shima ya zo da babban abokinsa alhaj ameer sun gama gaida hajiya mairo kenan zai rakasa, tana ganin su harzata ki sauka a motar ibaad ya hade ransa yafito ya bude mata kofa yana kallonta yace baby muje ciki
..jikinta a sanyaye ta sauke kafarta kasa tana daga ido taga ya miƙa mata hannunsa ahnkli ta kama hannunsan har tafito ta tsaya agefensa snn ya kulle motar,hannunsu sarkafe da juna suka fara tahowa gata da bala'in iya shige masa wani irin daf daf dashi take kmr zata koma cikinsa.
suna tahowa tundaga kofa Su uncle moh din suka zuba musu ido kamar wanda zasu hadiyesu da kallo, ayaanah ta kasa daga idonta, gashi fuskar ibaad babu sauki he is wearing one all black hoodie na puma yadaura hular hoodien akan bakin facecap da white medicated glass a idonsa daya toshe dashi daga ganinsa kao kasan ba weathern mutunci yazo gidan dashi ba..
shida abokinsa suka kalle juna alhaj ameer din ya masa wani irin kallo da yay sake...
wani irin shiru harabar gidan yay su ibaad suna daf zasu kai kofa uncle moh ya kasa hakuri da karfi da kuma izza da iko a muryansa yace' "ke ayaanah kizo nan...
maimakon yaga ta juyo saiyaga ta kara tantame hannun ibaad din sosai tay kamar batajishi suka cigaba da tafiyarsu ahankli har suka shiga ciki.
da wani irin huci ya taso zai biyosu ciki alhaj ameer yace kai da Allah kyaleta, inka bisu yanxu sai ya gasa maka baqar magana. yaran ne akwaisu da rashin kunya amma kwana nawa nema ya rage ta dawo naka..u will have all the time in the world to deal with her dan ya kamata ka gyara mata zama ta dena bibiyar maza
rai abace uncle moh yace ai ba ita kadai bama harda wancan marar kunyar yaron kaga yadda ya wuce kamar ba mutane yagani ba
alhaj ameer yace jst let it go muje kawai kai meye naka na fushi ma in 2 days time fa zaka more wahalarka ajikintq saura kuma ka karka bita ahnkli dan naga yarinya ce danya shataf ...
dariya sukay uncle moh yace ai banaji ranar akwai bacci kaima check out mana how did u see her..najima ban taba fresh nonon budurwa ba
suka kara fashewa da dariya alhaj ameer yace ai sabuwar mota ce zaka jima kana morarta kuwa ..
yace hmm toh i hope so..dan naga kanta na rawa sosai
Allah yasa in sameta a mace dan wallh inbansameta a mace ba washe gari zan saketa dan ban isa inci raguwar wani kato ba..
daga haka suka shiga mota suka fita joint insu banda hirar batsa da first nite babu abinda sukeyi...
fannin su ibaad kuwa suna shiga cikin gidan ya tura ayaanah tawuce sashen ammi karama after giving her a wa comforting hug to calm her down
yana kallo saida har ta shiga snn ya juyo kai tsaye ya wuce sashen hajiya mairo kasar wuyarsa yay mata sallama ya sameta tabaza tsokokin gasashen kaji da alhaj ameer ya kawo mata a plate ita daya tana kan ci tana jan santi
...yanayin yadda taga ya karaso ciki fuskrsa a mugun daure saida yasa taji gabanta ya mugun faduwa yana kawowa gabanta daga tsaye yasaka booth dinsa ya wani irin ture plate din gabantan gefe da wani nauin rashin mutunci akwayar idonsa saida duka abunda ke ciki ya zube
ransa mugun harde yace "hajy wai me nakeji batun wai zaki ma ayanah auren dole agidan nan?who ask u to make dat decision..
a take idonta ya ciko da ruwa daga zaunen ta kallesa tace shine zaka wani shigo min kamar..
cikin runtse idonsa da budewa yace "Don't joke with me ni bazuwa nayi muyi musanyr yawu ba...yadda kika kulla wann shashancin haka zaki warware kona miki abunda zai dameki agidan nan...
jikinta har na rawa ta mike tsaye da masifa tana cewa aa kai fa ba ubana bane rayyanu akan me bazan ma yarinya aure ba tadau hanyar lalacewa kuma ai akwai hannunka aciki
"..cikin daka mata tsawar dayasa ta razana yace sai akace kimata auren dole? ke kika haifeta ne da zaki yanke mata wann hukuncin wazatay rayuwa dashi ke waya miki haka ko tsabar zalunci da son zuciya kike son kara nunawa duniya wanda kowa yasan kin jima kina da shi..i am sure he just selfishly asked and obliged...sabida gaki katuwar pushover ko?bakisan abunda ya dace wanda bai dace ba komi da zaibi ta kan favourn yaranki shine kawai zakiyi toh wallah wallah wann karon kam baki isa ba. i am warning you for the last time to call this weding off this night..
a mugun rude ta saka masa ihu wayyo Allah na rayyanu zai min duka muhammad muhammadu wayoo Allah kuzo ku ceceni
tana kan ihu ya jawo hannunta da karfin bacin ran dake ci a idonsa yace ki kira kowaye yazo nan ina daidai daku, kuma wallah daureki zanyi saikije can prison kigaya musu uban waye ya baki ryt kima yarinyan nan auren dole da sokon danki wanda baisan ya girma ma kuma tunda kince ke zalunci zakiyi daga ke har shidin saina daureku wallh
yana sake mata hannun ya saka kai ya fita baiko je sashen mamansa ba saboda ransa sosai yake bace, cos bayan ayaana ta fita a dakinsa dazu he called maheer on phone babu wani abunda maheer bai sanar dashi ba.
har yakai motarsa yana jin ihun hajiya mairo bai sake sanin meya faru ba ya ja motarsa ya wuce gida.
ko 2 min da fita baiy ba ihunta yasa aka cika akanta hawaye sharbe sharbe na zuba a idonta tana ihun radadi tana cewa wayyo hannu na wayyo hannu na fatima danki yace zai kasheni,zaikaini prusona wayyo hannuna wayyooo
....kusan ba acikin hayyacinta take ihun ba duk ta razana ta gigice
ammi karama tana duba hannun kuwa taga har ya langwashe da sauri sauri ta dagata suka dunguma har dasu ayaanah aka kaita asbiti acikin daren..
ihun azaba kawai hajy take tana raki ana dubawa aka samu karyewa ashe wajen daya riken yayi.
gabaki daya hajy mairo ta dawo abar tausayi radadi yabi ya sa tafice a hayyacinta
aka kira likitan kashi
maza maza akay ciki da ita, sauran kaza da akay fero dashi safiya ta makalo suna zaune tanaci suna jiyo ihun hajy mairo aciki bataji sauki ba kuwa har saida aka mata alluran bacci bayan angama daure mata hannu
uncle moh bai dawo gidan ba ammi karama kuma bata masa magana bare ta kirasa suka dai suka kwana a asibitin duk basu samu daman magana da ibaad ba dan yana isa gida ya kashe wayarsa
washe gari friday da sassafe aka tashi da hargitsatsen case uncle moh yana jin labarin an karya masa hanuun uwarsa yazo har yana wani fuffuka wai zai je ya dake ibaad babu wanda ya kulashi
still hajy mairon ne ta hanashi dan tunda ta farfado take kuka tace masa wallh shegen karfi rayyanu yake dashi daya rike mata hannu ma ji tay kamar hannun baya jikinta karyaje aje a kashe shi ana gobe daurin aurensa kawai ya bari ai zaidu zai dawo bayan auren zasu taru suci uban rayyanu..
wuni yay yana kumburi ammi karama data fishi tsiya ko abinci bata saka safiya ta kawo a asabitin ba, goma nayi na safiya haka ta tattara yaranta suka barsa da uwarsa anan.
gobe auren anata shiri kasa kasa, wasu suna ta mamakin yadda anty safeera tay burus tay sanyi kamar ma bata gidan, da yamma liss tay girki takai ma hajy mairo ta samesu su biyu a asbitin kamr mayu
...duk sun sha mamaki da suka ganta tace oo oo ita abinci ta kawo musu..cikin gasa musu baqar magana ta dinga cewa duk dama an tozartata bashi zai hana ta manta dutynta na matar gida ba. dacan suna dar dar kamr bazasu ci abincin ba har saida sukaga dagske ta deba a plate taci snn suma sukaci borin kunya yasaka bai iya zama ba da yamma lis ya bar anty safeera da hajy asibiti snn shi ya wuce wajen aboknsa sabida babban hotel suka kama anan zasu kwana su shiryawa gobe daurin aure gashi as early as 11:am aka saka time...
daga fannin ayaana kuwa tunda suka dawo gidan bata samu ibaad a waya ba, later later sai sukyi waya sultana
wanda sai yaune sukayi hira me tsayin da har tagaya mata cewa tanason ibaad sosai kuma tana ganin kmr shima yanasonta nd they have planed thier future life together.
bakaramin tausayinta sultana taji ba, ace wanda kakeso zai aure wata kai kuma zaa bada ka ma wani..
sanyaya mata zuciya sultana ta dingay da kalamai na ban hakuri har ta gaggaya ma ayaanam rules nd regulations din da akasa masa akan batun aurensa da zainab arifa da irin severity na ciwon brain datake dashi akansa, tana cewa ai shima bada son ransa zai aure zainab din ba dan haka kawai suyi hakuri da qaddarar da Allah ya zabar musu...
shiru ayaana tay har ta gama jinta tana share hawayenta acikin ranta tace muddin kuwa auren nan zaiyu gobe toh babu abunda zai hanata guduwa kuma bazata dawo ba har sai an warwareshi....
idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata
*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*
*WATTAPAD @SURAYYAHMS*
*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*
#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025
[16/12, 23:01] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫
arewabooks@surayyahm.
Book1
⏯️5️⃣0️⃣FINAL PAGE
tunda suka gama waya da sultana ayaana ta koma bakin gado ta rafka wani uban tagumi dan kwata kwata kalman qaddara ko hakuri akan lamarin rabuwarta da ibaad baya sanyaya mata zuciyarta ko kadan
ana gobe da safe daurin aurenta for the first time ranar daya kamata ace tafi kowa zumudin gani saidai tamkar mutuwar ta haka takejin fargaban tunkararsa, she stayed up very late har wajajen 2pm nadare tana xaune tana tunani, saican data juya taga safiya har tay wani lalle dasu kitso na shagalin bikin yayanta kyabe baki tay sai taji kishi gabaki daya ya dawo mata sabuwa..
mikewa tay da sanyin jiki ta fara tattara iya kayan da zata gudun dashi adan karamin jaka within few min ta gama, da tunanin gobe zata gaya ma ibaad inda zataje inyaso inyay auren nasa saiyana zuwa inda take dan suna haduwa, harsai sun samu mafita dan tasan inhar yana sonta sosai bazai hanata kubutar da kanta gobe daga wann mummunan qaddarar